Showing 15001 words to 18000 words out of 62823 words

Chapter 6 - UKUBAR KISHIYATA Sirrin Da Ya Rushe Aure by Ummee Yusuf

29 Jul 2026

33

mata amma ba kada maraba da gauro.

Ameera sai juyi take tana murmushi ita kad'ai ta kasa bacci sai wani nishad'i take a ranta tana mamakin dama haka so yake?da k'yar ta samu bacci ya d'auke .

After 2 days Alhaji Mudassir ya samu duk wani information da yake son ya samu akan Ameera kuma ya gamsu sosa dan haka ba b'ata lokaci ya k'ira Al'ameen yace ya sanar da ita zasu je gidansu gobe da yamma.


Cikin tsananin farinciki ya k'ira ta a lokacin suna d'aki ita da Fateema tana tayata drawing d'in heart da aka basu assignment a makaranta.

Murmushine ya sub'uce mata ganin kiran hrt beat d'inta dan yanzu ta sake dashi suna shan hiran su yanda ya kamata amma fa a waya.

D'agawa tayi tare da sallama,amsawa yayi cikke da nishad'i dan ji yake kaman har an d'aura auren.

"Guess wat"

" i'm not gud at guessing just fad'a min nima in taya ka farinciki da alama abin farinciki ne ya samu" ta bashi amsa.

"Hakane kince u re nit gud at guessing but gashi kuwa har kinyi".

"Hmmmm ta muryarka na gane kana cikin nishad'i yau".

"Ba kad'an ba kuwa ki sanar da Abba gobe Alhajina zasu zo gidanku".

Sassauta murya ya k'arayi yace sunga na fara zaucewa akanki shi zasu taimaka su kawo min ke dan kar in ida zauc......".

Katse wayar tayi tana murmushi dan wani lokacin kunya yake bata.

Zungure ta Fateema tayi ta juyo da sauri suka sa dariya.

" kin fad'a dayawa sis " Fatema tace tana dariya.

" Fateema kenan ba zaki gane ba a yanzu har sai kema Allah ya had'aki da real love d'inki,kinga yanzu je ki fad'awa Umma yace gobe Alhajin shi zasu zo wajan Abba".

Cikin tsananin murna Fateema ta rungumeta sannan.ta sake ta ta fita da.gudu zuwa tsakar gida tana kiran Umma.

Fitowa Umma tayi daga d'aki har tana tuntub'e saboda rud'ewa.

Clashing tayi da Fateema tana washe baki,cikin fad'a Umma ta fara mata fad'a.

Hak'uri ta bata tare da fad'a mata sakon Al'ameen.

" Allah sarki ameera ita kunya ya hanata fad'a sai ke ko uwar rawan kai".

Komawa tayi daki tana dariya.

Alhaji sun cika alkawari sun zo neman auren d'an autan shi tare da jama'rshi.

Sun samu tarba mai k'yau wajan mallam Yawale da mutanen shi.nan akasa sa ranan aure 3weeks kacal bisa umarnin Al'ameen.

Mallam Yawale yaso a k'ara mishi lokaci saboda yanayin rayuwa amma Alhaji mudassir yace su basa bukatan komai daga gare shi dan su .ata suka nema kuma an basu shikenan.

Nan taro ya watse kowa cike da farinciki more especially Al'ameen da yake jk kaman ya zuba ruwa a k'asa ya sha.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€

*~UKUBAR KISHIYATA~*

😭😭😭😭😭😭


( its all about love and betrayal)


Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«πŸ’«~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

*~part fourteen~*



Lateefa tana can tana budurinta hankali k'wance bata san wainar da ake toyawa ba dan ko kad'an Al'ameen bai nuna mata wata alama ba.

Ana saura 2weeks biki,aka kawo kayan lefe na gani na fad'a.akwati set 2 masu k'yau da tsada kuma fad'an kayan cikin b'ata lokaci ne.

'Yan uwan Abba da Umma abin ya basu mamaki dan basu tab'a ganin lefe haka ba.

A wannan lokacin kuma wani irin soyayya da shak'uwace ta shiga tsakanin Ameera da Al'ameen dan kullum sai yazo da safe ya ganta before ya wuce office,haka ma da yamma sai yazo sun sha hiransu sannan zai wuce gida.

At night ma suna manne a waya sai sun kusan raba dare suna yi sai dai in Lateefa ta shigo ne ba zasuyi ba.

Ana saura 1 week biki Al'ameen ya har ya gama gyara gida duk da gidan da k'yansa amma hakan bai hana shi yiba more especially part d'in amarya yafi ko ina shan gyara.

Tun ana saura 2 weeks musamman yayi ordern kayan funutres daga italy kayan kitchen kuma daga dubai.

Ameera amarya itama tasha gyara ciki da waje dan kullum Umma cikin yi mata d'ure-d'ure take.

'Yar gwaggonta basira kuma itace ta d'auki nauyin gyaran fata da kamshin jiki,cikin lokaci kad'an ta canza fatanta yayi wani irin k'yau abinka da farin fata har wani shek'i taje ga kamshi da jikinta yake na musamman.

Duk irin gyaran da ake a gidanta Lateefa bata kawo komai a ranta ba saboda tasan abinda ta taka.

Ana saura 1 week kayan da Al'ameen yayi oder suka iso.

Lateefa da k'annenta suna zaune a palour suna hira suka ga aka fara shigowa da kaya nik'i-nik'i.

Cikin tashin hankali Fa'iza tace " Aunty wai meye yake faruwa ne naga anata shigowa da kaya ?"

Shamsiya tayi carab tace " ko dai Ya Al'ameen ne zaiyi aure?"

Zabura Lateefa tayi daga kishingid'en da take tare da yayimo wata uwar ashar ta d'ura sannan tace " ke daina irin wannan maganan a cikin gidan nan,yama isa yace zaiyi aure a gidan nan".

Fa'iza ta girgiza kai tace " Aunty maganan Shamsiya fa abin dubawa ne,ki tuna how many days akayi ana gyara a gidan nan ga kuma kayan da yanzu ake shigowa dasu ma sun isa shaida".

Jiki a sanyaye take binsu da kallo can tace " amma fa kunsa jikina yayi sanyi but bari ya dawo ya same ni,wallahi in dai da gaske auren zaiyi wallahi Allah ya d'ebo ruwan dafa kanshi.

nan fa suka rinka masifa ita da k'annenta kaman zasu ari baki.

5pm dai dai Al'ameen ya dawo gida bayan ya biya wajan Ameeransa suka sha hiransu,dan haka ran shi fari kal ya shigo gidan rik'e da brief case d'inshi.

Sallama yayi ya shigo su Fa'iza ne kad'ai suka amsa sallaman banda Latifa da sai cika take tana batsewa ga wata uwar harara da take wurga mishi.

Ko kulata baiyi ba ya wuce up stairs abinshi.

Da saurinta ta tashi tabi shi part d'inshi.

Jikinta har rawa yake saboda tsabar masufa da yake cinta.

Banko k'ofanta tayi da karfin gaske wanda har yasa shi d'an razana.

A fusace yace " meye hakane Lateefa,wani irin rashin hankali ne wannan?"

" eh lalle Al'ameen dole kace banida hankali,meye nufinka na gyara wancan part d'in harda canza kayan da suke ciki?" tace tana huci.

" aure zanyi " yace a takaice a lokacin da ya nufi hanyan bathroom.

Da gudu Lateefa tasha gaban shi " what did u jst saida,aure or wat?"

" eh ko haramun ne?" ya jeho mata tambaya yanakallon cikin idonta.

K'walan shi taci a masifance tace " wallahi baka isa ba ni kake gayawa zakayi aure?

Fizge hannunta yayi daga jikin rigan shi ya shige bathroom ya barta a tsaye sai huci take kaman maciji.

Da gudu ta fito tayi part d'inta wayanta ta d'auka ta fara dialing number Aina'u.

Ringing 2kawai yayi Aina'u tayi recieving tana " Hajiya ya akayi ne?"

" Aina'u ba lafiya"tace murya na rawa.

" Subhanallah meya far najiki haka?"

"Komai ya warware Aina'u wai yau ni Al'ameen yake cewa zaiyi aure?"

A kid'ime Aina'u tace " uban shima yayi kad'an,shi Al'ameen d'in ne har ya bud'i ya gaya miki zaiyi aure?"

"duk yanda za'ayi gobe kizo muje wajan boka dan insan halin da nake ciki.dan Allah kizo da wuri Aina'u kinji?"tace cikin marairaicewa.

Cikin rarrashi Aina'u tace " karki damu besty zan zo da wuri ai bamu gata zama ba dole mu koma ki k'wantar da hankalinki kema ai kin san aikin boka kaman kaifin wuk'a yake".

Sai alokacin ta samu sauk'e wani ajiyan zuciya dan ta san tabbas aikin boka ba wasa nan tace " shikenan sai kin zo goben".


10am a gidan Lateefa yayiwa Aina'u.

Lateefa dama tun 8 ta gama shiryawa ta zauna jiran Aina'u yau ba baccin safe.

Ba b'ata lokaci suka kama hanya zuwa wajan boka.

Suna isowa wajan boka tun kamin suyi mishi bayani ya daka musu tsawa yace " auren nan ba makawa sai anyi shi,sai dai zan taimaka miki ya zamti ta zama hoto a gidan balle ta kai gahaihuwa da kike tsoro.karki damu ki k'wantar da hankalinki in anyi auran da wata 1 sai ki dawo komai zai tafi dai-dai kaman yanda kike buk'ata".

Zuciyar Lateefa ta d'anyi sanyi akan bayanan boka,sai dai bata so ace anyi auren ba amma Aina'u tayi warning d'inta tun farko akan cewa ba 'yi mishi musu dan haka ta tsuke bakinta tayi shiru badan taso ba.

Kud'i suka kawo mai yawa suka bashi tare da yi mishi sallama suka fita.

Akan hanyarsu ta dawowa Lateefa tace " Aina'u inba dan kin hanani yiwa bokan nan musu ba,gaskiya banso ayi auren nan ba.saboda a ganina in an d'aura komai zai iya faruwa".


" besty some time ki n cika surutu,ki hak'ura mana tunda yace komai zai tafi dai-dai kaman yanda kik so.kinsan akwai wata k'awar k'wata datavtab'a yiwa boka musu,,hmmmm kinga abinda ya same ta?"

A d'an tsorace Lateefa ta juyo ta tambaya " meya same ta besty?"

"Hmmm wallahi sai data zama kare ya fita daraja,ta zama abin k'tama cikin mutane.ke in short uwarta ma saida ta guje ta saboda wasu kuraje da suka fito mata duk jikinta ga wani da take,hankalunta ma saida ya zama ba dai-dai ba".

Wani irin yawu Lateefa ta had'iye tare da cewa " kice nayi babban sa'a".

" offcourse yes sai ki kiyaye sosai".

A haka suka iso gida,Aina'u itama ta wuce gidansu bayan Lateefa tayi mata sha tara na arziki kaman yanda ta saba.

Yau saturday kuma a yaune duban jama 'a suka shaida d'aurin auren Al'ameen da amaryan shi Ameera .

Toh koya zaman nasu zai kasance?
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€


*~UKUBAR KISHIYATA~*

😭😭😭😭😭😭


(Its all about love and betrayal)


Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)



*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«πŸ’«~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen xBe hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*


*~part fifteen ~*

Al'ameen bakin shi yaki rufuwa saboda farinciki,yanda yake rawan kai sai ka zaci auren na farko ne wannan.

Bangaren amarya ameera ma hakan take tana can cikin 'yan tsiraru frnds d'inta na makaranta sai cousin sisters d'inta da suka zazzo sai shewa ke tashi a d'akin da suke taro.


Lateefa kuwa tunda suka dawo daga wajan boka hankalinta ya gaza k'wanciya,more especially yau.dan tunda ta tashi gabanta yake ta fad'uwa saboda haka take kunshe a can cikin bedroom d'inta ko palour ta kasa fitowa.

Amarya tasha nasihohi daga wajan Ummanta da Abbanta kan zamanta kewar aure tsakanin ta da mijinta da abokiyar zamanta,sai kuka take kaman ranta ya fita.

Da aka zo fita da ita da k'yar aka b'anb'areta daga jikin Fateema aka sata a mota.nan abokanen ango suke sanar da 'yan matan akwai dinner da za'ayi before akai amarya gidanta.

Nan 'yan mata suka hau shiri ciikin farinciki.

Ameera sai kuka take a cikin mota ji take a cikin ranta zata ta hak'ura da auren,ta koma ga Ummanta.

Ido kawai ya zuba mata yana kallon yanda take kukan kuma ga dukkan alamu bata san yana cikin motan ba.

Hannu ya kai ya kamo hannunta na dama,a firgice ta juyo ganin angonta ne yasa ta k'ara sautin kukanta.

Jawo ta yayi ya rungume yana sauk'e ajiyar heart saboda kullum suka had'u ba k'aramin yaki da zuciyar shi yake wajan kar ya tab'ata ba.

Mutsu mutsu ta fara nason k'wace kanta amma ta kasa.

D'ago kai tayi suka had'a ido ko wannensu ido ya canza yayi jawur dashi Ameera nata na kukan da tasha ne Al'ameen kuma na tsaban fitina ce.

Kallon d'an k'aramin lips d'inta da yake bala'in k'wad'ayi yake,ganin tak'i barin kukan yasa ya had'e bakinsu ya kama tsotsa kaman ya cire su.

Motance ta tsaya a bakin wani lafiyayen beauty saloon amma Al'ameen gaba daya baisan ma inda suke ba har ya fara fita hayyacin shi.

Gyaran murya da bilal abokin shi yayi shi ya dawo dashi hayyacin shi ya tuna ashe fa a mota suke kuma basu kad'ai bane.

Da k'yar ya sake ta yana maida numfashi tare da zuba mata ido yana murmushi,wasu special feelings yake ji akan yariyan nan shi kan shi bai san adadin son da yake mata ba.

Ameera kuwa wannan abinda ya faru tsakanin su yasa wani irin kunyar shi ta gama rufeta sai sunne kai take tana blushing dan tunda take hakan bai tab'a faruwa da ita ba.

Leken fuskanta yake yana murmushi yace " woah my prety bride ashe dama kukan bana gaske bane na in........ ko?

Bata san lokacin da ta zaro ido waje tana kallon shi jin wannan sharrin da ya mata.

Dariya Al'ameen ya k'yalk'yale dashi tare da hure mata ido yace " haba mana prety ko irin kunyan nan na amare babu kika tsare ango da ido haka?"

Rasa abinyi tayi ganin kome tayi sai ya musu negetive fassara.

Shi kuma he was enjoying every part of the time they spend together but na yau is diffrent ji yake kaman su dawwama haka just d 2 of them.

Gyara mata lullubi yayi shima ya gyara rigan shi sannan ya bud'e motan suka fito zuwa cikin saloon d'in.

Nan ya barta bayan yayi musu bayanin to do there very best amarya ce,sannan suka wuce shi da bilal dan suje su shirya kamin a gama mata.

Kasa gane Ameera nayi saboda yanda ta canza completely cikin wani material golden colour ga havy make up data sha.kanta yasha gyara amma an yafa mata wani hadadden net a kai,poss da high hills duk white tayi bala'in k'yau ta fito a amaryarta sak.

Koda Al'ameen ya dawo suka kama hanya,ba k'aramin dauriya ya nemo yasawa zuciyarshi ba na ganin bai bata mata k'walliya ba.

Hall ya cika tam su kad'ai ake jira,dan haka ana cewa sun iso d.j ya saki wakan aurensu.

Ameera ji tayi kaman ta zura da gudu ta koma bcos bata saba shiga cikin jama'a haka ba ga kuma idon mutane duka a kansu bama kamar ita dan 'yan uwanshi da frnds d'inshi sai yabonta suke suna cewa sai yanzu Al'ameen ya samu mata.

Shagali akayi sosai a wurin,anci ansha sannan aka tashi kowa ya tafi cike da farinciki.

Lateefa tana k'wance a cikin bedroom d'inta tana wondering me ya hana Al'ameen dawowa har yanzu,sama-sama kunnenta yake jiwo mata gud'a.

Firgita tayi ta tashi zaune bcos kaman a mafarki take ji dan haka ta k'ara kasa kunne.aiko wata mai murya cikin 'yan uwan Umma ta rangad'a gud'an dai-dai sun shigo main palour dan haka har tsakiyan kanta taji shi.

Zumbur ta mik'e tsaye tare da dafe kirji tana " na shiga uku dama yaune auren nashi?shikenan na kad'e na lalace ".

Goge hawayenta tayi tace " wallahi Al'ameen ya d'ebo ruwan dafa kanshi dan wallahi sai auren nan ya zama fitina a rayuwanshi sai yayi nadama dan zan goge sauran son da nake maka nayi maganinka "haka ta cigaba da sumbatu kaman zararriya,sai kaiwa da komowa take a tsakiyan d'akinta.

Su kuwa 'yan kawo amarya sai mamaki da jinjina suke sunga gida kaman aljannan duniya,suna zaune sunata hira da bark'wanci anata dariya da shewa harda gud'a wanda Lateefa take ji kaman mashi suke dab'a mata a zuciya.

Basu wani jima ba aka maida su,aka bar amarya ita kad'ai sai kamshi take.

Jin gidan ya zama shiru ya tabbatarwa Lateefa 'yan kawo amarya sun tafi nan taji wani b'angare na zuciyarta na ingizata taje taci ubanta d'ayan kuma na cewa k'yaleta tukun.

Tana zaune a bakin gadonta sai tsaka da warwara take.sallaman Al'ameen ne ya katse mata tunani.

Juyowa tayi cike da tsiwa da masifa tana mishi kallon wulakance.

Bai kulata ba ya zauna kusa da ita a bakin gadon tare da ajiye mata ledan hannunshi.kamin ya bud'i baki yayi magan ta wawuro ledan ta jefa mishi a jiki,kaji da drinks da suke ciki suka zube a k'asa.

" wallah Al'ameen baka isa ka wulakanta ni ba a gidan nan daga kai har wannan 'yar iskan nan da ka kawo gidan".

" karki k'ara yunkurin kiran mata ta da makamacin suna irin wannan dan wallahi zan iya miki abinda baki tab'a tsammani ba"yace yana kokarin danne fushinshi.

Cike da mamaki take kallon shi tace " Al'ameen ni kake zarewa ido ? wallahi bari kaji kamin kamin abinda kake....."

Wucewa yayi ba tare da ya tsaya jin sauran maganganun ta ba dan a yanda yake ji zai iya karyata ne in ya cigaba da sa insa da ita.


Part d'in amaryan shi ya bud'e ya shiga tare da sallama,ba kowa a palourn dan haka bedroom d'in ya wuce.

Sallama ya k'arayi ko motsi batayi ba balle ta amsa.wani sanyayan ajiyan zuciya ya sauke daya hango ta can karshen gado cikin lulub'i,d'akin yana fitar da wani ni'imantaccen kamshi

Murmushi yayi tare da maida k'ofan zai rufe yaji an banko k'ofan da karfin tsiya.

A razane ya juya sai ganin Lateefa yayi ta shigo tana dube-dube a d'akin.

Ameera itama duk ta rikice ta rasa inda zata sa kanta dan a rayuwa ba abinda ta tsana irin tashin hankali.

A guje Lateefa tayi kan Ameera da ta hango can ta mak'ale a karshen gado.

Cikin zafin nama Al"ameen ya cafkota yana " meye haka baki da hankali ko Lateefa,me kike shirin aikatawa?"

Hayayyak'o mishi tayi " a tsammaninka zaka Iya shigowa da wata karuwa ku k'wana a cikin gidan nan?wallahi sai......".

Tagwayen maruka da tasmu a fu
Kanta shi ya katse mata masifan da take .

Dafe da kuncinta take kallon shi tace " Al'ameen ni ka mara?"

"Abinda yafi mari ma zaki gani in dai akan mata tace,ke har kina da bakin kiran wani da mugayrn suna?"

Zatayi magana ya fizgota da karfin tsiya duk kokarinta na ganin ta k'wace hannunTa kasawa tayi dan ba k'aramin rik'o ya mata ba.

Bai tsaya a ko ina ba sai a main palour,jefata yayi kan kujera ta bugu da karfin gaske sannan ya nunata da yatsa yace " wallahi in kin cika mahaukaciya ki koma d'akin nan ki ga abinda zan miki,banza dabba mara hankali".ya juya ya koma d'akin amaryanshi cikin tsanan halayyarta.

Lateefa kasa motsi tayi saboda ta tsorata da yanayin shi gaba d'aya ya canza lokaci 1 kuma tunda take bata tab'a ganin shi cikin irin wannan yanayin ba dan haka tashi tayi ta koma part d'inta da gudu tana kuka.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€


*~UKUBAR KISHIYATA~*

😭😭😭😭😭😭


(Its all about love and betrayal)


Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)



*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«πŸ’«~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login