Showing 6001 words to 9000 words out of 62823 words
Chapter 3 - UKUBAR KISHIYATA Sirrin Da Ya Rushe Aure by Ummee Yusuf
shi tayi tana dariya,yayin da shi kuma ya k'arasa shiga bathroom d'in.
Direct wajansu salees ta dawo tazo ta rungume shi sannan tace" yanzu ku tafi sai munyi waya zaka ji komai zan san dai yanda zanyi yayi signing dinsu karkaji komai".
Manna mata kiss yayi a kumatu yace " nasan zaki iya babyna, sai naji ki".
Fitowa sukayi ya d'auki motan shi da latifa ta saya mishi suka fita daga gidan.
Latifa dawowa tayi palour na biyu tare da duba kan dining taga an shirya komai,neman guri tayi ta zauna tana jiran fitowan shi.
Sanye da kananan kaya wanda suka yi matukar karb'an shi ya fito ya zauna a d'aya daga kujerun dining.
Plate ta jawo ta fara serving d'in shi, cus cus ce da miyar ganye tasha tsokar kaji har ta gaji.
Fara ci yayi hankali kaman wanda baya son cin abincin.
Gyara zama Latifa tayi tace " my Ameen na nayi maka maganan kwangila nan amma har yanzu bakayi magana ba,kasan k'anne na maza 'ya'yan yayan baban mu basu da aikinyi shiyasa nake son taimaka musu da abinyi".
yana kallon ta yana tauna abincin dake bakin shi cikin natsuwa sannan yace " aina gaya miki duk wani abu inza kiyi na taimako ba sai kin tambayeni ba dan nasanki ta hanya mai kyau zaki sarrafa su".
Tayi yar dariya tace "toh wannan d'in yana bukatan sa hannunka shiyasa".
"Ok d'auko mana insa hannun".
Mik'ewa tayi ta shiga part d'inta,sai gata ta fito da files a hannu.
Batare da ya karantaba ya rantama hannu ya mik'a mata
Karb'a tayi cike da jin dad'i saboda kwangila ce har ta million ashirin.
Tashi tayi da saurita tayi d'akinta ta kira salees a lokacin yana wani hotel da wata karuwan shi suna holewan su.
Ya d'auka yace "ina jinki a akayine"?
Cike da farin ciki tace" my dear ya saka hannu ga files d'in a hannuna gobe aina zan sameka?"
Yace inda muka saba had'uwa mana ko kin saki d'akin ne?"
Tace " na isa in saki d'akin? suma 'yan hotel d'in ganin na mak'alewa d'akin har kara min kud'i sukayi"
Yace "amma ai nasan kud'i ba matsalarki bace ko"?
Tace"kaima kasan da hakan just sai mun had'u goben"
"To bye my heartbeat".
Fitowa tayi bayan sun gama wayan.Al' ameen yana zauna yana kallon bbc news
Zama tayi kusa dashi suna hira sai fara'a take kaman ba ita ba.
Yau dai yayi sa'a albarkacin signing d'in da yayi yau,da kanta ta kawo kanta.
Gaba d'aya ya rikice ce jikin shi har b'ari yake saboda rabansa da ita ya kai sati 2,dan haka kusan raba dare yayi yana abu d'aya sannan ya samu natsuwa.ranan dai ya samu bacci mai dad'i.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . πββπββπββπββπββπββ
*~UKUBAR KISHIYATA~*
ππππππ
( its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
π«*~FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION~*π«
*Gidan zaman lafiya,aminci hadin kai da yardar juna insha Allah*π€
*~part SIX~*
Da washe gari Al'ameen da wuri ya shirya ya fita office.
Fitowa tayi cikin shirin fita da wasu english wears matsassu riga da skirt har shatin pant d'inta ana gani,ba bata lokaci ta ja mota sai prince hotel.
Reception ta nufa bayan tayi parking,ma'akatan hotel d'in suna ganinta fara well come Hajiya.
Duk wani ma'aikacin hotel d'in sun santa saboda regular customer ce.
Bata damu da kama room daban daban ba tunda ta kama room number 35, shikenan ta makale mishi.
Duk ranan da taso holewa sai dai tazo ta karbi mukulli ta wuce kuma ga kyautan kud'i da take musu shiyasa suke bala'in girmamata.
Dan haka yauma suna ganinta suka hau murna,bayan sun gaisa aka miko mata key ta fito da bounch d'in 'yan d'ari biyar ta basu su raba, suka karb'a tare da godiya ta wuce d'akin bayan ta rufe ta rage kayan jikinta daga ita sai karamar vest skirt, ta kwanta akan gado tana kiran wayan Salees.
Yana d'aka wayar yace mata gashi nan ya shigo compound d'in hotel.
Tana ajiye wayan kaman da 10 mins sai gashi nan da kwalban wine a hannunshi ya shigo ya maida k'ofar ya rufe.
Bata motsa ba daga kwanciyar da tayi ba yana kallonta da irin kallon daya saba yi mata na zallan so.
Ya zauna dab da ita yace"ya dai babyna ya na ganki haka?"
Kamo hannun shi tayi da karfi ta jawo shi ya fad'a kanta suka rungume juna suna ta juyi akan gadon tace"kasan nayi missing d'inka sosai".
Tashi yayi ya zauna tare da d'ago ta itama ta zauna sannan ya bud'e kwalban wine ya fara sha.
Ya sha kusan rabi sannan ya mik'o mata itama ta karb'a ta sha sosai dan ta kwana biyu bata sha ba.
Ahaka har suka shanye gaba d'aya suka koma suka kwanta suka cigaba da sheke ayansu san ransu.
Bayan sun natsu,ta bud'e hand bag ta fito da files d'in ta mika mishi tace"ina so mufara business dashi dan kud'in suyi albarka saboda haka na mika maka wuka da nama sai yanda kayi".
Yaca"karki damu zanyi duk iya kokarina dan muyi nasara kaman yanda kema kikayi naki kokarin". Yace yana jujjuya file di'n a hannun sa.
Sai kusa la'asar suka rabu ta wuce gida. shima ya wuce inda ya fito.
A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah,dan yanzu Latifa sun shiga 12years of marrage amma ba wanda ya k'ara takura mata akan haihuwa.tana abinda taga dama.
Hajiya Halima wato mahaifiyar su Al'ameen ta shigo palour d'auke da karamin tray ta d'aura bottle water da glass cups 2 akai.
Ajiye trayn tayi akan wani d'an karamin table na glass a gaban mijinta wato Alhaji mudassir.
Bud'e ruwan tayi tare da zubawa a glass cup d'in ta mik'a mishi sannan ta nemi waje ta zauna kusa da shi.
Ajiye cup d'in yayi bayan ya shanye ruwan,ya juyo yana kallonta yace " dazu munyi waya da Hajiyar katsina tace gobe zasu shigo ita da 'yar wajan Laure Sakeena".
Hajiya cikin farin ciki tace Allah sarki ashe gobe muna da manyan baki,bari mu fara shirin tabarsu tun yanzu".
Dariya Alhaji yayi cikin jin dad'in yanda matar shi take karrama mishi dangi a koda yaushe.
Da safe tunda wuri hajiya tasa aka gyra d'akin da surkuwar ta zata sauka ga kuma girke-girke da sukayi na musamman aka jera su kan din ing ana jiran zuwansu.
3:00pm su Hajiyan katsina suka isohajiya ta karb'e su kamn yanda ta saba yi,
Bayan sun ci sun sha kuma sun huta aka zauna hira a palour.
" wai ina angwayen nawa ne banga ko d'aya ba ko kishiyoyin nawa ne suka rik'e su?"cewar hajiyar katsina.
Hajiyar su Al'ameen tayi dariya tace " aiko sun rike su dole su kyale tunda uwar gida ta zo".
Alhaji yana murmushi yace Sakeena ya wajan ummanki da sauran kannenki?"
Yarinyan da aka kira da Sakeena ta sauke kai k'asa tace duk suna gaishe ku".
" muna amsawa " hajiya tace tana shafa kanta.
Alhaji ya ciro waya ya fara kiran boyz dinsa ya sanar dasu zuwan Hajiyar katsina.
Bayan ya gama kiransu ne Hajiyar katsina tace ya labarin matar Aminu har yanzu shiru ko?"
Hajjiya ta amsa mata " eh har yanzu lokaci baiyi ba".
Tab'e baki hajiyar katsina tayi tace " hmm gobe yazo ya same ni musan abinyi tunda kun kasa nema masa mafita".
Next day saturday ba aiki saboda haka Al'ameen yana gida.
Suna zaune tare da Latifa yake gaya mata zai je can gidansu gaishe da Hajiyar katsina da tazo jiya.
Yamutsa fuska tayi ba tare da ta kalle shi ba tace " noo my Ameen yau fa weekend ne ya kamata ka zauna ka huta a gida dan bana son ka wahala".
" alright " yace kawai suka rufe zancen but kasan zuciyar shi ba haka yaso ba,yana son zuwa su gaisa dan ya dad'e bai sata a ido ba.amma ya rasa dalilin da yasa baya iya mata musu.
Ita kuma Latifa tun lolacin da boka yace mata a cikin 'yan uwansa akwai wanda zai lalata mata sihiri take taka tsan-tsan da al'amuransa ta hana shi shiga cikin 'yan uwansa.
" let me take a shower " tace tare d wucewa part d'inta.
Tana shiga bedroom wayarta ya fara ringin kuma ringin tone d'in salees ne.
Tana d'agawa tace " my only love".
" i need u right now coz i missed u alot hak'uri na ya kare kizo mu had'u" salees yace.
" but salees i have an important thing to do at home "
" Bana son jin komai wato am not importan to u " yace cikin fushi.
Jin muryan shi da alamun fushi yasa tace " pls come down Salees ba haka nake nufi bayi hak'uri gani nan zuwa".
" better " yace yayi hanging call d'in.
Bata son fita yau tafi son ta zauna a gida tayi gadin Al'ameen amma bata son bacin ran salees dan haka tashi tayi ta fad'a bathroom dan yin wanka.
Bayan ta fito daga wanka ta sheka kwalliya da wani leshi maroon d'inkin dogowar riga sai kamshi turare take, ta iske shi a inda ta barshi yana zaune, ta zauna kusa dashi ya juyo yana kallonta dan taci ado harna fitan hankali tace"my meen kun dade baku had'u dasu hajjiyar katsina bako?"
Ta sosa mishi inda yake mishi kaikayi yace"ai shekarune ma zance"
Tace"hmm shikenan kaje ku gaisa,nima zaje gidan mama in dawo"
Ya kama washe baki yace"toh shikenan ki gaida ta nima ba d'ad'ewa zanyi ba ke sai yaushe?"
Tace"my meen kenan zaria fa zanje kaga kuma na d'ade banje ba ina ga sai kusan magrib zan dawo".
" sai kin dawo," yace tare da mikewa yayi part d'in shi .ya shirya cikin manyan kaya na shadda dark green ya sha bugu sai maik'o yake.
Shi kad'ai ya d'auki mota ya fita,bai nemi drivern shi ba.
Direct gidansu dake unguwar rimi ya nufa,yana zuwa mai gadi ya bude mishi gate ya shiga.
A parking space yaga motocin brodthers d'in shi dan haka shima cikin farin ciki ya nufi palour.
Tun daga bakin k'ofa ya fara jin muryoyinsu anata hira da raha,sallama yayi suka juyo gaba 1 su suka amsa ya nemi guri kusa da kkafar hajiyar shi ya zauna.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . πββπββπββπββπββπββ
*~UKUBAR KISHIYATA~*
ππππππ
( its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
π«*~FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION~*π«
*Gidsn zaman lafiya,aminci hadin kai da yardar juna insha Allah*π€
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~ADDU'AR DA ZAKUYI A LOKACIN DA ZAKU BAR GIDANKU~*
Ψ¨ΩΨ³ΩΩ
Ω Ψ§ΩΩΩΩΩΩ ΨͺΩΩΩΩΩΩΩΩΩΨͺΩ ΨΉΩΩΩΩ Ψ§ΩΩΩΩΩΩΨ ΩΩΩΨ§Ω ΨΩΩΩΩΩ ΩΩΩΨ§Ω ΩΩΩΩΩΩΨ©Ω Ψ₯ΩΩΨ§ΩΩ Ψ¨ΩΨ§ΩΩΩΩΩΩ
~Bismillaahi, tawakkaltu 'alallaahi, wa laa hawla wa laa quwwata β illaa billaah.~
*~In the Name of Allah, I have placed my trust in Allah, there is no might and no power except by Allah.~*
*Part seven*
Gaishe da Hajiyar katsina ya farayi sannan ya gaishe da iyayensa da brothers d'in shi tare da matansu.
Bayan gaisawan ne ya d'auki babyn yayan shi Sa'ad wanda bai wuce 6months ba yana masa wasa.
Hajiyar katsina ce take tambayarsa ina Latifa me ya hana ta zuwa su gaisa ko taji tsoron uwar gida ne?
Dariya yayi yace " a'a ba ko mzaria 1ta tafi dubo mamrta bata jin dad'i".
Allah ya suwak'a kowa ya mata sannan suka cigaba da hiran su cikin raha da zolayan juna.
Ganin yanda Al'ameen hankalkn shi ya tafi kan affan yana ta mishi wasa yasa Hajiyar katsina magana tace " kai k Ameenu matarka har yanzu ba labari ko?"
Bai tsaya da wasan ba yace mata " eh Hajiya lokaci baiyi ba kinsan komai lokaci ne".
Hajiyar su itama tace " haka ne komai lokaci ne".
Shiru hajiyar katsina tayi na d'an lokaci kana tace " toh me zai hana ka kara aure ko rabo 'yar uwarta ce ya danne nata kadan hakan yana faruwa".
Al'meen gumi ne ya fara karyo mishi ta kowane hujin gashin jikinsa.ga wani irin damuwa da tashin hankali da suka bayyana karara akan fuskan shi lokaci guda.
Hajiyar katsina ce ta lura da halin da ya ahiga tace "mai gidan lafiya kuwa daga maganan aure sai ka birkice haka?"
Share gumin da ya tsatsofo mishi a goshi yayi sannan yace " gaskiya a bar maganan dan ni ba wani aure da zan iya k'arawa.haihuwa Γ i na Allah ne,a yanda muka dage da addu'a nasan Allah zai share mana hawaye lokaci ne bAiyiba".
Rik'e baki Hajiyar katsina tayi tana kallon shi a matukar mamakince can dai ta daure tace " dan nace ka kara aure shine kake min suratan banza,ni zaka gayawa Allah?toh tun kafin a haifi ubanka nadan Allah.in yarinyar da zaka aura ne baka samu ba sai ka duba nan cikin 'yan uwa ka aura"
Cikin firgici yake kallonta yama rasa me zaice mata,yana zaman-zamansa zata zo taja mishi bala'i dan in Latifa taji zancen nan ya shiga 9 ba 3 ba.
Alhaji ya kalla yace ",dan Allah ku fahimtar da ita ta rufa min asiri ni ban tashi aure ba.pls leave me alone".
Hajiyar katsina ta kasa magana saima hangame baki da tayi tana kallon 'yan palourn duka saboda bata ga wanda ya d'auki maganan serious ba saima ce mata da sukayi ta bar maganan tunda bai tashi auren ba.
Sa'ad ne kad'ai yayi shiru bai tanka ba sai da suka gama magana sannan ya bud'i baki ya cewa Hajiyar katsina " karki damu zamu tafi gidana dashi zansa shi ya fahimta".
" Oh ni 'yasu yau naga abinda yafi karfina".inji Hajiyar katsina tana girgiza kai cikin jimami dan tabbas taga alamu 'yan gidan ba cikin haiyacinsu suke ba.
Hankalinta bai kwanta ba saida suka keb'e da Sa'ad ya fad'a mata abinda yake ranshi.nan itama tace ba Al'ameen kad'ai abin ya shafa ba harda sauran 'yan uwansa da iyayensu.
Fita Sa'ad yayi bayan sallahn azahar,sai kusan la'asar ya dawo da wani jerry can cike da ruwan addu'a da yasha ganyen magarya.
Tambayansa Alhajinsu yayi z ruwan menene wannan?"
" Ruwan addu'ace ta kariya na kawo dukkan mu muyi amfani dashi".ya amsa mishi a ladabce.
Ba b'ata lokaci mai aiki ta kawo cups,duk suka sha sannan yace musu " mallam yace kullum zamu rinka sha har zuwa 7days dan haka daga yau duk wanda ya tashi tafiya office ya biyo yasha kafin ya wuce".
Yayi hakan ne sabida shi tun kamin aurensu shi bai yarda da Latifa ba,bare ma da yaga yanda kaninshi ya birkice lokacin da yaji maganan aure,bayan b4 yayi aure bashi da wani buri da ya wuce ace yayi aure ya tara ya yara amma yanzu ko zancen baya so.
Ga Ahajin su yasan halin shi yana d'an zafi wani lokacin gashi yau Al'ameen yana fad'awa Hajiyarsa magana amma ko kallon banza bai mishi ba ga Hajiyarsu itama a baya bata da buri da ya wuce taga jinin autanta,sai gashi itama ta canza.
Addu'ansa 1ce Allah yada duk wani surkullen da tayi ya warware albarcin wannan addu'an.
Da daddare da zasu rabu sauda yajawa Al'ameen kunne kan yaja bakin shi kar ya bawa Latifa labarin ruwan addu'an da zasu rinka zuwa sha kullum.
Yau kwana uku kenan kullum Al'ameen da safe sai yaje yasha ruwan add'ua sannan ya wuce office.
Da wuri yau ya tashi a office ya dawo gida asual ya tarar da gidan cike da samari da 'yan mata da samari ana ta hira,a karo na farko da yaji ba dad'i a zuciyarshi amma ya danne bai nuna ba ya wuce ciki bayan yayi wanka ya zauna ya fara aiki a system d'in shi.
Haka kawai ya rinka jin shi wani iri yau.
Latifa ce ta shigo ta zauna kusa dashi tace " my ameen lafiya yau baka sauko kasa ba?"
" Lafiya lau ina wasu aiyuka ne shiyasa".yace mata.
Kallonsa tayi tace " abincin fa ?"
Yace " naci a gidan ya Sa'ad kamin inzo".
Shiru tayi tana mamakin yaushe har ya far zuwa gidan wasu ba tare daya gaya mata ba?
Kawar da zancen tayi a ranta tace " toh ni zan sauka kasa sai ka fito".
" Toh " kawai yace ba tare da ya dube ta ba ya cigaba da aikinsa.
Saukowa tayi ta kyale shi.
Yau friday kuma yaune kwana 5 da fara shan ruwan addu'an,yana zuwa ya tarar da duk brodas dinsa suma sun zo.
Bayan sun gaisa kuma sunyi abinda ya kawo su Ai'ameen yace " nifa Hajiya na kasa gane me Latifa take nufi dani,ta mayar min da kaman wani bariki kullum cikin tara min mutane take baya ga haka rabin danginta a.gidan suka tare".
"Hajiya tayi caraf tace " wannan shashanci ne bangane rabin dangin taba".
Alhaji yace "
Wanna ai zancen banza ne kuma laifinka ne kai ka sake mata"
Murmushi mai kayatarwa Sa'ad yayi tare da cewa "ALHAMDULLILAH Ala kulli halin".
Alhaji ne ya kalle shi yace " d'an uwanka yana cikin matsala abinda zaka ce kenan?"
" ba haka nake nufi ba"yace
" Toh me kake nufi?" Hajiya ta katse shi.
Nan ya kwashe komai ya fad'a musu sannan yace " Alhamdullih sauki ya samu tunda har ka fara ganin laifinta saidai abinda nake so da kai ka bar maganan a zuciyarka ka cigaba da pretending har yanzu asirin bai bar ka ba dan bamu san iya lokacin da ta d'eba tana aikatawa ba in ba haka kayi ba ba zamu samu bakin zaren ba.
Cikeda takaici Al'ameen ya fara magana yace " wallahi bazanyi shiru ba yanzu zanje in nuna mata bokanta yayi kad'an dan bazata kwana min a gida ba.
Alhaji ne ya shiga tausan shi akan Sa'ad yana da gaskiya abi komai a sannu.
Kowa yayi na'am da shawaran Sa'ad tare da add'uan Allah ya tsare gaba.
Haka ya wuce office cikin k'unan rai tare da tsanan Latifa a ran shi.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . πββπββπββπββπββπββ
*~UKUBAR KISHIYATA~*
ππππππ
( its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
π«*~FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION~*π«
*Gidsn zaman lafiya,aminci hadin kai da yardar juna insha Allah*π€
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Alhmdllh mama ta samu lafiya ina mika godiyata gare ku my fans kan addu'oin ku Allah ya bar kaunaππ
*~part eight~*
Al'ameen yan zuwa office ya samu mutane da yawa masu son ganin shi ga aiki sun taru sunyi yawa,dan haka sake ranshi yayi ya cigaba da harkokin shi hankali kwance.
Bayan sati Sa'ad yaje har company Al'ameen inda tace yazo ya raka shi unguwa,barin aikin shi Al'smeen yayi ya bishi suka fita su 2 a motan Sa'ad.
A sabon gari gidan mallam nuhu yake,a kofar gidan Sa'ad ya tsaya suka shiga ciki wajan mallam.
Yana kishingid'e a palourn shi sukayi sallama,daga ciki mallam ya amsa ya basu izin shigowa.
Zubewa sukayi gaba 1suka kwashi gaisuwa a wajan mallam sannan Sa'ad ya nuna Al'ameen yace ga kanin shi da ya kab'awa magani kwanaki kuma Alhmdllh sauki ya samu shine suka zo godiya.
Gyran murya mallam yayi sannan ya tashi zaune shima yayiwa Allah godiya tare da basu wasu addu'oi da zasu rik'e