Showing 21001 words to 24000 words out of 62823 words
Chapter 8 - UKUBAR KISHIYATA Sirrin Da Ya Rushe Aure by Ummee Yusuf
takure waje guda.
Dariya Al'ameen yake harda rik'e ciki yace..." dama ganina ne yasa kike shiga wanka da hijab? Tohyau Allah yau ya kamaki cos akan idona kikayi komai nd dis kunya zanyi maganinta"yace tare da zuwa gaban sip d'inta ya ciro mata wani gown na material maroon mai adon black flowers a jiki ya ajiye mata akan gado ya fita zuwa palour ya barta dan taji dad'in shiryawa.
Yana fita ta sauk'e wani ajiyan zuciya sannan tacigaba da shiryawanta,perfumes masu sanyin kamshi tayi amfani dasu wajan feshe jikinta dasu.bata saka d'an k'walin kayan ba sai wani black veil da tayi rolling kanta dashi sannan ta nufo palourn tana taku a hankali cikin natsuwa.
Zuba mata ido har ta k'araso gefe shi ta zauna ba tare da tace komai ba,shine yace..." i'm sorry my baby na tafi na barki ke kad'ai ko?"
Murmushi tayi tace" a'a su Fateema sunzo bayan fitanka,tare muka yini dasu dan basu dade da tafiya ba".
K'wantar da ita yayi akan cinyan shi ya zame mata veil d'in yana wasa da gashin kanta yace" ni ina can na wuni da tunanin na barki ke d'aya ashe ke wunin dad'i ma kikayi".
Dariya tayi tare da gyara k'wanciyarta a jikin shi suka cigaba da hiran su na masoya har aka k'ira sallahn magrib sannan suka mik'e dan gabatar da farali.
Bai shigo cikin gida ba saida yayi sallahn isha'i sannan ya shigo ya sameta ta canza k'walliyarta,doguwar rigar shadda dark blue yasha aiki har kasa ga d'an k'walin tayi mishi irin d'aurin nan mai steps ya matukar yi mata k'yau.
Tana zaune a kan kujera ya shigo ya karaso gabanta ya tsuguna tare da rik'o hannayenta yayi kissing sannan yace " irin wannan make up haka ai sai kisa in manta kaina,kin ganki kuwa kaman mai zuwa beauty contents ".
Waro ido tayi tace " haba mana zaka fara ko?"
"Fad'an gaskiya ba"yace yana dariya.
Hannunta ya kama zuwa kan dinning table dan cin abinci,kaman yanda sukayi breakfast yanzu ma haka akan cinyanshi ya d'aurata ta zaunasuka rink'a ciyar da juna a baki har suka gama.
" zoki rakani inyi wanka "yace yana mik'a
Mak'e kafad'a tayi tare da yin kasa da kai.
Lek'o fuskanta yayi yace " zaki rakani ne ko kuma.....?"
"Ehh....ehh zzzzan raka ka"ta amsa muryanta yana cracking
Dariyan mugunta yayi cos ya san ya gama tsorata ta,sannan ya shige ya barta a tsaye.
Kaman bazata je ba amma tasan in bata je bama zai iya zuwa ya tafi da ita yasa ta fara jan k'afa a hankali har zuwa bakin k'ofan bathroom d'in ta tsaya.
Shahada tayi da ta gaji da tsayuwa ta bud'e ta shiga ciki,jikin k'ofan ta jingina ta tsaya kanta a kasa.
Tana d'agowa sukayi 4eyes dashi yana k'wance cikin bathtube,da hannu ya mata alaman ta karaso.
A ranta take mita ,wai mesa baya ganewa tana kunyan shine?
"Oya come on babyna ke nake jira" ya katse mata zancen zuci da take.
Bata da wani option daya wuce na zuwa.
Da dabara ya rinka janta har tasaki jiki sosai dashi,sun kai 1gud hour suna wankan sannan suka fito.
Shi ya zab'a mata night gown da zata saka,nan sukayi shirin k'wanciya suka k'wanta ya rungumeta sosai kaman wani zai kwace mishi ita sukayi baccinsu mai dad'i.
Haka suka yi ta zuba love kaman su lashe juna dan yanda Al'meen yake nuna mata luv yasa itama ta sake sosai dashi suka ci amarcinsu har 7 days da zaiyi a d'akinta suka kare,kuma a yau ne zai koma d'akin Lateefa.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
πββπββπββπββπββπββ
*~UKUBAR KISHIYATA~*
ππππππ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπ«π«π«~*
*~βWe beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part nineteen*
Ameera tana zaune a palourn ta bayan tayi sallahn isha'i duk ta rasa me yake mata dad'i.
Al'ameen yana dawowa daga masallaci direct part d'in Lateefa ya wuce,ya samu ta baje a palournta tana waya,tana ganinshi ta katse wayan tayi tare da
K'irk'iro murmushi tanayi mishi barka da zuwa.
Bai zauna ba yace ta fito main palour yana son magana dasu,ta amsa da toh sannan ya fita zuwa part d'in Ameera.
Yana shiga parlourn yaganta ta zuba tagumi da hannu 2,tsayawa yayi yana kallonta yana jin ba dad'i a zuciyar shi dan yasan abinda yake ji a zuciyar shi itama shi take ji,gashi kuma ya sabar mata da abubuwa da yawa wanda yasan dole yanzu su dame ta.
Cire mata tagumin yayi lokacin da yake zama kusa da ita.
A d'an firgice ta juyo ganin shine yasa ta d'anyi dariya tace " yaushe ka shigo ne?"
" tayaya zakiji shigowata while u re lost in ur thought,wai tunanin me kike ne haka?"
" nothing just bana jin dad'ine".ta amsa mishi cikin dauriya.
Jawota yayi jikinshi yayi huging d'inta sannan ya fara rad'a mata magana cikin kunnenta yace..." am sorry Babyna nasan abinda yake damunki but am asuring u bai kai rabin yanda nake ji ba cos i will miss u badly.sai dai ina so ki k'wantar da hankalinki dan after 2days zamu kasance tare kinji?"
Gyad'a kai kawai take dan kukan da take ba zai barta tayi magana ba.hannu yasa yana share mata fuskanta,sannan ya d'ago fuskanta suka had'a ido,murmushi yayi mata itama ta mayar mishi.
Kissing d'inta ya shiga yi sosai,bai barta ba saida yaga ta samu natsuwa sannan yace ta tashi su fita main palour zaiyi magana dasu.
Yana rik'e da hannunta suka fito zuwa palour,nan suka tarar da Lateefa zaune tana jiransu.
Ameera da Lateefa suna had'a ido kowacce zuciyarta saisa ya buga,bama kaman Lateefa dan k'yaun Ameera shi ya razanata,ashe rannan kallon tsoro tayi mata.
Ita kuma Ameera ganin Lateefa goggayiyar mata kuma wayayyayiya shi ya bata tsoro,tayaya zata iya kishi da ita?
Gyaran murya Al'ameen yayi bayan sun zauna sannan ya fara magana yace...Lateefa dake zan fara tunda kece gaba da ita muna tare dake yau 14years kenen dan haka kinfi kowa sanin gidanki dani kaina kuma wannan..."ya nuna Ameera dake zaune tana wasa da wani zoben gold dake d'an yatsanta yace....
" k'wanwarki ce kuma bak'uwa,ina son kija girmanki ki rik'eta da amana kuma kijata a jiki.ke kuma Ameera ina son ki bata girmanta ku zauna lafiya tunda kinga ni ba zamaunin gida bane,soo in kin bata had'in kai kuka zauna lafiya jin dad'inku ne dukkan ku,nima hankalina zai k'wanta".
Gyara zamanta Lateefa tayi tana tab'e baki tace..."muna godiya my Ameen kuma ka taya mu da addu'a Allah ya had'a kanmu muma zamuyi iya k'okarinmu na ganin bamu baka kunya ba".
Murmushi yake cikin jin dad'i dan wani irin nishad'i yake ji cos baiyi zaton haka daga Lateefa ba,kallon gefen da Ameera take yayi sannan yace" kina da magana ne babyna?"
Girgiza kai tayi da sauri ba tare da ta d'ago kai ba.
"Alhamdullilah naji dad'in haka wannan ya nuna min tun yanzu zaman lafiya ya samu a cikin gidan nan,now sai kuyi shawara k'wana nawa-nawa zaku yanke?"
" ni a ganina k'wana 2 yayi koya kika ce Babyn angonta"Lateefa tace tana hararan Ameera cos tunda Al'ameen yace mata babyna ta kasa controling kanta.
Ameera ko tunda ta shigo kanta a k'asa yake dan haka bata san ma tanayi ba.
Yanzu ma da Al'ameen ya nemi ta fad'i ra'ayinta cewa tayi duk abinda sukayi dai-daine.
" toh ni zan shiga in k'wanta sai da safenku "tashi tayi ta nufi part d'inta ba tare da ta tsaya taji amsan su ba.
Da ido ya rakata har ta shige sannan ya dawo da duban shi kan Ameera da har yanzu kanta yana k'asa.
Zuwa yayi ya tsugunawa a gabanta yace..."ya dai babyna?"
Ajiyan zuciya ta sauk'e tana dubansa tare da k'ak'alo murmushi.
Cike da damuwa yace..."bana son in ganki cikin damuwa pls idan ba ki saki ranki ba bazan iya tafiya in barki ba".
Gefen fuskan shi ta shafa tace " ba damuwace a raina ba just ina tunanin yanda zanyi 2days without u,but dont worry ya wuce na daina"tace tana murmushi.
"Tashi muje in rakaki d'aki".
Tashi tayi suna tafiya kaman basa so har suka shigo palourn ta,rungumeta yayi tsam kaman Zai maida ta ciki yana shinshina wuyanta,daga nan kuma maganan ya sauya dan kissing d'inta yake tare da romancin d'inta da zafi-zafi.
Ture shi tayi da taga yana shirin zarcewa.sake ta yayi suna maida numfashi dak'yar.
Juyawa yayi da sauri ya fita ko sai da safe bai tsayayi mata ba dan yasan in ya cigaba da tsayuwa ba zai iya controling kanshi ba
Yana fita ta zube a wajan tana kuka zuciyarta a cunkuse da kishi a ranta tana dole Lateefa ta musu hauka ranan da a kawota dan duk macen data d'and'ani zama da miji irin Al'ameen dole ta guji duk wani abinda zai rabasu koda na minti1 ne.
Mikewa tayi ta hau kan gado ta k'wanta taji duk pillown da ta d'aura kanta akai baya mata dad'i dan rabonta da k'wanciya akan pillow tun tana gida,juyi ta rink'a yi akan gadon dak'yar ta samu bacci ya d'auketa.
Al'ameen part d'inshi ya nufa yana tsammanin zai samu Lateefa a can amma yaga wayam bata nan dan haka bathroom ya fad'a da niyan wanka amma sai yaji ba dad'i saboda cikin k'wanaki da sukayi tare da Ameera ya saba da abubuwa dayawa wanda da bai san dasu ba a auren su da Lateefa.
A daddafe yayi wankan ya fito still bata zo ba har ya shirya cikin white pyjames d'inshi ya fito ya nufi part d'in Lateefa amma ga mamakin shi yaji k'*ofan ta a bud'e .
Bud'ewa yayi ya shiga sannan ya mayar da k'ofan ya rufe.
Tana k'wance suna waya ita da Salees d'inta taji motsi a palourn ta dan haka cikin sauri ta katse wayan ta tura shi karkashin pillow ta runtse ido kaman me bacci.
Ya dad'e tsaye a kanta yaga alama baccin take da gaske.
Hawa gadon tare da shigewa cikin duvet da ta rufu dashi,rungumeta yace " har kinyi bacci?"
Mik'a tayi (irin ita mai baccin nan).
Bud'e ido tayi a hankali tace "my Ameen ka shigone,ina amarya?"
"Kema kinsan yau Ameen nakine meye na pretending"yace yan k'ara rugumeta.
" no ba pretending bane just kaima kasan yanda ciwon kaina yake in ya tashi but na sha magani,let me sleep for while i wiil b alright"tace tan yamutsa fuska tare da lumshe ido.
Wani kululun bakinciki ne ya tokare mishi mak'ok'ora dan ya fara gajiya da wannan wanda halinta wanda bata tashi rashin lafiyanta sai taga yazo gare ta.ba dan ya kasance mai yaki da zuciyarshi ba da tuni ya fad'a halaka.
Cike da jin haushin kanshi ya fice daga part d'inta yayi nashi tare da alkawarin ba zai k'ara waiwayanta ba tunda Allah ya mishi canji.
Yana k'wance a kan lallausar gadon shi sai juyi yake ya kasa bacci Ameera kawai yake bukata a wannan lokacin.
Kasa daurewa yayi ya jawo wayanshi dage side drower yayi dialing no Ameera.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
πββπββπββπββπββπββ
*~UKUBAR KISHIYATA~*
ππππππ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)
βββββββ
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
βββββββ
*~βWe beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*β
*part twenty*
Ameera tana cikin bacci ta rinka jin ringin d'in wayarta sama-sama,dak'yar take iya bud'e ido saboda nauyin da sukayi mata.
A take ta nemi baccin ta rasa sakamakon sunan Al'ameen da tagani yana yawo akan screen d'in wayan.
Sallama tayi mishi cikin muryan jan hankali bayan tayi recieving.
Wani sanyi yaji yana ratsa zuciyar shi har ya nemi bacin ran da Lateefa ta sa mishi ya rasa.
Tana jin shi ta cikin wayan ya sauke ajiyan zuciya sannan yace..." sorry Babyna kina bacci na tashe kiko?"
" bakayi bacci ba har yanzu"ta tambaye shi cikin mamakin ya akayi Lateefa ta bar shi har ya kirata a waya a wannan lokaci?
" tunaninki ne ya hana ni bacci,I'm really missing u Babyna wanda har nake jin ba zan iya controling d'in kaina ba.i'm coming to ur room right now".yace mata in a serious tone.
Duk da taji dad'in kalaman shi amma hakan bai hana ta
Saurin katse ba tace... " no Yayana kayi hak'uri kada kazo ka manta d'azu kai kake gaya min cewa inyi hak'uri zamu rink'a kasancewa bayan ko wani k'wana 2,kuma in kazo yanzu ita kuma kaga ai bamu k'yauta mata ba" a zuciyar shi yake cewa da kinsan wacece Lateefa da baki bakin kiba......
Muryarta ne ya sake katse shi a karo na 2 tace..." kuma bana son ka kasance cikin masu shanyayen jiki ranar gobe k'iyama".
Jikin shine yayi mugun sanyi jin kalamanta kuma ya godewa Allah da ya bashi mace mai natsuwa kamarta cos he know Ameera is a blessing frm Allah.dan haka yace..." hakane Babyna nagode da kika tunatar dani gaskiya i will try my best wajan k'watanta adalci a tsakaninku insha Allah,nan suka kama hira kaman ba dare ba sun dad'e kamin suka hak'ura suka k'wanta bacci.
Da washe gari ya kasance monday ne dan haka Al'ameen tun 8 na safe ya shirya fita zai office,ko kallon kayan breakfast dake jere akan table baiyi ba ya wuce part d'in Ameera a lokacin kuma Lateefa tana can tana baccin asara da ta saba.
Yana shiga part d'int Ameera ya same ta fes taci k'walliya da wani material peach clour riga da skirt sun zauna das a jikinta saboda dinkin yabi jikinta tayi matuk'ar k'yau duk da ba wani k'waliya tayi ba.
Tana ganin shi ta tashi ta tare shi da murnanta dan ba k'arya tayi missing d'in mijinta.
Ajiye brief case d'in hannunshi yayi tare da bud'a mata bud'e hannayen shi,da gudu tazo ta fad'a kirjinshi suka rungume juna suna dariya.d'ago hab'anta yayi suna kallon juna yace.." i missed u so much Babyna..."
K'wantar da kanta tayi akan kirjin tana shakan daddad'an kamshinsa tace..."ina k'wana my one".
D'agota yayi tare da bata peck a goshi sannan yace..." kin tashi lafiya Babyna?"
" lafiya lau,ya na ganka da jaka ko yau zaka fara fita aiki ne?"
" yes yau zan fara kuma in na tafi sai 6:00pm" yace mata cikin tsokana.
Shagwab'e fuska tayi kaman zatayi kuka tace..." wai gasikya yayi yawa ni dai ka rage time d'in ko in bika office d'in"tace cikin shagwab'a har da dire-diren k'afa.
Shiko kallonta ya tsayayi cike da sha'awa dan yana matukar son mace mai shagwab'a.kasa jurewa yayi saida yayi kissing d'inta sosai sannan ya saketa ya juya zai fita ta tsayar dashi ta hanyan tambayan shi " kayi breakfast kuwa?"
Tsayawa yayi ya dawo da baya yace...."dont worry in naje office zan sha tea acan".
Bata bashi amsa ba ta kama hannun shi har zuwa kan table ta zaunar dashi,nan da nan ta zuba mishi chips da fried egg a plate sannan ta had'a mishi tea mai kauri tace .." bismilla".
Tunda ta fara mishi hidima yake binta da wani irin kallo mai cike da zallan so,yaushe rabon da ya samu kulawa a wajan Lateefa haka ita da kullum tana bacci yake fita office ba ruwanta da yaci ko bai ci ba.
Ameera bata barshi ba saida ya cika tumbinsa sannan ta rako shi har bakin k'ofan palourn ta tace..."Allah ya bada sa'a ya kare ka daga dukan abin k'i".
Hancinta yaja yana murmushi yace" ameen Babyna Allah yayi miki albarka"zuciyar shi fari sol kuma cike da jin dad'in addu'ointa ya fita zuwa office,zai iya cewa tunda yake da Lateefa bata tab'a yi mishi irin wannan addu'an ba shiyasa yake jinta daban a cikin zuciyar shi gata dai yarinya ce k'arama amma abinda take wajan kula da miji tafi manyan mata dayawa.
Lateefa duk ta fita hayyacinta saboda yanda taga Al'amern ya susuce akan Ameera,duk ta rame ji take kaman ta k'ona su kowa ya huta amma in ta tuna da maganan bokanta sai hankalinta ya d'an k'wanta saboda ta yarda da aikin shi.
A daddafe tayi wata 1da boka ya basu,lokaci yanayi suka hanya ita da Aina'u sai gidan boka.
" boka gamu nan mun dawo dai-dai lokacin da ka bamu"Aina'u ce takewa boka bayani yayin da Lateefa kuma tana zaune ta k'osa taji mai boka zaice.
Boka saida yayi wasu tsurkullen shi sannan ya d'ago kai yana kallonsu yace..."aikinki na yau ba mai sauki ne bane kaman da saboda yariyan tana da ibada sosai ba wani aljani da zai iya tunkarar ta a halin yanzu".
Gumi Lateefa ta goge zuciyarta na bugawa da karfi jin abinda boka yace,cikin matuk'ar tashin hankali tace...." na shiga uku boka da kai kad'ai na dogara yanzu ya zanyi?" (waiyazubillah)
Dariya boka ya kece dashi sannan yace..." bukarar ki zata biya amma wannan karpn saida taimakon ki"
Cikin sauri ta katse shi tare da cewa..." ka gaya min komenene zanyi boka".
Wani bakin kulli ya mik'o mata yace..." ga wannan ki sa mata a abin sha tana sha bacci mai nauyi zai d'auketa,ke kuma a lokacin da take baccin sai kije d'akinta ki samo rigarta dana mijinku zan baki wasu layu da guraye saiki nannad'e su da kayan ki tura su a k'arkashin gadonta.in kikayi haka toh kin gama kama gidan dan ba abinda zasu iya aiwatarwa saida umarninki,zasu kasance cikin matuk'ar tsoronki da shakkarki yanda ba k'ya zato.kece zaki mulke su son ranki dafatan hakan yayi miki".
Wani irin dariyan farinciki ta fashe dashi cikin tsananin murna tace..." yayi boka zan aiwatar da komai yanda kac,wallahi sai na sa sun bauta min dukkan su 2 sai sun gane basu da wayo"
Makud'an kud'ad'e ta ajiye mushi wanda yafi na kullum sannan suka fito.
A hanyarsu ta dawowa gida Aina'u ta dubi lateefa tace..." besty yanzu ya zakiyi ki bata wannan maganin tasha?"
Harar Lateefa ta wurga mata tare da tab'e baki sannan tace..." sai kace baki san dawa kike magana ba?"
"Toh ai gani nayi ko fitowa batayi kikace".
"Ke dai zuba ido kisha kallo"tace cikin isa.
" nasan zaki iya ba abinda zai baki wuya mata a gidan Ameenu"Aina'u tace tana k'ara zugata.
Cike da k'warin guiwa ta iso gida.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
πββπββπββπββπββπββ
*~UKUBAR KISHIYATA~*
ππππππ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπ«π«π«~*
*~βWe beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*part twenty one*
Bayan dawowarsu daga gidan boka Lateefa duk