Showing 12001 words to 15000 words out of 62823 words
Chapter 5 - UKUBAR KISHIYATA Sirrin Da Ya Rushe Aure by Ummee Yusuf
Abban ku ba".
Fateema tana fita ta same shi yana tsaye a inda suka barshi,tace " gani"
" Fateema dama dan muyi sallama ne kuma ga wannan ki sayi choculate".
Zaro ido tayi gani kud'i sabbi fil suna d'aukan ido tace " lah-lah Abba zai min fad'a ba zan karb'a ba".
" ki kaiwa Umma " yace .
"A'a itama ba zata karb'a ba " tace tana baya dan sisai kud'in sun tsoratata.
" in kince injini zata karb'a " yace yana kara mik'o mata kud'in.
Hannu 2 tasa ta kar'ba sannan tace " ka jira ni anan dan in tace ba zata karb'a ba zan kawo maka kud'inka ".
Murmushi yayi ganin yarintar ta yace mata " na yarda je ki kai mata ina jiran ki"
Da sauri tayi hanyan cikin gida.
Yafito musa yayi da gannu suka shiga mota suka bar anguwan.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . πββπββπββπββπββπββ
*~UKUBAR KISHIYATA~*
ππππππ
( its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
/βββββββ
GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION
βββββββ
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπ«π«π«~*
*~βWe beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*~part eleven*~
Fateema tana shiga cikin gida ta mik'owa Umma kud'in tace " gashi Umma wai yace in kawo miki"
Fad'a Umma ta hauta dashi kan ta mayar mata da kud'in shi tun kan ranta ya b'aci.
Ba musu ta juya ta fita mayar mishi da kud'in shi kaman yanda Umma ta umarce ta.
Sai dai me tana fita taga wayam ba Al'ameen ba motan su,cikin sanyin jiki ta koma gida.
Tana shiga ta tarar har yanzu Umma bata daina fad'a ba.
Zama tayi kusa da Amira tace kiyi hak'uri Umma dana fita bangan su ba sun tafi.
Amira ra saci kallon Umma da ta kasa magana saboda takaici tace " mesa kika karb'a Fateema nima ya bani kin karb'a nayi".
Girgiza kai Umma tayi cikin takaici tace " kinsan hankali bai ishe ta ba inba haka ba me yasa kika karb'i kud'in shi me zancewa Abban ku in ya dawo?"
"Umma ki rik'e kawai tunda ya riga ya baki kawai mu sayi abin karyawa dashi tunda tun safe bamu ci komai ba".
Duka Umma ta kai mata a cinya tace " taya zamu tab'a kud'in da bamu san daga ina ya fito ba,duniyan yanzu ba abin yarda bane bamu san daga ina yake ba dan haka ajiyewa zanyi mujira zuwan Abban ku ya yanke hukunci.kuma ina son ku kasance masu hak'uri a duk yanda kuka sami kanku a ciki dan ba yau kuka saba zama ba abinci ba,dafatan kun fahimce ni".
" eh Umma " suka ce a tare.
Al'ameen kuwa tunda yaje office ya kasa tab'uka aikin kirki gaba d'aya tunanin Amira nan ya addabe, shi wani special feelings yake ji akanta wanda bai tab'a ji a kan ko wace mace ba.ji yake kaman ya koma ya k'ara kallonta ko zaiji d'an ji relief.
A daddafe yayi sallahn la'asar yana idarwa ya fad'a mota ko ta kan musa driver bai bi ba sai tudun wada gidansu Amira.
Abba ne yayi sallama ya shigo cikin gidan shi.
Fateema ce ta tashi cikin sauri ta karb'i 'yar ledan da ya shigo da ita ta mik'awa Umma tare da kawo mishi ruwa a randa mai sanyi a kofin silver.
Sannu da zuwa Umma ta mishi,sai da ya sha ruwan da Fateema ta kawo mishi sannan ya amsa.
"Ya kasuwan Mallam" tace tana bud"e ledan da ya shigo dashi.
" kasuwa alhmdllilah kin ganni sai yanzu ko,ina Amira take?"
"Amira ta tafi islamiya" Umma ta bashi amsa.
" haba ya zaki barta ta tafi bata ci komai ba " Abba yace cikin damuwa.
Umma tana juye garin rogo da suger da ya kawo a k'wano tace " toh ya zanyi?nace ta hak'ura da zuwa makarantan amma tace dole taje dan yau zasu bada hadda shiyasa na k'yaleta ta tafi".
"Allah sarki Amira akwai kok'ari Allah ya musu albarka" Abba yace .
"Ameen " Umma tace sannan tacigaba da cewa " bayan ftanka Mallam wannan mutumin da ya taimaki Amira jiya ya dawo ya nemi su gaisa,bayan sun gaisa ya bata kudi da taki karb'a shine yayi wannan mai rawan kan dabara wai ta kawo min inna k'i karb'a ta mayar mishi da kayan shi.tana shigowa na hauta da fad'a nace ta mayar mishi da kud'in shi,tana fita taga sun tafi shine na ajiye nace idan ka dawo sai kasan yanda za'ayi dasu.ke tashi ki kawo yagani" tace tana hararan Fateema.
Tashi Fateema tayi jiki a sanyaye ta kawo kud'in ta mik"awa Abba.
Cike da mamaki Abba yake jujjuya kud'in a hannu,ya bud'i baki da niyan magana sallaman wani yaro ya katse shi.
" wai ana sallama da Mallam inji wani a waje" yace bayan sun amsa mishi sallaman.
Tabarma Abba yace a bawa yaron ya shimfid'a a zaure kuma yace yana zuwa saboda ya d'auka cikin irin mutanen nane masu zuwa neman sani.
" karb'i ki ajiye ina zuwa " yace tare da fita zuwa zaure.
Had'e rai yayi sosai ganin Al'ameen zaune kan tabarman da yaron ya shimfid'a.
" d'an samari lafiya,me kake buk'ata me yasa kake bibitan gidana?"Abba ya jero mishi wa'yanan tambayoyin.
Kasa da kai Al'ameen yayi yace " Mallam kayi hak'uri bakomai a raina sai alkhairi,ammmm dama......nace Amira nagani nake...in ba'ayi mata miji ba"ya karasa cikin ladabi.
Kallon shi Abba yayi da k'yau sannan yace " waye kai kuma daga ina kake?"
Gyara zama Al'ameen yayi yace " suna na Al'ameen mudassir kuma ni d'ane ga Alhaji mudassir Inuwa".
Nan da nan fuskan Abba ya washe fara'a ya cika fuskan shi saboda ba wanda bai san shi ba a cikin garin k.d saboda halayyarsa masu k'yau ga taimakon talakawa " Alhaji Mudassir da sani ?"
Murmushi kawai Al'ameen yayi ya sunkuyar da kai.
Abba yace " kasan san samarin yanzu ne basu da tabbas sai ka d'auki shekaru kana bawa 'ya'yanka tarbiya wani yazo lokaci d'aya ya rusa maka shiyasa kaga nak'i baka fuska tun farko amma yanzu tunda naji daga inda kake ba komai sai ka nemi amincewanta dan banyi mata miji ba Allah ya zab'a abinda yafi alkhairi"
Godiya Al'ameen yake ta zabgawa kaman wanda aka mishi albishir da gidan aljanna. cike da farin ciki ya tashi ya fad'a mitan shi sai gida.
Abba yana shigowa yacewa Umma " ke mik'o min kud'in nan inje bakin kasuwa in sayo mana balangu"
Umma tace " haba Mallam yanzu kaima cewa zakayi ma tab'a kud'in nan?bayan bamu san daga inda ya fito ba".
"Waya fad'a miki ba'asan daga inda ya fito ba?"nan Abba ya k'washe yanda sukayi da Al'ameen ya fad'a mata.
Shiru Umma tayi dan ita maganan bai mata ba ina au ina gidan Alhaji Mudassir.
Fateema kuwa dad'i kaman ya kashe ta 'yar uwarta ta samu mijin nunawa sa'a.
Sallama Amira tayi ta shigo tayiwa Abba da Ummanta sannu da gida ta wuce d'akinsu ran cire unifirm.
Kaman wacce aka tsikara haka fateema ta mike tabi bayanta da gulsa mata abinda ya faru
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . πββπββπββπββπββπββ
*~UKUBAR KISHIYATA~*
ππππππ
( its all about love and betrayal)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
βββββββ
GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION
βββββββ
Sis zara Allah ya raya mana baby samha Allah ya albarkace ta da sauran zuri'an mu baki daya ameen.
*~part twelve*~
"Sis ya k'ara zuwa".Fateema tace cike da zumud'i.
Kallonta Amira tayi tace "waye yazo kuma?"
"Al'ameen ".
Zuciyarta sai da ya buga jin sunan amma ta dake tace " waye kuma Al'meen kuma?"
Matsowa Fateema tayi kusa da ita tana washe baki tace " wanda yazo wanki d'azu da safe".
Dafe kirji tayi tana zaro ido tace " Allah yasa Abba bai ganshi ba".
" na nawa kuma Abba ya ganshi har sunyi magana".
"Innalillahi wa inna ilahi rajiun!! Na shiga uku me Abba yace?"ta tambaya a rud'e.
Dariya Fateema tayi ganin yanda Amira ta rud'e tace " k'wantar da hankalinki sis bcos Abba ya amince dashi 100% dan yanzu ma kud'in da ya bayar.yana hannun shi wai zaije bakin kasuwa ya sayo mana balangu".
Dariya itama Amira tayi tace " ke Fateema bakin nan naki akwai son cin dad'i".
K'asan ranta kuwa fap farin ciki dan itama tun da ta had'a ido dashi ta kasa daina tunanin shi a ranta.
********************
Bayan 2 days Al'ameen ne zaune a palourn gidansu suna hira da parent d'in shi sai dai hajiya hankalinta gaba1 yana kan wani program na larabawa da take kallo.
Al'ameen ya gyra zaman shi kusan yafi a k'irga dan baisan mesa ba yake jin nauyin maganan da yazo dashi kaman wani sabon shiga.
Alhaji yana ankare dashi yace " yaya dai kaman kana da magana ko?"
Murmushi yayi ya sunkuyar da kai yace " eh toh kusan hakane nazo neman shawara ne akan wata yarinya da muka had'u da ita 2days ago and da ikon Allah tun daga lokacin sha'awan k'ara aure ya shiga raina".
" masha Allah!!"Alhaji yake ta makmaitawa.
Hajiya kuma cikin farin ciki ta juyo tace " Alhamdullilah naji dad'in maganan nan Allah ya sanya alkhairi yasa muga jikokinmu".
"Ameen ameen a ina yarinyan take ne?"Alhaji ya tambaya.
"A can tudun wada take 'yar gidan Mallam Yawale ".
" toh masha Allah zan sa a min bincike akanta gudun fad'awa gidan jiya,in har ba'a samu zamu je bayan k'wana 2".
Hajiya ta gyra zama tace" Al'ameen abinda nake so da kai kar ka kuskura matarka taji labarin nan kasan halinta ba abinda ba zata iya aikatawa ba,saboda haka k rufe maganan har saikomai ya kammala sai ka gaya mata".
Cikin gamsuwa da maganan Hajiyarsa Al'ameen yayi godiya sannan ya musu sallama da sunan zuwa office office ya wuce.
A wani babban shopping mall Al'a.een ya tsaya ya saya mata waya iphone 7 pink colour,ya had'a da kayan ciye-ciye yayi hanyan gidan su Amira.
Parking yana neman d'an aiken da zai tura dan kira mishi ita.
Cikin sa'a yaga wata yarinya da tallan awara akanta.
Ba b'ata lokaci ya kirata tazo da gudunta ta ganin mai mota zai sayi awaranta.
"Na nawa zan baka"ta tambaya cike da jin dad'i.
Dariya yayi yace mata " na nawa ne a ciki?"
" na 350 ne "ta amsa cikin gaggawa.
500 ya mik'a mata yace taje tayi sadaka kuma ta shiga gidan can ta k'ira mishi Ameera.
Karb'an kud'in tayi sannan ta ajiye roban ta ruga da gudu zuwa cikin gidan tayi sallama.
Fateema ce a tsakar gidan tana wanke-wanke ta amsa mata.
" wai wani mai mota yana kiran Ameera" tace tana haki.
" mai mota kuma" Fateema ta tambaya"
Kamin ta amsa Umma ta lek'o a dak'i tace " je ki gani mana ko yaron nan ne ?"
Da sauri ta tashi tayi hanyan fita bayan ta zura hijabinta.
"Tana zuwa akace kuma banida cangi dan banyi ciniki ba tun d'azu na fito".
Kallon tausayi yayiwa yarinyan yace " jeki abinki ngode ".
Da murna ta d'auki robanta ta tafi.
Fateema tana lek'owa zaure suka had'a ido dashi murmushi tayi ta koma cikin gida da sauri.
"Umma shine yazo"
"Toh d'auki tabarma ki kai mishi zaure bai kamata su tsaya a waje ba yanzu tunda Abbanku ya amince dashi".Umma tace mata.
Tabarman ta d'auka ta fita zauren dashi ta shimfid'a sannan ta fita zuwa insa yake tsaye.
Sallama tayi mishi ya amsa yana tambayanta mutanen gida.
Amsawa tayi da lafiya sannan ta.mishi iso cikin zaure.
Gaba tayi ya biyo bayanta har cikin zauren nan ya zauna kan tabarman ita kuma tayi cikin gida.
D'akinsu ta shiga ta tarar da Ameera tana k'wance ta lumshe ido kaman mai bacci sai da a zahiri ba baccin take ba tana dai tunanin ya zatayi in ta fita wajan shi dan bata tab'a tsayawa da wani namiji da sunan zance ba.
Tashinta Fateema ta farayi ta bud'e ido tana kallon Fateema tace "lafiya ina baccina zaki tashe ni?"
" sis nasan fa ba bacci kike ba u re just pretending tashi mai sonki yazo yana jiranki".
" nifa Fateema bansan ya zanyi ba in na fita nifa kunya nake ji "tace kaman tayi kuka.
" kunya?haba sis sai kace a zamanin su Umma kike?tashi kiyi light make up kije dont keep him waiting".
Kamin ta bata amsa Umma ta d'aga labulen d'akin tace " zaman me kike Ameera tundazu kin bar bak'o yana jiranki?tashi ki wuce bana son shashanci".
Tashi tayi tana tura baki tasa wani white long hijab d'inta sannan ta nufi zauren.
Tundaga bakin zauren take jin fitinannen kamshin turaren yana tashi sallama tayi mishi da sweet voice d'inta,amsawa yayi yana kallonta da murmushi akan fuskan shi.can gefe nesa dashi ta samu waje ta zauna kanta a k'asa.
Jin idanun shi akanta yasa ta d'ago suka had'a ido turo baki tayi tare da kallon gefe dan ta tsani yawan kallo.
" ina wuni "tace ba tare da ta kalle shi ba.
Kallonta kawai yake cikin shauk'in sinta dan turo bakin nan da tayi saida ya.jefa shi wani hali da k'yar ya tattaro natsuwa yace" rik'e gaisuwarki dan bazan amsa.ba,haba prety haka ake gaisuwa?"
Satan kallon shi tayi ta gefen ido taga har yanzu idon shi akanta,kara turo bakin tayi cikin ranta ta mitan yana bata kunya.cike da shagwab'a tace " toh ya akeyi ?"
Ya Salam yace a ranshi dan yanda yarinyan take sashi rasa natsuwa.
Mik'ewa yayi ta ajiye shopping bag d'in a gabanta yace toh shi kenan tunda na lura kunyata kike ji ga waya nan a ciki ki sakata a charge zan kira ki anjima maybe zaki fi sakewamu gaisa sosai ta wayan".
Tana nan zaune ya juya yace " saina kira prety na wuce office".
Har yasa kai zai fita yaji muryanta a bayan shi tace " nagode Allah ya kiyaye".
Juyowa yayi ya fasa fitan yana kallonta saboda yanda yaji dad'in addu'an data mishi har cikin ranshi dan duk tsawon zaman shi da Lateefa bata tab'a mishi addu'a dan yayi mata wani abu ko dan zai fita ba.amma yau gashi 'yar k'aramar yarinya tayi mishi nan yaji ta k'ara samun waje na musamman a zuciyar shi.
" Ameen prety nima nagode " yace sannan yasa kai ya fice.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . πββπββπββπββπββπββ
*~UKUBAR KISHIYATA~*
ππππππ
( its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
βββββββ
GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION
βββββββ
*~part thirteen~*
Saida taga fitan shi sannan ta tashi tare da nannad'e tabarman ta shiga cikin gida bakinta d'auke da sallama.
Jingine tabarman tayi a jikin bango sannan tazo ta mik'awa Umma shopping bag d'in a hannunta.
" shi baya gajiya da hidimane?" Umma tace lokacin da take bud'e bag d'in.
Ihu Fateema tayi had'e da salle sai gata a gaban Umma ,cikin tsananin murna take magana " lah sis iphone 7 nefa".
Harara Umma ta banka mata tace " ke ko Fateema ba zaki natsu bako?"
Komawa tayi ta zauna tana "kiyi hak'uri Umma na daina".
Mik'awa Ameera ledan wayan Umma tayi,aiko kamin ta karb'a har Fateema ta rigata.
Rik'e baki Umma tayi ta bita da ido tana "Allah ya shirya min ke Fateema".
" Ameeeen Ummana" ta amsa daga ciki tana dariya.
Kiranta Umma ta k'arayi ta basu kayan ciye-ciye da Al'ameen ya kawo.
Zama sukayi dirshan a d'aki suna cin kayan ciye-ciyen Fateema tana taya ta oprating wayan dan duk gidan basu da waya sai Abbansu da yake da k'aramar tecno.
Fateema ta fita sanin kan waya dan tana karb'an na frnds d'inta a school.tsab'anin Ameera bata da karambani shiyasa bata wani iya kan waya sosai ba balle wannan mai tsadan.
Saida sukayi mai isarsu sannan ta jona ta a charging suka fito tsakar gida dan taya Umma aiki.
Kusan 11pm Ameera ta kasa bacci sai latse-latsen wayarta take.
Wani irin zabura tayi jin ringing d'in wayan saura kiris ya tsub'uce a hannunta.
Tsayawa tayi tana kallo kaman ba karta d'auka.
Saida ya kusan tsinkewa sannan ta d'aga cikin sanyin muryarta tace " Assalamu alaikum".
Wani irin sanyine ya ziyarci shi wanda ya haddasa mishi sauke ajiyan zuciya har tana jiwo shi ta cikin wayan.
"Wa alaikis salam my prety,me kike yi har yanzu bakiyi bacci ba?"
" na fara bacci ringing wayan ya tashe ni "
A rud'e yace " Ya Salam i'm soo sorry pls ki koma baccinki kinji?"
Dariyama ya bata ganing yanda ya wani rud'e dan tace tana bacci ne ya tashe ta.
Jikin shine ya mutu murus jin dariyarta kunnen shi,how he wish a gaban shi tayi baisan halin da zai shiga ba bcos yarinyan nan komai nata daban yake.
Shi baisan wani irin so yakewa yarinyan nan ba dan abinda yake ji akanta bai tab'a jin ko quatern haka akan matar shi Lateefa ba balle wata macen.
"Wasa fa nake maka banyi bacci ba " ya sake jin muryanta ta katse mishi zancen zuci da yake."keko hmmmmm' ina Fateema?"
"Gata nan tana bacci"ta bashi amsa.
"Ameera...."ya k'irata da wani irin murya da baisan yana da ita ba.
Da k'yar Ameera ta iya amsawa da ummm dan bakin ta yayi mata nauyi jin yanda ya kira sunanta for d first time kuma in a in a special way.
"Bansan ta ina zan fara ba prety but all i knw is dat i totaly fall 4 u since d day met.shiyasa na kasa hak'uri har nazo wajan Abba da fargaban ko anyi miki miji,sai dai Alhamdullilah Abba ta tabbatar min da bai bada ke.so its only me in d field kenan?"
Shiru tayi mishi ba tare da tayi magana ba,but murmushine k'wance a fuskanta.
" y re u silent prety bani amsa mana ko sai nazo da kaina zaki bani amsan?"
A hankali ta bashi amsa da " eh".
" ok gani nan zuwa yanzu".
Cikin sauri ta katse shi da cewa " kasan karfe nawa ne yanzu?"
" koma karfe nawa ne i don't care dole inzo inji amsata bcos i can't wait till morning dan kona k'wanta bazan iya bacci ba".
'Yar dariya tayi tace " yi hak'uri ba sai kazo ba".
"Then" yace yana d'aga gira 1 kaman yana gabanta.
Still shiru tayi tana murmushi.
Canza topic d'in yayi na yanda zata saki jiki suyi hira.
" kina j.s.s 2 ko 3 a secondry school?"
Dariya tayi.dan tambayan dariya y ya bata
"Oh na d'ebo dayawa ko"
" na gama dis year ko Fateema tana s.s 2".ta bashi amsa tana dariya.
" woah ashe da babban yarinya nake magana wat abt islamiya?"ya kara jeho mata da tambaya.
" hmmm mun kusa had'a haddan mu "
" afuwan yaah mu'allima" yace yana sassauta murya.
Nan ma dariya ta rink'ayi,kaman wasa sai gashi cikin dabara ya sa ta saki jiki suka sha hiran su har kusan 1:30am sannan ya hak'ura ya k'yaleta dan tayi bacci ba dan ya gaji ba.
Yana ajiye wayan ya kalli wall clock dake manne a jikin bangon d'akin,tsiririn tsaki yaja a ranshi yana mita kana da