Showing 30001 words to 33000 words out of 62823 words
Chapter 11 - UKUBAR KISHIYATA Sirrin Da Ya Rushe Aure by Ummee Yusuf
know i dont like it,just hold on gani nan zuwa" yana fad'an haka ya kashe wayan ba tare da ya jira amsan Al'ameen d'in ba.
Duk da abinda yake ji a jikin shi amma bai hana shi murmusawa ba saboda yanda yayunshi suke ji dashi.
Yana ajiye waya Lateefa ta shigo cikin k'walliyarta kaman mdi zuwa dinner sai baza kamshi take.
Turus tayiganin Al'ameen still cikin bargo,k'arasowa tayi gaban gadon tana " my Ameen lafiya kuwa har yanzu baka tashi ba ?"
" fever ce take son kamani "yace mata lokacin da take zama kusa dashi.
Tashi tayi da sauri dan d'auko mishi magani ya dakatar da ita ta hanyan cewa "ya Sa'ad is on d way".
Gaba d'aya ranta taji ya b'aci jin cewa Sa'ad zai shigo mata gida dan ita tun kamin auren su da taji ya kushe ta take jin haushin shi amma kuma koda wasa bata iya nunawa a gaban shi sabida duk rashin mututuncinta shakkan shi take.
"Okay " kawai tace ta fice zuwa kasa ta sami Ameera tana goge-goge tana layi kaman zata fad'i.
"Keee" ta daka mata tsawa,a razane Ameera ta juyo tare da durkusawa k'asa tace..." Aunty ina k'wana".
A wulakance take dubanta tace" ke rik'e gaisuwarki kuma ki tattara ki wuce part d'inki nd kada ki kuskura ki fito sai na neme ki".
Amsawa tayi da "toh" ta tashi ta wuce part d'inta tana godewa Allah cos atleast zata samu hutu koda kad'an ne kamin su nemetan.
Wasu masu aiki ta kira suka cigaba da hidimomin gidan.
Cikin 20mins Ya Sa'ad ya k'araso gidan hankali tashe.
Sai da ya duba shi hankalin shi ya d'an k'wanta ganin cewa stress ne ya mishi yawa.
Sama- sama suka gaisa da Lateefa,ya kama hanyan fita Lateefa har ajiyan zuciya ta saki na samun relief.
Har ya kai bakin k'ofan fita ya dakata tare da juyowa yace..." bros ina amaryarka ne ban ganta ba? Ina ganin sau 1 na ganta lokacin da muka had'u da ku a gidan Hajiya har kamin alkawari zaku je mana yini muka ji shiru da alama rowanta kake" ya k'arasa cikin zolaya yana dariya.
Lateefa ji tayi kaman ta shak'e shi ya mutu.
Bata gama kulewa bama saida ta tsinci muryan shi yana ce mata " uwar gida kirawo min kanwar taki pls".
Bata da bakin musu haka ta fita tana tsine mishi albarka.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
πββπββπββπββπββπββ
*~UKUBAR KISHIYATA~*
ππππππ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπ«π«π«~*
*~βWe beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part twenty eight*
A main palour suka yada zango anata hira da raha,Hajiya tasa 'yar aikinta ta gyarawa Ameera d'akin da zata zauna,cikin k'ank'anin lokaci ta gyara yayi fes.
Nan Hajiya ta umarce ta shiga ta k'wanta ta huta.
Bayan ta shiga Hajiya ta dube su tace..." ina son maganan nan a rufe shi anan ya zama tsakaninmu kad'ai zai tsaya,kaima Al'ameen ban yarda ka fad'awa matarka ba ka bari in lokaci yayi ta gani ina fatan kun fahimta ?"
Duk amsawa sukayi da "eh sun fahimta kuma zasu kiyaye,a haka taro ya watse duk suka tafi gidajen su amma banda Al'ameen da ya mak'ale yaki tafiya.
Yana ganin Hajiya ta shiga bedroom d'inta ya sulale yabi Ameera d'akinta.
Yana shiga ya maida k'ofan ya rufe,a tsaye ya sameta fitowanta kenan daga wanka.
Zuwa wajanta ya farayi idonshi akanta yana murmushi,yana k'arasowa ya jawota jikinshi ya rungume yana mata godiya.
Had'e bakinsu yayi ya fara kissing d'inta har suka fad'a kan gado,sun dad'e a haka sannan ya sake ta ya d'ora kanta akan kirginshi yana shafata a hankali yace...",Babyna ranan da kika haifa min abinda yake cikinki bansan yanda zanyi ba dan farinciki da zanyi ba zai misaltu ba".
Ita dai murmushi kawai take ta rasa bakin magana,saboda yanda taga duk sun rikice gaba d'aya saboda cikin dake jikinta toh ranan da d'an ya fito kuma fa?
K'ara narkewa tayi a jikinshi cikin shagwab'a tace..." yayana yunwa nake ji amma fresh milk nake so mai sanyi"
Kwatar da ita yayi akan gadon ya tashi yana " bari in dubo miki yanzu amma ya kamata kici wani abu saboda Ya Sa'ad yace kar a barki da yunwa".
" ni dai koma menene ka had'o da fresh milk"tace tana gyara k'wanciyarta.
Yana fita direct bedroom d'in Hajiya ya nufa lokacin tana shirin shiga wanka,ganin d'an autan nata yasa ta dakata tana dubansa.
Yana shafa k'eya yace..."Hajiya me za'a samu ne a gidan?Ameera ce take jin yunwa".
Fasa shiga wankan tayi ta dawo da baya tace..." yanzu nake shirin insa Altine ta kai mata abinci,ko akwai abinda tace tana son ci?"
" komai ma zata iya ci sai dai wai a had'a mata da fresh milk" ya bata amsa.
Girgiza kai Hajiya tayi tace..." banyi zaton akwai fresh milk a gidan nan ba,kayi maza kaje ka sayo mata ni kuma zan sama mata abinda zataci da kaina".
"Toh" yace ya fita da saurinshi zuwa wani mall dake kusa da gidansu,caton 6 na fresh milk ya siyo ya dawo gida ya samu Hajiya tayi mata peppe soup na hanta da k'oda yaji kayan kamshi da yaji yanda mai ciki zata ji dad'in ci.
Mai wankinsu Hajiya shi mallam tukur shi ya rink'a shigowa da kayan da Al'ameen ya sayo.
Hajiya baki bud'e ta kallon catons na fresh milk d'in tace..." lalle Al'ameen d'aukin ne haka?ina mutum d'aya zai iya shanye wannan kayan duka?"
Murmushi yayi yana sosa kai yace.."Hajiya aina zata tana bukatarsu dayawa ne".
Dariya tayi tace..." hmmmm kai dai ka sani,yanzu ka bud'e 1 ka zuba a frdge daga nan kuma ga abincin can ka d'auka ka kai mata d'aki,kasan bata da lafiya kuma tunda cikin baiyi k'wari ba,bai kamata ace tana yawan zirga-zirga ba".
Amsawa mata yayi sannan ya d'auki trayn abincn ya wuce d'akin ya sameta tana bacci abinta hankali k'wance.
Ajiye kayan yayi a hankali ya fita zuwa masallaci dan gabatar da sallahn la'asar.
Bayan ya idar da sallah ya dawo cikin gida tare da mahaifin shi,wajan frdge ya ya nufa ya bud'e ya d'auko k'wali 2 na fresh milk ya wuce d'akin Ameera dasu a hannu.
Akan sallaya ya sameta ta tana sallah itama.
K'arasawa yayi ya zauna a bakin gado yana jiran ta idar.
Bayan ta sallame ta dube shi tace..." Yayana baka je office ba yau?"
Jawota yayi ta fad'a jikinshi yace..." Babyna yau ba zancen zuwa office,ga babban office anan ".
Murmushi tayi kawai ba tare da tace komai ba l.
Saukowa yayi ya zuba mata peppe soup d'in a plate sannan yace..." Bismillah ga abinci harda fresh milk da kika bukata".
Zamowa tayi itama ta zauna kusa dashi,sosai taci peppe soup d'in tana ta santi shi kuma yana zaune yana kallonta har saida ya tabbatar ta k'oshi sannan shima ya ci kad'an.
Dariyarta yake yanda take shan fresh milk d'in har tana lumshe ido saboda santi.
Tana k'wance a cinyanshi suna ta hira abinsu har 5pm.
Knocking suka ji daga bakin k'ofa Ameera tayi saurin tashi daga jikin shi Al'ameen ya bada izinin shigowa.
Hajiyace ta shigo ta dubi Al'ameen tace..." ka manta ne da tafiya gida yau?"
"ban manta ba Hajiya" yace yana sosa kai.
" tunda baka manta ba tashi ka tafi gida gashi har 5 ta gota".
Agogon azurfa dake d'aure hannunshi yayi saurin dubawa yana cewa..." dama haka lokaci ya tafi ban sani ba?"
" mu da bama son matarka ta gane in har kana zuwa ka dad'e haka zata iya sa zargin wani abu a ranta kuma bana so kazo ka takura min ita dan ta huta na dawo da ita gidan nan dan haka tashi ka wuce".
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
πββπββπββπββπββπββ
*~UKUBAR KISHIYATA~*
ππππππ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπ«π«π«~*
*~βWe beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part twenty seven*
A parlour ta Tatar da Ameera a baje a k'asa har ta fara bacci wai dad'in sanyin tiles d'in take ji.
K'afa tasa ta haure ta maimakon ta tashe ta,a firgice ta farka tana raba ido.
K'ara rud'ewa tayi ganin Lateefa akanta tana aika mata da muguwar harara.
Jiki na rawa ta durkusa ta fara bata hak'uri a zatonta tayi bacci mai nisa ne sosai har tayi laifi Dan bata manta maruka da tasha ba jiya.
A wulakance ta d'aga mata hannu tace..." Keep quite idiot, me kika min da zaki ban hak'uri?ki wuce muje part d'in my Ameen Ku gaisa da yayan shi"
Kamin Ameera ta samu bakin bata amsa taji an murd'e mata kunne da karfin tsiya sannan tace mata.." Saura kiyi misbehaving da zaki nuna halinki na jakuna a wajan,hmmmm kema kinsan sauran ba saina bata bakina ba".
Tana fad'an haka ta dugure mata kai tayi gaba abinta.
Da sauri ta mik'e tana gyara zaman hijabinta tabi bayanta tare da shafa kunnenta daya sha murd'a.
Sun same su suna tsakiyar hira da dariya shida d'an uwan shi,Ameera tayi sallama ta durkusa daga bakin k'ofa tana gaishe shi.yayin da Lateefa ta wuce ba tare da sallama ba ta zauna a bakin gado tayi crossing legs d'in tana kad'asu.
Ya Sa'ad Yana amsa gaisuwan tare observing d'in yanayinta a matsayin shi na doctor.
Al'ameen yana daga k'wance yana kallonta ba bakin magana amma ji yake kaman yaje ya rungumeta ya tambaye ya jikinta.
Suna gama gaisawa bata wani tsaya b'ata lokaci ba ta mik'e dan komawa part d'inta saboda ta kiyaye gargad'in da akayi mata.
Tana tashi jiri ya kwashe ta sakamakon zafin zazzab'in dake dake jikinta ga cikinta tun jiya baiga k'wayar hatsi ba,saurin dafa bango da tayi shi ya hanata fad'uwa.
"Subhanallah ba dai kema baki da lafiyan ba ya barki a gida?"ya Sa'ad ya tambsya Yana aikawa Al'ameen mugun kallo.
Sadda kai k'asa yayi ganin Lateefa nayi mishi kallon warning ta k'asan ido.
Ameera batace komai ba saima kokarin barin d'akin da tacigaba dayi.
Dakatar da ita yayi da sauri ganin da gaske fitan zatayi.yace..." Wai meyasa kake Al'ameen? In kai Baka son hospital meyasa zaka bar iyalinka cikin irin wannan hali".
Tsaki yaja yana mai mik'ewa yacewa Ameera da take tsaye waje 1 ta kasa gaba
ta kasa baya " muje hospital in duba ki i can't tolarate dis".
Yana fita Ameera bata tsaya bata lokaci ba ta mara masa saboda itama tana bukatar ganin doctorn.
Yana zuwa bakin motan shi ya bud'e mata back seat ta shiga ta zauna ya rufe sannan ya zagayo ya bud'e driver seat ya zauna ya juya ya kalli k'ofan palourn yaga da gaske Al'ameen bashida niyan biyosu dan haka ya ciro wayarshi ya danna mishi k'ira a lokacin Lateefa tana zaune agefen shi tana mitan halin Ya Sa'ad kiran ya shigo wayarshi.
Bai kulata ba ya d'aga wayan yasa a kunnen shi,kamin yayi magana yaji muryan yayanshi yana cewa.."fito muu tafi tare dan kaima ban gama da kaiba" yana gama fad'an haka ya katse k'iran tare da maida hankalin shi hanyan fitowa daga palourn.
Ajiye wayan Al'ameen yayi tare da mik'ewa daga kan gadon,da ido Lateefa tabi shi har zuwa bakin closet d'inshi ya cire rigan baccin shi ya zura jallabiya milk colour akan wandon rigan baccin shi.
Dawowa yayi bakin gado ya k'washe phones d'in shi yayi hanyar fita ba tare da yace mata cikanki ba.
Da gudu Lateefa ta tari gabanshi tana aika mishi mugun kallo tace..." ina zuwa haka mallam?"
" Ya Sa'ad ne yake k'irana" ya bata amsa yana murmushi saboda yasan ba yanda ta iya dashi.
Wucewa yayi abinshi ya barta nan tsaye cike da tashin hankalin me zai faru in suka fita tare.
Cike da farinciki Al'ameen ya fito kasancewar zuciyarshi ta k'wad'aitu da zuwa amma tsoro ya hana shi Allah ya kawo mishi hanya cikin sauki.
Front seat ya bud'e ya shiga,Ya Sa'ad yaja mota suka bar gidan.
Lateefa tana jin tashin motansu tayi bedroom d'inta cikin matukar tashin hankali ta k'ira Aina'u.
Ringing 2 yayi ta d'aga tana " Hajiya a gidan Al'ameen ya akayine da sassafen nan?"
"Aina'u ba lafiya wannan yayanshi mara mutuncin yana son rusa min aikina".
Wani yayan shi kuma?" Aina'u ta tambaya.
Nan Lateefa ta k'washe abinda ya faru ta fad'a mata sannan ta d'ora da cewa.." pls besty ina son yanzu kije gun boka ya rufe musu baki kar su iya furtawa kowa abinda yake faruwa,yanzu zan miki transfer ta acc d'inki".
"Toh " tace tare da tabbatar mata da samun nasara sannan sukayi hanging.
A hospital kuwa suna zuwa ya Sa'ad ya bata gado tare da jona mata drip wanda ya had'ata da alluran bacci a private room da yake duba familynsu kawai sannan ya fara dubata.
Jininta ya d'eba ya bayar aje lab a g'wada yanzu-yanzu sannan ya fita a d'akin ya barsu.
Al'ameen jawo kujeran roba dake gefe yayi zuwa gaban gadon ya zauna ya kallon yanda fuskarta tayi fayau ya k'ara haske tana bacci.
Jikinshi yayi sanyi sosai ganin yanda Ya Sa'ad ya share shi tun a mota har zuwa yanzu,yasan fushi da yayi ba karami bane kasancewar shi baya fushi da wuri.
Toh shi ya zaiyi ya fahimtar dashi ba laifinshi bane?
Tsam ya mik'e da niyan zuwa office d'inshi dan ya gaya mishi halin da suka tsincin kansu shida Ameerar shi a ciki ko zasu samu mafita.a bakin k'ofa suka had'u dashi yana shigowa da wata peper a hannunshi fuskarshi kuwa kaman gonan auduga babu sauran fushin nan da ya fita dashi.
Kallon mamaki Al'ameen ya bishi dashi har ya manta abinda yayi niyan gaya mishi.
Hannunshi Ya Sa'ad ya rik'o suka dawo cikin d'akin har bakin gadon da Ameera take bacci,shi dai Al'ameen da ido yabishi yana neman karin bayani.
Huggin d'inshi yayi yana furta " alhamdullilah!!!."
Mik'awa Al'ameen papern yayi yana dariya wanda rabon Al'ameen da yaga yayi irinta har ya manta,kasancewar shi ba ma'abocin yin dariya bane sai dai murmushi.
Karanta result d'in yayi amma kwata-kwata bai fahinci me yake nufi ba,idon shi inba gizo yake ba pregnany test ya gani kuma da sunan Ameera akai.
D'agowa yayi yana kallon yayan nashi tare da neman karin bayani.
"Yes bro ur wife is 2 months pregnant"ya kara tabbatar mishi.
Wani yanayin da bai tab'a tsintan kanshi a ciki ba ba yau yake ji.
Hawaye ne yake zuba a idonshi bakin shi yana motsi alamun yaΓ±a son yin magana amma ya kasa fidda sauti ko kad'an.
Rungume Ya Sa'ad yayi yana hawayen farinciki,ashe shima yana da rabon ganin k'wanshi a duniya.
Da k'yar Ya Sa'ad ya fitar dashi daga d'akin dan yana kokarin katsewa Ameera bacci wajan murna.
Office d'inshi ya kaishi ya zaunar dashi sannan ya k'ira iyayensu yayi musu albishir na samun jika daga d'an autansu,daga nan kuma ya cigaba da kiran sauran 'yan uwansu suma ya sanar dasu duk cike farinciki suka ce gasu nan zuwa.
Cikin k'ankanin lokaci suka cika hospital d'in anata taya juna murna kaman riga da anyi haihuwar.
Ameera bata san wainar da ake toyawa tana ta baccinta,sai bayan sallahn azahar ta farka daga baccin.
Har rige-rigen yi mata sannu suke duk sai taji kunya ya rufe ta ganin harda Hajiyar Al'ameen a ciki.
Bayan tayi wanka tayi sallah,tea mai kauri Hajiya ta had'a mata tare da peppe soup na naman rago zallah sannan ta zo ta zauna a gefenta ta fara bata amma Ameera ta kasa sakewa taci abin kirki.
Ganin haka yasa Hajiya tace duk su fita a barta ta samu taci abinci,ba musu duk suka fice tare da ja musu k'ofa.
Al'ameen kaman jira yake suna fita ya taso da sassarfa ya rungumeta yana sauke ajiyan zuciya,ture shi Ameera ta fara tana cewa..." haba yayana ka bari mana kar wani ya shigo ya ganmu a haka".
Ba tare da ya sake ta ba yace..." let me feel u Ameera yau ina cikin farinciki wanda ban tab'a tsintan kaina a ciki ba, bani kad'ai ba all my family re happy because of u".
D'ago kanta tayi tana kallonshi taga idonshi duk yayi ja alamun hawaye zai iya saukowa at anytime.
" ni kuma me nayi haka?"ta tambaya idonta itama yana cikowa da hawaye.
Result d'in da yake rik'e dashi a hannu tun d'azu ya mik'o mata,karb'a tayi ta fara karantawa ai bata gama karantawa ba tayi jifa dashi ta rufe bakinta da hannunta na dama hannunta na hagu kuma tana yarfe shi tace..." na shiga 3 yanzu dukkansu sun sani?"
Dariya ma ta bashi ganin yanda yarintarta ya fito a fili,maimakon yayi dariya yab'ata fuska yace..." kinga kuwa kowa ya sani har Hajiya saida tayi fad'a".
Waro ido idonta tayi gaba d'aya tana kallonshi cikin tashin hankali can kuma ta fashe da kuka tana " wallahi ni ba zan zauna anan ba tafiyata zanyi".
Kunshe dariyarshi yayi yace.." ki tafi ina? Ai kina tafiya kuma ace kinyi rashin kunya".
Yarfe hannu ta cigaba dayi tana.." wayyo toh ya zanyi wai?"
Haka ya rink'a zolayarta tana k'ara rud'ewa da k'yar ya. rarrasheta tayi shiru ,yace mata wasa yake mata tare suka ci abincin suna hirarsu cike da nishad'i.
Bayan sun gama yana tattare wajan su Hajiya suka shigo suna k'ara mata ya jiki,ita kuma ji take kaman ta nutse k'asa saboda kunya.
Ya Sa'ad ne yace..." Alhamdullilah jikinta kam yanzu da sauki zan sallame ta amma ba zan yarda Al'ameen ya tafi da ita gida ba saboda bashida kula zan kaita gidana incigaba da kula da ita har cikin yayi k'wari sannan zan yarda ta koma gidanta".
Hajiya tayi caraf tace..." ban yarda da wannan idean ba, ni zan tafi da ita ta zauna a karkashin kulawata sai dai kullum ka rinka zuwa gida kana duba min ita".
Nan yace "shikenan Hajiya ai duk 1ne".
Al'ameen yana jinsu baisa baki ba amma zuciyarshi fari kal jin cewa ba zata koma cikin *UKUBAR* Lateefa ba kuma yana ganin k'ila su samu solution d'in matsalarsu kamin ta samu lafiya.
Cikin 'yan mintina suka harhad'a kayansu sukayi gidansu Al'ameen.
Alhamdullilah naji sauki sosai kuma ina mika gdy ta tare da jinjina ku my fans ,ina yinku irin sosai din na
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: πββπββπββπββπββπββ
*~UKUBAR KISHIYATA~*
ππππππ
(Its all about love and betrayal)
Story by ~UMMEE YUSUF~
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION~*β¨β¨β¨
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπ«π«π«~*
*~βWe beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*part thirty*
Ameera suna shiga d'akin,d'an k'aramin fridge dake gefen gadon ta nufa ta bud'e ta d'auki fresh