Showing 24001 words to 27000 words out of 62823 words

Chapter 9 - UKUBAR KISHIYATA Sirrin Da Ya Rushe Aure by Ummee Yusuf

29 Jul 2026

32

ta tashi hankalinta kullum cikin tunanin ya za'ayi ta zubawa Ameera magani take,k'watsam rannan suna zaune da kannen ta a palour suna kallo wata dabara ta fad'o mata.

Cikin sauri ta juyo wajansu tace....
"ke fa'iza ina son kuje kifito min da 'yar iskan can da my Ameen ya ajiye a can part d'in yanzu amma fa cikin dabara ". ta k'arasa maganan tana duba lek'en part d'in Ameera.

Shamsiya ta ajiye remote d'in hannunta sannan tace..."dats great Aunty dama ni kullum mamaki kike bani da kika k'yaleta ta samu k'wanciyar hankali a gidan nan,yanzu kuwa zakiga aiki da cikawa,taso muje Fa'iza".

Shamsiya tayi gaba Fa'iza tana binta a baya har bak'in k'ofan palourn Ameera,knocking sukayi har su biyu sannan suka ji ta amsa da" da waye ne ? ina zuwa".


Sanye take cikin wata black abaya tayi rolling da veil d'in kayan,sosai yayi mata k'yau kuma ya kara fito mata da haskenta. tana tunanin waye haka by dis time? tasan dai ba mijin ta bane dan shi yana da key a wajen shi ko yazo sai dai ya bud'e ya shigo.

Har ta k'araso k'ofan bata daina zancen zucin ba.


Bakin fuska ta gani bayan ta bud'e k'ofan.

Fa'iza da Shamsiya baki da hanci suka sake suna kallonta dan basuyi especting zasu ganta haka ba.


"Sanun ku da zuwa, tace ganin basu da niyan maga saina mujiya da suka zuba mata.

Shamsiya ce tayi karfin halin cewa..." uhummm amarya dama mun zone dan mu gaishiki".

Fara'anta fuskantata ne ya fad'ad'a, ta d'an matsa ta basu hanya, sannan tace " ku shigo mana ya kuka tsaya a waje".

Shigowa sukayi suna k'arewa palourn ta kallo cos ba karya ya burge su.

Saida suka zauna sanna Fa'iza tace.." nasan baki samu ba ko?"

Murmushi tayi tana wasa da yatsin hannunta tace.." eh gaskiya ban gane ku ba".

Tab'e baki Fa'iza tayi tana gyara zama sannan tace.." muna cikin gida 1 amma bamu san juna ba,toh mu k'annen Aunty Lateefa ne ganin har kinfi wata a gidan bamu sanki ba shiyasa muka zo dan mu gaisa".

Shamsiyya ta karb'e da " ina zamu ganta kullum tana cikin part d'inta a kulle".

Dariya Ameera tayi tana " wallahi ba haka bane,kinsan in kana bak'o sai a hankali".

" eh hakane kam amma tunda mun biyo ki yanzu kin wuce bak'uwa,sai ki saki jiki damu mu saba ayi zaman tare kema zaki fi jin dad'in gidan".

Cikin jin dad'i Ameera tace...hakane kuma nagoda da zumuncin,let me get u something to drink".

Rik'eta Fa'iza tayi tana " noo da kin barshi kawai ".

B'ata fuska Ameera tayi tace.." haba mana ya haka kuma,ku da kuka ce in saki jiki daku mun zama d'aya shine za kuce ba zaku ci abincina ba?"ta karasa cikin shagwab'a.

Kallon sha'awa Fa'iza take binta dashi,can ta daure tace..." is ok ba sai kinyi mana kuka ba je ki kawo mana koma menene zamu ci kinji".

Tana dariya tayi hanyan kitchen still idon Fa'iza na kanta.

Mari Shamsiyya ta zuba mata a cinya sannan ta dawo hayyacinta,ta juyo tana kallon yayarta spechless.

" come back to ur sence Fa'iza nd stop stairing at dat bitch"Shamsiyya tace tana hararnta cike da kishi.

Yawu ta had'iye tana kallon Shamsiyya still bakinta ya kasa furta komai.

" karki soma nagetive tinking akan yarinyan nan saboda dalili 2,first ina son ki tuna wacece ita nd 2 kuma zaki iya samu a wani hali bcos u re not sure she will accept u or not.pls Baby think twice b4 doing something" Shamsiyya tace mata tana shafa mata gefen fuska.

Ajiyan zuciya ta sauke tare da kamo hannun Shamsiyya ta rike tace " tnx da kika tunatar dani if not i have done something rubbish" ta k'arasa da dariya but deep down her bata hak'ura ba kuma ta tabbatarwa kanta she will surely have her one day.

Suna cikin dariyan Ameera ta iso d'auke da katon tray ta cika shi da kayan ciye-ciye da drinks kala-kala ta ajiye a gabansu.

Sunfi 30 mins suna hira sannan suka ce mata zasu tafi.

B'ata fuska Ameera tayi tana " har zaku tafi,pls ku zauna mana muyi hira".

Da sauri Fa'iza ta d'auke kai cos in taga tana wannan shagwab'ar da ya zama al'adarta ji take kaman taje ta rungumeta.


" a'a in kina so ki fito muje main palour muyhiran acan,kinga sai mu k'ara sabawa ".

" ku bari zuwa gobe sai in fito muyi hiran acan" Ameera tace musu tana murmushi.

Fizgo hannun Fa'iza Shamsiyya tayi sukayi hanyan fita tana mita " muyi tafiyar mu Fa'iza dama ba wani bak'unta dama kawai bata son alaka damune take wani fakewa da bakunta" Fa'iza dai binta kawai take dan sosai take nadaman shigowanta part d'in nan.

Har sun kai bakin k'ofa tayi saurin dakatar dasu ta hanyan cewa " pls ku tsaya mu muje,dan Allah karkuyi fushi dani ba nufi na ba kenan".

Tsayawa sukayi suna murmushi tare da cewa " ko kefa".

Jerawa sukayi tare suka fito palourn suka zauna tare da cigaba da hiransu.

Shamsiyya ce rike da phone d'inta tana rubatawa Auntynta short msg kan cewa gasu nan a palourn sun fito da ita.

Cikin minti 1 reply d'in Lateefa ya shigo mata.


Mikewa tayi bayan ta karanta massage d'in tace..." ammm ina zuwa pls" sannan tayi hanyan part d'in Auntynsu.

A tsakiyan palournta ta same ta sai kaiwa da komowa take " gani Aunty" tace lokacin da iso gabanta ta tsaya.

" take dis ku tabbata kunsa mata shi a drink ta sha,pls try ur best my lovely sisters".tace mata pleadlly.

"Don't worry Aunty consider it done ".tace mata tana zuba maganin cikin wani drink dake cikin glass cup,ta zuba wasu glass 2 suka zama uku sai dai ta banbant zaman cups d'in sannan ta d'auki katon trayn ta fita zuwa palourn da ta barsu.

Ameera da Fa'iza sunan zaune a inda ta barsu suna ta kwasan dariya.

Dire trayn tayi akan center table na glass dake tsakiyan palourn sannan ta jawo shi gaban su.

" wai hiran me kuke ne?naga kuna ta kwasar dariya haka?"tace lokacin da take zama.

"Labarin k'wawarki Aisha nake bata,yanda tasha k'asa a gaban saurayinta"Fa'za tace tana dariya.

Dariya Shamsiyya tayi sannan ta d'auko drink mai ta mikawa Ameeera tace " toh ya isa ga drink nan kowa ya ya sha dan muji dad'in hira".


Ba tare da tunanin komai ba Ameera ta karba,suma suka d'auka suka fara sha suna hira.

Sun gama sha kaman da minti 10 Ameera ta fara jin dizzness ko bud'e ido dak'yar take yi can kuma ta yanki jiki ta fad'i kan kujeran da take Zaune ta kama bacci kaman matatciya.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€


*~UKUBAR KISHIYATA~*

😭😭😭😭😭😭


(Its all about love and betrayal)


Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)



*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«πŸ’«~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*



*part twenty two*


Zuba mata ido sukayi dukan su 2 kowacce da abinda take tsak'awa a ranta.

Dawo da dubanta Fa'iza tayi kan yayarta fuska d'auke da damuwa tace..." sis me kika bata ne a cikin drink d'in nan tasha har ya jefata cikin wannan halin?"

Fuska cike da fara'a Shamsiyya ta amsa mata da cewa..." ni ba abinda na saka mata,hasalima Aunty ce ta bani tace mu bata tasha.i don't know her mission amma let me call her"ta k'arasa zancen tare da dannawa Lateefa k'ira nan da nan ta fad'a mata halin da Ameera take ciki,cike da zumud'i tace gata nan fitowa.

Cinkin abinda baifi minti 2 ba sai gata ta fad'o cikin palourn kaman an jefota.

Sauri- sauri gudu-gudu ta k'araso hannunta na dama rik'e da tsurkullen da boka ya bata hannunta na hagu kuma rik'e da rigan Al'ameen ta k'araso wajansu tana" ke Shamsiyya zo ki raka ni ke kuma Fa'iza ki zauna da ita kamin mu fito"

Ta nufi part d'in Ameera ba tare da ta jira amsarsu ba Shamsiyya ta mara mata baya suka bar Fa'iza da taradaddin kar Allah ya basu sa'an cutar da ita dan yanzu ita tausayi take bata.

Suna shiga part d'in direct bedroom d'inta suka wuce,wani riganta na atanfm Lateefa ta binciko a cikin sip d'inta ta had'a da rigan Al'ameen ta nannad'e kaya tsafin boka dasu, Shamsiyya ta taya ta suka d'aga gadon suka tura kayan karkashin gadon sannan suka gyara komai kaman ba abinda ya faru suka fito palour.

Ameera saida ta k'washi gud 4 hrs tana bacci sannan ta farka.cikin baccin da tayi boka yayi nasaran yin aikin shi a kanta sannan ya turo wata aljana da zata zauna a jikinta ta hana ta addu'oin da take saboda kar aikinsu ya lalace.

Da ido kawai take binsu d'aya bayan d'aya ta kasa tantance wani hali take ciki har idonta ya sauka kan Lateefa da itama idon ta zuba mata dan taga reaciton d'inta.

Wani irin bugawa taji zuciyarta yayi kaman ya fad'o k'asa.

A take taji wani irin tsoron Lateefa na ratsa duk jinin jikinta,a yanda take ji a yanzu komai ta saka ta ΕΊata iyayi.

Tsawa Lateefa ta daka mata tana " wace irin mayya ce ke da zaki zo ki tsare mutane da ido kaman na mujiya?"

Murya na rawa tace" Aunty kiyi hak'uri ba kallon ku nake ba".

Wani malalacin murmushi tayi ganin tarkonta ya kama tsuntsu duk da dama ta yarda da aikin bokanta,yanzu saura Al'ameen take jira shima yazo taga yanda zaiyi.

Hada rai tayi tace " oya tashi kije ki d'aura mana dinner"

Sunkuyar da kai tayi k'asa zuciyarta na k'ara speed tace..." me zan dafa Aunty?"

Tsawa ta k'ara daka mata cike da masifa tace..." ke dak'ik'iyar inace ina baki comand kina min tambayoyi...?

Shamsiyya ce tayi caraf tace..." ai dole ta tambaya Aunty ba'a saba cin mai maik'o ba a gida,so gwara ki bata order kar aje ayi mana k'wamacala".

Gyara zama tayi tana wani huhhura hanci a garance tace..." je kiyi mana tuwon shinkafa miyan taushe sannan kiyi peppe soup d'in d'anyan kifi da fruit salad...kuma saura ayi sallahn magrib baki gama ba kiga yanda zanci ubanki a gidan nan".

Jiki na b'ari ta mik'e cikin sauri kaman zata kifa ta fara laluben babban kitchen d'in gidan kasancewar tunda aka kawota gidan bata tab'a fita daga part d'inta ba.


Dariya Shamsiyya ta kwashe dashi tana " shikenan mun samu sabuwar 'yar aiki".

"K'yale ni dasu sai sun gane shayi ruwane,dole ta bauta min daga yau zan dakatar da masu aikin cikin gidan nan".

Fa'iza dai shiru tayi tana jin ba dad'i cikin zuciyarta saboda tausayinta.

Murmushine ya k'wace mata da ta tuna cewa itama zata iya amfani da wannan daman ta cimma burinta akanta.cikin jin dad'i itama ta shiga cikin hiran da suke.

Kujeran da ta gani guda d'aya a kitchen d'in Ameera ta zauna dafe da kirjinta da har yanzu bai bar bugawa ba,tana mamakin sudden change daya same ta.

Tasan tabbas tun farko tana tsoron Lateefa amma na yanzu na musamman ne tunda ko ido bata iya had'awa da ita balle tayi mata musu, gata harda sakata girki.

Cikin zuciyarta take cewa tasan Al'ameen yana zuwa zaiyi maganin abin yayi musu iyaka saboda ba zai yarda da wannan zaluncin ba.

Pls kuyi mange da wannan dan yau sau 3 ina typing yana gogewa.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€


*~UKUBAR KISHIYATA~*

😭😭😭😭😭😭


(Its all about love and betrayal)


Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)



*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«πŸ’«~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*



*part twenty three*


Tashi tayi ta fara girkin da aka sata,saboda kar lokaci da aka bata ya kure gashi kuma tayi warning d'inta.

Bata dad'e ba ta kammala girkin gaba d'aya gidan ya karad'e da kamshin girkinta.

Wani had'dd'en set d'in warmers ta d'auka ta zuzzuba abincin a ciki sannan ta k'washe su ta kai kan dinning ta jera su.

Dawowa tayi cikin kitchen ta zauna tana tunanin fita,ba dan komai take gudun fitan ba sai dan kar su had'u da Lateefa.

Gajiya tsyi da zama a kitchen d'in kuma tana son yin wanka kamim Al'ameen ya dawo daga wurin aiki,dole ta mik'e ta fita tana jan k'afa.

Suna nan zaune a inda ta barsu ga kayan ciye-ciye a gabansu suna ci suna hira,yawancin hiran akan samun nasararta akan Ameera ne.

Daga can nesa dasu ta tsaya kanta a kasa tace..." Aunty na gama ".

Juyowa sukayi suka zuba mata ido suna mamakin wai har ta gama girkin bayan har kala 2 ta bata dan kar ta gama da wuri ta samu abin ci mata mutunci,sai gashi harta gama.daga ita har k'annenta ba abinda suka iya a fannin kitchen kasancewar mamarsu ba ruwanta da sasu aiki in dai zasu fita su kawo mata kud'i toh bata da case da su.

Kallon up nd down Lateefa take mata,cikin tsawa ta fara matq magana..." waye sa'an ki anan da zaki zo ki tsaya a kan mu kina magana without any respect ,daga yau in har zaki min magana ki tabbatar kin rage tsawonki ".


A hankali ta kai guwowinta k'asa idonta tab da hawaye amma bata bari sun zubo ba.

Murna fal cikin zuciyarta tace.." je ki gyara min bedroom da toilet d'ina yanzun nan kuma as from today kece mai gyaran duk bedrooms da toilets na gidan nan".

Bata ce komai ba ta mik'e tayi hanyan part d'in Lateefa.

Tana b'ace musu Fa'iza ta mik'e itama tana d'an soshe-soshen rashin gaskiya tace..." ummm Aunty na bari in d'auko system na a bedroom d'inki ".

" ok kuma ki duba min ko wancan banzan tana min gyaran yanda ya kamata".

Cike da murnan samun nasara tayi hanyan part d'in da saurinta,Shamsiyya ta bita da ido saboda tadan karya take komai na bukatansu yana part d'insu.

Ameera tana tsakiya gyaran palour Fa'iza ta shigo da sauri ta kama hannun Ameera suka koma kan kujera suka zauna,ita dai Ameera zuciyarta sai dakan 3 yake dan bata san da wacce muguntar tazo mata ba.


Cikin k'wantar da murya tace..." kiyi hak'uri Ameera ban san me yake damun Aunty ba take miki haka amma nayi miki alkawari duk lokacin da kike neman taimako kizo wajena zan miki koma menene....kinji?"tace tana shafa gefen fuskanta .

Mik'ewa tayi tsaye kanta a k'asa tace " nagode da kulawarki Aunty bari in k'arasa sauran aikina".

Bedroom d'in Lateefa ta shiga tana mamakin Fa'iza duk da kalamanta sunyi mata dad'i amma tana da kokonto a kai ga wani shafa mata jiki da take shiyasa ma ta shi ta bar mata palourn dan banbarak'wai abin yazo mata.

Tsab ta gyara mata ko ina sannan ta fito palour zuciyarta na bugawa

Tana shigowa da tsawa Lateefa wai me ya fito da ita bayan tasa ta aiki.

" na gama Aunty shiyasa na fito"tace kanta a k'asa.

" sauran toilets d'in gidan wa zai wanke miki ?" ta tambaya tana banko mata harara.

Juyawa tayi ta koma ta hau sama zuwa part d'in Al'meen ta hau gyaran parlourn duk da dama ko ina a kintse yake,ta kama handle d'in kofan bedroom taji muryan Lateefa ta hayyako mata.....


"Ubanwa ya baki izinn shigowa part d'in mijina?"

Ameera duk ta rud'e murya na rawa tace...." kiyi hak'uri Aunty ke kika ce in wanke toilets na gidan man duka shiyasa na shigo amma dan Allah ki yafe min".

" tashi ki bani guri munfuka,sai ana magana ta rink'a wani sunne kai k'asa kaman mutuniyar k'warai".

Tsimi-tsimi ta fice zuwa nata part d'in ,direct bathroom ta wuce ta had'a ruwan zafi ta shiga ciki ta kwanta dan yanda take jin bayanta kaman zai balle saboda tunda tazo duniya bata tab'a aikatuwa irin na yau ba.

Alwalan magrib ta d'auro bayan ta gama wankan sannan ta fito tayi sallah,tana addu'an Allah yasa lafiya ganin har anyi sallah Al'ameen bai dawo ba.

Al'ameen driving yake a mota ya taso daga gidansu sakamakon amsa k'iran Alhajin shi da yayi bayan ya tashi a office, murmushi yake shi kad'ai saboda yana cike da farincikin zaiga sanyin idaniyan shi wato Ameera cos yayi missing d'inta sosai.dan haka duk ya k'osa yaga ya isa gida.

Yana zuwa mai gadi ya bud'e mishi gate ya shigo cikin gidan.

Ya dade a cikin motan sannan ya samu courage d'in fitwowa a ciki sakamakon yana shigowa haraban gidan yaji haka kawai gaban shi yana fad'uwa ga wata fargaba da mutuwar jiki da suka sauko mishi lokaci 1 wanda baisan dalili ba.

Da k'yar da jan k'afa yayayi sallama ya shigo palourn farko, bakowa nan ya k'arasa main palour anan ya tarar da Lateefa zaune tana sanar da rabi cewa ta dakatar dasu daga aikin.

A razane rabi ta d'ago da kai tana kallonta saboda tashin hankali ta rasa bakin magana cos tun Lateefa tana amarya suke tare har ya zamanto ta kasance leader.

Dariya Lateefa tayi tana " k'wantar da hankalinki ba na sallame ku bane hutu na baku saboda nasamu sabuwar 'yar aiki,ina son ku bar mata aikin tayi ita kad'ai na d'sn wani lokaci saboda ta saba".

Rabi zatayi magana taga shigowar Al'amee,ba shiri ta had'iye maganarta jiki na rawa tayi mishi sannu da zuwa ta fita ta basu waje.

Kallon inda yake Lateefa tayi dan bata san da shigowar shi ba,suna had'a ido yaji duk duniya ba wanda yake tsoro da shakka sama da ita.

Cike da dauriya yayi yak'e yace..." my Lateefa kina hutawa ne?"

Harara ta galla mishi tace..." kai meye haka daga zuwa zaka wani cika ni da sututu,haba Ameeenu" ta k'arasa da jan gajeran tsaki.

Sassauta murya yayi yace..."Allah huci zuciyarki my queen ".

Tashi tayi tana murmushin nasara ta k'araso gabanshi tare da kama hannun shi tace..." muje kayi wanka sannan kaci abinci ko?"

Bashida bakin magana bare musu,haka yabi bayanta kaman rak'umi da akala har cikin bedroom d'in shi.

Fitowa tayi bayan shigarshi wanka ta shiga k'wakawa Ameera k'ira, wacce zamanta kenan a gaban dreesing mirrow danyiwa angonta k'walliya amma jin muryan Lateefa yasa ta tashi jiki na b'ari ta zumbula hijabi ta fito palour.

Zubewa tayi a gaban Lateefa kai a k'asa tace..." gani Aunty".

Al'ameen yana sauk'owa daga stairs idonshi ya sauka kan Ameera da take durkushe gaban Lateefa tana masifance ta nan yaji zuciyar shi tana bugawa da sauri-sauri har ya k'araso wajansu.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€πŸ™†β€β™€


*~UKUBAR KISHIYATA~*

😭😭😭😭😭😭


(Its all about love and betrayal)


Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)



*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«πŸ’«~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login