Showing 9001 words to 12000 words out of 62823 words

Chapter 4 - UKUBAR KISHIYATA Sirrin Da Ya Rushe Aure by Ummee Yusuf

29 Jul 2026

30

saboda kariya.kuma yace kar suyi wasa da azkar na safe rana dare shima in mutum ya rik'e babban kariyace.

Godiya suka karayi mishi sannan suka bashi abin sadaka suka fito.

Yau Al'ameen ya dawo daga aiki da wuri,ya tarar da Latifa suna zaune a waiting palour tare da Salees da abokanen shi 2 suna hira.

Wani rirn bakin cikine ya tokare mishi zuciya.

Suna mishi sannu da zuwa amma ko kallonsu baiyi ba ya wuce part d'inshi a zuciye.

Zama yayi a bakin bed ya dafa kashi da hannaye 2,magana ya fara cikin bacin rai shi kaf'ai.

" i cant tolarete dis nonsence in my house,i have to do somting.wa yasan lokacin da ta d'auka ta tara min kartin banza a gida,sai kace ita kad'ai ce mai dangi......"

Ringing din wayarsa ce ta katse shi,ciro phone d'in yayi daga aljihu.sunan da ya gani yana yawo akan screen ya sa shi sauke ajiyan zuciya sannan yayi recieving.

" Salamu alaikum Hajiyata,barka da yamma".

" Lafiya lau Al'ameen ya gida,ya naji muryanka wani iri hop dai kana lafiya?" Hajiya ta tambaye shi cikin kulawa.

Tana ji cikin wayan yana sauke ajiyar zuciya wato yana kokarin calming kansa yace " Hajiya na gaji am fed about Latifa,gaskiya i cant take it any more.ace wai any time na shigo gida sai raina ya baci".

" nasan akwai ciwo amma fa dole ne ka danne zuciyarka for some time muga abinda Allah zaiyi karka manta Alhajin kuma ya bada goyon baya kan hakan so pls ban yarda ka kula taba.zan samu Alhajin inji me ya kamata kayi next,kaji ko?" cewar Hajiya.

" naji kuma insha Allah zan kiyaye " yace cikin sanyin murya.

" yauwa d'an albarka Allah ya tsare ka daga dukkan abin ki".

" Ameen Hajiya nagode sai anjima" yace tare da ajiye wayan.

Latifa tana can wajan su Salees,Al'ameen yana shigewa ciki abokansa suka mike jiki na rawa akan suzo su wuce dan basu san hukuncin da d'auka ba akan su.


Salees ya kalle su ya murmushi yace " kwantar dahankalin ku guys ba abinda zai faru".

Latifa kuwa dariya take sosai harda rik'e ciki tace " wai me ya tsorata ku haka?kun d'auka dan ya ganku ne yayi haka,ina ganin a office ne wani ya tab'a shi saboda haka kusha zaman ku".

D'ayan hanyan waje yayi yace " no lets get going tunda ya dawo,just kema ki bishi kar yayi suspecting wani abu".

Salees mik'ewa yayi yace " yeah hakane baby kije kawai mu zamu wuce sai munyi waya,but pls kisan yanda zakiyi yayi signig documents d'in".

" dont worry kai ma kasan wannan yafi komai sauki " tace tana tashi danyi masa good bye hug,a lokacin abokanen saless har sun tsufa a mota.

Da fara'anta ta shigo part d'in Al'ameen tana " waue ya tab'a min my Ameen ne ya shigo ba fara'a haka?"

D'an murmushi ya kakalo yace " bana jin dad'i ne kuma ga ciwon kai da nake ji".

" eyyah sorry let me get u drugs cikin first aid box".

Paracetamol ta ballo mishi guda 2 ta kawo had'e da bottle water.

Ba musu ya karba ya sha dan da gaske yake jin ciwon kan saboda bacin rai da suka saka shi.


Driving yake a hankali shi kad'ai a mota sakamakon ya aik8 drivern shi bai dawo da wuri ba,ya kama hanyan gida.

Yamma tayi lis a lokacin pass 5 ne,ya biyo ta tudun wada gun wani frnd d'insa da sukayi karatu tare a anguwan.

Kamin ya isa gidan abokin nashi ya hango wasu samari sun kai 6 sun sa wata yarinya a tsakiya,sai faman kuka ,rok'o da magiya take musu akan su bata hanya ta tafi amma sai wani dariyan mugunta suke mata.

Parking motan shi yayi ya fito ya nufi inda suke,a lokacin har har daya daga cikinsu ya kama hijabinta yana ja.

Uniform ne a jikinta na islamiya kuma hijabin har kasa.

Al'ameen yana zuwa yace musu " ya dai,me ta muku ne haka?ku bata hanya ta wuce mana".

1 ne ya juyo ya bashi amsa ga kayan maye a hannunsa yace " kai dallah ina ruwanka damu,ko kanwarkace?"

" eh kanwata ce ku kyaleta ta wuce"

Wani d'an dogon cikin su yace" nd so wat in karwar kace,yau sai mun tafi da ita dan rainin wayon nata yayi yawa".

Al'ameen ganin ba zasu saurare shi ba gashi kafa ya d'auke saboda irin tsukukun lungu ne.

Hannu yasa a aljihu ya kwaso duk kud'in dake ciki wanda shima baisan adadin suba ya mik'awa dogon yace " ga wannan ku sha ruwa da shi pls ku kyaleta ta tafi".

Kusan wawa suka dakawa hannun shi,suna ihun murna tare da jinjina mishi harda kirari.nan suka dubi yariyan da yanzu har ta durkushe a wajan tana kuka.

Wani mai katon kan cikin su yace mata " ke wallahi kinci arzikin oga,badan shiba da yau sai kin yabawa aya zakinta.kuzo muje yau akwai hawa network dan yau ni service zan hauma ba network ba".

Haka suka tafi suna ta iface-ifacen da suratansu har suka sha wani coner.

Al'ameeen zubawa yarinyan ido yayi for some seconds yajhna kallonta duk da ko tafin hannunta baya waje ko ina na jikinta a lullub'e suke sai shasshekar kukanta yake tashi.

Lumshe ido yayi ya bud'e yace " meye ya had'aki da wa'yan kuma?"

Cikin kukan ta bashi amsa tace " wallahi ban musu komai ba,sun ce in tsaya in saurare su dan.....da....."kuka yaci karfinta ra kasa karasawa.

" ya isa haka tashi in karasa dake gida saboda kar in tafi su kara dawo kinsan wa'yan nan ba hankali ne dasu ba".yace still idon shi kanta.


A sanyaye ta mik'e tsaye kanta a kas'a tana share hawaye,ganin haka shima ya juya ya nufi mota.

Bin bayansa tayi har zuwa inda yayi parking motan shi,bud'e mata front seat yayi ta shiga ta zauna.shima ya zagaya ya shiga yaja suka bar wajan.
Driving yake yana satan kallonta amma taki d'ago da kanta bare ya samu daman kallon fuskanta.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . 🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀

*~UKUBAR KISHIYATA~*

😭😭😭😭😭😭


( its all about love and betrayal)


Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)

✍✍✍✍✍✍✍
GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION
✍✍✍✍✍✍✍


*~part nine~*


Dai-dai wani rugujajjen tsohon gida tace ya tsaya,tsayawa yayi ya juyo gaba 1 ya zuba mata ido.

" Nagode Allah ya saka da alkhairi" tace a hankali kaman bata so kuma ba tare da ta d'ago ta kalle shi ba.

Kamin ya samu abin fad'a har ta bud'e murfin motan ta fita.

A sukuwane ya fito shima saboda yana da burin koda sunanta ne ya sani.

Wani wawan birik yaja ya tsaya ganin wani d'an dattijo ya fito daga gida da buta da tabarma a hannun shi.

D'an rusunawa tayi ta gaishe da tsohon sannan ta shige ciki, ganin yanayinta yasa tsohon kallon A'ameen cikin tuhuma yace " bawan Allah meye had'inka da 'yata har zaka d'auko ta a mota?"

Har kasa Al'ameen ya durkusa ya gaishe shi,a taikaice ya amsa yana jiran yaji amsan tambayan shi.

" Baba wallahi nima a hanya na samu wasu yara suna kokarin hi mata rashin mutunci,shine na tsaya na raba su kuma tsoron karsu k'ara biyota yasa na kawota gida". Yace cikin ladabi.

" toh-toh madallah d'an samari Allah yayi albarka nagode kaji?"wannan tsohon yace masa cikin jin dad'i.

Sallama yayi masa sannan ya shiga motan shi yayi gaba.shi kuma wannan tsohon ya shimfid'a tabarman shi tare da fara alwala.

Da sallama ta shiga cikin gida Umma tana ganinta ta bar kwashe tuwo da take a bakin murhu tace " AMIRA me ya same ki na ganki haka ga yanda idonki da fuakanki suka kumbura?"

Share gutun hawaye da ya gangaro mata tayi sannan tace " wallahi Umma wasu ne ina dawowa a hanya dan sunyi min magana naki kulasu shine suka tare min hanya da kyar wani bawan Allah ya shiga tsakanin mu suka barni.shine ma ya kawo ni har kofar gida dan karsu kara biyoni".

Umma tana tafa hannu tare da salati tace " kema Amira ba kya ji bance ki daina bin wannan layin ba,kuma daga yau kar in kara jin kin shiga motan wani dan duniyan nan yanzu ta zama abin tsoro".

" kiyi hak'uri Umma insha Allah zan kiyaye".Amira tace cikin maraicewa.

"Allah ya tsare gaba" Umma tace tare da cigaba da aikinta.

D'akinsu Amira ta shiga dan cire uniform,k'anwarta Fateema ta taso cikin sauri tace " tab Ameera ashe yau kin auni arziki".

Murmushi Ameera tayi " hmmm sis bari kawai da Allah bai kawo mutumin nan ba da ban san wani hali zan kasance ba".


Allah ya kiyaye fateema tayi mata ta amsa tare da d'aukan buta zuwa toilet.

Mallam yawale shine maifin Ameera,da mahaifarsu Hadiza wacce suje kira da Umma dukkan su cikakkun 'yan Kaduna ne.

Malam Yawale talakane bashi da komai illa gidan da yake ciki,shima gada yayi a wajan mahaifinsu shi k'anwarsa basira.itama tana aure a nan cikin garin kaduna da 'ya'yanta.

Mallam Yawale ya kasance masani ne shi ta fannin adsinin islam dan yayi saukan alqur'ani tun yana shekara sha bakwai a duniya sannan yayi karatun litattafai da dama,dan haka kullum kullum kofar gidan shi cike yake da masu d'aukan karatu manya da kanana.

Malam ya bawa 'yan matansa ilimi na boko da arabi ga kuma tarbiya da ya basu,kowa yana sha'awar su a anguwan su.

Al'ameen kuwa yana tafiya cikin motan shi zuwa gida amma hankalin shi gaba d'aya yana kan yarinyan da ya gani domin shi asalima yana son mace kamila gata tayi shigan mutunci wanda matan aure ma da dama basayi suna fito da tsaraicinsu a ganin su wayewa ce amma kuma b'atace babba Allah ka shirye mu baki d'aya ameen.

Da irin tune-tunen nan ya isa gida,sallama yayi ya shigo waiting palour,cikin ikon Allah yau ba taron mutane da ya saba gani kuma hakan ya d'anji sanyi a ranshi.

Kai tsaye main palour ya shiga ya samu Latifa da k'annenta suna kallo,tashi tayi cikin fara'a ta tare shi.sannu da zuwa k'annenta suka mishi sannan suka wuce part d'in su.

Bayan yayi wanka ya fito sanye da jallabiya fari kal,dinning ya wuce cikin jagorancin Latifa yaci abinci sannan suka dawo palour suka zaune kallo.

Suna cikin kallo Latifa ta tashi ta shiga part d'inta,jimawa kad'an ta fito da wasu files a hannunta ta zauna kusa dashi.

Mik'o mishi tayi tace " gashi yi signing a nan"

Karb'a yayi yana jujjuyawa yace " what for?"

Kin kula shi tayi ta cigaba da kallonta hankali kwance.

Ganin haka yasa ya bud'e ya fara karantawa......

"Ai ba sai ka karanta ba, taimako nake sonyi kasan 'ya'yanGwaggona na can garin mu basuda aikin yi shiyasa".

Kallonta kawai yake yandatak koro bayani tare da maimaita a ranshi 50 millions!!!.kuttt toh wai wani tsawon lokaci ta d'auka tana cutansa?coz da alamu ba yau ta fara ba.

Murmushin takaici ya mata yace " good my Lateefa,taimako abune mai kyau amma ki bari zan samu contract na 100 millions next month sai in baki kinga sai kiyi yanda kike so kin huta da kad'an-kad'an daga nan ki taimakawa duk wanda kika ga yana bukatan taimako".

Washe baki tayi cikin murna tace " gaskiyane my Ameen hakan yayi min sosai zan jira zuwa next month d'in".

Tashi tayi cikin sauri tayi hanyan part d'inta.

Shi kuma kallon takaici ya.bita.dashi a ranshi yana aiyana matakin da ya kamata ya d'auka a kanta kamin next month d'in.daga nan shima ya mik'e zuwa part d'insa.

Kallon system d'in shi yake kaman mai neman wani abu amma a zahiri a shi yake kallo ba yarinyan d'azun yake tunani kuma ba abunda yake so kaman kallon fuskan yarinyan.

Rufe system d'in yayi ganin ya kasa tab'uka komai,kwanciya yayi flat akan gadon shi yana wasi-wasi yaushe rabon da ya kalli mace a matsayinta na mace har ya manta amma yau yar yarinya k'arama da ko fuskanta bai kalla ba bare ya san sunanta ta hana shi bacci.

Daga baya ya yanke hukunci gobe zai koma gidansu ya tambayi koda sunan tane.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . 🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀

*~UKUBAR KISHIYATA~*

😭😭😭😭😭😭


( its all about love and betrayal)


Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)


✍✍✍✍✍✍✍
GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION
✍✍✍✍✍✍✍


*~part ten~*


Da washe gari Al'ameen da wuri ya shirya ya fito cikin wani shadda light blue wanda ya k'ara fito da k'yansa.

Ko kallon dining area da yake cike da kayan break fast baiyi ba yayi ficewarsa.saboda ya matsu ya kalli fuskan yaruyan nan dan jiya ko baccin kirki bai samu ba.

Latifa kuwa ko tashi ba tayi ba daga bacci.

Musa driver yana ganin fitowan shi ya taso cikin sauri ya bud'e mishi owner seat ya shiga ya zauna.

Duk'awa yayi ya gaishe shi sannan shima ya bud'e driver seat ya shiga ya zauna tare da yiwa motan key suka fita a gidan.

Al'ameen ne yace " ammm musa mu fara zuwa tudun wada kafin mu wuce office".

" toh ranka ya dade" musa yace cikin girmamawa.

Nuna mishi hanya ya fara har suka iso k'ofar gidan mallam Yawale,nan yace mishi ya tsaya anan

Brick Musa yaja ya tsaya tare da mamakin meye mai gidansa zaiyina wannan rugujajjen gidan.

Fitowa Al'ameen yayi daga cikin motan ya jingina da jikin motan yana kallon gidan.

Ganin haka yasa Musa daga motan shima ko akwai wani abinda zaiyiwa mai gidan nashi.


Shi kuwa Al'amewn tunani yake ya zaiyi yaga yarinyan da ko sunanta bai sani ba.

Wani almajiri ya gani ya fito daga cikin gidan da k'wanon baran shi a hannu,

kiran shi Al'ameen yayi,nan ya taho da gudun shi.

Al'ameen yace " kasan mutanen cikin gidan nan ne?"

" a'a nima bara na shiga yi kuma ban samu komai ba" almajirin ya amsa mishi.

"Da ka shiga kaga wata yarinya a cikin gidan " Al'ameen ya kara jeho mishi tambaya.

" eh nagani ai su 2 ne" shima ya amsa mishi.

Tunani ya tsaya yi,ya zaiyi tunda ance su 2 ne kuma gashi bai san sunan wacce yake nema ba.

Dabara ce ta fad'o mishi ya kalli almajirin yace " yi maza ka koma kace ana sallama da 'yan matan gidan".

Da toh ya amsa ya koma cikin gidan yayi sallama,

Umma ta sauke uban tagumi da zabga tace " haba almajiri nace maka Allah ya bafa sa'a tundazu ko?"

" ni ba bara nazi yiba wani ne a waje yace ana sallama da su 2 nan" yace yana nuna su amira dake zaune da yatsa.

" su 2nan?" Umma ta k'ara tambaya tare da dafe kirji.

" eh da mota ma yazo " yace tare da ficewa abin shi.

Zuciyar Amira sai bugawa yake tace " oh! ni Amira kar dai mutumin jiya ne ya dawo?"

Umma ne ta katse mata zancen zuci da take tace " sai kuje ku gani dame yazo kuma kar ku mantavda maganan Babanku".

Dogayen hijabansu suka sa sannan suka fita suka bar Umma da tunanin waye yake neman 'yan matan ta duka 2 kuma harda mota.

Al'ameen yana nan tsaye almajirin yazo yace " wai suna zuwa".

Hannu Al'ameen yasa a aljihu ya ciro 200 note ya mik'a mishi tare da cewa ya gode.shima karb'a yayi yana ta murna ya tafi.

Tun a zaure Fateema ta fara yiwa Amira magana " kina ganin waye zai zo neman mu anya ba mutumin da ya taimake ki jiya bane?"

Ganin sun fito k'ofar gida yasa Amira k'ara yin k'asa da kai ba tare da ta amsa mata ba.

Tunda suka fito ya kafe Amira da ido yana kallon yanda take taku cikin natsuwa.

D'an nesa da shi suka tsaya a tare suka d'an duk'a suka gaishe shi.

Amsawa yayi cikin murmushi yace " dan Allah wacece a cikin ku jiya muka had'u da ita ta taso daga makaranta?"

Fateema ce ta d'ago kai suka had'a ido ta kalli k'yawawan mutumin nan tayi murmushi tace " gata nan yayata ce".

" ok good ya sunanki please?"

" Fateema"

" yayarki fa ?" ya k'ara tambaya.

" Amira sunan ta" ta bashi amsa.

Murmushi ne ya kwace mai jin sunan ta mai dad'i yace " toh fateema nagode dama Amira nake son gani".

Sallama tayi mishi ta koma ciki.

Musa ma ganin haka yasa yayi gaba ya basu waje.

Kallonta yake ba ko kitawa ganin har yanzu tak'i d'ago kai.

Gyaran murya yayi sannan ya kira sunata cikin sanyin murya.

Amsawa tayi da tsiririn muryarta still kanta a k'asa.

" tunda nake ban tab'a ganin mai suna amira marowaciya ba sai a kanki".

A d'an razane tace " rowan me nayi maka kuma?"still kanta yana k'asa at d same time tana mamakin wannan mutumin ita meye gare ta da har zaice tayi masa rowa.

" kusan 24 hrs da mu amma kin hana ni kallon prity face d'inki".


Bata san lokacin da ta saki 'yar dariya ba har tsiririn wushiryan ta ya bayyana sannan ta d'ago kai a hankali suka had'a ido.

Tasbihi ya fara a zuciyan shi ganin k'yaunta mai firgitarwa.

Amira fara ce sol wanda har ja-ja take gata da dogon hanci da ya dace fuskanta ga maidaicin bakinta tare da idanun ta masu oval shape.in short Amira tayi 100%.

Kanta ta mayar k'asa dan ba zata iya jure irin kallon k'yakyawan fuskan shi ba.

Cike da tsokana yace " woah ashe da 2 kike b'oye min fuskan ki dan u re so ugl....."yasa hannu ya rufe bakin shi yana dariya tare da hana bakin shi k'arasa maganan.

B'ata fuska tayi ta d'ago tana kallon shi dan ta rasa bakin magana.

Shi kuwa shagala yayi da kallonta dan gani yayi tkaman ma tafi k'yau da ta b'ata fuskan.


Dariya yayi yace " am sorry just kidding u re d most beautiful girl dat i hav ever seen in my life".


Batayi magana baba sai dai murmushi da tayi tanan kallon gefe.

"Duk da baki damu ki san suna ba i'm Al 'ameen nazo ne mu gaisa kuma mu san juna ".

Hannu yasa a aljihu ya ciro bounch 'yan 200 yace " ga wannan ki sayawa k'anne na choculate ni zan wuce office".

Kallon kud'in tayi ba tare da ta karba ba tace " nagode ka barshi kawai dan in na shiga ciki da shi Umma zata min fad'a kuma ko fitowan nan da nayi in Abba yazo shima fad'a zaiyi".


Ji yayi ta k'ara burge shi tare da samun special place a hrt d'in shi.yace " toh shike nan ki turo min Fateema muyi sallama".

Amsawa tayi tare fa yi mishi sallama ta shiga ciki.

Tana shiga ta tarar da Fateema ta zage tana bawa Umma labarin wanda yazo gun Amira .

Waje ta samu gefen Umma ta zauna sannan ta kalli Fateema tace " wai kije kuyi sallama".

Cikin zumud'i Fateema ta fice.

Umma kallon Amira tayi tace " da fatan kin fada mishi Abban ku baya so ko"?

Tace " na fad'a mishi Umma".

" yauwa gara ki ki fad'a in ba haka ba koni ba fita zanyi a wajan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login