Showing 27001 words to 30000 words out of 62823 words
Chapter 10 - UKUBAR KISHIYATA Sirrin Da Ya Rushe Aure by Ummee Yusuf
so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part twenty five*
Rufe k'ofan yayi da key ta ciki sanna cikin hanzari ya wuce bedroom d'inta.
Tana k'wance daga ita sai kayan bacci a jikinta wanda gaba d'aya ya tattare yayi sama ga gashin kanta duk sun baje kan pillown da ta d'ora kanta tana ta baccin gajiya.
Ya dad'e a tsaye a kanta yana kallonta dan ba k'aramin k'yau tayi mishi ba duk da ta rame tayi duhu cikin 'yan k'wanakin nan.
A hankali ya lallab'a ya hau gadon ya k'wanta a gefenta yana gyara mata gashinta yana shafa ta a hankali.
Motsi tayi ta juyo kaman zata bud'e ido amma baccin yafi karfinta.
Matsota sosai yayi jikinshi ya rungumeta tsam yana mata rad'a a kunne yace..." wake up my sleepin beauty".
Kaman a mafarki take jin kamshin turaren shi ga kuma d'umin jikin shi da taji yasa ta k'ara gyara k'wanciyarta a jikin shi tana shakan kamshim da tayi missing.amma jin muryan yasa ta bud'e ido a firgice.
A rud'e ta fara k'okarin zare jikinta daga nashi tana " yayana dan Allah ka tafi kar Aunty tazo ta same wallahi zan shiga matsla babba".
Rik'ota yayi da sauri yana shafa bayanta a hankali yace..." cool down mana ki k'wantar da hankalinki ba wanda zai shigo nan dan tana can tana bacci kinji.."
Fashewa tayi da matsanacin kuka mai tsuma zuciya tare da k'ank'ame shi ta fara magana.
"Yayana wai me yake faruwane?,ka taimake ni ka sanar dani me yake faruwa...?
Bai samu bakin magana ba sai shafa bayanta da yake har yanzu alamun rarrashi,toh shi mema zaice mata saboda shi kanshi baisan me yake faruwan ba.
Had'e bakin su yayi ya fara bata hot kiss yana aika mata da sak'onni cikin zafi-zafi saboda ba k'aramin missing d'inta yayi ba.
Bai barta ba saida suka faranta ran juna sannan ya shiga lallashinta da kalamai masu dad'i da taushi sai gata nan tana k'yalkalan dariya kaman ba ita ba,nan suka shiga hiransu ta masoya kaman basu da wata matsala har zuwa 3am sannan yayi mata saida safe ya fita da k'yar dan ji suke kaman kada su rabu.
Da fargaba ko zsi tarar Lateefa ta dawo d'akinshi,zuciyarshi sai bugawa yake kaman wanda yayiwa sarki babban laifi amma ga mamakinsa yana shiga d'akin yaga ba kowa kaman yanda ya tafi ya bari.
Zuciyar shi fari kal ya haye gadonshi ya k'wanta cike da nishad'i.
Ameera haka tacigaba da rayuwa a gidan Lateefa tana gana mata *UKUBA* iri-iri duk tayi bak'i ta rame ta fita hayyacinta,duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata hatta masu aikin gidan suna tausaya mata dan ba yanda suka iyane amma wani lokaci suna fakan ido su tayata aiki bama kaman Rabi duk tafisu taimakonta.
Al'ameen shima duk ranan da Lateefa ta koma d'akinta sai ya lallab'a yaje d'akin Ameera su sha love abinsu.har yau baisan dalilin da take guduwa cikin dare ta barshi ba,yafi alakanta hakan da kin bashi hakkin shi da take baisan cewa raba dare suke da Salees d'inta suna waya ba.
Yau monday Ameera da k'yar ta fito daga part d'inta saboda k'wata-k'wata bata jin dad'in jikinta,kasala ce zallah yake damunta ga wani azababben ciwon kai da take ji tun cikin dare dan haka a daddafe ta gama aikinta na safe ta koma part d'inta tana neman magani bata samu ba dole ta hak'ura ta dawo ta cigaba da aikin saboda lokacin d'aura abincin rana yayi.
Faten doya da yaji ice fish da kayan lambu tayi musu,ta jera musubakan table kaman yanda ta saba sannan ta k'arasa palour inda ta samu Lateefa sun baje itada k'annenta sun cika palourn suna kallo.
Can nesa dasu ta durkusa dak'yar tace...Aunty na gama".
Zuba mata ido sukayi a wulakance banda Fa'iza da take binta da murmushi.
Cikin basarwa da gadara Lateefa tace..." naji ina sauran aikin kinyisu?"
"Kainane yake ciwo Aunty banyi ba amma yanzu zanje...."a tsawace tace.." wat?,lallema yarinyan nan wuyanki yayi k'wari ya isa yanka har insaki aiki ki tsaya kina kawo min k'abli da ba'adi?,ba ciwon kai ba uban ciwon kai kike ba abinda ya dameni dan haka ki bace min da gani kamin in b'allaki banza kawai" ta k'arasa maganan tare da jan digon tsaki.
Daurewa ta k'ara yi ta yunkura ta tashita koma aikinta.
Shamsiyya tayi dariya tana jinjinawa Auntynta tace "Aunty kina wuta muna binki da fetir".
Cike da ji da kai tace..." kad'an ma suka gani dan yanzu na fara bautar da ita".
Ajiyan zuciya Fa'iza dake sauraransu tayi kana tace..." ni dai Aunty ina ganin da gaske take fa bata da lafiyat".
"Ina ruwana da rashin lafiyarta kai ta mutuma mana ni meya dame ni?"tace tana wani tab'e baki.
K'ara k'wantar da kai Fa'iza tayi tace.." ai shiyasa nake ganin ya kamata ta samu kulawa daga wajanki ko dan kiji dad'in bautar da ita".
Murmushi Lateefa tayi tace..."ke Fa'iza in kin fara wannan nacin naki nasan ba bari zakiyi ba saboda haka kije ki d'auki paracetamol 2 cikin first aid box ki bata ta sha nd na bata hutun 10 mins kawai ta dawo kan aikinta".
A kitchen Fa'iza ta taddata zaune rik'e da kanta da yake barazan fashewa.
Dafa shouldernta Fa'iza tayi,a firgice ta mik'e tana " kiyi hak'uri Aunty yanzu zanyi wallahi".
Rik'ota Fa'iza tayi da sauri tana mata murmushi tace.." k'wantar da hankalinki ba Aunty bace nice ".
Hankalinta ya d'an k'wanta da ganin Fa'izan dan ba laifi ita tana k'yautata mata ba kaman sauran sisters d'inta ba.
Da kanta ta bud'e fridge ta ta d'ebo mata ruwa tare da b'allo mata paracetamol 2 ta bata.
Ba musu tasa hannu ta kab'a ta watsa a bakinta tare da kora ruwan.
" kije d'aki ki k'wanta ki huta inji Aunty".
Murmushi tayi tace " nagode Aunty Fa'iza Allah ya saka da alkhairi".
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
πββπββπββπββπββπββ
*~UKUBAR KISHIYATA~*
ππππππ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπ«π«π«~*
*~βWe beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part twenty four*
Gadan-gadan ya nufo su zuciyar shi na bugawa,rai a matuk'ar b'ace ya iso gaban Lateefa ya tsaya da niyyan yi mata magana.amma suna had'a ido ya manta me ya kawo shi wajan saima wani murmushi da ya sake mata yace..." my Lateefa yunwa nake ji".
Murmushin itama ta mayar mishi tare da kama hannun shi sukayi hanyan dinning tana" dont worry ur food is ready my Ameen".
Ameera ta dade a durkushe a inda suka barta saboda ta rasa kuzarin tashi daga wajan,dama a tunaninta Al'ameen yana dawowa komai zai daidaita komai,sai gashi ko kallon inda take baiyi ba bare tasa ran zai kulata ko d'aukan mataki.
Muryan Lateefa taji tana k'wala mata k'ira kaman tana wata duniyar.
Amsawa tayi ta mik'e cikin sauri ta isa dinning d'in ta durkusa nesa dasu kanta a k'asa tace..." gani Aunty".
" k'washe kayan nan kije ki wanke su tas kamin ki k'wanta dan bana sin k'azanta".
Wani abu ya rink'a ji a k'asan zuciyarshi lokacin da yaga tana k'washe kayan,yana son kallon fuskanta amma ya kasa yana tsoron kar Lateefa ta ganshi.
Ameera tana barin wajan Lateefa ta jashi zuwa parlour dan suyi hira amma shi ya kasa maida hankali kan hiran saboda rabin hankalin shi yana kan Ameera.
Dube-dube take a kitchen d'in inda ta bar abincinta amma cikin ikon Allah ta neme shi sama da k'asa ta rasa,gata sosai take jin yunwa cos yau ko lunch batayi ba.
Abinda bata sani ba Lateefa ce ta d'auke abincin nata ta bayar dashi dan mugunta.ganin yunwa na neman halakata yasa ta jawo sauran abincin dasu Lateefa suka rage ta cinye sannan tayi wanke-wankenta tare da gyara kitchen d'in tsab ta fito.
Ba kowa a palourn ta wuce part d'inta zuciyarta a cunkushe kan sabon rayuwa da ta tsinci kanta a ciki,bata dad'e da kwanciya ba bacci mai nauyin gaske yayi gaba da ita sakamakon gajiya da take tattare da ita.
Al'ameen zubawa Lateefa ido yayi wacce take bacinta cikin k'wanciyar hankali,yana son zuwa d'akin Ameera saboda yau k'wananta ne amma tsoron Lateefa ya hana shi koda yunkurin tashi ne bare yayi gigin fita a d'akin.
Yanzu da yana wajan Ameera ne suna can suna tattalin juna amma ita saidai ma ta kara mishi damuwa
Yasan kuma da gayya tazo ta k'wanta mishi a d'aki dan kar ya samu daman keb'ewa da Ameera.tunda sai suyi kusan sati 2 bai isheta kallo ba dama a wajan Ameeran shi yake samun kulawa.
Juyi yake yana ta sak'e-sak'e a zuciyar shi da k'yar bacci yayi nasaran d'auke shi.
Ameera data farka da asuba bayi mamakin rashin ganin Al'ameen ba saboda yanda taga jiya ya wofintar da ita.
Tana idar da sallah asuba bata tsaya yin addu'a ko azkar ba tayi hanyar kitchen,hasalima mantawa tayi anayi saboda wannan shine amfanin aljanin da aka turo mata.
Ruwan zafi daya sha kayan kamshi ta fara d'aurawa sannan ta d'ebo irish da take ganin zai ishi gidan ta fara aikin ferewa.
Kamin tagama firan har ruwan tean ya tafasa yanata kamshi,juyewa tayi a wani babban tea flask sannan ta fara soya irish d'in.
Tana gama soyawa ta samu wani babban bowl ta fasa eggs a ciki ta yayyanka mishi wadatattacen albasa ta soya shima,ta k'ara musu da kunun k'wak'wa sannan ta fito dasu kan dinning ta jerasu.
Komawa kitchen d'in tayi ta gyara ko ina sannan ta fito palourn ta share tare da yin mopping,b4 8am harta gama aikinta tayi wanka taci k'walliyarta da wani less peach colour da white stones a jiki tayi bala'in k'yau.
Zama tayi a bakin gadonta tana jira taji k'ira dan tasan basu tashi ba.
Ba tafi 10mins da zama ba taji ana zabga mata k'ira,cikin azama ta fito.
Kamshin turaren ta yasu d'ago kai suna kallonta.
Al'ameen kam kasa d'auke idonshi daga kanta yayi saboda gaba d'aya ta rikita shi.
Tsawan da Lateefa tayi yasa shi dawowa cikin hayyacin shi kuma ya nemo natsuwa cikin d'an k'ankanin lokaci ya sunkuyar da kai tare da wayancewa.
Ameera itama tuni tasha jinin jikinta ta fara karkarwa.
Lafiyayen marin da tajine ya sata mik'ewa ba shiri tare da dafe fuskanta inda Lateefa ta mara dan ga yatsunta nan tsab sun fito abinka da farar fata.
Nunata take da yatsa cike da masifa take magana..." ke k'aramar 'yar iska wallahi zanyi maganin kine a gidan nan wato tsabar kinyi degree a karuwanci shine kikayi wannan k'waliyan harda saka ture kika zo gaban mijina ?"
Kama 1 kunnenta tayi ta murd'e iya karfinta sannan tace..." zanyi miki last warning a gidan nan,duk ranan da naga kinyi k'walliya ko kika saka turare a gidan nan hmmmm....." murmushin mugunta tayi sannan ta cigaba" wallah sai na lahira ya fiki jin dad'i.dallah b'ace min daga nan bak'ar munafuka.."
Da gudu ta koma part d'inta tana kuka kaman ranta ya fita.
Lateefa ta juyo tana kallon Al'ameen daya sunkuyar da kai k'asa ba zaka tab'a tantance yanayin da yake ciki ba tace..." sorry my Ameen wannan munafukar tana son b'ata min rai da sassafen nan".
Ajiyar zuciya yayi ya dago kai tare da kirkiro murmushin dole yace..." sorry my Lateefa kema kinsan bana son b'acin ranki".
Jawo warmers d'in gabansu tayi ta fara serving d'insu cikin jin dad'i tace..." shikenan my Ameen na hak'ura".
Abincin yayi mishi dad'i sosai tsakanin jiya da yau yasan an samu canji wajan girki a gidan dan ya lura Ameerarsa ce take girkin amma hakan baisa yaci ba sai jujjuya fork d'in hannun shi yake.
Ganin irin kallon tuhuma da Lateefa take aika mishi yasa ya zage ya fara tutturawa.
Suna gamawa ta rako shi har waitin palour abinda bata tab'a yiba wai dan kar ya samu daman branching a wajan Ameera.
Tun kamin ta karaso cikin palourn ta fara k'iran Ameera.
Fitowa tayi cikin wani jallabiya red fuskanta a kumbure babu make up d'in dazu sakamakon kukan da tasha.
" wuce ki gyara kan table d'in sannan ki gyara min bedroom kuma ki wanke min toilet tas " tace mata a gadarance.
"Toh Aunty " tace tana yunkurin mik'ewa domin taje ta aiwatar da abinda aka sakata.
Yauma bata samu zama ba sai kusan tara na dare dan haka wanka kawai tayi tabi lafiyar gado,cikin minti 2 bacci mai nauyi yayi gaba da ita.
Al'ameen yana k'wance amma duk a takure yake saboda yau k'wata-k'wata baisa Ameera a idonshi ba saboda Lateefa ta kara tsanta doka kan cewa in Al'ameen yana gida kar ta yarda ta fito ko tabi inda yake.
Abinda Lateefa bata sani ba shine boka yayi nasaran dasa tsoronta a zukatansu amma soyayyar da suke ma juna yana nan daram.
Bai saba k'wanciya tare da ita yasa yake jinsa a matse.
Motsinta daya ji shiya shi saurin rufe ido kaman mai bacci,yana jinta tana sauk'owa a hankali har ta iso bakin k'ofa ba tayi wani babban motsi ba gudun kar ya farka.
Yana ji ta bud'e k'ofan ta fita tare da maida k'ofan ta rufe duk a hankali tayi su.
Bayan ta fita kaman da 5mins ya bud'e idonshi yaga tabbas bata d'akin,zama yayi a bakin gadon ya kai minti 10 zaune amma baiji motsinta ba.
Tashi shima yayi cikin tsand'a kaman wani b'arawo ya iso main palourn yaga bata nan,rab'ewa ya dinga yi tsakanin cushins d'in palourn har ya isa hanyan part d'in Ameera cikin sa'a ya samu k'ofan a bud'e,ba wata wata ya bud'e k'ofan ya shiga.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
πββπββπββπββπββπββ
*~UKUBAR KISHIYATA~*
ππππππ
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπ«π«π«~*
*~βWe beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part twenty six*
Sakamakon gajiya da take fama dashi kuma ya hadu da kasala tana k'wanciya bacci mai dad'i yayi awon gaba da ita.
Baccinta take harda mafarkin su Umma da Fateema tana musu korafin sunk'i zuwa dubata daga nan suka bige da wasa da dariya ita da fateema wanda har yake fitowa a zahiri.
Ruwa mai bala'in sanyi da aka shek'a mata shi sanadin katse mata baccinta mai dad'i.
A gigice ta farka tana neman hanyan guduwa.
Ficikota akayi taji tare da kifa mata wani wawan mari da ya k'ara gigita ta tare da k'ara mata ciwon kai.
Muryan Lateefa da Shamsiyya suna zazzaga mata k'wandon rashin mutunci akan meyasa tayi bacci har lokaci ya k'ure gashi 5 ta gota batayi girkin rana ba har time d'in d'ora na dare yayi.
Shamsiyya itace a gaba wajan neman nad'a mata na jaki ,Fa'iza ta shigo da k'yar ta k'waceta tana basu hak'uri.
Hankad'a keyarta sukayi zuwa har cikin kitchen d'in sannan suka k'yaleta.
Tana kici-kicin d'ora girki Fa'iza ta shigo ta same ta.
Rik'ota Fa'iza tayi tana kallon yanda fuskanta ya kumbura yayi jah sai hawaye da take sharewa.
Zaunar da ita tayi ta fita sai gata sun shigo da rabi,tacewa rabi ta cigaba da aikin ita kuma Ameera taje ta k'wanta ta huta.
Har k'asa Ameera ta duka zatayi mata godiya tayi saurin rik'eta tana " bana son haka Ameera ni sonki nake shiyasa bana juran inganki cikin wahala yanzu jeki k'wanta ki huta sun fita ba zasu dawo da wuri ba.
Fita tayi zuwa part d'inta zuciyarta cike da farinciki tare da bawa Fa'iza daraja na musamman a cikin zuciyarta.
Rabi sai jinjina abin take a ranta saboda tana da shakku akan Fa'iza meye dalilinta na yin haka alhalin tasan Shamsyya rashin mutunci,koma menene tana mata addu'an neman tsari daga masifar Lateefa da k'annenta.
Allah ya taimake ta har dare ba wanda yabi ta kanta,amma zazzabi da ciwon kai sun hanata bacci sai juyi take akan gado tana hawaye.
12:30 am Al'ameen ya lallab'o ya shigo part d'inta ya same ta a haka.
Hankalin shi inyayi dubu to ya tashi jin zafin jikinta har yayi over ga fuskanta da ya kumbura suntum saboda maruka da tasha a wajan Lateefa.
A rud'e ya d'agota yana jero mata tambayoyi..." Babyna meke damunki?,tun yaushe kike k'wance haka?"
Da k'yar ta iya d'aga hannunta na dama ta nuna mishi kanta.
K'wantar da ita yayi ya shiga cikin bathroom d'inta ya d'ebo ruwa a bowl da towel ya dawo kan gadon.
Rage mata kayan jikinta yayi sannan ya fara goge mata jiki da ruwan sanyi,daga nan ya fita parlour zuwa inda suke ajiye first aid box ya had'o mata drugs harda na zazzab'i.
K'ara d'agata yayi ya bata drugs d'in sannan ya k'wantar da ita yana ta mata sannu.
Zuwa 30 mins bacci yayi awon gaba da ita,yana zaune ya zuba mata ido yana jin wani abu a zuciyarshi wanda baisan dame zai fassarata ba.
Shi bai bar d'akin ba sai wajan karfe uku na asuba a lokacin jikin yayi sanyin sosai,haka ya wuce ba dan ranshi ya so ba.
Koda ya dawo d'akin shi kaman yanda ya zata Lateefa bata nan,rannan dai bai wani samu baccin kirki ba.
Kiran sallahn farko a kunnen Ameera,wanka ta farayi da ruwan zafi ko zataji dad'in jikinta .kuma ba laifi ta d'an ji dama-dama.
Sallah tayi sannan ta zura doguwar riganta na atamfa ta zumbula hijab ta fito aiki.
Haka kawai taji yau ranta ba abinda yake so kaman fresh milk,bata tsaya b'ata lokacinta wajan duba fridge d'in palourn ta ba saboda ya dade da zama empty rabonta dasu tun kamin Lateefa tayi nasara akansu.
Tana zuwa main palourn ta bud'e fridge Allah ya taimake akwaisu aciki,guda 2 ta k'wasa ta wuce kitchen gudun kar wani ya ganta duk da tasan cewa yanzu ko sallah basuyi ba.
Tana shiga kitchen kuwa ta kafa kai ta shanye k'wali d'aya sannannta fara aikinta cikin karfi hali dan har yanzu tana jin zazzab'in.
Al'ameen shima da saboda rashin baccin da baiyi ba last night ya tashi da ciwon kai har da zazzab'i.
Yana k'wance bayan yayi sallahn asuba basida niyan tashi bare yayi shirin office.
D'ayan wayarshi da yake kusa dashi ya fara ringing d k'yar ya mik'a hannu ya jawo wayan.
Sunan yayanshi Sa'ad ya gani yana yawo akan screen d'in dan haka ba b'ata lokaci yayi recieving call d'in yayi sallama.
Amsa sallaman yaya Sa'ad yayi bayan yana ce masa ya biyo hospital d'inshi yana da magana dashi.
" bros yau bazan fita office ba" ya bashi amsa.
" why wat happend"ya buk'ata.
Numfashi yaja yake cewa fever ce kawai yake d'an ji amma yanzu zai sha paracetamol.
" don't u try dis kasan self madication ne nd u