Showing 18001 words to 21000 words out of 117287 words

Chapter 7 - Na Huce Sabuwar Rayuwa BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

matsananciyar faduwar gaba. Kafin ta soma yunkurin tashi ta kuma fashe da kuka."

"""Amma Dr. Widad kin cuce ni. "" ta fada cikin kuka sosai, kamar Dr. Na jin harshen nata, tayi Allah ya isa da"

"fillanci, tayi da hausa, tayi da German, tayi davduk yaren data iya. Duk akan Dr. Widad data shigo mata da Habibu dakin haihuwa. Nene tana ta bata baki kan ta yi hakuri. Shikuwa ya harde hannuwa a kirji yana kallon ta da wani irin murmushin SO. In da a ce zai iya, zai iya ciro zuciyar dake kirjin sa ya bata a halin yanzu don kawai ya nuna mata dimbin godiyar sa da soyayyar sa gareta. Bisa bashi farin cikin da wani a duniya bai taba bashi ba. Bisa maida shi UBA, bisa bashi precious gem din da kudi ko mulki basu isa su bawa dan adam ba."

"Dr. Ta mika mata Babyn bayan ta gama kukan bakin ciki ta share hawayen ta, da sauri ta karbe shi tana kallo. Ba shiri ta daga ido ta dubi Habibu. Yaro kamar Ubansa yayi khaki ya tofar. Ya lumshe mata lumsassun idanun sa ya kuma daga mata girar sa daya, ""eh dani yake kama ba da ke ba, kamar ya san ba kya son uban sa"". Ta gatsina baki ta cigaba da kallon babyn tana tazbihi a zuciyar ta. Wata irin kauna ta da da mahaifi na keta ruhin ta da zuciyar ta. Her only relative, her only blood! Ta yaya bazata so shi sama da komai a duniya ba?"

Bata yi aune ba ta ji Habib ya kashe su da hoto da camerar wayar sa.

"Hararar sa tayi, duk wani abu da zai bakan ta mata ya san shi, yanzun ma Nene na bada baya ya matso gabanta, ""wai sabida kin haihu gabana kike wannan kukan? Yo wane dare ne jemage bai gani ba? Bani Da na nan in ji dumin sa, kin wani kama shi kin kankame kamar ke kadai kika yi nakudarsa"". Ya mika hannu, ta yi maza ta janye dan ta."

"""Ba zaka dauke shi ba!"""

"Ya saki baki yana kallon ta da mamaki, Nene ta shigo jin sautun kukan ta, tace ""lafiya? Ki bashi yaron mana ya yi masa khutbah?""""Nene bazan bashi ba, da na ne nikadai, ba ruwan shi da mu ba ruwan mu da shi"" Nene tace ""Rahinah kin san abinda kike fada kuwa? Mahaifin sa ne fa? Yau na ji karfin hali wai barawo da sallama. Ki bashi yaron nan kafin raina ya baci akan hakan"". Rahinah ta saka kuka sannan ta mika masa yaron. Ya karbeshi da wata irin kulawa tamkar ya maida shi cikin sa. Yayi masa khutbah da sunan da ya zaba masa wato sunan mahaifin Manzo SAW. Ya tauna dabino (ajwa) ya sanya masa a baki, yaron ya hau motsa dan bakin sa gwanin sha'awa, Habib bai san lokacin da wasu irin zafafan hawaye suka zubo masa ba. Ya rungume yaron a kirjin sa. A haka Ambasada ya shigo ya same su. Safinah ta biyo bayan sa dauke da kwandon abinci. Ya yi wa Habib da Rahinah ""congratulations"" sannan ya karbi yaron yayi masa addu'a."

"Washegari aka sallame su. Suka koma gida. Tun daga ranar Habib yake zarya, sayo banza sayo hopi, duk don ya farantawa Rahinah. Amma ina! Zuciyarta ta riga ta kekashe akan Habibu, babu wani repenting da zai yi ya burge ta."

"Babban tashin haankalin sa shine Rahinah ta gama iddah, gashi yayi alkawarin bazai maida ita ba da amincewa da yardarta ba, shima Ambasada bazai taba amincewa ba yayi forcing din ta akan abinda ta nuna ta gama bashi baya."

"Tsayin watanni uku tana shayar da Abdallah kasancewar suna cikin hutun summer. Ta saba da yaron sosai, bata barci sai yana kan kirjin ta, har fargabar komawa makaranta take, don ta san dole zai koma haunnun mai raino. Ita kam ba wanda take jin zata iya baiwa dan ta ya rike mata yadda take ji da abun ta. Ko Habibu bata bari ya dauke shi sai in Ambasada yana gidan yayi mata jan ido. Gabadaya Habibu Nahuche ya gama susucewa, ya fita hayyacin sa don zuwa yanzu ya tabbatar da ya rasa Rahinah."

"Lokacin da suka koma hutu Nene tace zata samar mata mai raino, amma Rahinah ta fito fili tace da Nene zata yi deferring karatun ta zuwa shekara ta gaba don ta samu damar kulawa da Abdallah. Da bashi cikakken lokacin ta a lokacin da yafi bukatar hakan."

"Nene da Ambasada na jinjina soyayyar Rahinah ga dan ta, amma a zuciyar su suna tausaya mata. Don sun san irin wannan kaunar sai ka samu a karshe iyayen da 'ya'yan basa rayuwa tare. Kaunar tata tayi yawa kuma silence din Habibu na nufin wani abu. Yafi watanni uku bai kara takowa inda suke ba tun wani wulakanci da Rahinah tayi masa, inda tace idan ba ita ce autar mata ba, kuma ba daga kanta an daina haifar mata ba, sannan shi ba maye bane to ya fita hanyar ta ya je ya nemi wani gantalallen auren amma ba nata ba, tun daga ranar bai kara takowa ba, amma sakon shigar kudi basa yankewa a tsakanin su."

"A wannan watan da ake ciki ya kammala rubutun proposal din sa, ya karbi shaidar kammala masters din sa, aka yi musu convocation na graduating. A ranar da ya karbi kwalin sa ya hada komai nasa don barin kasar Jamus. In bai yi kuskure ba yau ne Abdallah ya cika shekara daya da haihuwa kuma yana gudun sa ko'ina. Don daga baya ya kan je ganin sa amma iyakar sa falon saukar bakin Ambasada, a kawo masa yaron suyi soyayyar su ta uba da da, ya bashi sayayyar da ya yo masa, ya tafi ya bar shi yana kukan sai ya bi shi. Sun yi wani irin sabo wanda in zaka ga sanda zasu rabu sai zuciyar ka ta motsa, ka kuma tambayi kan ka shin ita Rahina wace irin zuciya gareta? Anya ma tana da tsokar zuciya a cikin kirjin ta?"

"A wani zuwa da yayi ganin Abdallah, ba tareda sanin ta ba ya fice da shi a mota, tun safe har yamma, a ranar Rahinah har dan karamin hauka ta yi, Nene na kwantar mata da hankali tana gaya mata bazai ki dawo mata da dan ta ba tunda nono yake sha. Yafendo kam haushin Rahinah ta koma ji sabida rashin kawaicin ta akan yaron, tace ita bata taba ganin mara kunyar bafullatana irin Rahinah ba, rashin kunyar tata shahararriya ce kuma a kan dan fari, inji Yafendo. Idan ta kaita bango kuma ta ce ""kinibabbiya, sanda tasa Uban sa a daki yayi mata cikin sa ai bata ce masa rowar sa zata yi masa ba idan sun haife shi, in da gaske take son yaron ta koma gidan ubansa mana?"

Dukkansu basu san inda Habib ya kai Abdallah ya kuma dawo dashi ba.

Rahinah kamar ta shide da Abdallah ya dawo don murna.

****

"Yayi sallama a falon Ambasada Shehu, shi kuma ya amsa cikin sakin fuska da mutuntawa kamar yadda suka saba a kowacce haduwar su. Har kasa ya tsugunna ya gaishe shi. Shikuma ya soma yi masa fada akan irin ramar da yake yi, da kyar idan yana cin abinci yadda ya kamata. Ya ce ""shi mace bata isa tasa shi a wannan halin ba, don dukkansu daga karkataccen hakarkari aka halicce su. Yana da tabbacin Rahinah zata huce watarana kuma da kanta zata nemeshi ta nemi dawowa dakin ta. Haihuwa a tsakani ba wasa bace. Don haka ya kwantar da hankalin sa."

"Habib sai yayi murmushi, his beautiful serene smiles. Ya ce ""ai komai ya zo karshe ranka ya dade, na kammala karatuna zamana a kasar Jamus ya kare. Nazo ne in dauki Abdallah bisa iznin ku, zamu koma gida Zamfara""."

"Ambasada shiru yayi, hukuncin da yaron ya yanke yayi matukar impressing din sa. Da gaske gara yayi nisa da Rahinah ya kuma dauke dan sa, watakila hakan yasa ta yi gaggawar gano muhimmancin su cikin rayuwar ta."

"""Amma ka san mai raba ta da dan nan sai Allah ko? Kuma kana da wadda zata kula da shi kamar yadda mahaifiyar sa zata kula da shi? Idan babu, kai namiji bazaka iya rainon da ba, na gaya maka""."

"""Mahaifiyata tana raye ranka ya dade, sannan Yayata Badiyya, duk cikin su babu wanda bazai rike min shi kamar koma fiye da yana gaban mahaifiyar sa. Albarkar ku kawai nake bida, da fatan alkhairin ku""."

Ambasada couldn't keep his tears wato ya kasa maida hawayen sa. Yayi saurin share su kafin Habibu ya gani. Ya kira Nene ya gaya mata ko me kenan. Itama Nene tafi mijin ta shiga rudun tunanin mai iya raba Rahinah da Abdallah.

"Sai ga yaron ya shigo tinkis-tinkis, cikin tafiyar shi mara kwari, ya yi kyau cikin kayan sanyi, yana ganin Babansa ya tafi da gudu ya fada jikin sa. Habib sai ya ga kawai bari yayi amfani da wannan damar, kada dama ta biyu ta sake kubuce masa."

"""Zan tafi dashi yanzun nan ranka ya dade, ku gafarce ni"""

"Nene ta soma kuka, ta saba da yaron ya shiga ranta da zuciyar ta duka. Daga ita har Ambasada aka rasa mai karfin halin hana Habibu wannan danyen aikin, har ya fice falon da yaron a kafadun sa. A lokacin da Rahinah ke dakin ta tayi dai-dai a tsakiyar gadon ta tana ta sharar barci abinta."

""""""""""

"Koda ta farka bata ga yaron ba bata damu ba, ta dauka yana wasan sa ne a dakin su Ahlan kamar yadda ya saba. Tayi wanka ta ci abinci ta koshi ta janyo littafanta ta karkade, gobe ne zata koma makaranta daga deferring din ta. Saboda haka tana bukatar dumama kwakwalwar ta, duk da cewa a son karatu irin na Rahina ko da bata zuwa makaranta kuma babu jarrabawa a gaban ta bata fasa bitar littafanta ba lokaci-zuwa lokaci."

"Amma ga mamakin ta har tayi sallahr maghriba da Isha Abdallah bai shigo ba, bata kuma ji tashin muryar sa ba. Nene kuma tana sassan Daddy a irin wannan lokacin, watakila kuma ya bita can din ne."

"Amma da lokacin kwanciyar su yayi bata ganshi ba dole ta fito tana kwala masa kira. Gaban Nene da ke daki ya bada dam! Tayi zamanta a daki ta ki fitowa, sai ga Rahinah ta shigo."

"""Nene ashe kina nan? Abdallah nake ta nema tun rana rabo na da shi"". Nene ta daga ido ta dubeta idon ta fal tausayi, ta ce ""yaki Rahinah, zo nan mu yi magana""."

"Rahinah ta soma shiga tashin hankali, ta dafe kirjin ta da hannayen ta da karfi, ""ba dai wani abu ne ya same shi ba Nene?""""Ba abinda ya same shi Rahinah, he's healthy and vibrant, amma Baban sa ya ce mu gaya miki ya zo ya tafi da shi, idan kin canza ra'ayin ki kan zaman ku tare ku raini yaron tare ki fada masa zai dawo ku koma auren ku!"""

"Rahinah ta dora hannuwa aka ta zuba ihu, sannan ta sulale a wurin babu yadda take, tamkar wata mai tashin jinnu ta koma tana kuka tana birgima a kasa tana kiran Abdallah "" wayyo da na, wayyo Abdallah!"" Nene sai da ta firgita"

"ta kuma yi nadamar gaya mata ta wannan sigar, ita ta fada ne don Rahina ta ce ta amince zata koma dakin ta su kuma su yi wa Habibu magana ya dawo. Amma a yadda Rahina ta karbi lamarin babu zancen sulhu face Habibu Nahuche yayi mata kidnapping Da."

"Data gaji da ihu da birgima hawaye ya hade da majina duk jama'ar gidan na kanta har Yafendo, hatta Safeenah da bata son ta yau ta tausaya mata. Nene na bata hakuri tana gaya mata abu ne mai sauki, ta yarda kawai ta koma dakin ta ta raini dan ta a gaban ta amma ina! Tunanin Rahina yayi fintinkau da tunanin kowa. It goes far beyond mere or casual assumption ta riga ta sanyawa zuciyarta tsanar Habibu kuma bata jin akwai abinda zai kankare wannan"

tsanar ban da ikon Allah.

"Hanya ta saba babu ko lullubi data faki idon Nene ta shiga sallah, Yafendo ma ta koma daki ta rabu da ita, bata manta nisan dake tsakanin Cologne da Frankfurt ba tafiyar awanni biyu ce kwarara a mota, amma ji take zata iya zuwa a kafa....."

Tafe take a gefen titi tana kuka kamar mahaukaciya. Daidai lokacin da anka rufe kofar jirgin Lufthansa. wanda zai

"tashi zuwa kasar mu mai dimbin albarka. Ba da jimawa ba ya soma rugugin sa mai gigitarwa kafin ya dauki hanya dodar, ya daidaita sosai, ya cigaba da keta hazo a sararin samaniya......"

Ya tafi tareda duk wani farin cikin RAHINAH OMAR.....Ya kassara ta. ya raunata jarumtakar ta. A da tana ganin

"ita jaruma ce zata iya fuskantar komai don ta kwaci 'yancin ta wajen Habibu Nahuche. Ashe wani 'yancin ba ya kwatuwa ta karfi duk yanda anka so, Habibu bai shigo rayuwar ta don ya fita a sanda take so ba. Ya shigo ne don ya dai-daita (shattering) farin cikin ta ya raba ta da sauran hope din da ya saura mata a rayuwa......"

"""Allah ya isa na. Allah ya isa tsakanina da kai Habibu! Kuma ko zan mutu ba aure, ko haka zan kare rayuwata"

"single bazan koma gidan ka ba. mugu, magulmaci, maketaci, maha'inci, the rapist!""."

"Ita kadai take tafiya tana hada hanya tana sakin zance kamar zautacciya. Habibu ya shammace ta, shammatar da da ace idanun ta biyu ko duk kotun duniya zata taru a kanta bazata raba ta da danta ba. Ai addinin ma da ya bashi wannan damar sai idan dan ya fara girman da zai iya kula da kan sa."

"""Jahilin banza jahilin hopi, algungumi munafiki, in ba tsoro ba ka dauke shi gabana mana? Ai faduwar gaba asarar namiji ce ""."

"Babu wani mummunan suna da bata kira Habibu da shi ba, babu mugun alkaba'in da bata yi masa fata ba. A karshe ta fashe da kuka ta durkushe a inda take, data ga ta dauki hanyar barin Frankfurt kuma tafiya ta ki ci ta ki cinyewa."

"Hankalin ta ya fara dawowa jikin ta ta tabbata bazata iya kai kanta ga inda zata riski Habibu ba kuma bata da kudin motar da za ta biya a kaita, haka babu katin bankin ta a tare da ita."

Wannan ya tabbatar mata har yanzu tana cikin hankalin ta bakin cikin Nahuche bai haukatata ba.

"Zata yi amfani da sauran hankalin da ya rage mata wajen gina rayuwar ta, ta ga cewa bata kamu da ciwon damuwa ba, da wajen ganin cewa bai yi amfani da soyayyar da take wa Dan ta ya karasa cin galaba a kan ta ba, ya kara kassara ta, ta hanyar maida ta kurkukkun auren sa, wanda babu komai a ciki sai biyan bukatar ran sa."

"A tunanin ta har abada bata son Habibu, kuma har abadan bazata so shi ba. Abin da bata sani ba SO daban, haka bacin rai daban. Bacin rai is *mortal* and LOVE is *inevitable* . Watakila kuma ganin ta da shi na farko abinda ta ji akan sa wani abu ne daban ba so ba, wanda ta dinga fatan in sun zo mutuwa a jirgi...to Allah ya sa ta mutu manne cikin jikin sa."

*****

*NA HUCE..* ..is not for freee. It's 1000 via 3094856450

Sumayyah Kabara Firstbank

Shaidar biya 07030137870

": Habibu Mustapha Nahuche ya sauka a filin jirgin saman Abuja daga Frankfurt ta kasar Jamus da misalin karfe shidda na safiyar Jumaah, yana rungume da dan sa Abdallah a kafadun sa na dama, wanda ke ta barci sadidan cikin gajiya tun suna cikin jirgi."

"Kai in ka ga irin rikon tsantsenin da yayi ma dan na sa, gami da tsantsar kulawar da ya ke baiwa kankanin yaron, tsammani za ka yi cikin sa zai maida shi don tsananin So da kauna irin ta mahaifi. Mahaifin ma irin Habibu Nahuche wanda samun Uban da ke son dan sa kamar sa sai an tona. Har ila yau, tsatstsauran rikon da ya yi wa yaron, yana da nasaba da kasantuwar sa cikin fargaba da tsoron ko Raheenah za ta biyo bayan su afujajan kafin su kai ga sauka a kasar su ta haihuwa, Najeriya."

"Duk da ya san hakan ba mai yiyuwa bane ba tare da shiri ba. Amma hanakalin sa bai kwanta ba har sai da ya gan shi a filin jirgin saman birnin tarayyah. Saboda yana da tabbacin abu daya: A yadda Raheenah ke son Dan ta, da yadda ta damu da kasancewa tare da shi ko barci bai taba raba su ba, da kuma yadda ya san ta wajen kafiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login