Showing 81001 words to 84000 words out of 117287 words

Chapter 28 - Na Huce Sabuwar Rayuwa BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

aikinta duka dadi ba. Musamman Dr. Irshad. Ta ba su hakuri ta gaya musu ta yi aure ne ga hidimar iyali ta dawo wuyan ta, hada ayyuka biyu yanzu zai mata wahala, amma da yardar Allah tana nan a National Hospital in sun cimma conclusion a kai da maigidan ta, kuma za ta dinga kawo musu ziyara."

"Ta yi shawara da Nene ta waya kan tana son kai Abdallah islamiyyah, Nene ce ta zabi islamiyyar da za a kai shi, wato (I Scholars), ita da kanta ta je ta yi masa rijista a nan kusa da su makarantar ta ke, wato Gwarimpha, tunda uban sa boko kawai yake masa fata ita ba za ta bar shi ba karatun addini ba. Ba ta san cewa yana da niyyar kai shi idan ya dawo ba."

"Duk da haka uwa ta fi uba kulawa akan komai, uwa mafi uba ko da uban Sarki ne. Amma dai in reality Habib Nahuce bai da ragowa a kan kulawa da dan sa, yana kula da shi da komai nasa har fiye da yadda yake kula da Hotels din sa, kai dai bar shi da sangarta shi da jika shi da gata don a cewar sa don shi kadai (Abdallah) yake neman kudin."

******

NA HUCE

PAID BOOK

ABDALLAH

Ya tattara hankalin sa duka a kan calculations din da yake yi da karamar kwamfutar sa lokacin da Maman sa Rahinah ta shigo dakin.

"""Abdallah lokacin kwanciya ya yi, ka kashe komai ka zo mu tafi daki na mu kwanta, tunda dai yau Daddy ba ya nan""."

Ya tsuke fuska cikin gardama.

"""Daddy zai min fada in ya ji na kwana a dakin ki""."

"Ta zauna dab da shi, ta kai hannunta bisa tarin sumar kan sa da tarin kauna fal cikin idanun ta, tattare da kulawa irin ta uwa, ta ce, ""Abdallah ka kwantar da hankali da ni ka ji? Don kai na dawo gidan nan idan baka sani ba, bana jin dadi kana biye wa fada na da Baban ka, ni mahaifiyar ka ce wadda ba ka da kamar ta duk duniya, ka ji?"""

"Muryarsa na rawa ya ce, ""Ke ce ba kya son Baba na, ke ce ki ke wa Babana fada, in ya dau abincinki ki ce Allah ya isa, ni kuma bana so""."

"Rahinah ta yi maza ta ce, ""Ba ka ji daidai ba Abdallah, wallahi shi ne yake min laifi, shiga fadan iyaye babu kyau, ko yi musu labe, saboda kai na aje karatu na a baya, don in baka kulawa a shekarar farko ta rayuwar ka, yanzu ma kuma na aje duka ayyuka na don dai in rayu tare da kai, in cike kewar ka da na yi ta shekaru goma"". Ta soma matsar kwallah."

"""Allah ya yi umarni da a bi Uwa, a bi Uwa, a bi Uwa kafin ya ce a bi Uba Abdallah""."

Kalamai na kashe zuciya da sanya soyayya iri-iri Rahinah ta yi amfani da su a yau wajen brain-washing yaron da kwanyar sa ta riga ta gurbata a kan ta.

"Bai ce komai ba, amma sun sanya shi a rudani, ya shiga tunanin shin tsakanin ita da Daddy waye mai gaskiya? Waye yake cutar da dan uwan sa ko da da kalaman fatar baki ne? Bai taba jin sun gayawa junan su kalma mai dadi cikin murmushi da lumana ba."

"Duk yadda ta yi kokari don ya kwana a dakin ta bai yarda ba. A karshe ta ce,"

"""To shi ke nan Abdallah, amma ka yarda daga yau in dinga kai ka makaranta ina dauko ka? Ka yarda in sa ka a islamiyya? Ka yarda in ringa koya maka karatu?"""

"Sai ya gyada kai a hankali, exactly yadda Habibu ke gyada kan sa, wato ya amince da wannan. Amma ba zai kwana a dakin ta ba sai ta daina fada da Daddy."

"Tun daga ranar Rahinah ta ci gaba da kai shi makaranta tana dauko shi, girki iri-iri ta ke musu suna ci, aikin gwamnatin ma ta sanya wa ranta ta hakura da shi saboda Abdallah."

"Da daddare kafin su kwanta za su biya karatun da aka koya masa a islamiyya ta yi masa kari, ta yadda kafin su zo wajen a aji shi ya iya tiryan-tiryan. In sun gama sai ta taimaka masa ya yi home work din sa wato aikin gida na makarantar boko."

"Duk weekend kuma sai ta kai shi Children's Park, su biya (Dominos) su ci pizza ta saya masa ice cream sannan su dawo gida. Duk dai abinda ta san zai sanya shi nishadi da farin ciki da sakin jiki da ita. A kullum kuma tana gaya masa how much she loves him."

Yau da Abdallah ya dawo makaranta ya ci karo da dirkeken BIKE a kofar dakin sa. An makala greeting card a jiki ana yi masa murnar kammala jarrabawa lafiya.

*From MUM Rahinah Nahuche.*

"Wani tsalle Abdallah ya saka yana murna, ya ce,"

"""Mummy you are the best, thank you so much. I love you!"". Don haka kafin Habibu ya yi sati hudun sa a PortHearcourt ya dawo, Rahinah ta gama janye dan ta tas, ya saki jikin sa da ita, sannan ne ta ba wa Sahura damar dawowa gidan. Don ta rika taimaka mata da ayyukan gida."

******

*NA HUCE is not for free. It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara

First Bank*

"Daga inda ta ke tsaye tana iya jiyo tashin dariyar yaron suna takowa da sassarfa a tare zuwa upstairs din, dariyar da ta tafi tare da sautin bugun zuciyar Rahinah Omar, ta tabo can kasan ruhin ta da wani irin sabon son Dan ta, wani shaukin soyayyar uwa ya debe ta da gudun gaske ya kai ta bakin kofa, ta bude kofar gabadaya ta wangale ta tana jiran hawowar Abdallah, daidai lokacin da suka hawo saman, Abdallah na fadi da accent din sa na Zamfarawa."

"""Is she really inside?"" Wato (da gaske tana ciki)?"

"Sai ta ji duk damuwar ta ta yaye, damuwar da ya sanyata a ciki yanzunan, bakin cikin duniya da Habibu ya gama cusa mata na hana ta aiki a Nizamiye ya gushe nan da nan, wani farin ciki mara misaltuwa ya maye gurbin sa sakamakon jin dariyar Abdallah da sautin muryar sa kawai cikin kunnen ta."

"Habibu yana takawa da sassarfa zuwa saman benen, yana amsawa Abdallah."

"""Yo wa ya sani ne ko tana nan din? Ko kuma ta tsallake magana ta ta zame ta tafi Nizamiye din nata?"""

"Yana rufe baki idanun sa suka sauka cikin nata, wadanda ta ke kokarin lumshewa don kauda bacin ran da ke kwance kasan jijiyoyin su, da Habibun ya gama dasa mata yanzun nan ta waya."

"Yaron ya tsaya kawai yana kallon ta da kallo na rashin sabo, ita ma tana kallon sa with so much adoration cikin fararen kwayan idanun ta. Ta tuno shi yana karami, yadda baya iya barci sai ya ji shi cikin jikin ta, ta tuno dabdalar sa gidan Ambasada ya shiga nan ya fita can tare da su Ahlan. Ta tuno rana ta karshe da ta rabu da shi daga kwanciya"

"barcin laasar sai ta ji kwalla ta taram mata. Habibu ya cuce ta da yawa Allah ne kadai zai musu alkalanci amma don cuta ya gama cutar ta. Abdallah bai zurfafa kallon da yake mata ba ya kauda kai, ya bi bayan Baban sa wanda ya bude dakin sa ya shige ba tare da ya ce mata komai ba. Haka bai kara yi mata kallon arziki ba."

"Abdallah yana gab da shigewa shima, ta bude baki a hankali ta ce da shi cikin shaukin da bazai misaltu ba; ""Abdallah!!!""."

"Sai ya dakata kadan, shi bai dawo ba shi bai juyo ba haka shi bai shige dakin ba. Murmushi Rahinah ta yi wanda bai gama karade fuskar ta ba ta ce da shi."

"""Im saying Welcome Abdallah"". (Ina yi maka barka da zuwa)."

"Yana so ya amsa, because he dont know why he likes her, amma kuma sai ya tuno abubuwan da Habibu ya gaya masa a kan ta daren jiya a Lagos."

"""Wallahi ba ta son mu, tunda ta iya barin mu shekaru goma muna watangaririya cikin maraicin ta, ba ta taba neman mu ba."

"Ba ta zo don ta zauna da mu har abada ba Abdallah, sai don ta kwace ka daga hannu na ta kara gaba. Imagine Abdallah har kotu ta kai ni don a kwace ka daga hannuna a bata...""."

"Sai kawai ya yi mata wani irin kallo da ya fi kama da na rashin yarda da jin haushi zallah, ya sa kai zuwa dakin Baban sa ba tare da ya ce da ita ko uffan ba."

"In ta ce ran ta bai sosu ba, da biris din da Abdallah ya yi da ita, hakika ta yi karya. Amma sai ta ce a ran ta ""Da dai ba Habibu ne ya haife ka ba, shi ne za'a yi tsammanin halin ku ba zai zo daya ba""."

"Duk da gwiwar ta ta yi sanyi da irin karbar da dan ta Abdallah ya yi mata, for the first time na zuwan ta gare shi a matsayin mahaifiyar sa a tsayin rayuwar sa ta yanzu, kuma tana da tabbacin yaron ya san da hakan, don ta san zuwa yanzu ba zai kasa gaya masa gaskiyar wacece ita a gare shi ba, hakan bai hana ta tunanin me za ta ba shi ya ci ba. Daga yau zata fara rayuwar motherhood, zata dasa tubalin irin rayuwar da kowacce uwa take yi da yayan ta."

"Kitchen ta shiga ta soma tunanin me za ta dafa masa, ba ta san komai a kan likes and dislikes din sa ba wannan ma cuta ce mai zaman kanta da Habibu ya yi mata."

"Musaddiq ya fado mata a rai, da sauri ta latso shi a waya. Bayan sun gaisa da tambayar mutanen gida, ta ce, ""Musaddiq ni me ye favourite food din Junior ne?"""

"Musaddiq ya yi dariya, ya ce, ""Wannan ai shazumamu ne, kawai ki ba shi cornflakes din Kelloggs ya ji madara da suga zau, shikenan kin gama masa komai."

"Wasu lokutan kuma Mummy (Aunty Badiya) tana yi masa danwake ta sa shi a gaba ta ce sai ya fara ci zai sha Kelloggs""."

"Ta yi wa Musaddiq godiya, ta ce a ran ta, ""To ni kuma daga yau abincin da zai gina masa jiki ya kara masa girma zan koya masa ci (carbohydrate). Ni ba zan biye masa ba, gashi nan da jiki lange - lange kamar na Uban sa""."

Girki sosai Rahinah ta zage tana yi har da sanya apron. Farin cikin ganin sa ya sa ta maida tension din da Habibu ya hada mata a kan maganar aikin ta a ba komai ba. Za ta ba shi mamaki kuma. Wannan karon da gaske ta gama da BOKO; motherhood din ta ke so. Shine kuma ya saura mata yanzu. In ma da gatse ya fada don yana ganin bazata iya ba to ya yi sara a kan gaba.

"Ta kammala girkin ta mai rai da motsi tana kwashewa a sundukin abinci na zani (warmers), cous-cous ne ta yi wa wata irin dahuwa da %i eggies % da %i pices % masu sanya kiran yunwa, ga hanta ta wadace shi. Duk kitchen din da ma area din benen nasu ya dauki kamshin girkin Rahinah."

"Habibu ya shigo karamin kitchen din wanda anan upstairs din nasu yake, bayan yayi wanka yana sanya maballan wuyan rigar shi TommyHilfiger fara sol. Bakin wandon Jeans ne mai kauri a jikin sa. Kitchen ne na zamani mai aji da mukami da ya ji komai na na'urorin zamani amma karami ne. Ya shigo ne da niyyar daukar ruwan FARO mara sanyi domin ya hada wa Junior Kelloggs. Ko kusa bai kawo a ran sa Rahinah zata yi musu girki ba. Kai shi ba ya jin ma Rahinah ta iya shiga kicin banda rike allura. Ta wutsiyar ido ya hango lafiyayyen abincin da ta ke kwashewa a food warmers wanda kamshin sa kadai azaba ne ga mai jin yunwa kamar sa. Rabon sa da abinci tun na daren jiya a Ikko."

"Ya dauki ruwan da ya zo dauka har zai wuce ya yi wani tunani, in ya bar abincin nan bai ci ba bata da asara, ita gaba ma ta kai ta, kuma ya tabbata ba da shi ta dafa ba, bari kawai ya yi wa kan sa gata in ba haka ba da yunwa zai kwana, ya juyo gabadaya ya yi facing dinta hannun sa daya cikin aljihun wandon shi, daya rike da gorar ruwan Faro, ya ce cikin tsokana."

"""Sabbeni mu ina namu?"""

"Hararar sa ta yi son ran ta, ba tare da ta tanka ba, tamkar idanun ta zasu fado kasa, wata zuciyar ta ce ta rabu da shi shiru ma amsa ce, wata ta ce dan yaba masa mara dadi wadda zai kwana tana nukurkusar sa."

"""Na yi kama da kukun gidan ka ne? Aikin banza!""."

"Takowa ya yi zuwa gaban ta a hankali, ya tsaya dab da ita, har numfashin sa na dukan fuskar ta, ya kankance ido ya hade giran sama da na kasa tare da yin kasa da murya yadda ita kadai za ta ji shi ya ce."

Waye mai aikin banzan?%

Ta murguda baki ta ce duk wanda ya tsargu.....

"Kafin ta rufe baki ya kai hannu zai dauke warmer din gabadaya, ta yi maza ta danne hannun sa da iyakacin karfin ta ta rike foodflask din tamau."

"""Idan ka ci min abinci Habibu Allah ya isa!"""

"Karaf! A kunnen Junior da ke shigowa kicin din, don shirun Baban sa ya yi yawa daga zuwa dauko ruwa a firji, shine ya taso ya biyo bayan sa, jin abinda Rahinah ta fada, sai ya dan dakata cikin jin tsoro, ya rakube a jikin kofa jin yadda ta yi maganar cikin tsiwa kuma da daga sauti sannan ga uban sa ta dannewa hannu kamar zata karya shi. Da sauri ya juya ya koma daki kirjin sa na bugawa lokacin da ya ji Baban sa na fadin."

"""ina rokon ki Rahinah. Ki cigaba da yi min Allah ya isa, because it %j turning to BLESSINGS upon BLESSINGS. Allah ya isan ki ba ta tsiro, da tana tsiro da ban kawo yau ba, don Allah ki cigaba da yarfa min ita, shekaru goma ki kai kina jefo min ita tun daga Jamus zuwa Zamfara don na dauke miki Da, kin ga wani abu ya same ni ban da progresses da tarin achievments?"

"Ke kuwa yau ga ki kin kare a gidan auren da ki ke gudu. Qualifications sun zama na banza! Tunda na hana aikin. Na fada, na hana!"

"Da ma kin yi zaman aure na shekaru goman da ya fi miki alkhairi, da yanzu kin tara 'ya'ya biyar wadanda za su ji kan ki a tsufanki, at the very long last auren da ba kya so da shi ki ka tsira""."

"Ta yi maza ta dauke hannun ta daga kan nasa, sakamakon wani irin shock da ya bakunce su su duka. Lokacin da Habibu ya matse nata hannun shima da dayan hannun sa. Har yanzu tana ignoring kallon cikin idanun sa da ya ke binta da su ba tare da ya sani ba, ta ce,"

"""Idan kai ka dauki nauyin karatun nawa sai ka hana ni aikin in gani. Yaro kuma ya zo kenan hannun mahaifiyar sa, da shi da aikin al'umma duk zan iya hadawa in kula da abina. Babu ruwan ka."

"Me ye naka a ciki? Auren da aka maida da wannan ka'idar ta hana ni aiki aka mayar da shi? Ko ko salon muguntar ka da zaluncin ka da ba ya taba karewa a kai na?"""

"Habibu ya kara matsawa zuwa gaban ta sosai, kirjin sa da nata na bugawa wani irin fat-fat, ya kai hannu ya dago habar ta. Ta yi maza ta runtse ido gam! Tare da doke hannun nasa daga habar ta. Da azama ya matsa ya sumbaci eye-lashes din ta, sannan ya sauko a hankali kan karan hancin ta ya dora lips din sa a kai shima ya bashi kyakkwar sumba. Rahinah ta yi maza ta ja da baya tana hararar sa, domin hakika ya shammace ta, ya kawo sumbar a lokacin da bata zata ba, bata tsammana ba. Shi ko ido lumshe yake kallon ta tamkar ya hadiye ta ya huta da azabar soyayyar da ke kwance kasan kirjin sa, ya ce cikin sassanyar murya wadda ta samu rauni sanadin sumbar da ya yi. Kamar kuma baya so Abdallah ya jiyo su."

"""Aiki a Nizamiye na hana, na soke shi bakidaya daga yau. Idan kuma kina ganin ban isa ba, ko wasa nake, ko na yi kadan in yi umarni ki bi, to ki sake sa kafa a Nizamiye ki ga abin da zai faru %."

"Ya dauki flask din abincin gabadaya da plate da cokula biyu ya kama hanyar ficewa. Kasa ko motsi ta yi har ya fice daga kicin din. Bai ga Abdallah a dakin sa ba, don haka ya sauka zuwa downstairs inda main falon gidan yake."

"A can ya tadda shi ya yi zugum da remote din talabijin a hannu, amma hankalin sa ba ya kan cartoon din da ya kunna, ya yi nisa a tunani. Da sauri ya karasa gare shi, ya ce,"

"""Abdallah, what's up?"""

"Firgigit yaron ya juyo ya dube shi, shi bai taba jin wani ya yi wa Baban sa Allah ya isa ba, ko ya daga masa murya, everyone treats his father with utmost respect including Hajiyar Nahuche da ita ta haife shi, in tana so yayi mata abu lallashin sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login