Showing 78001 words to 81000 words out of 117287 words

Chapter 27 - Na Huce Sabuwar Rayuwa BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

na yi hakuri iya hakuri a kan ki, irin wanda ba kowane namiji ne kama na mai shekaru na zai iya ba. Shekaru goma kenan baki bar zuciyata da gangar jiki na sun huta ba, kin dawo cikin rayuwa ta again kina azabtar da ni da muguntar ki, bayan ban roke ki ki dawo ba tunda na fi kowa sanin wacece ke, tunda dai ni din mutum ne dan adam mai jini a jika kamar kowa ba daga sassake aka halicce ni ba dole yau in nemawa kai na mafita. Don haka yau daga ni sai Allah sai ke a dakin nan zaa goge raini da duk wani guntun munafunci da ke tsakani na da ke Rahinah ......"

"Ta wara dukkan idanun ta da gabadayan girman su tana kallon sa cikin sabon tsoron da kwayar idon ta ce kawai ta bayyana shi banda action din ta. Wato a idon ta tsoro ne karara, a zahiri kuma ego din ta da pride din ta na nuna akasin hakan. Habibu ya karanto hakan, ya hango tsananin tsoron abinda ya tunkaro ta shi din tsakiyar (almond shaped eyes) din ta, kwatankwacin na shekarun kuruciyar ta."

"Sai Habibu ya sassauta murya ya koma lallashi da ban baki. Irin wadanda shi kan sa bai san iya iya su ba ko a ina ya koyo su ba, ya yarda circumstances na rayuwa yana koyawa dan adam komai. Murya can kasa ya soma bayani cikin lallashi."

"Tafiya zan yi zuwa Portharcourt wadda za ta debe ni har sati hudu, kin ga kuwa ai akwai babbar matsala alhalin na san yanzu ina da mata wadda ke zaman bukatu na. Azumin kamar kamar ya daina aiki a jikina a kwanakin nan"

"Rahinah, wallahi ba na iya barci, a duk dare nikadai na san ya na ke wayar gari cikin soyayyar ki. Alhalin na san wannan karon ban tursasa ki ga aure na ba yardar kan ki da ta iyayen ki ce ta kawo ki cikin sa?"

"Don haka ga zabi; ko dai mu tafi tare mu yi honeymoon wanda bamu taba yi ba sai rikici da balai wanda ni na fara gajiya da su, rayuwa mai maana nake bukata yanzu, in yaso Abdallah a kai shi gidan Ambasada har mu dawo; ko kuma please yau daya kar ki yi kokawa da ni. Give me this night, I don't want it to be hurting only loving and"

"romantic!""."

"Da fadin hakan ya yi maza ya hada ta da jikin sa ya rungume ta tsam-tsam, wata irin kyakkyawar runguma tamkar zai tsaga kirjin sa ya sanya ta ciki ko ya samu sa'idah daga azabar da yake dandana na kauna da soyayyar ta, Rahinah Omar, na iya jin yadda sautin bugun zuciyar Habibu ke dokawa, tana harbawa da karfin gaske a nata kirjin da nauyin soyayyar dake addabar sa cikin ta."

"At the same time da Habibu Nahuche ya soma kissing din ta a zafafe, kamar kuma a yunwace, koko ta ce a urunce (hungrily) sannan in perfect style. Sumbatar ta kawai yake yadda ran sa ya ke so (tun daga sama har kasa. )!"

"Ko ta yi kokarin gocewa ko nokewa a zuwan pretending a wannan karon, a wannan dan tsukin, a wadannan yan dakikan gangar jikin ta bata bada goyon bayan hakan ba %’, domin ta kasa yin hakan ko yatsar ta ta kasa motsawa da nufin kwatar kai, sakamakon ruhin ta da ya yi accepting komai (with a warm welcome) gangar jikin ta kuma ta amsa kyakkyawan kiran mijin nata Habibu, wanda abinda ta jima tana buri tana fata tana kuma mafarki kenan daga gare shi wato (soyayyah)."

"The way and manner da Habibu yake sumbatar nata in style bai taba yin irin hakan ba, it's so soothing. Hatta babbar yatsar kafar ta ta tabbata yau Habibu bai bari ba, sai da ya kama ya tsotse in a soothing romantic manner, yana gaya mata wasu irin kalamai cikin kunnuwan ta da suka zam sirri ne a tsakanin su su biyu, wadanda duk na ban hakuri ne"

"da neman hadin kai, wadanda suka gigita Rahinah Omar, suka kuma hautsina kwanyar ta, suka gusar da hayyacin ta na wucin gadi."

"Wani tunani ne ya zo wa Rahinah a wannan lokacin, wato Habibu ya dauka ya ci banza raba ta da aikin ta da ya yi? Aikin da ta kwashe shekara goma tana karantawa don ta tsaya da kafafun ta. Ta zama abar hutun sa kawai daga yau tunda ta dage sai ta zauna da dan sa ko? An ce babu kyau kawo wani issue ga maigida a irin wannan lokacin, amma ita kam, ba ta da hanyar ramawa sai ta nan din. In yaso daga baya zata yi istigfari. Har kuma in da ahali ta nemi gafarar sa. Amma yau dinnan bata shirya karbar sa a matsayin miji ba, bata gama amincewa da canzawar sa ba, sannan ban hakurin sa bai gamsar da ita ba tunda yayi ne a lokacin da yake cikin halin bukatuwa."

"""Shin ka manta cewa zaman Da na na zo ba zaman ka nake ba? Ai zaman kula da Da nake yi babu wannan responsibility din cikin ajandar mu""."

Idanun Habibu ko buduwa ba sa iya yi a wannan lokacin. Cikin rikicewa da gigicewa ya soma ya daga ido ya dube ta ya soma begging.......

"""Ki yi wa Allah ki yi hakuri ki yi min rai Dr. Rahinah, likitar zuciya ta. likitar kunnen duk duniya, na kara fadi with"

"respect Dr. Rahinah ba Rahinah ba, wallahi za ki ci gaba da aikin ki amma ban da Nizamiye...... sabida wancan"

CMD din ne ba zan iya jurewa ba.

"Tuntuben harshe ne ya sa na ce kin bar aiki ba nufi na kwatakwata ba, kin san na san muhimmancin ilmin ki ba zan hana ki aiki ba no matter what ""."

"Ya durkusa a gabanta ya rungume kugun ta, ""I'm very sorry Dr. Rahinah, for everything, for all the past inconveniences......"

"Yanzu dai ki dubi girman Allah ki bar maganar komai kada ki shiga fushin Ubangijin ki, wallahi a bukace nake, na yi alkawarin daga baya zan saurare ki a kan duk abin da ki ke so ""."

"Rahinah ta tabbata kalaman da Habibu Nahuche yake amayarwa yau ba cikin hayyacin sa yake yin su ba, amma yau kam ta rantse sai dai ya mutu. Duk da ta tabbatar wannan din SABON Habibu ne, ba her Ex-Habibu ba. !!!"

"Juyawa ta yi da azama za ta fice daga dakin, ya yi maza ya sha gaban ta, murya a wahale ya ce."

"""Yau shekara goma sha daya da watanni rabon jiki na da naki Rahinah, rabon sa da na kowacce mace ma, rabon sa da wannan rayuwar, don duk wadda na kalla bata burge ni balle ta ban sha'awa sai ke kadai nake mafarki kullum."

Kin tafi ne tare da gangar jikin Habibun bakidaya ba zuciyar sa kadai ba. Da wannan na gane cewa don ke kadai aka halicce ni.....

"Don Allah Rahina. ki ci gaba da hukunta ni bayan haka, amma ki ba ni wannan hakkin ko na yau ne kadai, in ki ka"

"so daga yau ki shata min layin shekara guda na amince, please and please ki ji tausayi na Dr. Rahinah ""."

Ya tsugunna a kan gwiwoyin sa ya rungume kafafun ta. In tace zuciyar ta bata yi laushi ba ta yi karya. A take ya tuno raping din ta da ya rika yi babu ko tausayi at a very tender age sai ya ji hawayen nadama na zubo masa.

"Ita ma abin da ta ke tunawa kenan tana nata kananan hawayen. Wanda ya zo yayi fatali da kalaman sa na karshe da ke son kassara ta. Suna a haka suka ji Abdallah na buga kofa da sauri da sauri yana kiran sunan mahaifin sa. ""Daddy where are you?"""

"Da sauri Rahinah ta janye jiki daga gare shi ta shige bandakin ta ta rufe, shi kuma jiki ba kwari ya mike ya bude wa Abdallah kofar, bayan ya maida kayan jikin sa."

"""Daddy, dakin ta kuma ka zo? Tana ina? Ba ka ce ba ruwan mu da ita ba?"""

"Rahina na bandaki tana jin su, ya kasa bai wa Abdallah amsa sai diri-diri ya ke yi, duk da hawaye ne makale a idon ta sai ta ji dariya ta kwace mata. Ah to, yaro sarkin gaskiya, mai magana daya shi, in ba ruwan ku da ita me ya kawo ka dakin ta har da rufo kofa kuma?"

"Tana ji suka fice yana ta borin kunyar sa wa yaron, wai A.C din ta ce ta ke wuta shi ne ya gyara mata kada gobara ta kama musu gida."

"Abdallah ya ki yarda ya koma dakin sa, ya ce shi yau tsoro yake ji, lallai-lallai tare za su kwana. Ita da ma haka ta ke so Abdallah ya cece ta a wannan daren kuma sai haduwa ta gaba, all thanks to Abdallah."

Suna fita ta rufe kofar ta ba ta kuma zare mukullin daga jiki ba.

"Ta yi shirin barci ta kwanta kenan, ba ta dade da soma barcin ba ta ji Habibu na knocking kofar ta, yana kuma hadawa da rokon ta da murya kasa-kasa kan ta bude. Rahinah ta ce cikin murmushin keta,"

"""ka manta ne halan? Ni fa muguwa ce, kuma azzaluma ce already, don haka mu je a haka Malam Habibu, zan cigaba da amsa wadannan sunayen in practice (a aikace), har zuwa ranar da ka canza min suna""."

"""Idan kuma na ce na janye kalamai na fa Dr. Rahinah?"

"In kin so daga yau kada ki kara kebewa da ni sai bayan wata shekara goman na amince, in ki ka bar ni a yau zan cutu, zan halaka, wallahi ba zan iya jurewa ba. Zan nema wani wajen ko ta halin kaka""."

"Jikin ta ne ya hau rawa, ta ce, ""Wallahi Habibu ba zan bude maka ba, in ka yi forcing dina kuma zan tada Abdallah""."

"""Rahinah, don Allah... ki yi min rai. Na tuba na bi Allah na bi ki"" Ya fada cikin karkarwar murya da tsananin nadama da tashin hankali. Ganin da gasken ta ke bazata bude ba. Ga shi ya yi alkawarin babu shi babu sake forcing Rahinah a kan komai ma baa kan shimfidar sa kadai ba daga nan har zuwa karshen rayuwar su."

"Da ya tabbatar ba za ta bude din ba sai ya juya zuwa dakin sa zuciyar sa, ruhin sa da gangar jikinsa baki daya na wani irin tukuki da azabtuwa."

"A wannan daren daga shi har Rahinah babu wanda ya runtsa, ita (guilt) ne ya hana ta barcin don ta san ba ta kyauta ba, tana cikin fushin mala'iku in har ba ta nemi afuwar wannan zunubin ba, amma ba ta da courage (karfin zuciya) din da wani al'amari mai girma makamancin na baya zai sake gudana a tsakanin ta da Habibu Nahuche."

"Ta kuma gane wani abu, kamar ita din ba ta da sha'awa irin ta auratayya sam, ba ta sani ba ko duk mata haka suke a kan mazajen su? Ko kuwa memories din abin da ya faru a baya ne yake farautar ta har yanzu? Ya cire mata kaunar abun ma gabadaya?"

Ita kadai ce hakan ke faruwa da ita ko kuwa duka sauran mata ne???

"Ga shi ba ta da kawa balle aminiya ta jiki sai abokan aiki, wadda za ta iya tattauna irin wannan masalar da ita. Ta dade da gane hakan cewa ita bata da sexual desire, ko kuma kadan ne da ita? Ko kwatakwata ne babu ba ta gama ganewa ba har yanzu."

Yayin da Habibu ya samu kan sa da kwana yana nema wa Rahinah Omar gafara a wurin Ubangijin ta. Yana cewa a fili;

"Na yafe mata ya Allah, laifin da ta yi min komin yawan sa, wanda ta yi min a baya da duk wanda zata yi min anan gaba. Im the culprit. Komai ta yi min nine mai alhakin sa domin nine sila."

"Ya fi dauka nervousness din abin da ya yi mata a baya, shi yake haunting din ta har yanzu kuma shi ya hana ta appreciating love-making gaba daya shekarun girman ta, a gabadayan rayuwar ta ta yanzu."

"Duk sai ya ji ya tsani kan sa, ya kuma dorawa kan sa laifin komai."

Domin ya tabbatar ya riga ya yi wa zuciyar ta illah mai yawa. Don haka maganar yayi fushi da ita akan hakan ma bata taso ba.

Ya dauki alhakin komai ya dora a kan sa. At the end of all these yana son sanin consequences na forced sexual relation.

Yau sai ya samu kan sa da yin bincike a kan (psychological effects na forced sexual relation\marital rape) kawai don neman karin ilmi a kai ba don komai ba.

"Abubuwan da ya gani sun kara sa masa tausayin Rahinah, da nadamar abinda ya aikata mata a baya."

A binciken sa ya gano cewa forced sexual relation ko kuma a ce marital rape yana haifarwa da mata abubuwa masu tarin yawa psychologically. Sun hada da;

-Inferiority complex

-Depression

"-Feeling worthless and unloved, with no sense of dignity or pride"

-Fear of intimacy between couples.

A wasu lokutan mara karfin imani tana iya zama suicidal.

"Daga nan ya kara samun dalilin fushin Rahinah, dalilin ta na kasa yafe masa, why she is bitter with him and how he will try to overcome it."

A karshe ya yanke shawarar idan ya isa Portharcourt daga gobe zai fara yi wa Rahinah %’¯i exts messeges %’ na ban hakuri da nuna soyayya. Ba don ta bashi amsa ba. Zai kuma ci gaba da azumi da rokon Allah ya kare shi daga duk wani sharrin shaidan da ke giftawa a zuciyar sa.

******

WASHEGARI

"Da wuri ta tashi don ta shirya wa Abdallah abincin makaranta, duk da yana cewa ba ya son abincin ta ta dauki alwashin shirya masa abincin tafiya makaranta kullum. Sanda yunwa za ta kama shi a makarantar ya bude ya ci ai ba sani zai yi ba."

"Habibu ya fito cikin shirin sa tsaf na (Black Japanese Suit) mai jan neck tie, kafar shi rufe cikin rufaffen bakin takalmi da socks samfurin Armani, ya sanya siririn glasses din sa fari kal. Dakin Abdallah ya nufa don bayan ya yi barci jiya can ya maida shi, kuma sai direban ya sauke Abdallah ne zai wuce da shi filin jirgi ya wuce Fatakwal."

"Shi ya taimaka wa yaron ya yi wanka ya saka uniform din shi, sai ga ta ta shigo rike da (food-basket), rigar barci ce a jikin ta da hula, ta dora zanin atamfa a kan rigar. Habibu bai daga ido ya kalle ta ba, ta ce,"

"""Abdallah ga abincin ka, hope you will today eat Momma's food, (da fatan yau zaka ci abincin Maman ka) a yi karatu mai yawa, ban da guje-guje""."

"Daga dan har uban babu wanda ya tanka mata, daga bisani Habib ya dago cikin harara."

"""Please Ma'am, koma da abincin ki, ba ya bukata. Wannan wane irin naci ne? Ko da can ke ki ke ba shi?"""

"Ya fada cikin tsawar da ta firgita su ita da Abdallah. Ta san dalili, don haka ta juya tana kada masa bom-bom (irin kanka ake ji din nan) don ta san dole za su dauki abincin in ta bar wajen."

"Tana tafiya kuwa ya ce, ""Abdallah dauki mu je ka ji? Ai ba nata ba ne tunda ba ita ta saya ba""."

"Ya ba shi mukullai na gidan da na motocin gidan da cheque na kudi, ya ce ya kai mata da gudu ya ajiye kada ya ce komai ya zo su tafi."

Tana canza kaya za ta shiga wanka Abdallah ya shigo da gudu ya ajiye mukullai da cheque ya fice da gudu ba tare da ya ce mata komai ba.

"Ta ce, ""Ka daina gudu kada ka yi tuntube ka fadi"". Tana ji daga bakin kofa Habibu na ce da Abdallah."

"""Ko ina ruwanta in ka fadin? Na ga dai ba ta da asara?""."

"Abdallah ya ce, ""Wallahi kam Daddy. Shes annoying na ce ta daina kula ni amma ta ki"". Dariya suka yi kamar wasu abokai suka sarke hannun juna suna sauka zuwa wajen mota."

"Ba karamin jin dadin tafiyar Habibu PortHarcourt Rahinah ta yi ba, ko babu komai wannan ce damar da ta samu domin canza tunanin Abdallah a kan ta. Da ya riga ya gurbata masa. Tana tufka yana mata warwara kullum. Babu ko tsoron Allah ka dinga hada da da uwar sa. Gashi yace zai dade bai dawo ba."

"Kafin ya tafi ya aje masa direban da kullum zai kai shi ya dauko shi, wai shi Sani, amma tunda ya ba ta mukullin motoci da na gidan duka sai ta sa a ranta kullum ita za ta kai yaron da kan ta, ta kuma dauko shi. Hakan zai taimaka wajen sanya shakuwa ko ya ya a tsakanin su, kafin kanwa uwar gami ya dawo."

Ta rubuta takardar ajiye aiki ta kai asibitin Nizamiye.

"Barin Dr. Rahinah Nizamiye bai yi wa masu asibitin da ma abokan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login