Showing 24001 words to 27000 words out of 117287 words

Chapter 9 - Na Huce Sabuwar Rayuwa BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

da Shafa'atu ya zama tilas""."

"Habib da yake neman a yafe masa, ba abinda ba zai yi ba a lokacin. Ya ce da Yayar sa Badiyya ""ki bari na gama NYSC sannan a yi maganar auren, ni yanzu da ba ni da abin yi, da me zan yi auren?"""

"Badiyya ta ce, ""A can Jamus da me ka yi auren? Cewa nake karatu kake a inda baka da kowa ma? Balle anan da mu zamu rike maka matar. Ka yi auren ka dandani dadin sa da rashin dadin sa ne zaa kyale ka ka ci gaba da zama a haka?"

"In dai Shafa'atu ce ba bakuwar zafi ba ce, za ta iya zama a gidan nan tare da Hajiyar mu, sai a gyara muku sassan Baba""."

"Mikewa ya yi daga gurin yana kakkabe rigar sa, har da kunkuni kamar kuturu yana fadin."

"""Ke za ki dinga ciyar min da matar? An ce miki a Jamus ko kai dalibi ne kana rasa aikin yi da zai rike iyali? Nan kuwa fa? Ai ki ji da kan ki kawai Yaya Badiya, ki kyale ni in nemi kobo. In gwaninta za ki min, kawai ki kular min da Abdallah""."

"Yaron da ya riga ya shige zuciyar Dr. Badiyatu Nahuce farat daya, har fiye da son da takewa Habibu, ta kara rike shi sosai a jikin ta tana hararar Habibu, a lokaci guda tana mamakin irin karfin jinin sa. Yaro kamar Habibu yayi kakhi ya tofar, bai da maraba da shi a lokacin da yana kamar shi. Addu'a ta ke cikin ran ta Allah ya ba ta lafiya da tsawon ran kula da Abdallah, kamar, ko ma fiye da yana gaban mahaifiyar shi."

A washegari ta juya da Abdallah gidan ta a Kaduna.

******

NA HUCE Is not for free. It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara

Firstbank

Shaidar biya 07030137870

*SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI) 07030137870*

PAID BOOK

"Ba jimawa da dawowar sa ya yi registration na tafiya hidimar kasa. Aka tura shi Kwara State, ya tafi ya bar Abdallah hannun Yayar sa Aunty Badiya."

"Haka yaro Abdallah ya rayu karkashin kulawar Kakar sa Hajiyar Nahuce da Yar mahaifin sa Dr. Badiyatu Mustapha Nahuce, suna zuwa Kaduna ta sanya shi a Kindergarten na (Kad-Poly) tare da diyar ta Zahrah, kullum sai ta sauke su sannan ta wuce aiki."

"Sha biyun rana ta sa masinjanta ya dauko su, a can ofis din ta za su yi ta wasan su a gaban ta har ta gama abin da za ta yi su koma gida."

"In aka yi hutu kuma ta kawo shi Zamfara ya yi hutu a hannun Hajiya Kaltume, sabida wayon yaron da kokarin sa a karatu da hikimar sa da saurin shiga rai a wajen malamai (double promotion) aka yi ta yi masa ya koma Nursery 3 daga Nursery 1. Sanan duk karshen zango shi yake zuwa na daya a aji, kuma sai ya dawo da prizes gida. Dr. Badiya (is highly proud of her son Abdallah) tana fada a koda yaushe. Yana tuna mata da kuruciyar Abban sa shima haka yake da yana kamar sa. Duk inda yayi karatu sai yayi tambari."

"Zuwa wannan lokacin Abdallah ya manta da Raheenah, ya dauki Badiya a matsayin mahaifiyar sa. Hajiya Kaltume da yake kira ""Granny kuma ya san Kakar sa ce wadda ta haifi mahaifin sa. Yana kara girma yana fahimtar alaqar sa da kowa."

"Tsakanin shi da 'ya'yan Aunty Badiya ba za ka taba iya bambance wanne ne nata wanne ne na kanin ta Habib ba. Yayyen nasu Musaddiq, Mubaraq da Mu'allim suna kula da shi sosai shi da Zarah, don kuwa Uncle Habib (yadda suke kiran Habibu) ba su ajiye shi nan kusa ba, suna matukar son shi, sabida yadda yake nuna musu kauna shima duk lokacin da ya zo ganin Abdallah daga Kwara. Kaunar jini ce ta cakude da kauna ta musamman wadda suke yi wa Uncle Habibu, ta shafi dan sa Abdallah. Ko kuda in suna da iko ba zai sauka akan Abdallah ba."

"A haka ya kammala NYSC, sai Aunty Badiya ta karbi takardun sa ta baiwa Baban Musaddiq ya tafi da su Abuja don nema masa aikin yi."

"Kasancewar Baban Musaddiq babban ma'aikaci ne a Federal Ministry of Commerce and Industry wadanda Federal Govt. ke damawa da su a lokacin. Ga shi ya san manyan ma'aikata a can Abuja domin ya dade yana aiki, sai bai sha wahalar samar wa Habibu aiki ba tunda abu ne na wa ka sani, gashi da (qualifications) na Cologne University, ya samu aiki mai gwabi a babban Hotel din NICON NOGA, a lokacin shi ne hotel din da babu na biyun sa a Nigeria. Kuma fannin da Habibun ya karanta kenan wato (Hotel Administration)."

"Habib ya dade a Nicon - Noga, matsayi iri-iri a ya rike a cikin ta, daga karamin matsayi zuwa sama, promotion kan promotion akai-akai. Wani irin mutum ne shi mai nasibi akan duk abinda ya sa gaba. Ba don haka ba manyan mukaman da yake samu akai-akai a NICON cikin 'yan shekaru kalilan da bai isa ya same su a yan shekarun ba. Don akwai wadanda suka fi shi jimawa amma basu kawo matakin shi ba, abin kuma har da kwarewa da baiwa ta daban (exceptional talent) da Allah ya bashi."

"A lokacin ne aka bude babban hotel din Najeriya watau TRANSCORP HILTON inda Habib da wasu daga cikin manyan ma'aikatan (Nicon - Noga) suka samu karin matsayin komawa (Transcorp - Hilton), inda Habeeb ya rike mukamin mataimakin manager, ba kananan kudi ke shigo masa ba domin kuwa a Nigeria gabadaya babu hotel din da ya kama kafar (Transcorp - Hilton) a birnin tarayyah."

"Yawanci turawa, larabawa da sauran jajayen kunnuwa ke sauka a can idan suka zo Nigeria kan harkokin su, sai ko kusoshin kasar mu, da manyan 'yan kasuwanni, da ke yin conferences acan."

******

"NAHUCHE HOTELS, ZAMFARA"

"Idea din mallakar hotel nasa na kansa ta dade da ginuwa a ransa. A hankali yake saving, har ya tada tubalin ginin karamin gidan saukar baki 'guest inn' a kasar shi ta haihuwa wato ZAMFARA."

"Da nan ya fara kamar da wasa, sai gashi Allah ya sa masa albarka da ilhama a ciki, ya fadada guest inn din ya maida shi babban hotel mai zaman kan sa a jihar ta Zamfara cikin Gusau."

"Sabida yadda ba ya tsauwalawa ne da kuma kyawun hotel din gami da nagartar ma'aikatan sa ya sa ya yi attracting customers da masu kudin Zamfara nan da nan, inda ya fara da yi masa branch a birnin Tarayya, daga nan sai Lagos, inda can ne ya zamo (headquater) na (NAHUCHE GROUP OF HOTELS)."

"A cikin shekaru goma da dawowar sa daga kasar Jamus ya mallaki hotels manya-manya a duka manyan jihohin Najeriya. Ba ya wata sana'a sai wannan wadda ya karanta yake kuma da experience a kai, wato (Hotel Administration), ya san duk wata hanya ta bunkasa hotels (gidan saukar baki) a zamanance daga (Cologne) inda ya yi digirgiri da masta."

"Daga nan ne kuma 'yammata suka ce salamu alaykum, ta hanyar budewa Habibu wutar so da kokon bara, kamar za su cinye shi danyen sa, ga kuruciya ga rufin asiri ta ko'ina ya samu, amma babu iyali."

"Ga kyau na Zamfarawan usli tushen garin Nahuche. Ko marmarin aure ba ya yi, ba abinda baa cewa a kan sa a dalilin rashin aure, lokacin da sunan sa ya fara karade kafafan yada labarai a matsayin (Young Nigerian Hotels Owner) wasu ma sun ce neman maza ya hana shi aure."

"Irin wadanan miyagun maganganu da aka soma yi a kan Habibu Nahuche suna dawowa kunnen Yayar sa Badiya, kasancewar ta mai taammali da mutane daban-daban, ta sha titsiye shi ta ce, sai ya gaya mata ko ba shi da lafiyar da zai iya aure ne?"

"A irin wadannan lokutan, Habib Nahuche, dariya yake yi sosai, ya cewa Badiya,"

"""Ba ni da lafiyar ki ka gan ni da Da na mai tsananin kama da ni?"""

"Sai Badiya ta ce cikin kankantar da murya,"

"""To Habibu ko dai da gaske kana deviating ne saboda bakin cikin Maman Abdallah ta ki ka?"""

"A wannan karon ma murmushi ya yi wanda Badiya ta kasa fassarawa, yayi kasa da kai, sannan nan da nan murmushin ya bace daga kan kyakkyawar fuskar shi, sabida wannan ba shine karo na farko da yaji hakan ba (ana masa mummunan zargi), ya ce cikin Bazamfariyar Hausar shi mai dadin sauraro;"

"""Wannan kuma ai tsakkanin bawa... da Ubbangijin sa ne""."

*****

"Zuwa yanzu kam Shafa'atu 'ya'yan ta biyar kenan, tana auren ta a Talata-Mafara."

"Da farko ta gwada jiran sa kamar yadda Badiya ta kwadaitar da ita har ya gama NYSC ya samu aiki, amma tunda ya sa kafa a (Nicon - Noga) ba ta kara jin komai a kan sa ba. Bata kara jin duriyar Habibu ba. Zumunci ma ya yi rauni tsakanin iyayen su a dalilin hakan don iyayenta sun dauki laifin komai sun aza a kan Hajiyarsa, a ganinsu da ta takura masa da tuni ya auri Shafa'atu."

"Ita kuwa Hajiya Kaltume kullum Allah ta ke kai wa kukanta a kan auren dan ta Habibu, shi kuma ta bar wa zabi. Baa shaidar dan yau, amma ita kam ta shaidi nata. Sabida yawan ibada da tsaida sallah yana hani dga aikata alfasha wanda kuma kowa ya san dabiun Habibu kenan, ga yawan azumin tadawwui. Ta dade da sanin akwai abinda ya kulle a zuciyar sa tun daga kan Maman Abdallah. Wadda ita tasa ya ki jinin mata. Duk ya hada su yayi musu kudin goro. Har ila yau, Hajiya Kaltume ta gama fahimtar ba ya son Shafa'atu, in ta takura masa ya aure ta zaa bata goma ne daya ba ta gyaru ba. A lalata zumunci kuma auren bazai dore ba. Sannan ta fahimci baya yin wani abu na banza duk da ba"

"tare take da shi ba a yawancin lokuta amma ta fi kowa karantar sa, bata taba jin yana waya da 'yammata ba. Don ba wayar da ba ya iya amsawa a gaban ta."

"Ta fahimci in ta takura masa ya auri Shafa'atuba zai kula da ita ba don kwata-kwata yanzu hankalinsa bai kan mata. A duniya abu uku ya sanya a gaba; (bautar Allah da neman kudi, sai rainon dansa Abdallah, Dan da Raheenah Omar ta haifa masa)."

"Ita kan ta Dr. Badiya ba karamin gata ta ke samu a wurin Habibu ba, duk da kasancewarta mai albashi mai tsoka nata na kanta itama, to balle kuma mahaifiyarsa da Dansa. Wadanda duk abin da ya samo nasu ne, a cewar sa su yake nemawa. Duk fadi-tashin sa a rayuwa sabida su ne. Sau uku a jere Haj. Kaltume da Badiya na tafiya aikin Hajji duk shekara."

"Tuni ya buge gidan su an zuba gini na zamani na gani na fada, kai ka ce gidan wani minista ne ba gidan tsohuwa Kaltume matar marigayi Bilyamin Nahuce ba, duk fadin unguwar Kofar Jange babu gida mai fasali da zubin zamani da ya kai kwatankwacin GIDAN NAHUCE."

"Ga maaikata rututu Habibu ya zuba mata. Kullum zaka sameta zaune a tankareren falon ta akan kilishi mai taushi tana lazumi tana ibadah, don a cewar ta su kadai suka rage mata yanzu, sai ko ganin auren Habibullahi. Hajiyar Nahuche ta zama wanke goma ka tsoma biyar. Jawur da ita, tsafta da naira sun kama jikin ta. Ga hasken rikon addini. Gidan ta kullum cike da yan cin arziki daga jamaar unguwa dana garin su Nahuche."

"Daga baya Hajiya Kaltume ta soma karbar tayin hotunan 'yammata da ake kawo mata daga Nahuche da Bungudu, sannan yayan masu da shi anan Zamfara da iyayensu ke son hada auren 'ya'yansu da Lucky Habibu Nahuce duk haka ake kawowa Hajiyar Nahuche. Eh, wasu kan kira shi 'Lucky' sabida kafin ka samu mutum mai sa'a a kan duk abin da ya sa gaba kamar Habibu Mustapha za a dade."

"Komai ya sanyawa hannu na harkokin sa sai ya zama kamar magic sai ka ga ya bunkasa ya shahara ya yi albarka cikin dan lokaci. Wannan kuma albarkar bakin UWA ne da addu'o'inta da ba sa yankewa a gare shi. Kullum Haj. Kaltume a kan dugaduganta take kwana sallah, kuma duk yawancin addu'o'in ta akan Habibu ne."

"Nasarar rayuwa, kariya daga sharrin Shaidan, albarka a dukiyar sa, da mata tagari (wadda zata kaunace shi saboda Allah ba don dukiyar sa ba) su ne abubuwan da kullum take roka masa."

"Hotunan 'yammata iri-iri 'ya'yan manya a garin Zamfara da garin Bungudu da Nahuce an sha kawo wa Hajiya Kaltume, amma a duk lokacin da ta dumfari Habibu da su ko dubawa ba ya yi zai ce,"

"""Ki yi hakuri Hajiyata, ni na riga na gama aure a duniya""."

"In ta takura masa kan sai ya duba kuma sai ya fara mata yan kanan kwallah, da dole zata mayar dasu inda ta dauko cikin mutuwar jiki. In ya so tsokanar ta kuma sai yace."

"Hajiya kada ki damu akwai (hurul eeni a aljannah, inshaAllahu)."

"Bata taba daukar maganar sa a bakin komai ba, face lokaci ne bai yi ba, in lokacin yayi shi da kan sa zai kawo mata matar da yake so, bacin ran uwar Abdallah (Rahinah) ta yi amanna da cewa shi ke walagigi da shi har zuwa lokacin. Ya ke ganin don ita ta ki shi, ba zai samu mai kaunar sa ba. Ko kuwa an ce ita ce autar mata da za'a debewa sauran mata tsammani a kan ta??? A bisa wannan dalilin Hajiyar Nahuche ta ji ta fara tsanar wannan Rahinah duk da bata taba ganin ta ba ko a hoto."

******

"*MUTANEN JAMUS (BAYAN BARIN HABIBU FRANKFURT).* Tun daga lokacin da Habibu ya dauke mata Abdallah, rayuwa bata kara komawa yadda ta ke a baya ba ga Raheenah Omar. Sauran kadan ta zama depressed wato ciwon damuwa ya kama ta. Ita kadai sai ka same ta a dakinta tana magana cikin safah da marwah, karatu ta daina fahimtarsa kwata-kwata, zuwa makarantar tana yi ne kawai bisa tursasawar Nene da Ambasada Shehu, amma ta kasa concentrating a kan komai. Komai ya fice mata a ka. Hatta kasar Jamus bakidayan ta."

A jarrabawar karshen zangon da suka yi Ambasada Bichi bai ji dadin sakamakon Raheenah ba ko miskla zarrah; ta fadi courses har biyar. Don haka ya kira ta falonsa don su yi magana ta Uba da Da.

"""Rahinatuh. Ina son sanin hakikanin abinda ke damun ki? Akalla in ban miki maganin sa ba a matsayina na Uba zan baki shawara wadda nake ganin ta dace. Wannan wane irin mummunan sakamako ne nake gani haka?"""

"Raheenah ta share zufar da ta jika goshinta, cikin rauni da karaya ta ke wa Baban ta Ambasada magana. Ba tare da ta san maanar abinda take furtawa ba."

"""Ni kai na Daddy (ban san hakikanin abin da ke damuna ba), rayuwar ce kawai na gaji da ita. Na fi so in mutu in huta. Ji nake kamar ni kadai na yi saura a duniya, kamar rayuwata ta zo karshe........."

"Kamar babu wani sauran farin ciki da zan cimma a karshen ta, kamar duniya ta ta kare. Ji nake kamar wani tsuntsu ko kuma shaho ya zo daga sama ya tattare dukkan farin ciki na da burika na ya tashi sama firrr! Da su""."

"Wani irin murmushi Ambasada Shehu ya yi, irin nasu na manya da suka karanci halayyr dan adam, kafin ya ce,"

"""Kuma wannan TSUNTSU ko SHAHO ba kowa ba ne, HABIBU ne!!!."

He ran away with all your hopes and happiness... (ba tare da sanin ki ba ya tafi da dukkan fata da farin

cikin ki).

"Habibun da ki ke gujemawa da gangan, amma ruhin ki da zuciyar ki na tare da shi da Dan da ki ka haifa masa.."

"It's either two options; ko dai ki yi hankuri ki ba wa zuciyar ki abin da ta ke so don samun farin ciki da kwanciyar hankali, ko kuma ki ci gaba da horar da kan ki da kan ki a bisa kuskuren ki."

"Allah Ubangiji mai afuwa ne, Annabi (S.A.W) mai afuwa ne. Allah Ubangiji kuma yana son masu afuwa."

"Amma Rahinatu ke kin ce ba za ki yi afuwa ga Habibu ba a kan kankanin laifin da ya yi miki. Wanda ku kadai kuka san abin ku. Don haka sai ki koya wa zuciyarki juriyar rashin su, in har kina nan a kan bakanki, ki fuskanci rayuwar da ke fuskantar ki."

"Kina da babban aiki a gaban ki wanda ba ya son damuwa da rudani (karatun ta). A matsayi na na Baban ki, shawarar da zan ba ki ita ce ki koma addu'a, idan rabuwar ki da Uban dan ki ita ce mafi alkhairi, Allah ya ba ki zuciyar dangana."

"Idan dawowar su cikin rayuwar ki shi ne alkhairi Allah ya sanyaya miki zuciya su dawo cikin rayuwar ki ba da jimawa ba""."

"Raheenah ko kadan ba ta son yarda da abin da Ambasada ke fadi, wai- wai wai Habeebu ne tsuntsun da ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login