Showing 21001 words to 24000 words out of 117287 words

Chapter 8 - Na Huce Sabuwar Rayuwa BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

da naci akan abun data ke so, da bakin cikin shammatar da ya yi mata, ya tabbata za ta iya takowa ko da da rarrafe ne ko da akan gajimare ne tun daga Frankfurt, ta biyo bayan su ta cikin hazo don ta kwace dan ta Abdallah, shi ya sa bai je dauko Abdallah daga gidan Ambasada bama sai da ya kayyade ya kuma kintaci lokacin tashin jirgin su."

"A yayin da jirgin ya karci kasa ya bar babban birnin Frankfurt din Jamus, sai ya ji tamkar ya nannade komai na Raheenah Omar daga zuciyar sa, tamkar yadda ake nade tabarma, ya baro shi a can. Ya cire ta kenan HAR ABADA daga rayuwar sa, ya hakura da ita, ko da ita ce autar mata a duniya, kamar yadda babu shi babu kara yin aure a duniya."

"Raheenah Omar, ta kassara shi, ta raunata shi, ta ji masa ciwo mai muni a zuciya, bashi da sauran wata soyayya da zai iya baiwa wata diya mace, ta kashe duk wani burin sa a kan yaya mata (ko dama can bai da buri akan su, ita kadai Allah ya sallada zuciyar sa kan ta, ya jarrabce shi akan ta da mafi girman jarrabawa). Juya masa baya da ta yi da sulhun da ya nufa na alkhairi a gare su ya dauke duk wani farin ciki da walwalar sa, ta zagwanyar da farin cikin achievements din da ya dawo da su daga kasar Germany. Wato kwalayen sa guda biyu, masu daraja ta farko."

"A kan ta ya san so, a kan ta ya fara so, haka a kan ta ya kare so, kamar yadda daga kan ta ya rufe SO. Ta tafi da dukkan (charming and amiable) Habibu Nahuche bata bar shi da ko guda ba cikin dabiun sa da halayen sa na baya."

"Amma a matsayin sa na musulmi kuma haihuwar musulunci, ya san komai muqaddari ne daga Allah watakila Allah ya rubuta iya rayuwar auren da zai yi da Rahinah kenan ta kwanaki bakwai, watakila a rubutun kaddarar su; babu sauran zama a tsakanin su. Hakan ba zai sa ya kasa rayuwa a kasar haihuwar shi ba. Hakan ba zai hana shi godiyar Allah da ya bashi tsatso daga gare ta ba. Zai yi gammo ya dauki rayuwa a duk yadda ta zo masa, ba tare da Rahinah Omar a cikin ta ba."

"Abin da zai sa a gaba yanzu shi ne: hanyoyin da zai bi ya maida kobo ya koma dari don tserewa bakin ciki da takaicin duniya, don samawa Abdallah kyakkyawan future, da kuma hanyar da zai bi wajen rainon gudan ran sa (ABDALLAH), zai yi duk yadda zai yi wajen ganin ya bashi rayuwar da ta dace da kowanne Da mai gatan UBA har ma da UWA (tunda Hajiya da Badiya na raye) da kuma ilmi mai inganci."

"Ko a lahira ba ya fatan Allah ya sake hada shi ko a hanya da uwar Abdallah.. Infact, abinda ya lura a tare da Raheenah Omar; babu zuciyar imani ko kankani a cikin tsakiyar kirjin ta, babu compassion, babu love, babu affection, ita da sassakakken dutse basu da maraba. Taurin kai ko irin na mutanen farko, she has no love in her talk more of offering it to someone. To Idan so cuta ne. Hausawa suka ce hakuri ma magani ne!."

"Zai hadiyi hakurin nan komin dacin sa, komin baurin sa, komin girman sa, zai kuma hada da addu'a da rokon Allah dare da rana kan ya fidda Rahinah da komai nata daga zuciyar sa da rayuwar sa bakidaya."

"Daga Abuja shatar karamar mota ya dauka kai tsaye har garin su Zamfara, tun a wancan lokacin jihar Zamfara babu filin jirgi. Ya tsaya ya yi canjin kudin sa a Abuja daga Euros zuwa Naira, ya saya wa Abdallah abincin da zai rika ci a cikin mota har su isa Zamfara."

"A lokacin Abdallah ya tashi daga barci sai faman kalle kalle yake na ganin sa a bakon wuri da bakin fuskoki, amma ko tari bai yi da sunan kuka ba, tunda dama ya saba da Baban sa sosai."

******

UNGUWAR KOFAR JANGE ZAMFARA STATE (GIDAN MARIGAYI ALH. MUSTAPHA BILYAMIN NAHUCHE)

"Yau unguwar kofar Jange cike take makil da matasa, ana ta hada-hadar siyasa, unguwar ta cakude da hargowar samari da 'yan jagaliyar siyasa masu yawo da fastocin 'yan takara suna musu kamfen. Don haka da kyar direban da ya dauko su ya samu hanya suka kutsa suka isa har kofar gidan da ake kira 'GIDAN NAHUCE'."

"Duk inda suka gifta cikin unguwar tasu sai Habibu ya bi wurin da kallo (with nostalgia) da tsananin begen gida, yana mai tuno wani abu na dabdalar kuruciya da ya yi a wurin, shekaru bakwai kenan da barin sa gida idan har lissafin da yake yi daidai ne."

"Yau ga shi ya dawo gida lafiya, amma ba shi kadai ba kamar yadda ya tafi, ya dawo ne tare da wani replica din sa (photocopy of Habib Nahuce). Wanda kaddara ta tanadar masa, ta kuma ba shi ba tare da ya tsara ba."

"Yana godiya da wannan kaddara tasa da hannu bibbiyu, domin kyautar Da sukutum! Rahma ce daga Ubangijin Talikai. Wadda ba kowa Allah yak e baiwa ba."

Hajiyar Nahuce (kamar yadda kowa a dangi dama jamaar unguwar ke kiran ta) tana alwala da buta a gindin famfo lokacin da Habib ya yi sallama. Muryar sa ta dira a cikin kunnuwan ta kamar cikin mafarki.

"Sai ta dakata daga wanke kafafun ta da ta ke yi, ta yi tsam! Da ran ta, tana son gasgata abin da ta ji. Kafin ta dago manyan idanun ta wadanda da gani ka san babu tambaya ita ce ta haifi Habibu Mustapha Nahuce. Alamun girma da ya soma kamata bai boye zahirin kamannin su ba na Rumawan Nahuche."

"Bude baki ta yi cikin mamaki, da tuajjibi, don ko shekaranjiya sun yi waya dashi Habibun, amma bai ce mata yana tafe ba."

"""Wa nake gani kamar Habibuna? Habibullahi?"""

"Duk yadda Da ya kai ga canjawa, cikin halin jin dadi ne ko akasinsa, to fa Uwa ba ta kasa gane abinta. Don haka komawar Habibu kyakkyawan Bajamushe kuma gogaggen bakin bature bai hana Uwarsa Hajiya Kaltume gane shi ba, daga kallo na farko da ta yi masa."

"Har gabanta ya karaso ya sunkuya, cikin gajiya, sannan ba tare da ya ce komai ba ya mika mata Abdallah da ke hannunsa makale a kafadun sa. Amma sai Abdallah ya ki zuwa, ya makale sosai a jikin Baban nasa."

Jikin Hajiyar Nahuche ya hau rawa da makyarkyata.

"""Ni Kaltume Nahuce! Habibullahi ina ka samo yaro mai kama da kai haka???"""

"Ba jikin ta kadai ba, hatta muryar ta Hajiya karkarwa take yi."

"Magana ya shiga yi wa Abdullah da harshen German""Abdallah Sie istmeine Mutter, geh zuihr (she's my mother go to her)"". Yaron ya make kafada cikin rashin yarda, tare da sake makalewa cike da tsoro da kyuya a jikin Abban sa."

Yara suka soma shigo da jakunkunan Habibu manya-manyan trollies. Haj. Kaltume gabadaya mamaki da tsoro ya hana ta kokarin karbar yaron da yake ta faman son ta karba.

Sai ta fara hawaye daga tsaye. Sakamakon abinda zuciyar ta ta hasaso ta kissimo mata.

"""Sai ka fara gaya min ina ka samo shi tukunna zan karbe shi, Habibu Allah ya sa ba shegensa ka yi ba a can kasar masu jan kunne"". Idanunta na zub da hawaye suna nuna tsananin kidima da fargabar da ta ke ciki."

Da sauri Habib ya hau girgiza mata kai. Shima nasa idnun suka kawo kwallah.

"""Wannan ba rainon da ki ka yi min ba ne Hajiyata, ban taba yin zina ba, ban taba kusantar ta ba, tun ban san ma'anar ta ba kike nusar da ni illar ta, kuma har in mutu ba zan yi ba insha Allahu."

"Ina baki hakuri Hajiyarmu, domin hakika na miki laifi, (na yi aure a Jamus ba da saninki ba)"". Dogon Salati Hajiyar Nahuce ta saki,"

"""Aure kamar ya ya?"""

"Habibu bai bata amsa ba, sai ya kara mika mata Abdallah, wannan karon ba musu ta sa hannayen ta biyu ta karba, tunda dai ta samu tabbacin ba shegen sa akai ba. Sannan kalmar aure ta gitta. Komai zai biyo baya a ganinta zai kasance da sauki."

"Daki suka shiga, Habib ya shigo da jakunkunan sa, kafin ta yi komai flask ta jawo wanda dama ba ta rabo da kunun tsamiya a cikin sa, ta zuba a kofi ta saka dan suger ta motsa ta soma kokarin baiwa Abdallah."

"Kasancewar Yafendo tana ba shi ya san kunu sosai, ya karba yana sha, ta dora shi a cinyoyinta tana rirriga shi, sannan ta maida hankalinta kacokam a kan Habibun, wani irin mabayyanin bacin rai kwance-kwance baro-baro a kan dattijuwar fuskarta."

"""Yanzu Habibullahi wuyan ka har ya yi kaurin da za ka yi aure kan gaban kanka babu sanin kowa naka?"

"In Shafa'atu ce ba ka so ai ba sai ka yi haka zan san ba ka son ta ba, wane irin aure ni 'ya su sai ka ce wasan yara? Ina uwar dan da za ka dauko wannan dan tatsitsin yaron tun daga wata uwa duniya kai kadai?"""

"Habibu Nahuche, bai taba barin weakness din sa ya bayyana a gaban kowa ba, amma wannan UWA ce MAHAIFIYA ce, kafadar da kowanne dan Adam ke iya sauke damuwar sa babu haufin komai. Don haka sanda ya fara hawaye bai san sun zubo ba, dacin tuno kiyayyar Rahinah gare shi, sai da ya ji saukarsu a kan kundukukinsa, da damshinsu a kan fuskarsa."

"""Na yi duk iya kokari na a kan ta so ni, ta zauna da ni mu raini dan nan da Allah ya bamu tare abu ya faskara. Ban san meye aibu na har haka ba da Rahinah ta ki ni. A karshe mun rabu, rabuwa ta har abada, ni kuma na dauke Dan ba da saninta ba, amma marikanta sun san na dauke shi""."

"Ya kwashe gaskiyar komai, har sanadin auren ba-zatan ya gaya mata, sai dai wani sirrin ai bai faduwa, balle sirrin aure. Ya tsaya ya kafe a kan Raheenah ba ta sonsa kawai, sabida ya aure ta baa hannun iyayen ta ba, yace aurensu kaddara ne kawai da rabo rantsatstse daga Allah."

"Haj. Kaltume ta rasa abin da za ta ce, amma sai ta ji ya fi mata a kan a ce Habibu zina ya yi ya kawo mata yaron nan. Ta rungume Abdallah sosai a kirjinta, wanda zuwa lokacin ya samu barci yana sauke ajiyar zuciya."

"A daren ranar ta kira Badiyya wadda ke aure a garin Kaduna, ta ce duk abin da ta ke ta bari gobe ta zo Zamfara maganar ta fi karfin waya."

"Sannan ta sa almajiri ya share wa Habibu dakinsa, ya wanke masa toilet dinsa, sannan ya shigar masa da dukkan kayansa."

"Girki na musamman ta yi musu, tuwon shinkafa da miyar taushe da naman saniya zuku-zuku a ciki, ta yarfa man shanu sannan ta hadawa Habibu kunun zaki kasancewar yana son shi sosai mutumin sa ne, amma na gasara ziryan ba na farau-farau ba."

"Da dare ya yi Abdallah ya rikice kan bai kwana tare da Hajiya, sai Momin sa, don haka tare suka tafi dakin sa dake zaure yana ta rarrashin sa, sai da ya yi barci ya dauko shi ya maido wa Hajiyar shi."

"Hajiya Kaltume tana sallahr dare kamar yadda yake a aladar ta, jefe-jefi tana juyawa tana kallon kyakkyawan yaron dake barci cikin nutsuwa a gefen ta mai tsananin kama da Habibu, tamkar Habibun a lokacin da yana kamar sa, kaunar yaron na dada shiga ran ta, a cikin kowacce sujjadah data yi tana yi masa addua Allah ya raya shi rayuwa mai tsayi da albarka."

"Cikin wannan daren mai dimbin tarihi a rayuwar Habib da Raheenah. Dukkan su babu wanda ya runtsa. Ya fidda layinsa na kasar Jamus ya karairaya shi, ya taune shi ya zubar, ya saka MTN NG da ya saya a filin jirgin saman Abuja. Yana fatan yadda ya karairaya shi haka ya zubar, zuciyar sa ta karairaya Raheenah Omar ta zubar, da duk abinda ya shafe ta."

"Amma ko da ya so yin barci, sai barci ya ce dauke ni inda ka ajiye ni. Shin ko yaya rayuwa za ta ci gaba musu shi da Abdallah? Shi maraicin matar da yake so daya da daya a duniya? Abdallah maraicin uwar da ya budi ido da ita?"

"Wata Tambaya ce mai wuyar amsawa farat daya, da ya kasa amsawa kan sa, ya ce bai son ta ma ya san wannan yaudarar kai ne. Raheenah Omar, ta shigo rayuwar sa da wani irin karfi, ta yi tasiri mai yawa a cikin ta cikin auren da bai gaza kwanaki bakwai ba. Tasirin da kafin ya yi nasarar cire ta kwata-kwata, shi ma ya san zai sha wuya, kuma abu ne da ba zai tabbata a lokaci guda ba."

"But gradually, by trying to follow the path of reality; yana fatan canzuwar kaddararsu, yana fatan Raheena ta bar zuciyarsa ta sha iska haka, ta bar kwakwalwarsa ta sarara, ta bar gangar jikinsa da ruhin sa su huta. Ta bar sababbin abubuwa da suka fi ta muhimmanci su shigo."

"Ba shi ya iya runtsawa ba sai da ya dawo masallacin Kofar Jange sallar asubahi, sannan ne barcin gajiyar da ya tara ta zaman jirgi da shirye shiryen dawowa da ya jima yana yi ta karkashin kasa suka taru suka danne shi bakidaya."

******

"Kukan Abdallah ne ya tashe shi wajejen takwas na safe, ya karade gidan da kuka yana kiran ABBANSA da MOMIN SA... cikin harshen Jamusanci. Zuciyarsa ta yi wani irin karyewa, anya cikin hukuncin da ya yanke babu zalunci a ciki ga yaron da ma uwar kan ta?"

Yanzu haka yaron zai tashi bai san mahaifiyarsa ba alhalin tana raye a kololuwar duniya?

"Da tsananin mutuwar jiki ya fito tsakar gidan hannayensa zube cikin aljihu. Ya zubawa yaron ido daga bakin kofar shigowa cikin gidan. Idanun sa sun kada Abdallah na ganin sa ya taho da mugun gudu ya rungume shi, sannan ya soma gaya masa cikin harshen da yafi iyawa ya maida shi gun Mummyn sa, tashi Mummy din ba wannan ba, yana nufin Hajiyar sa."

Hajiya Kaltume ta fito daga daki tana ta mita.

"""Dan nema rigimamme, sakaltacce, ni bana son shagwaba ko kadan, da alama gidan ku can sun gama sangarta ka, in ba haka ba ta ya ya gotai-gotai da kai za ka saki kashi daga tsaye? A ba ka foo ka ki hawa?"""

"Murmushi Habib ya yi, shima ya san da gaske gidan Ambassada sun sakalta Abdallah, ya karaso inda ta ke yana dauke da Abdallahn."

"""Ke da maigidan naki za mu gan ku a rana, Maman shi pampers ta ke saka mishi ba ta dora shi a wani foo""."

"Hajiyar Nahuce ta ce, ""Au? Tunda irin 'ya'yan Badiya ne, to ba zan iya ba, ta zo ta dauki abin ta (Badiyar), su ma haka ta sangarta su da kin hawa foo, yaro dan shekara biyar sai ya saki kashi cikin auduga, mu ba haka iyayen mu suka raine mu ba, to ni ba zan iya wankin kashi a cikin pampers ba da girman yaro da komai""."

"Karshe Habibu ya je ya siyo pampers gari guda ya kawo mata, yana rokon ta kan ta lallaba Abdallah, a hankali zai koyi hawa foo din. Shi zai dinga yi masa tsarkin ya fidda pampers din. Hajiya sai ta ji su duka sun bata tausayi."

"Sai wajen la'asar Aunty Badiyya ta iso daga Kaduna, Aunty Badiya ba ta kama da Habeebu sam, bazaka ce ma cikin su daya ba, don ita mahaifin su sak ta dauko, fara ce ita Barumiyar Nahuce, sabanin Habeeb da yake wankan tarwada."

"Aunty Badiya 'yar boko ce sosai, domin kuwa (PHD holder) ce. A wannan lokacin ita ce mataimakiyar Provost ta (Kad-Poly), yayin da mijin ta babban ma'aikaci ne a Abuja, sabida aikinta ta ke zaune a Kaduna sai karshen mako yake zuwar musu."

"Yaran Aunty Badiya hudu ne duk maza ta karshen ce kawai mace, Zarah, wadda ba ta fi sa'ar Abdallah ba."

"Zuwan Badiya gida da ganin kanin ta da ta yi da Da, da labarin da ta tsinkaya daga bakin mahaifiyar su ya bata mata rai ba kadan ba."

"Ta yi fadan kamar ta yi ya ya! A karshe ta ce, ""Allah ya kara da ba ta son naka, Allah ya kara karawa, yanzu ai sai ka hakura ka zo ka auri mai son ka (tana nufin yar uwar sa Shafa'atu)""."

"Ita babban bacin ran ta yadda ya boye musu maganar auren nasa a Jamus, kamar wani wanda bashi da kowa, amma Hajiya Kaltume da ta ga fadan Badiya ya yi yawa, duk hakurin da Habibu ke ta bata ta ki sauraron sa, sai ta ce."

"""Maman Zarah, hakuri za ki yi mana, laifi kam ya riga ya yi sai dai tunda ya bada hakuri kuma ya ce ya yi ne don ya ceci kansa daga aikata zina a can, ai ina ga wannan ya isa hujjah, ni tuni na dauki kaddara."

"Yaro Allah ya raya mana shi, Ya sa Mahaddacin Alqur'ani ne""."

"Badiya ta ce ""Hakuri na daya ne Habibu ya auri Shafa'atu, ban ce ta rike masa yaro ba, ni zan hada da na waje na in rike, amma auren sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login