Showing 15001 words to 18000 words out of 117287 words

Chapter 6 - Na Huce Sabuwar Rayuwa BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

sau daya bata ji kewar sa ba. Bai bar mata wani abun tunawa a zaman da tayi da shi ba na kwanaki bakwai, banda kyakkyawar fuskarsa ta Rumawa data zauna a zuciyarta ta ki fita."

"""Na kira ka ne Habib, don in sanar da kai Raheenah na da ciki na watanni biyu""."

"Daga Habib har Raheenah, a tare zuciyarsu tayi wani irin dokawa, ta doka ta sake dokawa ta ci karo da bango. Idanuwan Rahinah kamar zasu fado kasa.....jin maganar tayi tamkar saukar aradu a kunnuwan ta, zata rantse ko mutuwar Dada da aka gaya mata a waya bata firgitata ta ruda ta kamar abinda Ambasada Shehu ya fada yanzu ba..."

"Yayin da Habib, Mustapha Nahuche ya wani irin lumshe idanunsa."

Wani albishir ne zai ce ko bushara da ba'a taba yi masa kwatankwacin sa ba.

Wani irin maganadisu ya ji yana fizgar zuciyar sa akan Raheenah da abinda ke cikin ta.. The feeling is so sweet da bai taba jin mai dadi a zuciyar sa kamar sa ba...nitsatstsen SO!

"A hankali ya bude idanun sa akan Raheenah, wadda ta tamke nata idanun tamau, hawaye na zirara ta gefe da gefen su."

"Which means she's not happy at all, she's mourning kaddar da ta afka mata rana daya. ta tabbata ta rasa farin cikin"

"ta daga yau, bata ga amfanin sauran rayuwar ta ba.."

Ashe dai ta yi gudun gara ne ta tadda zago Habib Nahuche bai shigo rayuwarta don ya fita a lokacin da take so ko

yake so ba.

"Kaddara bata kare tsakanin su ba, mai hada eternal dangantaka ya riga ya hada wato gamayyar jiki, wadda a yau ta maida ita matar Habib a karo na biyu har sai ta haife masa dan sa ko 'yar sa wanda take jin ba abinda ta tsana a duniya sama da kawo shi duniya..."

"A fili ta fada "". bai yi sa'ar mahaifi ba, he's but selfish by nature wato mutum ne mai son kan sa da yawa (tana"

nufin Habib din).

"Muryar Ambasada Shehu ta cigaba da ratsa mugun shirun da ya ratsa kamar daukewar ruwan sama. ""My dear Son and Daughter isn't it high time you reconcile? Tunda kun ga yadda kaddara tayi daku, kowanne Da yana burin ya tashi tsakanin iyayensa biyu, broken home shine babbar matsala ga tarbiyya da rayuwar kowanne yaro, rayuwa duka 'yar afuwa ce, in kuka afuwantawa juna kuka kuma zauna kuka gano matsalolin ku i'm sure zakuji dadin zama da juna tunda har ga rabo a tsakani. ""."

"Habibu yasa hanky dinsa ya goge gumin fuskarsa da hawayen da suka cika masa ido, wadanda yake da tabbacin na farin ciki ne. Ya dubi Raheenah wadda ta kautar da kai gefe tana jin tamkar Daddy na diga mata narkakkiyar dalma a kirjin ta da ya ce wai ta komawa auren Habibu. Ya ce ""ranka ya dade ni bani da matsala da hakan in har ta amince, abinda ba zanyi ba shine sake zaman aure da ita ba tare da amincewar ta 100% ba""."

"Rahinah ta juyo a hankali zuwa side din da yake, a hankali ta ce ""to in dai ko amincewata kake bukata to har abada bazamu koma ba, once beaten twice shy. Ba ciki ba ko 'ya'ya goma ne suka bayyana tsakani zan baka abin ka, yadda bana son ka haka bana maraba da duk abinda ya fito daga jikin ka. """

"""Rahinatu!"""

"Ambasada ya kira ta sounding fatherly, ""banda cin fuska ga wanda ya girme miki, balle mijin auren ki, wanda har yanzu kike cikin zummar auren sa, har sai idan kin haihu bai ce ya mayar dake ba. Tunda baki amincewa komen ba shikenan, amma ki janye munanan kalaman da kika yi masa""."

"Tana kuka sosai, kukan kaddarar da ta sameta, tace ""ka yi hakuri Daddy na maida kalamai na, amma har abada bazan koma masa ba""."

"""Shikenan zance ya kare, shima cewa yayi ai in kin amince. Kinga kuwa yasa tagociya kenan ga maganarsa. Don haka ki kwantar da hankalin ki kina hannun Daddyn ki, har Allah ya sauke ki lafiya""."

"Ya juya ga Habib, wanda tuni ya mike tsaye ya zuba hannayen sa cikin aljihun caftan din shi yana nufin barin dakin don in ya cigaba da zama zuciyar sa na iya fashewa ko tayi bindiga, a yiwa uwarsa da 'yar uwar sa asara! Ya gama saduda Rahinah bata son shi, kuma har abada bazata so shi ba, tunda rabon bazata da Allah ya kaddara a tsakanin su bai sa ta so shi din ba. Ya sha jin ance mace na fara son mijinta ne daga lokacin da rabo ya gifta a tsakanin su. Wanda ke nufin ita Rahinah is exceptional and extraordinary daga sauran mata......."

"""Daga wannan watan zaka dinga raba albashinka biyu kana bata rabi don ciyarwa har sai ta sauka. Ba don bazan iya daukar dawainiyar su ba sai don in baka damar ka ta uba da addini ya baka. Ka kuma koyi daukar responsibility na iyali tun daga yanzu""."

"Kansa a kasa idanunsa sun kada sun yi jazir yace babu damuwa insha Allahu. A turamin account number din ta"". ""Kana iya tafiya Habibu, Allah yayi muku albarka, yasa hakan shi ya fi alkhairi tsakanin ku""."

"Hawayen da yake ta rikewa ne suka kwace masa, ya juya kadan ya dubi Rahinah wadda ke kallon bayansa a lokacin, suka kuma hada ido, ji tayi zuciyarta na son karyewa (rauni irin na diya mace) amma ta amince wannan shine decision mai kyau ga rayuwar ta."

Sai ta maida idanunta ta lumshe su a hankali. Tana sauke ajiyar zuciya.

"Shikuma yasa kai ya fita daga dakin, babu ko waiwaye. Kamar yadda yake ji a ransa bazai kara waiwayar RAHINAH OMAR a rayuwar sa ba."

****

"Sai da ta kwashe kwanaki bakwai kafin ta samu karfin jikin ta, kuzarin jikin ta ya dawo ko ba duka ba. Har tana jin zata iya zuwa makaranta a gobe monday."

"Tana canza kayanta na barci zata kwanta Nene tayi sallama a dakin. ""Rahinatu kin yi barci ne?""""Yanzu dai nake shiri Nene""""to zo mu yi magana irin ta uwa da 'ya"" tayi murmushi, don Nene ta canza mata bakidaya tundaga samun cikin ta, sosai take janta a jiki yanzu, tana tausaya mata, domin gani take tayi kankanta da haihuwa kashin jikin ta kamar bai gama kwari ba. Sabida bata da manyan barage."

"Ta zauna daidai kafar Nene Bilki ita kuma tana daga saman gadon ta, tace ""Rahinah meyasa bazaki koma gidan mijin ki ba? Yaron nan ya bani tausayi sosai, da gani yana bukatar ki cikin rayuwar sa. Can you be open to me? Inaso in san meye matsalar ku? A matsayina na uwa zan iya bada shawara""."

"Rahinah ta sunkuyar da kai, tana tuno irin rashin tausayi da rashin soyayyar da Habib ya gwada mata, kullum tana ji a littafai cewa aure abu ne na soyayya, miji tarairayar matarsa yake yana bi da ita ta hanyar da bazata cutu a shimfida ba, amma Habib Nahuche a wannan fannin sai dai a kira shi NOVICE. Don haka bata ga amfanin zama dashi ba gara tayi rayuwarta single."

"Amma ta yaya zata iya gayawa Nene haka bata ga rashin kunyarta ba? Ita a ina tasan yadda ake rayuwar aure tunda ba taba yi tayi ba! She's just comparing and imagining. Don haka ta ga gara ta rike sirrin auren ta a zuciyarta, shi ciki ba anyi shi don cin tuwo ne kadai ba. Ta soma tunanin abinda ya kamata ta gayawa Nene, don ita duk wata shawara in dai akan ta komawa Habib ne to bata bukatar ta."

"""I don't love him Nene!"""

"Ta fada tana hawaye. ""Sabida bai aure ni cikin mutunci da daraja ba, ya sameni a arha da yawa. Cigaba da zama dashi zai iya janyomin psychological depression""."

"""Allah ya sawwake"" inji Nene Bilki, amma daga nan zuwa ki haihu ki nutsu ki fahimci zuciyar ki. Maiyiwuwa wani bacin rai ya sanya miki wanda ya lullube soyayyar. Bazan takura sai naji ba don tsakanin mace da mijinta sai Allah da ya halicce su. Amma shi AURE is not all about love my dear so many cirmustances na sanya mu zaman aure."

"Ni kinga so nake Saffenah ta samu mijin amma Allah bai bata ba, shikuwa Habibu har cikin kwayan idanun sa na hango SO mai yawa, wanda nake da yaqinin da zaki hakura ku koma zai isheku rabawa ku duka, ya yalwaci zuciyar kowannen ku."

"Yanzu mu bar maganar kome, mu yi ta karatun ki."

"Kinga dai position din jikin ki na da dana yanzu ba daya bane, ba zaki jure wannan zirga-zirgar tsakanin Frankfurt da Cologne ba. Don haka na kawo shawara me zai hana ki nemi iznin accessing lectures dinki online? In yaso lokacin jarabawa sai kije ki rubuta, doctor yace kina bukatar hutu sosai. In yaso in kika haihu sai ki cigaba yadda kike yi""."

"Rahina bata so ya zamo cewa kowacce shawara da Nene ta kawo bata dauki ko daya ba, banda haka da ta gaya mata. gara ta cigaba da zirga-zirga yadda cikin zai jijjigu ya bare. Cikin da bata maraba da shi ko kadan cikin"

rayuwar ta.

"""To shikenan Nene, insha Allah zan rubuta application na neman iznin hakan, sai a karbo takardar asibitin"" Nene tace ""hakan dai ya fi""."

"""Sai maganar abinci, duk abinda kika je shi kike so, shi zuciyar ki ta kwanta da shi, kada kiyi kauron baki ki gayamin, nikuma insha Allahu zan dafa miki muddin ina gida, in ma bana nan ga Yafendo, kada ki dinga zama ke kadai idan ba karatu kike ba"". ""Nagode, nagode Nene, Allah yayi muku sakayya da alkhairi, yadda kuka dubi maraici na Allah ya dubi haular ku a bayan ku""."

****

: *SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)* 07030137870

"A nata bangaren, Rahinah Omar, kwana tayi tunanin abinda ya faru a yau, tana mai tariyo komai dalla-dalla. Idan zuciyar jin tausayi ta kutso, sai zuciyar neman kwatar 'yanci ta hambare ta. Mutumin da bai ji tausayinta ba, ita akan me zata ji tausayin sa? Yana son ta koma ne don bukatun kansa amma bai taba tunanin ya tambayeta asalin ta ko na iyayen ta ba. Wanda ke kara tabbatar da cewa ba damuwar sa bace personal life din ta, abinda yake yimawa kawai shine a gaban sa."

"Ita wannan soyayya ta Habibu ta kasa ganeta, domin ta hada biyu da uku bata bata ma'ana ba. Tana burin auren mijin da ke matukar son ta, wanda zai rungumi maraicin ta kada yayi amfani da shi ya cutar da ita, wanda zai so ta da dukkan zuciyar sa. Amma Habibu fa? Ta tabbata ba don cikin nan ba da daga ranar da ya sake ta bazai kara waiwayota ba tunda duk abinda yake so daga gareta ya riga ya same shi."

"Tsaki tayi ta juya a hankali don taji dadin kwanciyar ta, sai taji gefen wuyan ta na kamshin Carolina Herrera (men) har zuwa lokacin. Abinda ya tuna mata da incidence din. Is what happened Haraam? Bata sani ba, in haramun ne tana neman gafarar Allah, domin kuwa bata da laifi, laifin ta shine kasa yi masa gardama wajen binsa tamkar rakumi da akala. ""Ya salamu sallim"". Ta fada a fili. Amma wani sako na zuciyar ta na gaya mata it's not haram din, tunda har yanzu cikin iddah take. Kuma abinda addini ke so a wannan tsakanin shine su yi sulhu. Sulhun da bata jin har abada zata yarda da shi."

"Washegari Nene ta rakata anti-natal da suke zuwa duk sati, likita ta dubata sosai ta kuma ce baby is breach sai an gyara masa kwanciya. Haka ta daure aka gyara sannan ta karasa duba ta, tace tanaso tayi mata alfarmar zuwa dakin haihuwa tare da mijin ta, sabida suna so mata su dinga haihuwa akan idanun mazajen su, domin neman karin kauna da soyayya, jin kai da tausayi a garesu. Gashi bata taba ganin ta ta zo tare da shi ba."

"Rahina dai bata ce komai ba, sai Nene ce ta ce baya kasar ne, amma in ya dawo kafin ta haihu da shi za'a shigo labour room."

"Rahinah ta daga 'yan idanun ta taba kallon Nene kamar tace da ita akan me za ki mata karya! Mun rabu, short and simple. Sai ta tuna abinda Ambasada ya taba gaya musu cewa saki ba karamin abu bane a kasar jamus, and it should be abiding by German law. Don haka rufe zancen da Nene tayi kawai shine daidai."

"Watanni biyu a gaba, ta shiga watan haihuwa, ta kuma gama shekarar farko ta karatun ta. Wato tsayin semester biyu. A haka take zuwa zana jarrabawa da tsohon ciki har ta kammala da kyakkyawan sakamako. Ambasada ya baiwa Nene kudi yace ta saya mata duk abinda zata bukata na haihuwa ba ruwansa da abinda Habibu zai bayar."

"A daren ranar ne kuma sai ga tarin akwatuna shaqe da sitturun jarirai unisex daga Habibu Nahuche. Hatta pampas da feeding bottle sai da ya sayawa dan sa, amma ita ko tsinke bai saka da sunan ta ba. Wannan ya sosa mata rai ba don tana son abin hannun sa ba, a'a yadda ya nuna yafi son abinda zata haifa yanzu akan ta shine abinda ya sosa zuciyar ta."

"""To a kan me?"""

Zuciyar ta tambaya.

"""A kan dalilin da nima ban sani ba!"" Ta amsawa kanta a fili."

****

EDD dinta saura kwana biyar rannan da daddare suna zaune a dakin Yafendo suna cin tuwo taji damshi-damshi daga kasan jikin ta. Bata kawo komai ba sabida sabida bata ji ciwon komai ba. An ce mata kuma ciwo ake ji mai tsanani.

Amma ba'a dauki wani dogon lokaci ba ta soma 'yan mutsu-mutsun da ya ja hankalin Yafendo kanta.

"""Yar nan lafiya kike yanka gumi haka?"" Tayi yake tace ""bakomai fa Yafendo, zafi kawai nake ji"" Yafendo ta gyada kai ba don ta harda ba suka cigaba da hira. Safeenah ta shigo ta gaida Yakumbo, sannan ta dubi Rahinah tace ""Nene ta ce kina da bako a falon Daddy "" amma kafin ta kai karshen maganar ta sai gani suka yi tana shure-shure."

"Yafendo tace ""Aha! Ni na san abun ne ya zo, kika yi mirsisi ke ga jaruma. Ke Safeentu kira Nenen ku ki gaya mata haihuwa ta zo a kawomin reza"". Safeenah ta zaro ido sannan ta fita a guje, kada taje ayi haihuwar a gabanta."

"Nene ta fado dakin da gudunta, tace ""Yafendo wace irin Reza? Ki rufa min asiri in mutu maza su kai ni, ba'a kasar mu muke ba inda ake haihuwar gida. Maza kwarara jikin ki Rahinah mu gangara asibiti, ga Habib nan yana nan ya zo sai ya kaimu tunda direba bai dawo ba har yanzu."""

"Tsananin halin da take ciki, shi ya hanata yin musun tafiya asibiti tare da Habibu kuma a cikin motarsa. Daga ita sai Nene a baya tana shafa mata kanta da bayan ta tana yi mata addu'a yayin da shi yake tuki cikin wani mawuyacin hali. Ji yake da zai iya da ya karba mata nakudar, kanar yadda ya zamo silar wahalar ta daga zuwa karatu."

"Sun samu ganin Dr. Saliha Widad wato likitar data ke gani itace on duty, nan da nan ta karbeta akan gadon tura marasa lafiya daga hannun Habibu da ya sunkotota gabadaya daga cikin mota zuwa cikin reception. Dr. Saliha ta duba ta tabbatar haihuwa ce gadan-gadan sai ta fito tana kiran sa. Ta tambayi Nene shine mijin Rahinah? Nene ta gyada kai ba tareda ta ce komai ba, yayin da likitar tace ""kazo ka tsaya tare da ita, ka ga yadda dan ka/'yar ka zai iso duniya""."

"Habibu ya hada kai da bango yana ce mata ""a'ah..."" tayi murmushi tace ""ashe raggo ne baban baby, Rahinah ta fika juriya. C'mmon ka biyo ni nace"". Ya juya yana kallon Nene sai ta gyada mai kai, don bata so a tsaya ana tone-tone. Ai har yanzu tana cikin zummar auren sa."

"Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki, haka ya daga kafa ya bi bayan Saliha Widad."

****

"""Dada!"""

"Kawai take kira hadi da sunan Allah,ta yi gumi kashirban, kanta na bisa cinyoyin Habibu gashin kanta ya bazu jikin sa. Ya rike hannayen ta cikin nasa, ita take nakudar amma ya fi ta hada gumi, jikin sa har kyarma yake. Dr. Saliha na fadi tayi nishi baby ya kusan isowa. Da ta daddage ta saki nishin kuwa sai gashi ya fado tare da mabiyar sa. Ya kuma canyara kuka a hannun Dr. Saliha wadda bakin ta ya kasa rufo, shekarar ta kusan goma tana karbar haihuwa amma bata taba ganin haihuwar katon baby black beauty irin na Rahinah ba. Saidai bai dauko komai nata ba har duhun fatar sa na mahaifin sa ne."

"Aka gyarata, aka gyara wajen haihuwar, aka dau baby ana gogewa da man zaitoon aka shirya shi tsaf cikin kayan sanyi, aka nannadeshi a shawul sannan aka kawo mata shi saitin kanta. Sai a lokacin ta soma dawowa hayyacin ta ta kuma ji kamar a jikin mutum take kwance. Tana so ta kalli fuskar babyn amma tana son ganin wanda ya baje mata jiki ta kanannade akai ta haihu haka. A hankali ta daga kanta, sai idanun ta cikin na Habibu, wanda hakan ya haifar mata da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login