Showing 84001 words to 87000 words out of 117287 words

Chapter 29 - Na Huce Sabuwar Rayuwa BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

take yi with love and respect, sabida son da take masa, ma'aikatan sa kuwa kamar su yi masa sujjada sabida ladabi, don haka sosai abin da Rahinah ta yi wa Daddyn sa ya tsaya masa a rai."

"Habibu bai kula da halin da yaron ke ciki ba ya hau zuba masa abincin yana cewa, ""Daure ka ci Abdallah, sai mu sha kelloggs din ko?""."

"Girgiza kai ya yi da sauri. Kamar mai kyamar abincin. ""Ni ma ba zan ci ba!""."

"""Saboda me Abdallah?"""

"Sai ya kasa gaya masa sabida ya ji ta yi masa Allah ya isa ne a kan abincin, kuma ta yi masa tsawa. Baban zai ce ya yi labe, bayan kullum yana hana shi sauraron zancen da ba nasa ba, kuma zai masa fada sosai."

"Don haka ya yi shiru, Habibu ya debo abincin a cokali zuwa bakin sa. Dole ya bude baki yana ci. Ga mamakin Habibu yau Junior ya ci abinci yau sosai, cin har ya wuce daidai cikin sa. Ko shi da ya yi loma daya da cous-cous din Dr. Rahinah, sai da ya ji hatta fatar kunnen sa yana wani irin motsawa. Sai ya gyara zama ya shiga ci sosai da wani irin shauki, ko kuwa santin hannun da ya sarrafa girkin ne? Ba zai iya cewa ba."

"Ko da ta koma daki kasa tabuka komai ta yi, sai safah da marwa da ta hau yi, yar sumbatar ta da Habibu yayi lightly duk ya birkitata ya kashe mata kuzari, ta fahimci Habibu zai iya barin komai a rayuwar sa amma banda kusantar jikin ta ko da accidently, wanda shi ma bai san lokacin da hakan ke faruwa da shi ba."

"Hakan ya faru sau biyu kenan daga zuwan ta gidan nan zuwa yau. To ashe da ma ya iya kiss din ne har haka a baya yayi mata kwauron sa, ko ko yanzu ne ya je ya koya tunda ya gane ire-iren abinda take so kenan? A sanin ta dai a hawan kawara kawai Habibu Nahuche ya iya yi wa matar sa yadda zata cutu. Sannan ya bi ta da bakar magana. Bai iya wannan sanyaya murya da lallashin ba irin wanda ya yi yanzu har abin ya tsirga a zuciyar mutum, ya wuce ya bar shi da tunanin abun. Tsaki tayi a fili."

"Haushin tunanin da ta ke yi din ne kuma ya zo ya kume ta, me ta zama ne haka? Me ya ke kokarin samun ta? Kada dai fa Habibu ya karya lagon ta cikin dan lokaci kalilan irin wannan ta tashi a tutar babu daga kan perception din ta. Yes, ta dade da gane shes romantic by nature, tana romance daga mijin auren ta, tana son romantic husband ba irin Habibu ba, tana son lallashi da tarairaya. Kuma akan haka ne ta tsani Habibu Nahuche, gashi tun baa je koina ba ta ga yana kokarin canzawa daga yadda ta san shi zuwa yadda ta ke son shi."

"Neman tsari ta shiga yi da shi a zuciyar ta, domin dama can ta sani, baa kidnapping Da kawai Habibu ya kware ba; har da sace zuciyar diya macen duk da ta yi kuskuren hawa kan hanyar sa."

Ta mike ta bi bayan su zuwa kasa don dai ta tabbatar Junior ya ci abincin da don shi ta girka ba don Uban sa ba.

"A ran ta ta yanke shawarar hakura da aikin Nizamiye din, don ta tabbatar masa da ba bokon ne a gabanta ba yanzu, kuma ba shi kadai ya ke son Abdallah ba, don ta gane kamar yana kokarin ya nuna wa yaron hakan, kamar ma ya zuge shi a kan bata son shi, amma aikin gwamnati ba za ta daina shi ba ko da hakan zai kai ga ta gurfanar da shi a gaban Baba Ambasada, tunda a maida auren su da aka yi ai babu wannan yarjejeniyar ta son zuciyar sa."

Uwa uba ta ci amfanin scholarship na gwamnatin kasar Najeriya wanda take fatan ta biya kasar ta wannan bashin ta hanyar cin moriyar ta. Tunda aikin ta halastacce ne a addinin muslunci.

"Ba ta daddara ba da shareta din da Abdallah yayi dazu, ta fito falon ta isa kusa da shi ta zauna. Da sauri ya matsa gefe kamar ta tsikare shi, yana ta faman sunkuyar da kai ga barin kallon ta, cikin mamaki Rahinah ta ce,"

"""Abdallah gudu na ka ke yi?"""

"Ya yi mata shiru, ya sunkuyar da kai kasa, ta ce, ""To tashi ka je ka yi sallah maza""."

"Ya yi kamar bai ji ta ba, don haka abin ya soma taba ran ta, ta tabbatar ba haka Habibu ya bar shi a kan ta ba kamar yadda ya ci mata alwashi. Tana iya ganin tsanar ta muraran cikin idanun yaron."

"Haka ta rabu da shi zuciyar ta na kuna ta koma daki, Habibu bai taba bakanta mata ba a tsayin dambarwar su irin yau, don me zai sako innocent yaro cikin rikicin su? Allah kadai ya san abinda ya gaya masa a kan ta. Ba haka yaron ya yi mata a gidan Aunty Badiyya ba. Amma babu komai baa san maci tuwo ba sai miya ta kare. Ita da shi zata ga wa yafi son Abdallahn."

"Ba ta daddara ba da daddare ta sake yi wa Abdallah girki. Wannan karon tuwon semo ne ta yi masa da miyar agushi, ta shirya abincin a kan tray ta nufi dakin Abdallah."

"Yana sauya kayan jikin sa zuwa na barci, lokacin da ta shigo da sallama. Abdallah a can cikin cikin sa ya amsa mata sallamar, don ya san muhimmancin amsa sallama a addini, ko ta waye balle ta iyaye, sannan duk ya bi ya bata rai, Rahinah ta langabar da kai rike da farantin da ta shiryo abincin da ruwa da lemo,"

"""Abdallah its time for dinner"". Wato Abdallah lokacin cin abincin dare yayi. Ya yi wani kicin-kicin da fuska, tare da turo baki gaba irin na yayan gata, ya ce,"

"""Na gode. Amma ba na ci""."

"Bata bata ran ta ba duk da kamar ya gwale ta ne (in a polite manner), kuma ta ji babu dadi, murmushi tayi ta ce. ""Ko da na ba ka a baki da hannu na?"""

Ta zauna a gefen sa ta bude plate din ta debo tuwon ta shafo miya da yatsun ta ta nufi bakin sa.

"Kin karba ya yi, ya kauda kai, sai da ta ce, ""Please Abdallah!"". Tare da yin narai-narai da idanun ta."

"Sai ya ji ya kasa tankwabar da wannan kyakkyawar kulawar tata, at least da girman sa dai ba wanda ya taba cewa zai bashi abinci a baki, har wata kunya ya ji, ya karbi plate din abincin daga hannun ta, ya ce a hankali kamar cikin rada."

"""Ki bari zan ci da kaina! Kada Daddy ya zo ya ga kina bani abinci a baki""."

"""That's my boy!"""

In ji Raheenah.

"Tana zaune har ya kammala ci, sai ta tattara kwanukan ta ce. ""Ka zo mu tafi daki na mu kwanta ko Abdallah? Kada mu makara sallar asubahi"". (Duk a kokarin ta na son ya sake da ita)."

"Ya dage kafada cikin rashin yarda. ""Ni ba zan kwana a dakin ki ba, sabida ban san ki ba, ina jiran Daddy na ya dawo ne, a dakin sa zan kwana, tare muke kwana in yana gari""."

""" And I'm also your Mum Abdallah"". ""Na sani!""."

"In ji yaron cikin kosawa,"

"""Amma don Allah ki daina shigowa daki na, don Allah""."

"Raheenah ta ji jikin ta ya fara yin la'asar ganin yaron ko hada ido da ita ba ya son yi, Allah kadai ya san irin hudubar da ya yi masa a kan ta."

"Sai ta mike zuwa dakin ta da sauri ba tare da ta iya daukan kwanukan da ya ci abincin ba, jin takun Habibu yana hawowa benen. Ya ga sanda ta shige daki da sauri, ita kuwa ko waiwayowa ba ta yi ba sakamakon kwallah da ta cika idanun ta."

"Ta dade ba ta samu barci ba yau, tana tunanin ta wace hanya za ta bi ta dawo da zuciyar dan ta gare ta? Gaskiya ba karamar cuta Habibu yai mata ba. Ya gama nesan ta ta da dan ta Abdallah."

"A dakin sa Habibu ya same shi ya yi tagumi da kwanukan abinci a gefe. Ya ce Abdallah ya ne? Wa ya baka abinci? Ita ce ta kawo ya amsa a gajarce, kuma Habibu ya gane wa ya ke nufi, amma sai ya ce ita wa? Abdallah ya yi shiru bai ce komai ba."

"Well Abdallah shes your Mum, and her food is nice, just eat, don ba ita ta kawo abincin ba ai ni na kawo, ita girkawa kawai ta yi, gyara zama mu cinye shi tas! Allah ne ya ce ta dafa ta bamu."

"Da safe ba ta gaza ba, ta sake shirya masa karin kumallo. Tana kokarin saukowa daga bene zuwa dining dake kasan bene don ta aje masa abincin, tunda dai don shi kadai ta ke girkin ta, ta ji muryar sa yana gaya wa Baban sa shi ba zai kara cin abincin ta ba, duk da cewa da dadi, ya tashi su tafi Eatry ko restaurant su samu abin da za su ci, tunda ta masa Allah ya isa a kan food (he will never love her)."

"Yana maganar (with a bitter tone) a kan harshen sa, shi kan sa Habibu ya yi mamakin maganganun yaron, daga yadda Abdallah yake maganar zaka fahimci abun ya tsaya masa a rai ya kasa wucewa, irin yaran nan ne da baa taba musu iyaye su kyale kuma yana da sanya abu a ran sa."

"Maganar da ta sa Rahinah komawa sama da gudu, shi kuma Habibu ya yi sakale yana kallon yaron, kafin ya ce, ""Junior kada ka kara labewa idan muna magana, ba Allah ya isa ta ce ba, ba ka ji daidai ba ne. Tashi mu tafi restaurant din""."

"Yana kokarin gayawa Habibu ba labewa ya yi ba shigar sa kicin din kenan ya ji tana fade Habibu ya yi masa tsawa..Cmmon, lets go i said. Dole yayi shiru yana kakkarwa. Ya saka takalmin sa ya bi bayan Baban nasa."

"Kwanansu uku kenan a haka, kullum sai ta musu girki sau uku a rana, ba ta damuwa don Junior ya ki ci, yaro sai zucciya kamar tsohon kuturu, tana samun wani irin pleasure ne a ranta idan tana hidimta masa. Ko kaya ya cire ba ta saka su a kwandon kayan wanki ita ke wanke masa su da kanta a injin wanki. Ta kuma shanya a toilet din sa."

Ya ki yarda ya kwana a dakin ta ko sau daya sai a nasa dakin. Duk lallashin data ke masa kuwa. Don haka da ta idar da sallar isha ta ke kulle kofar dakin ta ta bar mukullin a jiki.

"Abin da ba ta sani ba shi ne, ko da ta bar kofar a bude in dai Habibu ne ya dade da sallama ta ta wannan fuskar. Sex is now his last priority. Azumin tadawwu'in da yake yi duk Litinin da Alhamis har yanzu bai fasa ba. Musamman yanzu da yake tare da Rahinah Omar kullum, cikin gida daya, abubuwa ke neman canza masa a matsayin sa na namiji mai lafiya wanda ya san yana da iyali na halali, duk irin dauriyar sa wata rana baya iya barci, kusan kullum yanzun ya farlantawa kansa azumin nafilah baya shifting din ma. Duk ya kara ramewa dama ga jikin ba wani jiki ba. Sai ya kara nesanta kan sa da it aba ya bin ko hanyar dakin ta, ko motsin ta ya ji ta fito to kuwa zai kara zama a daki har sai ya ji ta koma dakin ta ta rufe."

"Sannan ba sa haduwa ma sam in ba a dakin Abdallah ba da safe. Yana da sabgogi masu yawa da yake gudanarwa a cikin Abuja da kuma Hotel din 'Transcorp Hilton' da suke dauke masa hankali daga Rahinah, ba ya zaman gidan ko kadan. Ko ba shi da abin yi a waje da dai ya zauna yana jin motsin ta yana kissime-kissimen da ba samu zai yi ba ya gwammace ya tafi gidan Ambasada ya karasa daren sa wajen su Yafendo. Ya ci abincin dare gun Nene tare da Abba Jakada."

Sanda zai koma zai tarar ta yi barci sai ya shige dakin sa bayan ya duba Abdallah wanda shi daman da wuri yak e barci.

"Satin su uku kenan da dawowar Abdallah Abuja har yau babu wani improvement tsakanin dan da uwar sa. Tana iya kokarin ta wajen jan sa a jiki da cusa masa akidu masu kyau, madadin na gata da ya tashi cikin su."

"Habibu bai gaya mata yau zai kai yaron makaranta ba. Ta makara ba ta fito da wuri ba, sai jin tashin motar su ta yi suna ficewa daga gidan. Da sauri ta daga labulen dakin ta sai ta hango su direba ya fita da su, Abdallah da kayan makaranta a jikin sa."

"Ya kamata a ce shi da ita sun zauna sun yi magana kafin yaron ya fara zuwa makaranta, amma sai ya ce wa kan sa ta yi kadan ya tsaya shawara da ita, don zai kai Abdallah makaranta."

Da can da yaron ya yi primary tana ina? Ba tana can tana gina kan ta ba? Don haka yanzu ma da ta ke cikin gidan in dai a kan al'amarin Abdallah ne ba ta da wani amfani a wurin sa.

*******

"""Pace-Setters Collage"" ya kai shi ya nema masa gurbi, aji daya na karamar sakandire, makaranta ce ta 'ya'yan masu ido da kwalli da ke wajejen Wuye, Life-Camp da Gwarimpha a Abuja."

"Can Habibu ya kai Abdallah, ya kuma ware direban da zai dinga kai shi yana dauko shi kasancewar shi ba mazauni ba, ko yana gari ba zai jure kai shi da dauko shi ba."

"A tsarin ayyukan hotels din sa bai iya sati guda cikakka a gari daya, don haka yanzu ma shirin wucewa Porthearcourt yake yi, kan ba yadda zai yi ne zai bar Abdallah daga shi sai Rahinah a gidan nan, wadda ya san neman duk hanyar da za ta samar mata kusanci da Abdallah ta ke yi."

"Tafiyar sa Portharcourt kuma a wannan dan tsakanin, daidai ta ke da ya bata filin da zata samu damar kanainaye masa yaro. Don kuwa shi yake kara zuga Abdallah kullum da cewa yayi a hankali da ita. Ba zama ta zo yi ba, in ya bari ya saba da ita ta zo ta kara gudar su shi zai sha wahala shi ba ruwan sa."

"Don haka da dacin rai yau ya shigo dakin ta, domin tilas zai yi tafiyar, an samu matsala tsakanin hotel din sa na PH da gwamnatin jihar ta Cross-Rivers suna so zasu saye filin wajen don amfanin gwamnati, don haka dole ya je ya daidaita komai in sayar musu zai yi ya sayar in ya so a sake gina wani a wani filin daban."

"Ya shiga dakin ne da niyyar gaya mata abinda zai bata mata rai, wanda har ya dawo zai hana ta shiga harkar Abdallah, ana-i-gobe zai tafi PH."

"Bai gan ta a dakin ba, har ya juya zai sauka kasa kuma sai ya jiyo maganar ta a dakin Abdallah. Don haka can ya bi su %’"

"Yana gab da shiga dakin ya ji tana dungure kan yaron tana cewa, ""Mai bakin hali da kuturwar zuciya kawai irin na Uban sa""."

"Yaron ya yi kicin-kicin da fuska, ya wani irin manne idon sa cikin takaici da bakin cikin kalaman ta, ya ce, ""Baban nawa ne mai bakin hali, mai kuturwar zuciya? Baba na!"""

"Rahinah ta ce, ""Exactly! Like father like son, ba ka baro shi a komai ba tun daga kamanni har halayya, ban da haka sau nawa zan gaya maka Abdallah ba'a yi wa uwa haka, ko ka ki ko ka so dai ni din nan dai, ni na haife ka, sai in gani in zaku iya sake ni, Allah ya ce a bi UWA sau uku, kafin ya ce A bi UBA, kuma ban gaya maka baa kwanciya da uniform ba? Da an dawo ake cirewa amma kullum sai na maimaita?"""

"Sai Abdallah ya ce cikin kunkuni, ""To ke Antyn gidan nan me ye damuwan ki da ni ne? Na roke ki ki daina shigowa daki na kin ki. Na fada miki I'm not your son, I'm Daddy's son!""."

"Sai jin sautin tafi suka yi daga bayan su, raf-raf-raf irin 'sound claps' dinnan. Habibu ya shigo dakin yana taku dai-dai cikin kasaita yana cewa,"

"""Ka haifu Abdallah! Ai ka san wasu mutanen ba su da zuciya kare ya cinye, in ba haka ba ban ga dalilin da za ta dinga shiga sabgar ka ba, bayan ta jefar da kai a zanin goyo ta rungumi boko""."

"Wannan karon a fusace ta ce, ""Ka daina yi min haka, ka daina fadin kowacce magana ta zo bakin ka a gaban sa... shi yasa yake kara tsana ta."

"Na jefar da shi ko ka sace shi? Ka dinga yi kana tsoron Allah cikin al'amarin ka""."

"Ta juya ta fice daga dakin hawaye fal idon ta. Ga ta da qi-fadi, ba ta son nuna raunin ta ko kadan a gaban Habibu Nahuce, shi yasa ta fice, kafin hawaye su gangaro mata, yaron sai ya ji dan tausayin ta ya kama shi yau, ganin tana hawaye da girman ta. Habibu kuwa ko a jikin sa, juyawa ya yi ya bi bayan ta zuwa dakin ta."

"8/24/22, 10:35 - Bilkisu Adam ƒ™©f•æ_Hq: U"

"ncle Usman ne ya yi mata waya yana neman karin bayani a kan barin aikin ta, don abokan aikin ta sun bi ta kan sa a kan ya roke ta ta dawo aiki. They cannot

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login