Showing 90001 words to 93000 words out of 117287 words

Chapter 31 - Na Huce Sabuwar Rayuwa BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

duk wani mataki da za ta dauka ko shawarar da za ta bayar wanda zai amfane su ne su duka, kuma ba ta taba mutuncin sa a idon wani ba. Idan kowa zai kalli da abin da ya yi din a baya ya hada shi da matsayin sa na yanzu da wani ido na daban, Badiya ba za ta kalle shi da haka ba."

Sai ga Rahinah yau tana voicing out damuwar ta ta shekara da shekaru tana yi tana kuka.

"""He has been sexually abusing me in my adolscent ages da sunan aure. Auren da aka yi ba da cikakkiyar yarda ta ba, a gantale babu martabar iyaye a ciki."

Abin da na fahimta ya saka karfi ya aure ni ne kawai a lokacin don biyan bukatar gangar jikinsa.

"A lokacin da ni kuma ina da abin da na saka a gaba, abin da ya kai ni kasar Jamus. Ban gama sanin hakikanin me aure ya kunsa ba sai a hannun sa."

"Sannan bai tsaya ya fahimtar da ni ta hanya mai kyau ba. Bai samar da fahimtar juna da kyakkyawar dangantaka ko kankani a tsakanin mu ba. Abinda ya sanya a gaba a wancan lokacin kawai shine ya sadu da ni anyhow, disregarding my feelings, my well being, my health and my humanity"

"A yanzu kuma da na girma na mallaki hankalin kai na da tunanin kaina, sai na gane cewa, a rayuwa ta ina son miji ma'abocin soyayyah (I want my husband to be loving, caring and romantic who is not given sex priority), don"

na fahimci ina da karancin bukata.

Na fi danganta hakan da psychological trauma din da Habibu ya gina a kwakwalwa ta a baya. Kwatakwata yanzu bana so ya kusance ni duk da na fahimci yana son canzawa ne...

To Anty kin ji abinda ke sanya mu samun sabani.

"Ta karasa fadin hakan cikin tsananin jin kunya da runtse idanun ta, tana mai sunkuyar da kai tana share hawaye. Amma yau sai ta ji ta sakayau, tunda ko ba komai ta amayar da abin da ba ta taba amayarwa kowa ba, abinda ta dade tana fama da shi ita kadai a ran ta, sai ta ji tamkar an zare mata kaya daga zuciyar ta."

"Aunty Badiya ta yi mamaki a kan labarin da Rahinah ta bata, kuma a kasan ran ta ta ji kunya sosai kamar ita ce Habibu Nahuchen, eh, dole Habibu Nahuche ya yi gummm da bakin sa in aka ce Rahinah ce autar mata da ya ki yin aure sabida ta ki shi, har wani lokacin ya bige da hawaye, ashe shi ya san danyen aikin da ya aikata mata, alhaki kuma yasa alamarin ya rikide masa zuwa soyayyah ta ce,"

"""In kin duba shekarun sa a wancan lokacin za ki gane sha'awa ce ta sa shi auren ki, irin ta tashen balaga, a irin wadannan lokutan maza kalilan ke tsallakewa hadarin zina ko masturbation. An gode Allah da ya bada sadaki aka daura muku aure bai bi ta wata hanyar ya same ki ba, kin san kuma in a can kasashen da ku ke ne hakan ba wani abu ba ne, na tabbata addu'ar UWA da tsayuwar daren ta a kan sa ne ya sa a ka kare a haka."

In kuma da ace yayi raping dinki ne ba auren a can Jamus yadda suka dauki rape case da muhimmanci fiye da kasar mu hukuncin sa a shariance mai girma ne. Banda hukuncin da yafi na kowanne wato na lahira.

"Amma a addinance mijin ki bai aikata haramun ba tunda a wani kaulin karbar sadaki na nufin amincewa, but zamu kira abun deviance tunda ya saki kyakkyawar koyarwar sunnah. Ayar da tace matan ku gonakin ku ne bata nufin ku afka musu babu dan aike babu amincewar su. (Allah shine mafi sani)"

"Don haka don Allah don Annabi Rahinah ki bar wannan ya shige daga zuciyar ki, na yarda Habibu yayi laifi kuma na tabbata duk da bai gaya min ba a halin yanzu da girma da hankali suka game jikin sa yana ta nadama, ki dubi Allah kani na ya ci darajar aure da ta alfarmar ya biya sadaki, ki ba shi dama ki ga irin repenting din sa."

"Allah Ubangiji muna masa laifin da ya fi wannan, amma kullum cikin afuwanta mana yake in mun nemi gafara. Allah ya ce ka yi wa musulmi uzuri sau sabain kafin ka kamashi da yi maka laifi, ki yi masa uzuri da tsoron Allahn da ya ji bai nemeki da zina ba a inda yake da duk wata dama ta samun hakan."

"Maimakon haka sai ya alkinta ki a dakin aure domin ya zama garkuwa kuma suttura a gare ki. Ki yafe masa Rahinah, ba don ni ba, ba don shi ba. Ki duba albarkar dan da Allah ya ba ku a sanadin hakan ki yi hakuri, ki sa a ran ki kaddarar zuwan Abdallah duniya ne ya janyo auren naku ma gabadaya""."

"Rahinah ta sa habar zanin ta tana share hawayen ta cikin shessheka, ta ce,"

"""Na hakura Aunty, wallahi daga yau na yafe masa, ba zan kara tada zancen nan ba""."

"Aunty Badiya ta rungumota jikin ta. ""Na ji dadin jin wannan. Allah ya yafe miki ke ma, tare da mu bakidaya, da iyayen mu da suka kwanta dama. Kuma ki nemi gafarar sa kan hakkin sa da ki ke ta dannewa ba tare da ya san me ye hakikanin matsalar ki ba."

"Yanzu ai Rahinah zamani ya ci gaba, bayan psychological trauma na abinda ya faru a baya akwai magunguna na zamani da na gargajiya da zasu gyara wannan matsalar, baa barin irin wadannan kananun matsalolin sakaka su hana zaman aure armashi, tuni ake maganin su."

"Mostly cutar sanyi ita ke kawo karancin sha'awa, akwai magunguna na gargajiya da na Bature wadanda za su daidaita sexual behaviour din ki, musamman na kasashen Indonesia da Asia."

"Nan Africa ma kasashenmu irin Nijar, da garuruwan Sokoto da Katsina suna sarrafa su don amfanin ma'aurata. Na yi alkawarin kawo miki wadanda za su daidaita wannan sabanin."

"Shi kuma Habibu ki ba shi dama, ki kwantar da hankalin ki da shi, don ta haka ne kadai za ki gane ya canza ko bai canza ba. Amma kina ta rikici da shi kullum a kan Da, yaushe ki ka san yadda yake in bed a yanzu? Bana ko tantamar har da bakin cikin hakan yake tunzura shi yake tono abin da zai sa ku hau sama ku fado a kan yaro, wanda babu ruwan sa. Maza a wannan fannin basu da ragowa Rahinah kuma ba sa uzuri."

"Dubi yadda walwalar Abdallah ta canza, amma ba ku kula ba, kun fi maida hankali ga tonon juna babu gaira babu dalili, yaro na ba haka yake ba, duk kun canza min shi. (He is healthy and energetic) kan ya zo hannun ku""."

"Murmushi ta yi, a ranta ta amince ta karbi duka shawarwarin Aunty Badiya, da niyyar za ta ba shi dama ta gani ya canza ko bai canza din ba?"

"Idan ta yarda ya canza din, sannan ne ita ma za ta yi amfani da daya shawarar ta Aunty, wato yin amfani da taimakon da za ta kawo mata."

"Tare suka shiga kicin da Aunty kamar kanwar miji ba Yar miji ba. Girki na musamman suka shirya suka aza a dining, sannan suka yi wanka suka yi sallah, suka zauna a falo suna kallo suna jiran dawowar sa."

"Amma sai waya ya bugowa Aunty ya ce, ba zai samu dawowa ba, ya wuce Lagos. Ran Aunty ya baci ta hau fada, ""Haba Habibu? Wannan wacce irin rayuwa ce? Da da yanzu da ka ke shawagin ka duk inda ka ke so babu notice din kowa da yanzu da ka aje iyali daban."

"Kada ka kara tafiya wani gari ba tare da cikakken sani da cikakkiyar sallama da iyalin ka ba, this is sheer nonsense"". Murmushin da ya yi har ta cikin wayar ta ji sautin sa. Ya ce,"

"""Maman Musaddiq ke nan! Matar da ta ke son ka, ta kuma damu da kai ita ke damuwa da zaman ka a gida, sometimes gara ma ka tafi inda ayyuka za su mantar da kai cewa ka aje iyalin. A bar kaza cikin gashin ta, amma 'yar ku duk ilminta na nasara ne kawai, tana bukatar training na UWA, a kan zaman aure saboda goyon Kaka ce..."" Aunty ta ce, ""Na sani Habibu, kuma na yarda da kai, as far as I'm concerned now zan yi iyaka kokari na a kawo karshen matsalolin nan duka, idan har ka bar maganar auren da ka rakito""."

"""Kun makara Aunty, its too late! Don har na samu mata a Bidda mun daidaita da Yayan ta yanzun nan, wanda tare muke da shi a Transcorp Hilton, in na dawo zan je Biddan in ganta ku kai kudin aure. Sunan ta Zeena""."

"Ya kara da cewa, ""Kada fa ki damu, ba zan hada ta gida daya da 'yar ku mai halin mutanen farko ba, ko don kada ta lalata min tarbiyyar ta da rashin sanin darajar aure""."

"Aunty ta ce, ""Yaa Salam! Habibu me yayi zafi? Ina raba ka da matan zamani, wallahi Allah duk wadda za ta aure ka a halin yanzu ba soyayyar Allah ba ce, abin hannun ka ta ke hange, ka fara dawowa gida tukunna ka bamu wata uku, daga nan in komai bai canza ba, na yarda ko uku za ka karo ka yi ta karowa""."

Bai san sanda ya ce.

"''Wata ukun zan kara nan gaba babu mace? Ai sai dai in mata sun kare a duniya ne. In ba za ki hado min lefe ba Maman Musaddiq ina da masu hadowa fa. Wannan da kudi na ma zan hada, in wancan gudunmawa ki ka ba ni don ki san cewa I'm serious""."

"Da ta ci gaba da turzawa kan sai ya bar maganar karin aure ya dawo gida tukunna, in ya so nan nan da wata uku sannan ya sake tado maganar (hausar ta zuwa lokacin ya ga irin canjin da aka samu sun daidaita da Rahinah), sai ya ce mata,"

"""Maman Musaddiq, bana jayayya da ke kin sani, amma yau kam, na yi."

"Ba zan kara sati biyu babu matar aure ta hakika a gida na ba. Ita 'yar ku tana Abuja, ita Zina tana Lagos ba shi ke nan ba? Kowacce ta zauna da irin halin ta da irin tarbiyyar ta a inda ta ke. I can handle them both""."

"Aunty Badiya sai ta kashe wayar ta, ganin Rahinah na hawaye. Bata san bakaken maganganun da zai cigaba da antayowa ba in ta cigaba da sauraron sa. Sabida Rahinah na jin komai."

"Duk abin da suke fadi a kunnen ta ne, don Aunty a fili ta saka wayar don dai Rahinah ta ji ta kara sanin matakin da za ta dauka."

"Washegari suka juya zuwa Kaduna. Ta ce nan da kwana uku za ta turo Musaddiq ya dawo ya kawo sakonnin nata, za ta gaya mata (Procedures) din ta waya. Kada kuma ta yi masa maganar auren da ya kafe a kai, ta rabu da shi."

"Ita kanta Aunty ta lura Rahinah ta yi sanyi, ta kuma yi laushi, ko magana ba ta iya yi sosai. Alamu ne na TA HUCE DAGA FUSHIN TA."

"A daren ranar da kyar ta iya yin barci. Washegari ba ta kai Abdallah makaranta da kanta ba, ta sa direban sa ya kai shi, tunda ya nuna ba ya son fitar tata kai Abdallah makaranta. Ita kuma daga yau duk abinda Habibu bai so ta daina shi duk son ta da abun kuwa."

*****

"PACE-SETTERS COLLEGE, WUYE, ABUJA T"

"sananin kulawa irin ta malaman wannan makaranta ya sa suka gane canzawar yaro Abdallah Nahuche. In ana karatu ba ya fahimtar komai yanzu, sannan in an fita break sai ya daina fita sai dai ya kwanta a kan tebir ya yi shiru."

"Performance din sa na contineous assessment very poor. Haka walwalar sa cikin yara 'yan uwan sa ta karanta. Abincin da ya zo da shi haka yake komawa da shi ko ya zubar, don kada Rahinah ta gani ta yi masa fadan maiyasa bai ci ba."

"Mrs. Easther Dekini wato classmistress din su ita ce ta lura da wadannan sauye-sauyen nasa, Mrs. Dekini sai ta hau jan yaron a jiki da wayo da tambaya tana son jin abin da ke damun sa. Rannan ta kawo katuwar ball ta ba shi, ta ce ya tashi ya shiga cikin yara 'yan uwan sa su yi wasa, sai ya bi ta da ido bai ce komai ba."

"Mrs Dekini ta zauna kusa da shi a kan desk din sa, ta ce, ""My dear Abdoulayi what's bothering you? Ka gaya min na yi maka alkawarin ba zan gaya wa kowa ba""."

"Yaron sai ya kama kuka. Ya yi kukan sa mai isar sa har yaba uku lada. Ta yi ta lallashin sa har ta samu ya yi shiru. Ta bude masa abincin sa, amma sai ya ce mata a'ah. Sai Daddy da Mummy sun daina fada zai dinga cin abinci."

Ba ya jin dadi kullum suna fada a kan sa.

A matsayin ta na malamar makaranta kuma mai ilmin psychology nan ta ga symptoms na kamuwa da depression a tare da shi.

"Da aka kada kararrawar tashi ya mike ya dauki jakar sa zai fita, kawai sai ya yanke jiki ya fadi, wata irin kumfa na fita daga bakin sa."

"Yara 'yan uwansa suka hau ihu suna fadin, ""Abdallah ya fadi"". Wanda hakan ya janyo hankalin malamai a kan sa. Lokacin direban sa bai iso ba, don haka a motar makarantar aka wuce da shi asibiti, sannan aka kira lambar Habibu aka gaya masa yaron sa yana National Hospital."

"Da direban sa ya je daukan sa ne a ka gaya masa an tafi da shi asibiti ba lafiya. Ya tambayi wane asibiti ne, aka gaya masa. Da gudu ya dawo gida ya sanar da Sahura don ta sanar da Rahinah."

"""Abdallahn da ya fita lafiya kalau?"""

"In ji Rahinah, cikin dimauta da gigita, irin wadda ba ta taba yi a rayuwar ta ba. ""Wallahi kuwa dai sun ce faduwa ya yi haka kawai""."

"National Hospital ba bakon ta ba ne, don haka kai tsaye (emergency paeditric unit) ta nufa gudu-gudu sauri-sauri har tan cin karo da mutane. Likitoci uku ta samu a kan sa, sun rufu a kan sa. Domin saita bugun zuciyar sa da ke yi rapidly. Wajen awanni biyu suna kan yaron kafin a samu kan sa, a kuma maida shi aminity."

"Awanni biyun da suka kasance tamkar shekaru biyu a idanun Dr. Rahinah Omar, domin ta gama sakankancewa dan ta Abdallah ba zai tashi ba."

"Sun samu sun ba shi dukkan taimakon da ya dace sun masa allurar barci a karshe, yana ta barcin sa sadidan, ana masa karin ruwa kansa bisa cinyoyin Rahinah sai sharar hawaye ta ke yi babu kakkautawa, wasu na korar wasu."

"Da sanyin safiya Habibu ya sauka a Abuja domin boarding flight ya biyo daga Lagos. Kuma ko gidan sa bai biya ba daga filin jirgi sai National Hospital afujajan da shi, domin zai iya cewa wannan ne karo na farko da aka ce Abdallah ya kwanta a asibiti a kan lalurar da bai san mece ce ba."

"Yana yin ciwo sama sama amma bai taba kaiwa ga kwanciya ba. In ka ce tashin hankali ga Habibu, to daya kenan domin kuwa lokacin da aka kira shi a kan maganar, meeting yake yi da ma'aikatan sa duka na Nahuche Hotel Lagos amma sai cewa ya yi,"

"""Excuse me...!""."

"Daga haka bai kara cewa komai ba. Ya tashi ya fita da sauri, sai Rasak ya bi bayan sa, ba su tsaya ko'ina ba sai filin jirgi."

"Cikin rashin sa'a jirgin Abuja bai jima da tashi ba a lokacin, sai kuma wanda zai tashi sha biyun dare, amma haka ya zauna a lounge din bai koma gida ba, don gani yake in ya koma za a kira shi kawai a ce babu Abdallah."

: *SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI 07030137870

NA HUCE*

PAID BOOK

"Jiran lokacin tashin boarding flight din da ya zame wa Habib Nahuche tamkar jiran ranar busa kaho, finally, jirgin ya zo ya kuma dauko su zuwa Abujan, sun bata lokaci sosai don sai shidda na safe suka samu baro filin jirgin zuwa cikin gari, daga nan zuwa National Hospital."

"Rahinah ba ta son tuno abin da likitan da ya jagoranci duba Abdallah ya fada mata, Abdallahnta is too young da samun wannan lalura, don haka yanzu ma da suke zaune su duka a gaban sa, ita da Habibun, ya kuma maimaita wa Habib Nahuche abin da Rahinah ta rigaye shi ji, Habibu bai san sanda ya juya ya kankame Rahinah ba."

"""Depression and Anxiety Disorder, sannan zuciyar sa ta fara tabuwa."

"Daga bayanin da Mrs Dekini ta makarantarsu ta bayar sanda aka kawo shi, mun tattara mun gano musabbabin matsalar sa."

"Ya dade yana ganin iyayen sa cikin halin da ba ya so. Me ya sa ku ke yin abin da zai daga masa hankali a gaban sa? He's too young da daukar matsalolin ku. Kwakwalwar sa karama ce, you all have to pay for that"". In ji likitan cikin bacin rai da matsanancin fushi."

"Rahinah ba ta san sanda ta daddage ta ture Habibu da ya kankame ta ba, dukkan su jikin su rawa ya hau yi. A fusace ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login