Showing 9001 words to 12000 words out of 117287 words

Chapter 4 - Na Huce Sabuwar Rayuwa BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

ta. Ya baro gini tun ran zane. zuciyar ta ta riga ta mace a tsanar sa."

Abinda kuma zai farfado da matacciyar zuciyar nan ba kankani bane. Ya riga ya raunata zuciyar ya yi mata illah. Tsanar data yi masa ba 'yar kadan bace. Kuma zata nuna masa ita ba yar tsana bace duk rashin gatanta ta san 'yancin kanta.

"Haka ya fita yana waiwayen ta, ita kam ko ido bata sake dagawa ta dube shi ba. Mintina goma sha biyar ta bayar bayan fitar sa, ta mike tasa jallabiyya, tasa jilbab, sannan ta tattara duk wasu muhimman takardun ta da passport dinta ta fice cikin zafin nama."

*****

"""Divorce ( *Scheidung* ) a kasar Germany: ba karamin abu bane. Domin tunda ke ke son sakin, sai kin dauki lawyer. Sannan zaki biya kusa '3,000 kudin kotu dana daukar lawyer. Ki rubuta application for divorce (divorce petition) in kin tabbatar kina da gamsassun hujjoji. Sannan ne za'a shiga family court a gudanar da sakin under German-law. Tunda dukkkannin ku kuna kasar Jamus. The divorce will run in accordance with German law regardless of your nationality (sakin zai kasance ne karkashin kundin tsarin shari'ar Jamus batare da la'akari da kasancewar ku ba 'yan kasa ba)."

"However, also in this case, sai kin jira end of the one-year-separation before starting the divorce procedure""."

"Ambasadan kasar Najeriya a kasar Jamus yayi mata bayani cikin nutsuwa. Da gani yarinyar is desperate, sakin kawai take so ba tareda ta san aikin dake gaban ta ba, ""tun farko me ya kai ki amincewa da auren sa in kin san ba kya son sa?"" Ya tambaya calmly, Rahina ta sanya gefen jilbaab dinta ta goge gumi da hawaye, ""ranka ya dade basu bani damata ba, uwardakina ta kasar nan ita tayi min fin karfi, hujjarta kakata tace kowa aka samu a aurar dani gareshi. Ni kuma ba na son sa, ban san shi ba, ban san komai a kan shi ba""."

"Ambasasada Shehu yace ""zaki iya gaya min hujjojin ki na rashin son zaman aure? Idan har akwai ci da sha da suttura?"""

"Rahinah ta rasa inda zata sa kanta, da kunya ta fadi hujjojin ta, balle a gaban alkali. Me take so daga gareshi banda SOYAYYAH??? Asalin sa, da sanin dalilin sa na auren ta?"""

"Kuma a yau ya ce, tayi hakuri in ya dawo zasu tattauna komai and he promised to become a changed person irin yadda duk take son sa. What else take so daga gareshi bayan wannan? Ya riga ya dasa kiyayyarsa a zuciyarta ne ta yadda babu wani repenting da zai yi ya wanke dattin laifukan da yayi mata."

"Ambasada ya ga shirun ta yayi yawa, yace ""bazan iya tsaya miki ba, har sai na san hujjojin ki masu karfi ne, sabida Jamus ba Najeriya bace, karshe a kare da cin ki tara. A yanzu haka ma in zai sake ki sai kin biya shi kudi masu yawa, do you have any source of income bayan alawus din ki na cin abinci?"""

"Rahinah ta kara rudewa, tace ""ka taimakeni yadda Allah ya taimake ka, banida komai da zan biya shi, bani da kowa da zai kwatar min 'yanci. Shin rashin so bai zama hujjah ba? Bana son sa ne, kuma bazan taba son sa ba""."

"Ambasada Shehu yayi murmushi, ya gama gane wauta da tarin kuruciya a tare da ita, banda haka auren, ai shine rufin asirin ta. Kowanne iri ne kuwa. Don haka yace."

"""'Ya ta, zan tsaya miki kamar Babanki, domin hakkin walwalar duk wani dan kasar Najeriya dake Jamus yana wuya na, amma hujjar ki bata isa hujja da za'a kai kotun Jamus ba, sannan baki da kudin da zasu nema. Don haka in zaki bi shawara ta in ma sakin zaki nema to ki nemeshi ta hanyar sulhu saki na addini tunda auren musulunci kuka yi ba tareda kin kai shi kotu ba."

"Ni zan kira yaron mu zauna mu uku, gara ya baki saki bisa doron musulunci tunda shi kika zaba amma ba ta hanyar kotun bature ba. Hakan zai jawo babbar matsala ga karatun ku ku duka, don dukkan ku ba abinda ya kawo ku ba kenan. Kuma in gwamnatin garin ki ta ji a inda kika kare a kotu zaki yi disappointing din ta ga kara sponsoring yara mata, sannan jami'ar ku zata shigo zancen wanda duka matsala ne ga karatun ku. Don haka ki barni in ganshi mu zauna mu duka."

"Idan rabuwar ku ita ce mafi alkhairi ya sake ki ta ruwan sanyi bisa doron saki na addini""."

"Jikin Rahina yayi sanyi sosai, kuma tana hango rashin yiwuwar hakan a idanun ta; Habib bazai yarda ya sake ta ta ruwan sanyi ba, ta gama gane mutum ne mai naci akan abinda yake so, kuma hargagi ko barazana basa razana shi. Shiyasa ta so ta kai shi kotu. But who is she to argue with this humble ambassador?"""

"""Na amince a kira shi in roke shi ya sake ni, a bisa hujja ta bana son sa""."

"Ta fada cikin matsananciyar faduwar gaba, tana mai jin tamkar hukuncin data yanke bai yanku ba, kamar zai dawo watarana yayi ta haunting din ta (evocative feelings)."

*****

NA HUCE is not for free. It's 1000 via;

3094856450

Sumayyah Kabara FirstBank

: SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

*NA HUCE* (Daga Fushi na)

PAID BOOK

"Sati uku kenan tana karatun ta conveniently online. Natsuwa ta soma shigar ta yadda ya kamata. Tunda bata ganin Habibu A. Bilyamin Nahuche bata da bacin rai, kuma bata da damuwa."

"Ciki dai har mantawa take yana makale a jikin ta, in banda mugun kwadayi da yake sa ta, kamar ta cinye Nene da Yafendo sabida dafa min kaza, dafa min kaza."

"To haka rayuwa take, komai lalacewar zamani baka rasa mutane na kwarai masu zuciyar taimako saboda Allah, iyalin Ambasada Shehu Bichi, ba abinda zata ce dasu sai addua da fatan Alkhairi."

"Hutun farko na summer mutanen gidan duka zasu je Paris, amma Ambasada yace banda ita da Yafendo, su zauna suyi kadin auduga a gida, ta sha jarabawa tana bukatar zaman waje daya ta nutsu, don su kam in sun tafi sai sun kwashe sati hudu suna yawo."

"Sun tashi ranar lahadi, gidan ya rage daga ita sai Yafendo, don haka ta lokewa tsohuwar, ba hirar data ke so su yi sai ta garin Girei da mutanen cikin sa. Duk yadda Yafendo ke son ta nusar da ita gara ta koma gidan ta taga gara ta kyaleta, tana cikin walwala da farin ciki a gaban nasu, kamar bacin ranta shine ace ta koma gidan Habibu Nahuche."

"Ita kuma haka kawai yaron ya shiga ranta, yana da wata irin Charisma da ba duka maza Allah ya mallakawa ba. Zuwan sa biyu gaida Daddy suna haduwa da Yafendon a falon saukar bakin Daddy, tayi ta zolayar sa wai biko yake zuwa a inda ba'a son sa. Shikuma baya shiru ramawa yake yi, yace yanada kamar ta me zai yi da wata Rahinah? Shi Yafendo ta ishe shi rayuwar duniya. Ya zo ne ya ji lafiyar dan sa a wurin Daddy he's not here for RAHINAH!"

"Bata jima da dawowa daga dakin Yafendo ba ta ga wayar ta na haske, alamar shigowar sako text. Ta dauka ta duba sai taga cewa alert ne na kudi Euros '3000. Daga Habibu Aminu Nahuche. Ya cika alkawari na farko da Daddy yasa shi ya dauka na ciyar da ita har sai ta haihu."

Bata san ya aka yi ya aka yi ba kawai ta ji kwalla ta cika idanun ta.

****

"Rayuwa ta cigaba da gudana yadda suka tsara ta, sai dai kuma sau tari ta kan zo wa dan adam da sauye-sauye; abin nufi, cikin ta na girma ra'ayin ta na canzawa akan sa. From negative to positive. A kullum ta ji shi yana wutsilniya sai ta ji gabanta ya fadi, sannan kauna irin ta UWA ta soma kanannade ta ba tareda ta yi shawara da ita ba. Bata son uban cikin, amma tana jin zata iya yin komai don tsira da wannan dan na cikin ta. Shi kadai ne ya rage wanda zata kalla ta kira jinin ta, tunda har gobe bata da wanda zata kira nata a gefen ta."

"Ta yi sallama a dakin Yafendo, ta sameta tana murza goge a magogi tana hambudawa, Yafendo tace ""yau tun safe ban ji motsin ki ba, inji dai lafiya kuka tashi?"" Ta zauna gefen Yafendon, tace ""lafiya na tashi Yafendo ina wani group discussion ne da 'yan class din mu via zoom. Sai yanzu muka gama kuma dole yau zan shiga makaranta akwai littafan da zan karbo a library"". Yafendo tace ""a wannan yanayin da kike 'yar nan? Zaki niki hanya ki bar gari zuwa makarantar nan taku mai nisa?"" Tayi murmushi ta dora hannunta akan na Yafendo tace ""kada ki damu tawan, ina jin karfin jikina sosai, kuma direba zan kira mu tafi tare"". Yafendo tace ""in kin ga wannan naman da ake cusawa cikin fulawa ki sayo min, irin wanda kika kawo min wancan zuwan naki makaranta"" tayi dariya tace ""bakin Yafendon mu akwai son cin dadi, zan kawo miki shawarma, nima yau ita nake son ci"". Da haka suka yi sallama ta daga wayar ta ta kira Yohana direba."

"Suna tafe akan titi tana nazarin wani practical da zasu yi cikin ipad dinta, tayi shigarta islamically cikin abaya ruwan makuba da mayafinta kirar kasar Oman, cikin ta ya fito sosai yayi toro don ta shiga wata na bakwai. Sake-sake take a ranta ko yaya haihuwa take? Is it painful? Shikuma raino da breast feeding ya suke? Kamar amsa ga tambayarta dan cikin ta yayi wani uban juyi da yasa saida tasa hannu ta dafe shi, tana mai addu'ar Allah ya raba su lafiya."

"Ta nunawa Yohana inda zai ajiyeta, wato parking lot na Cologne Public Library. Ta bude kofa ta fito a hankali tana taku irin na masu ciki, ta shiga library din da kafar dama domin kuwa shima shigowar sa kenan. Kamar kullum yana cikin kayan sa na hausawan usul jamfa da wando na farin boyel, amma yau bai sa hula ba, ya tara suma mai yawa akansa ta yadda farin gilashin da ya sanya ya nitse cikin gashin kansa. Yana zaune a kujerar sa cikin wani dan cabin na glass inda yake kula da bangaren ajiyar littafai masu muhimmanci (reserve section) ya ga wucewar ta amma ita bata lura da shi ba, kuma gabadaya ta manta a wajen da yake aiki kenan."

"Taje ta zabo littatafan da take bukata, amma bata samu guda biyu ba an ce suna reserve section."

"Ta tako a hankali zuwa reserve din, ya juya baya yana fuskantar allon kwamfutar dake gaban sa, kwarai ya ga sanda ta taho, kuma ta taho ne tare da bugun zuciyar sa. Ta kara wani itin kyau da sulbin fata tabbacin tana cikin kwanciyar hankali, sabanin shi da rayuwar sa ta jirkice bakidaya tun shigowar ta cikin ta. Rahinah muguwa ce mai son kanta da la'akari da maslahar kanta kadai. Idan wani barin na zuciyar sa ya so kare ta, wani baya mata uzuri cewa yake bata da hujjar kin koma maka. tunda ka ce zaka canza zuwa yadda take so."

Babu wani bangare na zuciyar sa dake yarda wai Rahinah bata son sa. tana amfani da kalmar ne don biyan bukatar

kanta.

"""Hi, can you please check these for me?%;"

-Diagnosis in Otorhinolaryngology

-New Aspects of Fundamental Problems of Laryngology and Otology

"Pediatric Otorhinolaryngology....Scott-Brown's Otorhino....."" sauran maganar ta makale gabadaya a makoshin ta sakamakon juyowar sa gabadaya. Saura kadan numfashin ta ya bar gangar jikin ta sabida wani mummunan kallo da Habib ya jefa mata. Dadi da cewa bata tsammaci ganin sa ba a daidai wannan lokacin. Sannan dadewar da ta yi bata ganshi ba ya dada haifar mata da faduwar gaban. Tayi kokarin maida numfashinta amma ya gagara isa huhunta."

"Daga sanda ya taso daga mazaunin sa zuwa isowar sa gabanta Rahina bata farfado daga suman tsayen data yi ba. Haka kama hannun ta da yayi suka bar cikin library din bata iya ta kwaci kanta ba. Saboda gabadaya bakin ta ya mutu ta kasa saita kanta a gabansa, ta kasa kuma yin kowacce irin hobbasa ta kwace hannun ta daga cikin nasa."

"A sanin ta da shi dai bashi da mota, amma ya bude bayan wata mota opel-astra ya sanya ta ciki ya rufe harda mukulli. Ya zagaya ta barin mazaunin sa ya zauna kuma ya tashi motar da wani irin mahaukacin gudu, bata raba daya biyun yau tata ta kare. Don ta san Habibu akan ta wani mahaukaci-mahaukaci yake komawa."

"Har kofar flat dinsa ya shiga da motar, ya kashe ta sannan ya dube ta da idanun da suka kada, suka kuma sanya hantar cikinta kadawa. ""Ki fita mu je, magana kawai zamu yi in mayar dake inda na dauko ki""."

"Rahinah ta soma hawaye, tace ""babu inda zani, nida shiga wannan gudan sai dai akai gawata""""ko? Zaki shiga ne kuma da ran ki da lafiyar ki, ko ta tsiya ko ta arziki, kina sane da cewa har yanzu matsayin matata kike?"""

"Wani karfin zuciya ne ya zo mata, ta ce ""wallahi ko ka bude min na fita, ko nayi maka ihun da zaka fada hannun hukuma, nace bana yi, bana so kuma bana auren dole ne?"""

"Ya kwantar da kai akan sitiyari yana kallon ta, masifa take yi tun karfin ta amma zakin muryarta kamar busar sarewa yake jin sa a kunnuwan sa. Haka mace mai cikin take komawa? Danya sharaf? Komai fresh? Idanuwan sa har wani kanakancewa suka yi suna dubanta da siga mai nuna bukatuwar miji zuwa ga matar sa......"

"""You can scream.... (kina iya yin ihun) amma ki sani nima inada nawa 'yancin da musulunci ya bani, kuma zan tabbatar miki shi yanzu"". Ya karasa maganr ta hanyar kamota da karfin gaske ya rungume ta, tana mutsu-mutsun kwatar kanta. Yace ""Rahinah ki dubi Allah ki tausaya mun my life is shattered without you. Ko me kike so zan"

"miki, ko me kike so zan zama. Nayi alkawarin fin Romeo iya soyayya. One more last chance ko don albarkar dana"

"dake karkashin marar ki. Rahinah ko a lahira wani kan ci albarkacin wani. In kika barni gabadaya bazan iya kara aure ba. Zan yi ta zama da dan ki ne yana debe min kewar ki har karshen rayuwata ""."

"Rahinah ta ga cewa hargagin ta ko cika bakin ta bai kwatar ta hannun Habibu a yau, he's ready to face anything don ganin ya kusance ta a yau, wanda hakan na nufin maida hannun agogo baya. Tun farko ita wane tsautsayi ya kawo ta library bayan ta san anan yake? Ta soma kuka tana rokon sa ""don Allah ka amida ni inda ka dauko ni, kaga bani da lafiya, bazan iya wannan abun ba zan mutu, da na ma zai mutu, wallahi nayi alkawarin zan saurareka da duk abinda ka zo da shi amma bayan na haihu "". Habib ya sassauta rikon da yayi mata, shima bazai so wani abu ya samu dan"

"sa ba, dan da yake jin duk duniya ba abinda yake so kamar sa in ka dauke Haj. Kaltume. ""Kin yi alkawari zaki saurare ni in kin haihu?"""

Ya tambaya in a subdued voice.

"Da sauri ta gyada kai, ba don ta yarda ta yi alkawarin a karkashin zuciyarta ba, fatan ta ta rabu da Habib lafiya ba tareda ya maida ita gidan nan nasa ba, data yi alkawarin ita da shi sai dai a kawo gawar ta."

"Sai jin Habibu tayi yana dauke hawayen fuskarta da halshen sa, wani al'amari tamkar electrical shocking ya bakunce ta. Ashe ba a iya nan zai tsaya ba? Al'amarin da ya biyo baya mai tsauri da nauyi ne da ya shallake tunanin ta. He began to kiss her passionately wani abu da bai taba faruwa tsakanin su ba. Ko ya manta a inda suke, ko kuma ita ta manta cewa sakakkiya ce a wurin sa. Wani incident da ya dauki tsayin mintuna masu yawa da bazai taba gogewa daga kwakwalwar Rahinah Omar ba. Ya kuma goge tabon abubuwa masu yawa da suka samu muhalli tuntuni akan Habibu Nahuche a zuciyar ta....."

Wayarta ce ta dauki tsuwwa....kira ake akai-akai. Da sauri ta ja baya. tana wani irin hararar sa tamkar idanun ta sa

"fado kasa. Habibu ya shafa kai, yana kallon ta da dukkan kauna da soyayya na zuciyar sa, idanun sa har shigewa ciki suke sabida azabar soyayya. Shi kadai ya san azabar da yake dandana. Komai ya dawo masa sabo, ji yake tamkar bai taba kusantar Rahinah ba sai a wannan lokacin. Amma ya san ko shi maye ne Rahinah bazata sake bashi wannan damar ba, idan har ba ya ya yi yaqin kwatowa kansa soyayya ba."

"""Nene!"""

Sunan da ya bayyana akan screen din kenan. Gabanta yayi wani irin faduwa. Me ta aikata? Me take aikatawa rayuwar ta? Dadin bakin namiji ne zai sa ta gurbata kyakkyawan ginin data faro? Ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login