Showing 99001 words to 102000 words out of 117287 words

Chapter 34 - Na Huce Sabuwar Rayuwa BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

san cewa a kan Abdallah bane Hajiya ta fadi. Hajiya Kaltume bata aje kaunar Abdallah anan kusa ba sabida shakuwar da ke tsakanin su wadda ta samo asali tun yana yaro. Ta yi addu'ar ko me yake damun Hajiyar Allah ya ba ta da sauki.

"Da Abdallah ya tashi ta yi masa brush ta yi masa wanka, sannan ta sa shi ya yi sallah. Sai ga sallamar Sahura ta kawo musu karin kumallo. Ba jimawa Nene da Ahlan ma suka zo, sai dakin ya yi albarka, nan ta ke gaya musu maganar rashin lafiyar Hajiyar Nahuche."

"Nene da Sahura duk suka yi wa Hajiya addu'a, nan suka taya Rahinah wuni a asibitin kasancewar karshen mako ne."

******

"ZAMFARA GALMA UWAR RUFI, KO BAKU SON MUTUM BAKU HWADI!"

S

"un isa garin su na haihuwa wato Zamfara shi da Badiya dukkan su ba cikin nutsuwa ba. Aunty Badiya ta yi nadamar gaya wa Hajiya rashin lafiyar Abdallah, ta manta shaf da halin ta na sanya abu a rai fiye da kima. Habibu ma ta sha fada a wurin shi kamar shine wan ita kanwar. Da ta gaya masa tana tsammanin abinda ya tada ciwon Hajiya kenan."

"Sun samu an ba ta gado a Aminity 'yan aikinta suna ta kula da ita. Amma ganin halin da Hajiya ke ciki ya rikita Habibu, tsufa ne ya hadu da dadadden ciwo da damuwa, sai ya ce da Badiya zai dauke Hajiya ne kawai zuwa Jamus cikin satin nan don ta samu kulawa yadda ya kamata. Ya fi yarda da hospitalization din su fiye da na ko'ina."

"Tun a lokacin ya soma tuntubar likitocin ta akan shawarar da ya yanke, duk sun ce ya bar ta zasu iya shawo kan matsalolin ta amma ina! Habibu gani ya ke basu iya komi ba, ba ya hada lamarin Hajiya da komai, a take ya kuma soma shirin tafiyar tasu ta yanar gizo, washegari suka tafi da Hajiya daga Zamfara don shigar da neman visa."

"A hanya suke shawarar wadanda ya kamata su tafi da Hajiyar asibiti cewa bai kamata su tafi dukkan su ba, dole daya ya tsaya sabida Abdallah da ba'a sallama ba. Habibu ya ce shi zai zauna tare da Abdallah har a sallame shi, in ya so sai ya biyo bayan su daga baya, Badiya kuma ta ce zai fi kyau su tafi har da Rahinah tunda likita ce, kuma a can ta yi karatun ta ta iya harshen German, she will have more rapport da likitocin can tunda ita Badiyan ba ta iya Jamusanci ba, sannan again Rahinah can play the role of a support doctor ga Hajiya, za ta taimaka dai ta kowanne bangare. (Badiya ta kawo wannan shawarar ne don tana son dinke 'yar barakar da ke tsakanin Hajiya da Rahinah). Don ta samar da 'yar shakuwa da fahimatar juna tsakanin su ko yaya ne."

"Ba bata lokaci ya amince da shawarar Yayar tasa, don haka suka bar Abdallah tare da Nene, suka dauki Rahinah a asibiti suka wuce %’dj erman Consulate %’ har da ita wanda ke a garin Lagos don neman %’fj ospital Visa %’. Masu abu da abun su, babu bata lokaci cikin sati aka yi musu komai da taimakon Ambassada Shehu, likita ya ki sallamar Abdallah ya ce sai ya gama karbar treatment."

"Sahura ce ta hada wa Rahinah kayan da ta ware don tafiya da su Germany. Ta sanya a ran ta in ta samu dama kuma Hajiya ta samu lafiya za ta nemi Aunty Laura a Germany don kawai ta gaishe ta, ko babu komai ita ce silar duk abubuwan da suka faru dasu a Jamus, tsakanin ta da Habibu Nahuche har zuwa inda yau ke motsi."

"Tunda ita tayi uwa ta yi makarbiya ta kulla auren su. Auren mai tsohon tarihi da dabaibayin zukata iri-iri. Har aka samu Dan da silar zuwan sa duniya ne ya yi connecting komai. ta wani bangaren, ba ta san dalili ba; a yau sai ta"

"samu kan ta tana mai gode wa Aunty Laura, tunda ita ta yi silar dukkan kaddarorin su; masu dadi da marassa dadi. Laura ta cancanci abinda yafi godiya yau daga gare ta in akwai, tunda ta mallaka mata Baban Abdallah (Habibu Mustapha Bilyamin Nahuche)."

****** JAMUS

S

"ai da ya gama musu komai a filin jirgin saman Murtala Mohamed dake Lagos ya kuma ga tashin su, sannan suka koma gida shi da P.A din sa Atiku, yana tafe yana waiwayen jirgin da ya daga da Yayar sa, Mahaifiyar sa da Matar sa; mata ukun da bai da ya su a duk fadin duniya, wadanda su ne farin cikin sa, kuma komai na sa."

"Habib Nahuche, sai ya ji tamkar shi kadai ya rage yanzu a fadin duniya in ka dauke dan sa Abdallah da ke gadon asibiti. Nene Balki na asibiti wajen sa ita da Sahura, sai dare zai koma musu."

"Dr. Rahinah Omar a Jamus a karo na biyu. Wannan karon ba a daliba ba a matsayin mai jinya. Ita ta rinka jagorantar su a komai har suka sauka a masaukin su. Asibitin da aka yi wa Hajiya booking yana 'Bonn City' wato St. Josef Hospital, Bonn. Rahinah ce tsaye a kan komai har aka ba su daki, cikin kwanaki uku da zuwan su Hajiya ta ga duk likitocin da ya kamata ta gani. Babu irin binciken da basu yi mata ba (complete check up) na duka abinda ya danganci lafiyar ta."

"Kuma a binciken su sun gano sugar (diabet) ma a jikin ta, sannan ciwon kafar Hajiya na da alaka da hawan jinin ta, treatment na kwararru kawai ake ba ta iri-iri."

"Tun zuwan su asibiti Rahinah ta ajiye komai ta ke hidima da Hajiya, ita ke kula da komai nata, wanka take mata da tawul kullum, kula da cin abincin ta irin na masu hawan jini wanda asibitin ne ke ba ta da kan sa, kula da shan maganin ta a kan lokaci da communicating da likitoci, Habibu sai dai kawai Badiya ta yi masa waya ta ba shi labarin abin da ake ciki da irin kokarin da Rahinah ke yi. Tace ita zaman kashe zani take yi kawai. Rahinah ce ke jinyar."

"Ita kanta Hajiya da ta ke a kwance ta san Rahinah a tsaye ta ke tsayin daka a kan lafiyar ta, ta baro nata yaron wanda shi ma kulawa yake bukata amma kacokam hankalin ta yana kan Hajiya. Duk abinda ya shafi lafiyar Hajiyar da ita likitocin ke tattaunawa."

"Wannan kokari na zuciya daya da kulawa kamar ita Hajiya ta haifa ba Habibu ba, ya wanke Rahinah a zuciyar Hajiya Kaltume, ta kuma fahimci abubuwa masu yawa a tare da Rahinah da a baya ta kasa fahimta, wato dai ta gane Rahinah mace ce mai saukin kai da dadin mu'amala akasin yadda ta ke kallon ta kuma dai tana son Habibullahin ta, ta sani in har da a ce ba ta son Habib din, ba za ta yi wannan tsayuwar dakan a kan ta ba."

"Balle kuma tana jin su cikin dare suna waya, wata irin waya da du kwakwar ka ba zaka gane me suke fada ba, a zaton Rahinah Hajiyar na barci ne, lokacin da Habib ke mata (midnight call), amma duk da kuskus din na su ta kan fahimci wasu daga kalaman Rahinan ga mijin nata Habibu a waya, duk na ban hakuri ne da tausasawa a kan kewar su da watakila yake cewa Rahinar yana yi, da kuma tambayar yaushe za ta dawo da Abdallah ke ta yi masa."

"A kwana goma da zuwan su Jamus Hajiya ta fara samun sauki sosai, tana zama sosai a yi hira da ita, ana i-gobe za su cika sati biyu a Jamus Badiyya ta ce, Habibu ya yi mata booking za ta koma gida, sabida yara da kuma aikin ta, don excuse din sati biyu ta dauka dama."

"Ta ce ""ka ga zaman nawa bai da wani amfani tunda Dr. Rahinah ke yin komai, ni 'yar taya su hira ce kawai. Asibitin kuma sun ce sai Hajiya ta yi sati uku za su sallame ta""."

Don haka Habib ya yi ma Badiya shiri ta dawo Kaduna.

"Badiya ta taho a washegari, shi kuma Habib ya yi booking din tahowa domin an sallami Abdallah daga gadon asibiti, Nene ta tafi da shi gidan ta wato gidan Ambassada."

"Ko a daren ranar sun yi waya har tsakar dare ita da shi, amma bai gaya mata cewa yana (on transit) ba ne ma lokacin a kasar Neitherlands, ya dai gaya mata an sallami Abdallah yana gun Nene Balki."

"Ta ko'ina yanzu Raheenah ta wanke kan ta a dan tsukin a wajen Hajiya Kaltume, ta saki ran ta da Rahinah, ta cire wa kan ta shakku a kan surukar tata, ta yarda ita ce daidai da rayuwar Habibullahin ta, wadda ya ke so saboda Allah, take kuma auren sa ba don wani abu da ya mallaka ba, in ka ji su suna hira da rigima a kan shan magani itada Hajiyar Nahuche kamar Yaya da kanwar ta."

"A yanzu kam Hajiyar ta amince za ta iya baiwa Rahinah amanar da a baya ta ke ganin ba za ta bata ba, wato zamowar ta abokiyar sirrin da za su kashe su rufe a kan komai na Habibu tare, ba zancen surukuta ko shakku a tsakani."

"Ta maida Rahinah 'yar cikin ta, ba maraba da Habib da Badiyya."

****** BAKON BAZATA

""""

"Daure ki sha Hajiya, daga yau zan roke su su rage yawan kwayoyin nan, tunda dai ba kya son hadiyar su, kullum sai mun fafata har waje ana jiyo mu akan shan maganin nan""."

"""Ke ko Rahinah shan maganin bature ai sai dole, dolen ma sai dole, amma ina ya ga dadi? Nafi gane in yi jikon sassake tunda alhmadllh babu cutar da bamu da maganin ta na gargajiya amma kun ki"""

"Hajiya ta koka, tana yamutsa fuska."

"""To in ba kya sha a kan kari Hajiya ai bazaki warware da wuri ba su sallame mu a kan lokaci, ki koma wajen maigidan ki Abdallahn ki da kullum ki ke damu na da zancen sa""."

"Hajiya ta dungure mata kai, ta ce, ""Abdallahn da ku ka sabauta min? Bawan Allah! Allah kadai ya san irin izayar da ku ke gana masa da sunan soyayya""."

"Dariya Rahinah ta hau yi. Wai izaya. Fada kawai suke yi shi kuma Abdallah ran sa baya so, ya sanyawa ran sa damuwar hakan har hakan ya taba masa kwanya. Amma ai lelen sa suke yi ba ita ba ba Uban ba, wannan na wane"

"wannan a son Abdallah, kowanne so ya ke ace shine gwarzon mahaifi a wajen Abdallah dayan ya gaza; wato dayan ne a baya."

Kuskuren da suka yi shine kwakwalwar yaron ta yi kadan da daukar matsalolin su. Rahinah na wannan tunanin taba ballewa Hajiya magani ta sunkuya domin dauko gorar ruwa a firji sai ji suka yi an murda kofar dakin nasu tare da sallama a natse.

"Muryar da ta ratsa har kasan zuciya da ruhin Rahinah Omar, ta sanya ta dagowa abruptly kuma cikin (slow motion). Baban Abdullahi dan mutanen Nahuche ya bayyana a dakin asibitin sanye cikin (Black - Grey German Suit), wadda ta taimaka ainun wajen kara fito da ilhama da cikar zatin sa na cikakken Bazamfare mai jini a jika. Kafar sa cikin rufaffen takalmi (cover) samfurin (Bloomingdale's) wanda ya dace da launin sutturar jikin sa, wato black/grey. Agogon rolex dake daure a damtsen hannun sa ma (Bloomingdale's) dinne na bakar fata. Agogon ya kwanta luf ya nitse cikin tarin lallausar sumar dake kwance a hannun sa ta Zamfarawan usli. Fatar jikin sa lub-lub mai nuna yanayin hutu da kwanciyar hankalin da yake ciki."

"Wannan sardidin matashin bazamfaren da a kullum ta gan shi ko ta ji muryar sa tun daga kuruciyar sa har zuwa matakin da ya ke kai a yanzu (at his fourteith), sai ya tafi da kafatanin numfashin ta na wucin gadi ya kuma tada tsigogin jikin ta."

"Daga ita har Hajiya babu wanda ya yi tsammanin ganin sa a wannan lokacin, don haka suka bi shi da kallo na mamaki da al'ajabi, na Rahinah cakude da boyayyen farin cikin ganin sa har kasan ran ta. Irin farin cikin da ta dade bata yi ba, kuma idanun ta sun nuna hakan. Ta saki wata siririyar ajiyar zuciya."

"Sai da Habib ya tabbatar ya sanya kwayan idanun sa cikin na Rahinah duk da yadda ta yi kokarin kaucewa hakan saboda Hajiya da ke zaune a gefen su, sannan ya karasa gaban gadon Hajiya da sassarfa."

"Hajiya ma ta kasa boye farin cikin ta na ganin sa, ta ce,"

"""Baban Abdullahi zuwa ba sako ba sanarwa? Amma ka shammace mu""."

"Hannayen ta duka biyu ya kama ya rike cikin nasa ya dora a kan kwantaccen sajen fuskar sa, ya ce, ""Hajiya ina sane na ki gaya muku zan zo, don cewa za ki yi ba sai na zo ba kin warke""."

"Hajiya Kaltume ta yi murmushi ta zare hannayen ta daga cikin nasa, Habibu ba ya girma in dai a gaban ta ya ke, ta ce,"

"""To ai shi ke nan, ka zo lafiya ya ya hanya, ya Abdallah da jiki?"""

"Suka koma gaggaisawa irin ta Da da mahaifi. Yana gaya mata rikicin Abdallah na cewa sai ya biyo shi. Hajiya ta dubi Rahinah da duk ta kasa sakewa ta takura a dakin sakamakon kallon da Habib ke mata na kurullah duk lokacin da tayi kuskuren dago kan ta sai idanun ta sun fada cikin nasa ta ce,"

"""Ke kuma haka ake karbar bako babu sannu da zuwa babu ruwan sha?"""

"Murmushi ta yi cikin jin kunya, kan ta a kasa ta kara nutsuwa hadi da takurewa, murya can kasa ta ce, ""Sannu da zuwa Baban Abdallah""."

"Habibu ya yi mata kallon tsaf, kafin ya ce. ""Rike sannu da zuwan ki tunda sai da a ka roka min"". Ya fadi hakan ne cikin gimtse fuska da nuna rashin jin dadi."

Yadda ya gimtse fuskar sai ta ga ya kara wani irin kyau a idanun ta. Ko kuwa ita kadai ta ga hakan don tana murna da zuwan sa? Ba zan iya sani ba.

"Tana murmushi ta nufi firij ta rasa lemon da za ta dauko masa, sai ta tuna ya taba cewa ba ya shan zaki, kawai sai ta bige da dauko ruwan roba mara sanyi da tambulan ta kawo masa."

Gabadaya ta rikice ta rude sosai da zuwan Habibu. Amma tana kokarin sarrafa kan ta saboda idon Hajiya da nasa idanun da ke ta bin ta.

Tana bashi ruwan ba tare da ta bari sun hada idanu ba ta juya musu baya ta tada sallah.

"Bai sha ruwan ba ya mike yana fadin, ""Hajiya zan karasa masauki in yi sallah sai dare zan dawo in ga likitocin ki"". Hajiya ta dubi Rahinah da ke ninke sallayar ta bayan ta idar da sallahr ishai da idanun kulawa da kauna, kamar mai magana da karamin yaro cikin lallashi ta ce."

"""Rahinatu sai ki raka shi masaukin ko, kun dawo tare zuwa goben, ni bana bukatar komai alhamdulillah kullum lafiya karuwa take yi, barci ma zan yi yanzu haka, Allah ya yi miki albarka yasa yayan ki su yi miki ninkin abinda kika yi min"""

"Rahinah ta zaro ido ta ce, ""Hajiya ba za mu barki ke kadai ba...""."

Kallon da Habib ya yi mata ya sa ta hadiye sauran maganar ta har ta kware. Domin kallo ne da bata taba gani a idanun sa ba.

"Hajiya kuwa sai ta hau fada,"

"""To in kin zauna goya ni za ki yi? Kin bani magani kin bani abinci barci kawai ya rage min. Mijin naki da ya taso kasa ya kasa ki ce ba za ki raka shi masauki ba, haka ake yi Rahinatu? Bayan ni bana bukatar komai? Duk wata kulawa kin gama bani, shima kulawar ki ya ke so. Tashi maza ku tafi, Allah ya yi muku albarka""."

"Shi tuni har ya kai bakin kofa ran sa kal da farin cikin kalaman mahaifiyar sa. Da tace da Rahinah shima kulawar ta ya ke so. Da gaske ne Hajiya ta fi kowa son sa, ta kuma fi kowa sanin sa da fahimtar sa."

"Ba abinda yake so a lokacin sai kadaicewa da Rahinah Omar. Ba kuma wai don wani abu ba, kawai so yake ya gan su daga shi sai ita a kebantaccen muhalli shine babban abinda yake sa masa nutsuwa a yanzu. Son samu ya dan runguma ta cikin jikin sa ya ji dumin da ke kasan dogon wuyan ta, wanda ya san ba mai yuwuwa bane."

"Rahinah ta gama 'yan mutsu-mutsun ta na jin kunyar Hajiya, sannan ta dauki kayan ta kala daya ta sanya a leda da rigar barci daya, da duk abin da ta san za ta bukata a daren zuwa gobe ta bi bayan sa kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. Tana ficewa daga dakin tana ce da Hajiya %’ún ajiya ki kunna waya ki bar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login