Showing 12001 words to 15000 words out of 117287 words

Chapter 5 - Na Huce Sabuwar Rayuwa BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

su Nene zasu ji in suka ji tana tare da Habib ne a kofar gidan sa cikin motar sa ba tasu ba? Bayan ba yadda basu yi da ita ba kan ta koma masa amma tace a'ah? Me yasa ta yarda ta biyo shi? Shin idan Nene ko Ambasada suka san tana tareda Habibu ba zasu zargeta da raina musu hankali ba?

"Da wani irin zafin nama ta bude murfin motar ta fice, Allah ya so ta ya saki lock din, ta leko ta window tace cikin muryar kuka."

"""Allah ya isa taba ni da kayi, Allah ya saka min!""."

"Habib Nahuce. Bai san sanda dariya ta kwace masa ba duk da halin da yake ciki. Yace ""Allah ya saka mana tare Rahinatu! Akwai mugu a duniya irin ki? Kin ci albarkacin Baby na, na rantse da sai kin kunshi wani sabon cikin a yau kin haifo su tare sun zama biyu "". Bata tsaya sauraron mugayen kalamansa ba masu kama da sabon Allah a"

kunnuwan ta ta nufi titi da mugun sauri tana tare taxi.

"Yohana sai ganin ta yayi taxi ta sauketa a gefen sa, ita da tace library zata shiga ta karbo littafi ta fito. In ya kirga daidai ta kwashe akwalla awanni biyu kenan. Ba wannan ne ya bashi mamaki ba sai yadda ta bude motar ta afko kamar wadda aka biyo."

"""Are you okey Madame?"""

Ya tambaya calmly.

"""I'm okey Yohana let's go, kada ka tsaya a ko'ina sai mun isa Frankfurt""."

"""Is someone following us? So that i report to police?"""

"""A'a babu mai bin mu, kaidai ka tafi da sauri ka bar harabar wajen nan""."

"Ya ja motar suka bar wajen yana cewa ""alright Madame, but kowanne karamin abu ki dinga gaggawar sanar da police""."

Ita dai tace masa ta ji.

"Sun yi nisa sosai wayar ta ta sake kara, tayi ajiyar zuciya sai yanzu ta fara samun nutsuwa data tabbatar sun fita daga shiyyar birnin Cologne. Sun kama hanyar da zata kai su Frankfurt."

Da ta duba sai ta ga 10 missed calls daga Nene.

"A take ta kira ta jikin ta har rawa yake, ji take kamar Nene ta ga komai da ya faru, ita da Habibu a mota suna kissing. Wani hawayen bakin ciki ya zubo mata, ta ji ta tsani kan ta, ta tsani karatun da ya fiddo ta daga gidan Ambasada, in bata yi wasa ba Habibu na gab da sake rusa mata rayuwa."

"""Nene wallahi ina cikin library ne wayar kuma na barta a mota"""

"""Meyasa kika je makaranta baki jira ni na dawo mun je tare ba idan zuwan ya zama dole? Kinsan Dr. Yace ki daina zirga-zirga"" ta share wani uban gumi daga kan goshin ta, tace ""Nene i'm sorry littafai na je amsow na clinical assignment dina, kinga ma ban samo su ba, bazan ma kara zuwa ba har sai na haihu. Zan gayawa Daddy a nemomin na saya kawai"" Nane tace ""better, me zan dafa miki kan ki iso?"" Tayi murmushin samun relief tace ""anything traditional""""to shikenan zan miki tuwon alabo miyar ugu leaf da alayyahu da ganda da busashshen kifi, yayi miki?"" Wani hawaye ya bullo mata, ashe haka soyayyar UWA ke da dadi? Allah ya barta da danta itama ta bashi kauna irin wannan. Allah yasa kuma kada mutuwa ta raba su yana karami sai ya mallaki hankalin kansa ko da zata mutu. Ya zamo cewa ta gama bashi duk wata kulawa da tarbiyyar da ya kamata ya samu daga gareta."

"A wannan daren, daga Habibu Nahuche har Rahina Omar, babu wanda ya iya ya runtsa. Dare ne mai matsanancin hazo, cikin watan Nuwamba, Habibu na nannade cikin bargo sanyin kasar Jamus na shigar sa, ba abinda yake so yake bukata a lokacin sai dumin matar sa Rahinah. Amma ta wace hanya zai bi ya dawo da damar da ya samu a baya? Masu iya magana dama sun ce opportunity comes only once in life! Ya bata komai, ya dade da bata komai, ya riga ya bata rawar sa da tsalle. Haduwar su a yau ta maida masa komai sabo in itsown special unique way girman"

"Rahinah da soyayyar ta sun karu sun ninku sun hauhawa a zuciyar sa, ya fahimci abubuwa da dama wadanda a baya bai sani ba; Rahinah na daga cikin kasaitattun mata da samun kamar su sai an tona. Irin matan nan ne one in million wadanda duk namijin da Allah yayiwa baiwar mallakar su ya gama bashi rabin addini sa, ya gama bashi farin cikin rayuwa, da duk wani jin dadi dake cikin ta."

"A yau ya amince da abinda a baya ya ki believing da gangan. Cewa zai iya rayuwa babu Rahinah, zai iya hakuri da rayuwar sa single ba tare da Rahinah cikin ta ba. A yau ya yarda ya amince rayuwar sa bazata taba zama straight ba ba tareda Rahinah a gefen sa ba. Ko zata yarda ta saurareshi idan ta haihun kamar yadda ta yi alkawari? Shi kuma zai yi komai don dawo da ita cikin rayuwar sa cikin martaba da mutuntawa, dadin dadawa soyayya mara yankewa har fiye da wadda bata tsammani. Daga wannan ranar yake bincike, wani irin bincike na yadda ake tafiyar da soyayyar mata. A rubuce-rubuce na masana ilmin psychology (self-help books and self-reflection). Ya samo wasu tips guda goma wadanda suka ce (How to keep your woman and make her love you forever). Marubucin ya ce; cikin abubuwanda zasu rike maka soyayyar matar ka sun hada da;"

-work on yourself ; ka yiwa kanka self-evaluation; ka cancanci ta so ka ko a'ah?

-listen to her (and i mean really-really listen); ka saurareta akan duk abinda ta zo da shi da cikakken attention ka bata hankalin ka a lokacin da take bukatar hakan.

-learn how she prefers to be loved; ka duba abinda tafi so ka nuna mata soyayyar ka da shi.

"-give her gifts (ka kasance mai yawan yi mata kyauta, kyauta tana kara dankon kauna)."

-be honest with her (ka zamo mai gaskiya da kyakkyawar manufa akan ta).

-respect her (ka girmamata) and treat her with this respect.

-find creative ways to tell her that you love her (ka zama mai iya kirkirar hanyoyin gaya mata yadda kake son ta in your own special way).

-allow yourself to be vulnerable; wato ka dinga nuna mata raunin ka. (Allow yourself to make mistakes and admit to them. Allow yourself to be real and true and not hide any of yourself from her.

"Don't be afraid to cry in front of her. And don't be afraid to let her cry, too.}€ Vulnerability allows for deep connection and bonding }€ in a relationship. If you can't be yourselves }€ in your most raw forms, how are you supposed to feel safe building a whole life together?"""

"Habeeb Nahuche sai ya ga cewa duka wadannan tips din da wannan masanin ya zano duk zurfin ilmin sa shi bai mallaki ko daya ba! Bai taba nuna wa Rahinah dayan su ba, yet yana blaming din ta da kasa son shi duk cancantar sa."

"Ita soyayya ta gaskiya ba ta ta'allaka da appearance din mutum, but the way he demonstrates himself."

"Ya yarda duk ilmin ka ilmi baya taba karew a a duniya, saidai ka dauki iya wanda zaka iya ka bar ragowar. Inama! Inama! Inama Rahinah ta yarda ta sake bashi dama koda sau daya ne a rayuwar su???"

****

"*NA HUCE* is not for free,"

It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara FirstBank

": A daren bata yi wani isashshen barci ba sabida taraddadi da ya cika ranta, ashe tana da rabon ganin wanda zai ce ya san wani nata ma bayan Dada? Excitement ya cika zuciyar ta, ta dokantu shekara ta zagayo ta bi iyalin gidannan Najeriya."

"Washegari da safe ta yi shirin makaranta, ta hada tea a dining din kitchen zata sha, kawai sai taji zuciyarta na tashi kuma ba abinda take so sai ramar Yafendo."

"Da sauri ta suri jakar ta ta nufi dakin Yafendo. Ta idar da sallahr walha kenan, ta shigo dakin kamar an jefo ta, ""Yafendo don Allah don annabi ki sammin rama da kuli, in ban ci ba yanzun nan mutuwa zan yi""."

"Yafendo ta katse lazimin ta jin abinda Rahinah ke cewa, kafin kuma ta bata amsa ta hau daddaga shirgin Yafendo tana neman Ramar, Yafendo tace ""Rama da safiyar nan 'yar nan? Ki tafi makaranta kafin ki dawo zan kwada miki, yanzu ki nemi ruwan dumi ki zuba a cikin ki""""na hada na kasa sha, tashin zuciya bambita yake sa ni, don Allah ki taimakeni""."

"Da sauri Yafendo ta dauko ramar, tace ""jona ruwan dumi a butar can"" cikin minti biyar tayi mata kwadon ta bata. Nan ta hau ci ba kakkkautawa hannu baka hannu kwarya. Yafendo tana ta mamaki a ranta, anya lafiyar ta?"

"Data dawo daga makaranta ma kai tsaye dakin Yafendo ta zarto. ""Na kwaso yunwa Yafendo, zan samu kwadin ramar ki?' Kawai sai ta ga Yafendo ta zaro kwano a rufe ta mika mata, already ta kwada tun kafin ta dawo""."

"""Allah ya kara nisan kwana Yafendo nagode"" ta soma ci a urunce. Yayin da Yafendo ta tsura mata ido."

"Ta koma dakin ta ta sunce zata yi wanka, amma sai ta bige da kallon kan ta a mudubi, a take ta hango wasu bakin sauyuka a halittar jikin ta. Abinda ya fi daukar hankalin ta shine karuwar girman kirjinta sosai, sannan tayi wani irin fari dau! Kamar babu jini a jikin ta."

"Rahinah bata damu ba ta cigaba da wankanta tana fadin mutum na kara girma ai dole kirjin sa ma ya kara girma. Tana fitowa Ahlan ya shigo da gudu, ""Aunty Rahina Nene tace wai yau baki ci abinci ba ko lafiya?"" Ta ce ""Ahlan ka gayawa Nene wallahi kwanan nan ban iya cin komai sai RAMA""."

"Ba jimawa sai ga Nenen da kanta, tayi sallama ta shigo, tace ""Rahinah me kika ce a gaya min? Ban gane hausar Ahlan ba, Jamusanci ya masa yawa"" nan ta maimaita mata. Tace ""ke a ina kika ga Ramar?""""Wajen Yafendo, tana da ita mai yawa"" Mami ta tsura mata ido, a take ta hango sauyukan data ke son gani. Tace ""Rahinah kina yin period kuwa?"" Kanta tsaye ta amsa ""ai ni rabo na da shi har na manta, amma kin san i'm too busy to notice that ba don kin fada ba""."

"Nene tayi mata kallon tausayi, sannan ta ce yanzu idan ramar ta kare ya za'ayi?"""

"""Nima ban sani ba Mami,na dai san in ina so ban samu ba mutuwa zan yi, yanzu kam na koshi sai kuma gobe in Allah ya kaimu""."

"Mami ta juya ta fita tana fadin ""on weekends zaki raka ni asibiti, mutum baya period ai gara a duba shi a san dalili"". Cikin damuwa tace ""Nene, is there any problen with that?"" Nene ta dafa kafadarta tace ""don't worry"". Sannan ta fita. Nene ta ce kar ta damu, amma sai ta ji ta damun, ko wata cuta ce rashin yin period din?"

"Nene na fita dakin Yafendo ta nufa, ta samu kujera ta zauna, tace ""Yafendo ko kin lura da abinda na lura da shi game da yarinyar nan?"""

"Yafendo ta ce ""kwarai kuwa, kallon ta kawai nake, in kuma jira in ga ko zaki kula da kiwon da Allah ya baki. Shi aure dama in Allah bai nufi karewar sa ba wa ya isa ya karar da shi? Da zata ji shawara ta gara mata ta koma gidan mijin ta ta cigaba da hakuri irin wanda kowacce mace ke yi a gidan auren ta, ba namijin da yake cikakke a komai dukkan su suna da gibi, amma yadda na lura tafi jin dadin rayuwar ta da mu a haka bata ko so a dago mata zancen sa"". ""Kwarai wannan haka ne, bari in je in samu Daddy muyi magana a kan ta""."

"Yana sauraron radio Jamus a 'yar karamar rediyon sa lokacin da Nene tayi sallama ta shiga. Ya amsa mata, sannan ta samu gefensa ta zauna."

"""Ranka ya dade magana ce ta kawo ni, akan yarinyar nan Rahinah""."

"Ya rage sautin rediyon sa ya bata hankalin sa. ""Ina zargin ciki ke gareta"". Radeyon hannun Ambasada ce ta subuce kasa, tace ""wallahi alamu sun gama nunawa, amma duk da haka ban tabbatar ba""""kuje asibiti a tabbatar pls"" Mami tace ""insha Allahu, amma in ya tabbata cikin ne yaya zamu yi da ita ga karatun ta mai tsayi?"" Ambasada ya nisa yace ""yadda zamu yi da Safeenah, idan irin haka ta same ta""."

****

"Rahinah bata san me ta rako Nene yi a asibiti ba, amma tunda suka zauna a gaban likita ya kuma ce ta bashi fitsarin ta komai ya fara kwance mata."

"As a medical student ta san awon fitsari na nufin abubuwa da yawa.....awon cuta ko awon ciki! Don haka kafin sakamako ya taddasu, ta yi ligib cikin tashin hankali da tararradi."

"""She's two months pregnant"". Likita ta fadawa Nene ita kadai, bayan ta ce Raheenah ta je reception ta jira ta. Sannan ya bata shaidar hakan a rubuce."

"Nene ta yi masa godiya, sannan ta fito ta tadda ita suka tafi, a hanya take gaya mata an ga shawara (jaundice) cikin fitsarin ta."

"Raheenah tayi wani ajiyar zuciya, feeling relieved. Har suka zo gida zancen rama take wa Nene, wai yanzu idan ranar Yafendo ta kare ina zata sa kanta? Nene tace ""sai ki ci salad, ai shima ganye ne""""amma bai da dan tsami- tsaminnan kamar na rama"" murmushi Nene tayi, tace ""sai a masa vineger""."

Suna sauka a mota kuwa ta tafi dakin Nene cin rama.

"Kwana bakwai kenan bata iya cin komai banda ramar, har yau gashi rama ta kare, babu kuma inda za'a sameta a Jamus."

"Don haka tun safe take cikin kunci, haushin kowa ta ke ji, da Ahlan ya shigo yana mata surutu sai ta shige toilet ta rufe kanta don bazata iya korar sa ba."

"Nene ta shigo dauke da plate a rufe ta sameta, ""Rahinah yau bazaki makaranta bane? Yara duk sun fita sun barki, ga wannan ko a mota sai ki ci kada ki tsaya ci ki makara, kin dai san kina da nisa""."

"""Nene yau ban iya zuwa makaranta"" ta fada hawaye na ciko idon ta. ""Sabida me?""""I'm not feeling well, sabida tun jiya ban ci rama ba, Yafendo ta ce ta kare""""try this"" ta fada tana mika mata plate din hannun ta."

"Bata yi musu ba ta karba ta bude, salad ne Nenen ta hada mata da kanta, yaji kuli da vinegar da tumatur, cocumbrr da albasa. Wani mugun yawu ya gudana a bakin ta, ta karba tun daga tsayen ta soma ci kafin ta zauna. Amma ko loma hudu bata yi ba ta dinga kwaro amai kamar zata amayar da hanjin ta."

"Tun daga ranar komai ta ci sai ya dawo, ta galabaita matuka, karfin jikin ta ya yi kasa sosai. Ambasada yace da Nene ta kaita asibiti, koda taimakon da zasu yi mata abinci ya dinga zama a cikin ta."

"Suna asibitin likita ya riketa, domin yace she's 60% dehydrated. Aka sa mata drip nan take. A ranar ne Ambasada ya kira Habib a waya."

"""In ka samu lokaci kazo 'Sachsenhausen Hospital' da daddare ina son ganin ka"". ""Insha Allah i will"". Ya fada cike da girmamawa."

"Karfe takwas na dare a Sachsenhausen ta yi wa Habibu Nahuche. Yana sanye da Native Hausa Attire dinsa na shadda sharaton ruwan makuba, ya kafa hula a gaban goshin sa ruwan toka mai turuwa sosai (deep grey), yayi kyau kamar koyaushe amma kallo daya Ambasada yayi masa ya gane muguwar ramar da yayi cikin watanni biyu da yayi bai ganshi ba."

"A wajen parking motoci suka hadu, direba ya sauke ambasada, shikuma taxi ta sauke shi. Ambasada ya bashi hannu sannan tare suka taka zuwa dakin da aka kwantar da Rahinah. Daga ita sai Nene a dakin. Kamshin turaren sa ne ya fara shiga hancin Raheenah, wani kamshi mai tasirin da bazata taba mantawa ba. da sauri ta juya kai zuwa bakin"

"kofar shigowa. Idanun su suka hadu, wanda hakan ya haifar da wani irin shock ga Rahinah dake kwance, domin ta ganshi ne ba zato ba tsammani."

"Yayin da Habibu Nahuche ya tsura mata ido, gabadaya ta zabge ta lalace, maimakon ya zo ya ganta very healthy and jovial tunda ta samu rayuwa yadda take so? Ta karbi 'yancin ta da take ikirarin ya danne mata? Banda girman idanun ambasada da yake gani babu abinda zai sa shi amsa wannan kiran, don bai ga dalilin sa ba. Tunda komai ya kare a tsakanin su."

"""To zauna mana kun tsaya kuna kallon-kallo kamar zakaru"" Ambasada ya furta masa sounding fatherly. Ya nemi guri can nesa da gadon da take kwance ya zauna. Wani irin abu na hankoro a zuciyar sa, ta shiga bugawa fat-fat-fat, bai san idanunsa sun yi kewar ta ba, sai yanzu da suka ganta kwance a gaban su, hatta zuciyar sa neman fitowa take daga tsakiyar kirjin sa. shikadai ya san halin ragaitar da ya samu kansa cikin wadannan watannin biyu masu kama da"

jiran tashin alkiyama a gare shi.

"Rahinah ta dauke kai daga kallon sa, ta mayar wani gefen daban, tunda suka rabu ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login