Showing 93001 words to 96000 words out of 117287 words

Chapter 32 - Na Huce Sabuwar Rayuwa BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

ce."

"""Duk ba kai ka jawo ba? Sau nawa zan gaya maka ka daina hantara ta a gaban sa, ka daina daga min murya a gaban idon sa?"""

"""Really? Ni na jawo ko ke ki ka jawo? Do you have the guts na fadar hakan? Shekara goma bai san ki ba sam sai yanzu, ina ya wani damu da ke har haka? Ciwo ne kawai daga Allah""."

"""In ma ba ku kuka jawo ba you all contributed immensely to it"". In ji likita Mansur. Yana buga tebirin gaban sa. Cikin kuka Rahinah ta ce,"

"""Tun farko ai kai ka fara poisoning mind din sa, da abin da shekarun sa, tunanin sa ba su isa ya gane, ko zuciyar sa ta dauka ba."

"Ni kokari na kullum shi ne ya saki jiki da ni kawai, ya dauke ni mahaifiya ban taba zaunar da shi na gaya masa laifuffukan ka ba, amma kai hum!! Allah kadai ya san iya abin da ka gaya masa, ban taba gaya masa cewa ka yi min wata rashin kyautawa ko guda daya ba""."

"A fuskar sa akwai nadama tsantsa, duk da haka bai yi admitting gabadaya ba. Hararar ta ya yi ya ce. ""Amma ai da kunnen sa yana ji kina min Allah ya isa in na debi abincin ki. Kuma ya gaya miki ba ya so""."

"Dramar ta su sai ta koma baiwa likita Mansur dariya, wadannan wadanne irin iyaye ne? Gasu duka educated and matured, amma suna behaving kamar yara."

"Haka suka yi ta mai da wa juna martani ba kakkautawa, likita Mansur na kallon ikon Allah. Suka yi suka gaji kamar zasu baiwa hammata iska, kuma a karshe suka bar ofishin sa zuwa dakin da yaron ke kwance a Aminity. Rahinah na hawaye."

"Bayan ya gaya musu a yanzu dai Abdallah yayi kankanta da shan antipsychotics, counselling yake bukata daga gare su iyayen nasa da sauran clinical treatments a nan asibiti, wanda zai kwantar masa da hankali ya koma cikin hankalin sa."

WA KE DA LAIFIN?

"Habibu da Rahinah sun tambayi kan su wannan tambaya har babu iyaka. A lokacin da suka tasa Abdallah a gaba suna kallo. Ya tashi daga baccin sai kallon ceiling yake, yana mamakin a ina yake haka? Shi da yake cikin ajin su? Kwana daya kacal duk ya rame."

"A tare kuma a sukwane suka isa gaban gadon sa har suna hada baki wajen tambaya. ""Abdallah ka tashi?"""

"Ta zauna tana matsar kwalla rike da hannun sa, yayin da Habibu ya zauna daidai kafafun sa ya dauki kafafun ya aza bisa cinyoyin sa yana matsa masa su sannu a hankali."

"""Sannu Abdallah na, Daddy is here, ba zan kara tafiya in barka ba Abdallah, duk inda za ni da kai da Mummy zan tafi."

"Mummy ai za ki bi ni Lagos ko?"""

Da sauri Rahinah ta gyada kai idanun ta a kan sa tana kakalo murmushin dole.

"""Sosai ma Dad, kafar ka-kafar mu ni da Abdallah, ai mun daina fada tuntuni ko Daddy? Abinda yasa ma ban bi ka PortHearcourt ba sabida makarantar Abdallah ne""."

Ta karasa fada tana gallawa Habib harara ganin Abdallah ya lumshe idanun sa yana sauraron su.

"Habibu ya ce ""ni ai na manta yaushe rabon mu yi fada, kin ga yau har zobe na sayo miki, yana mota in mun koma gida zan ba ki, ko kin fi so in saka miki da kai na?""."

"Likita Mansur na ci gaba da auna yaron yana jin su yana ta dariya a cikin sa. Iyaye da yawa ba su san cewa zaman lafiyar su ko akasin sa na affecting yaran su psychologically and morally ba. Daga Habibu har Rahinah babu wanda ya taba kawo wa ran sa wai Abdallah yana lura da abin da suke yi, yana kuma ajiye abin a ran sa."

"Nan suka wuni, kowanne da irin kulawar da yake yi wa Abdallah, a lallai sai sun nuna masa jiya ba yau ba, lafiya suke zaune. Amma duk sanda suka hada ido sai Habibu ya balla mata harara. Itama ta rama."

"Mr. Atiku ne ya kawo musu takeaway daga (Dominos) bayan azahar, suka ci tare a kan gadon Abdallah suna ba shi a baki suna masa hira, sai ga Nene da Sahura sun turo kofar sun yi sallama sun shigo, Sahura rike da basket din abinci. Rahinah kunya kamar ta nitse a wurin. Domin sun bararraje akan gadon ita da Habib sun sanya dan a tsakiyar su kamar zasu maida shi ciki. Ta yi maza ta diro daga gadon tana yi wa Nene barka da zuwa."

"Da sauri Nene ta iso jikin gadon ta kama hannun Abdallah ta ce,"

"""Sannu Abdullahi, me ke damun ka? Dazun nan Sahura tai min waya wai duk kuna asibiti an kwantar da Abdallah"". Rahinah da Habibu aka rasa mai bada amsa domin duk sun karaya, sai Habibu ne ya yi ta maza ya ce da Nene Balki, ""Sun ce Anxiety ke damun sa""."

"Nene ta yi salati, ta ce, ""Depression and Anxiety ba ciwon manya bane, ina Abdallah ina damuwar da za ta sa shi zama cikin Anxiety? To ikon Allah ya fi ga haka, ina fatan an dauki duk matakin da ya dace?"""

"""Sun yi iya kokarin su, amma sun ce, counselling ya fi bukata a kan kwayar magani sabidda karancin shekarun sa, sai Therapy da zai karba na sati biyu""."

"Zuwan Nene ya sa dole ya fita ya bar musu dakin, masallacin asibitin ya tafi don yin sallah. Nene Balki bakin ta bai yi shiru ba, sai kakabi ta ke kan me ya hada Abdallah da anxiety? Daga baya ta kira Aunty Badiya ta gaya mata."

"Badiya bata yi mamaki ba ta ce, ""Allah ya ba shi lafya, amma ai su suka jawo masa Nene, Habibu da Rahinah, sun ki yarda Annabi ya faku. Kullum kananan yara su ke maida kan su. In suka sabauta dan ai shi ke nan sun huta""."

Ta soma kwallah saboda ba karamin so ta ke yi wa Abdallah ba.

"Uncle Usman yana garin don haka da daddare ya zo duba Abdallah. Nan suka hadu da Ambasada a parking lot suka jera zuwa ciki, suna tafe suna hira wadda duk ta Habibu da Rahinah ce, da dan su Abdullahi. Maganar aikin Rahinah ya roki Ambasada ma ya saka baki Habibu ya bar ta ta koma. Ambasada ya ce,"

"""A'ah Usman, ka barshi ya yi cikakken iko da iyalin sa, in ya amince don kan sa, fine, in bai amince ba ta hakura babu rashin ci babu rashin sha, we are not to be interfering tunda dai mun yi mai wuyar mai kuma muhimmancin""."

"Sun duba Abdallah sun jajanta kafin su bar asibitin su duka. Direba ya maida Sahura gida, dakin daga Rahinah sai Abdallah."

"""Mummy zan sha Kelloggs"". Ya fada kan sa na bisa cinyar ta."

"Ta shafa kan sa ta ce, ""To Abdallah bari Daddy ya zo sai ya sayo ko?"". ""Ki masa waya mana! Yanzu nake so!""."

"Jiki na rawa ta zaro waya ta hau zakulo lambar sa, ashe ba ta yi saving ba, kawai sai ta shiga inbox din ta inda ta ga sauran sakonnin sa rututu da ya turo mata yana PortHearcourt, ba ta ko kai ga budewa ba, balle ta goge. Kawai sai ta yi sha'awar yau ta bude duka sakonnin Habib ta karanta da nutsuwa kafin ta kai ga kiran sa, don ya kawo sakon Abdallah."

Ga abin da Habibu ya rubuto wa Rahinar sa.

"1- ""Kin yi tasiri mai yawa cikin rayuwata, tasirin da a tarihin soyayya a rayuwar Bahaushe ban ga irin nawa ba RAHINAH. Kin jijjiga rayuwa ta tsayin shekaru goma da doriya, amma duk da haka ban fidda rai watarana na"

"zuwa da zamu koma daidai ba, har mu zama ma'aurata ababen misali. An ce abinda hakuri bai bayar ba rashin sa bai taba bayarwa, zan ci gaba da hakurin nan na wasu shekaru goman a gaba su zamo (two decades). Watakila sai a shekarun furfurata ne zan ci ribar hakurin nawa?!"""

"2- ""Ni Habibu ina mai ba ki hakuri Rahinah, da guiwowina a kasa.. a bisa duka laifuffukana na baya, wanda na sani da wadanda ban sani ba, irin hakurin da ban san yawan sa ba, ban san adadin sa ba, ban san iyakar sa ba."

"Na yi kuskure ina mai rokon a ba ni dama in gyara shi, ko da wannan ce dama ta karshe a gare ni. Na yi alkawarin zan goge tabon AUREN KWANA BAKWAI of the past Decade in only one night. idan kika bani dama!"

"Nayi alkawarin zan biya bashin soyayyar shekara goma da muka yi missing in only one night""."

"A hankali Rahinah ta wani lumshe idanun ta, kafin ta kai ga bude su daga lumshewar da ta yi musu, Habibu ya bude kofar dakin ya shigo da sallamar sa ba tare da ya san me ta ke yi ba."

"Sai ta kasa bude idanun har ya iso jikin gadon yana tambayar Abdallah,"

"""Ya ya dai apple of my eyes?"""

"Abdallah ya ce. ""Mummy na ce ta kira ka ka kawo min kelloggs tun dazu. I guessed she don't have your phone number, (na fahimci bata da lambar wayar ka), kai ma ba ka da lambar wayar ta?"""

"Da sauri ta bude ido ya sauka cikin nasa, duk suka kalli juna a tsorace. Habibu ya ce, ""Inquisitive Abdallah I have your mother's phone number, amma a nan (ya nuna saitin zuciyar sa) in ba ka yarda a yanzu in karanto maka ka ji"". ""Daddy na san ba ka karya, Mummy ke fa? Kina da number din Daddy na?"""

"Rahinah ta rasa abin da za ta ce, kafin ta tuna Abdallah is now a sick person, a mental patient wanda abin da yake bukata kawai shi ne a yi masa abin da zuciyar sa ke so, wanda ba komai ba ne sai shiryawar su."

"""Abdallah, I've your Daddy's phone number, yanzu ma ya turo min message da ita, kana so ka gani?"" ""A'a, ki dai karanto min in ji""."

"Da sauri ta dubi Habibu da idanun neman agaji, shi kuma ya kau da kai ya yana 'yar dariya, ya san yau Abdallah ya saka ta a kwana."

"""Abdallah zai fi kyau shi da ya turo sakon,ya karanta maka ko?""."

"Habibu ya ce me ye a cikin sakon banda I really-truely LOVE YOU? And I promised a changed person?"""

"Ya fada yana kallon cikin idon ta, kwayar idanun sa sun kada zuwa love colour bakidaya, wanda hakan yasa Rahinah jin kunya mai yawa, ba shiri ta hau rufe fuska da tafukan ta kamar wasu saurayi da budurwa, domin Habibu ya ki dauke rinannun idanun sa a kan ta, wanda hakan yasa Abdallah tuntsirewa da dariya yana fadin."

"""Mummy ki bude idon ki, we love you!"""

Likita Mansur ya turo kofar dakin ya shigo yana clapping hannayen sa. Don tun daga waje yake jiyo dariyar Abdallah.

"""Abdallah and parents, what a good scene? Ina fata sun daina fada Abdallah?"""

"Abdallah ya yi wani iri da fuska ya ce, ""Doctor sun daina ka sallame mu mu koma gidan mu, kuma ka roke ta ta karanta min text din da ta ce Daddy ya turo mata daga PH""."

Dariya likitan ya yi yana shafa kan yaron. Sosai ya ji yana son sa sabida wayon sa. Hes really smart.

"Ya ce, ""Abdallah this is their secret, ka ji? (Wannan sirrin su ne). Ba ruwan ka da abin da Daddy yake rubuta wa Mummy a waya, what matters most... (abin da ya ke muhimmi) shi ne su daina fada saboda ba ka so, su zauna lafiya har abada for you to stay healthy""."

"Ya gyada kai cikin fahimta, likita ya ce, ""That's my boy. Amma ba zan sallame ka yanzu ba Abdallah sai nan da sati uku, in na tabbatar (heart beat) din ka ya koma normal""."

"Bayan fitar likitan, Habibu ya dubi Rahinah ya ce,"

"""Abdullah abin da na tura wa Mummy ko ni ban san me na tura mata ba. I just texted her to check on you sanda ina PortHearcourt""."

"""Ina fatan ta ba ka amsa?"""

"""Sosai ma, na ba shi amsa tun a lokacin""."

"Habibu ya dago lumsassun danun sa ya yi mata wani irin kallo, da ya sa bakidaya ta nemi nutsuwar ta ta rasa ta rikirkice, sabida ita ba gwanar karya bace da ta yi ake gane ta. La shakka da a tsaye ta ke ba a zaune ba, ba abin da zai hana ta faduwa kasa sabida yadda Habib yake hukuntata da sexy idanun sa."

"""Mai karya dai, dan wuta!""."

"Rahinah ta juya kai gefe tana 'yar dariya a kan kalaman sa, ba tare da ta shirya yin hakan ba. Dariyar da ta shagalar da Habibu a cikin kallon ta da duk ya bi ya maida Rahinah unease, ta soma tunanin abin da zai tada ita daga gadon. Gashi kan Abdallah na cinyoyin ta, shi kuma yana zaune a daidai kafafun sa. Abdallah ya ce,"

"""Zan sha ruwa""."

"Tun bai rufe bakinsa ba uwar da uban suka mika hannu domin dauko masa a kan (bed-side drawer), hannun ta ya riga na Habibu sauka a kan gorar ruwan Faron, kasancewar ta fi shi kusa da lokar, sai hannunsa ya sauka a kan nata."

"Another unbearable chemistry like electrical shocking ya bakunce ta, wanda ya sa ta saurin dagowa ta dubi maigidan ta Habib Nahuche, sai aka yi sa'a idon ta ya sauka cikin nasa."

"Habib sai ya samu kansa da cure yatsun ta da ke kan robar Faro a cikin nasa hannun, wanda hakan ya sa Rahinah saurin runtse idanun ta. Tana karbar wasu sababbin pleasant feelings a zuciyar ta da ta kasa gane ko na mene ne, ko daga ina suke yunkuro mata."

"Habibu ya yi azamar dauke hannun sa daga kan nata sakamakon cewa abinda ya bakunce ta shima kwatankwacinsa ya ji, sannan ya dauki ruwan ya bude wa Abdallah."

"Kunya ta ji sosai kan irin reaction din da ta nuna. Kawai daga Habibu ya rike hannun ta. Dare ya fara yi sosai, dakin ya yi shiru domin Abdallah ya yi barci. Su kuma kamar masu ciwon baki sai zukata da ke adungure a cikin kirjin kowannen su."

"Rahinah na so ta ce ya tafi gida, tana so ta gyara gadon ta kwanta, ta rasa da bakin da za ta gaya masa hakan. Ya tattara hankalin sa kacokam ya dora a kan wayar sa, ga dukkan alamu chatting yake yi, kawai sai zuciyar ta ta gaya mata da mace ne, bazawarar da yake nema in ba haka ba da wa zai ke chatting karfe goma sha biyun dare? Kawai ta ji tsuka (tsaki) ya kubuce mata. Wani matsanancin kishi ya zo ya lullube ta."

"Habibu ya ji tsakin, amma bai zaci nasa bane, sai ya dago shanyayyyun idanun sa ya dube ta da idanuwan bidar bayani,"

"""Shin tsakin nan nawa ne ko na wani ne daban?"""

"Juyar da kai ta yi gefe, ciki-ciki ta ce, ""Don Allah ina son filin gadon, zan kwanta kusa da Da na. It's almost past twelve yanzun""."

"Kin dauke ido ya yi a kan ta, wanda hakan ya sa ta ji duk ta takura. Ya ce,"

"""Ni kuma yau till down zan yi a zaune ina kallon kyakkyawar fuskar bafulatanar mata ta Rahinah Omar. She's indeed a heroine. Domin a rayuwa ta ban taba ganin mace mai aji, mai kullata, rashin afuwa, rashin yafiya da kafaffiyar zuciyar ta ba."

"I wanted to ask Rahinah since, shin zuciyar ta ta dutse ce? Ko kuwa kurmar zuciya gare ta? Shin Rahinah ke a wurin ki lokaci ba ya maganin kullata, a tunani na time heals everything! It's almost a decade and above, amma har gobe Rahinah na nan a yadda na san ta."

"Ni Habibu Mustapha Nahuche, dan adam ne kamar kowa, mai tarin nakasu (flaws), kuma mai zuciya da gangar jiki irin na kowanne lafiyayyen dan adam."

"In haka ne ta ya ya ba zan kasance cikin masu aikata kuskure ba? In ankara, in so gyarawa, amma a hana ni damar gyarawar?"

"I'm not saying all these to own your body, I'm saying it because I want you to know that I'm human, not a saint, or a Prophet (ba ina fadar duka wadannan don in mallaki jikin ki da zuciyar ki bane, ina fada ne don ina son ki san cewa nima mutum ne kamar kowa, dan adam ajizi, ba waliyyi ba ba kuma Annabi ba, wadanda ko su ba su tsira da aikata kuskure ko sau daya ne a rayuwar su ba)."

"Allah shi kadai yake PERFECT a komai Rahinah. I'm saying SORRY for all that happened, a decade ago, from the bottom of my fragile heart."

"Sorry for all the grievances and inconveniences that I caused to you Dr. Rahinah, na yi miki alkawarin zama na soyayya da farin ciki mai dorewa har zuwa karshen rayuwar mu. I promised to be far-away from your body tunda"

"wannan shine babban abinda ya janyomin bakin jini a wajen ki""."

"Da sauri Rahinah ta shiga girgiza kai, ammma ta kasa cewa komai, domin kalaman dake fita daga bakin sa a yau bata taba zaton su ba. Anya Habibun ta ne? Her ex Habibu ne? ko wani mai tsananin kama da shi ne??"

"Bata fita daga wannan mamakin ba, Habib Nahuche, ya sake gigitata da sabon mamaki. Ta hanyar kamo hannayen ta ya rike su tsam cikin nasa."

"""Rahinah KIN HUCE?"""

"Tunda ya fara maganar zuciyar ta ke luguiguita tana kakkaryewa tana kara HUCEWA, domin ta yarda da dukkan kalaman da ke fita daga bakin sa, haka suke har kasan zuciyar sa."

"""Ni na ce maka ina fushi ne? To Habibu NA HUCE"". Ya yi mata kyar da ido."

"""In ba fushi ki ke ba, me ya hana ki biyo bayan mu? Ban taba tunanin zan isa Nigeria lafiya ba tare da kin tara min mutane a kaina ba da sunan na sace miki Da, bayan nan ki ka dawo ki ka kama ayyukan gaban ki ko sau daya ba ki taba tunanin ki neme

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login