Showing 96001 words to 99000 words out of 117287 words

Chapter 33 - Na Huce Sabuwar Rayuwa BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

mu ba."

"In ni ba ki neme ni ba don na yi miki laifi Rahinah, which I'm sure daga baya kin huce kin yi kewata yadda na rayu cikin kewar ki, abinda kike nunawa a zahiri ba haka ba ne a zuciyar ki ba, ai kya nemi dan ki ko? Ki binciki rayuwar sa ko lafiyar sa? Ki ga shin ya ya muke rayuwa? Amma ko sau daya! Baki yi hakan ba."

"In gaya miki gaskiya wannan shine babban abinda yayi min ciwo bayan rabuwar mu har fiye da takuramin sakin da kika yi. Kullum a tunani na da tsinkaye na shine zaki dawo da kan ki ki nemi mu koma saboda dan mu, a yayin da kika yi achieving goals din ki. Sai kika nuna min kashi ma ya fi mu daraja ko bayan actualizing goals din""."

"Ba ta san sanda ta yi dariya ba, ta ce, ""Ko? Bari in gaya maka abin da ba ka sani ba..."

Duk wani step further da ka taka a rayuwar ka bayan dawowar ka Nigeria ina bibiye da shi.

I'm the first to send an appreciation message to BBC HAUSA a shirin nan na DOMIN MATASA....

I'm the first to send an appreciation message zuwa ga jaridar NEW NIGERIA a kan shirin 'A ROLE MODEL NIGERIAS HOTELS OWNER....

"Ni ce ta farkon aika sakon jin dadin shirin ""The Legend of the Sahara... HABIBU NAHUCHE na gidan Radiyon Jamus a shekarun da suka gabata. ""."

Sakin baki ya yi galala! Yana kallon ta domin ta gama mamakantar da shi. Ta shammace shi da abin da bai taba sani ba.

"""Abin da kawai ban sani ba a kan ka cikin shekaru goman shi ne, kasancewar ka kanin Aunty Badiya, wadda nake tare da ita sama da shekaru shidda, tun zuwan mu daga Jamus na farko lokaci da na hadu da dangi na."

"Had I know ita ke rike da Junior kai ma ka san da tuni wani labarin ake ba wannan ba""."

"Tasowa ya yi daga inda yake zaune, ya zo ya durkusa a gaban ta daga gaban gadon, ya dora tafin hannun sa saman tafin kafar ta."

"""That is what I don't know either. Had I know da tuni ni ma wani labarin ake ba wannan ba"". 'Yar dariya ta subuce mata jin yana yi mata tausa a kafafun a hankali har da tafiyar tsutsa . Ta ce,"

"""Da wane labarin ake to zuwa yanzun?"""

"Yatsun sa biyar ya daga ya wara mata a kan fuskar ta. ""Da yanzu su biyar ne ba shi kadai ba""."

"Ta gane abin da yake nufi, wanda hakan ya sa ta murmushi (serene smile) amma sai ta nuna bata gane din ba. ""Su su wa kenan?"""

"Ya ce, ""Abdallah da kannen sa mana""."

Hira mai ban mamaki da ratsa zuciya ta ci gaba da gudana (heart to heart) wato daga zuciya zuwa zuciya tsakanin Habibu Nahuche da mai dakin sa Rahinar sa. Hira ce irin wadda ba su taba yi a tsayin rayuwar su ba. Ta ba shi labarin duk halin da ta shiga bayan tahowar su. A karshe ta ce.

"""...And evetually I moved on, kafin na gane rayuwar diya mace bata taba cika cikakka idan babu SOYAYYAR MIJI, sai dai hakan ba ya nufin faduwar diya mace warwas, in dai za ta iya kare mutuncin kan ta ta ribaci lokutan rayuwar ta da neman ilmi da neman lahira."

"Sabanin sauran mata da ke bata lokutan su wajen kuka da halin maza na sun musu, sun musu kaza da kaza, har hakan ya taba kwakwalwar su ya hana su cigaba. Ni Rahinah I'm apparently a strong woman, wadda ta dauki goal attainment (self-actualization) da matukar muhimmancin da ya danne soyayya."

"Shi ya sa na zauna lafiya kalau, in na ce lafiya kalau, ina nufin fa lafiya kalau...""."

"Irin kallon da Habibu ke mata ya sa ta saurin toshe bakin ta tana dariya. Domin kallo ne na karya kike yi, in fact, you are not well at all."

"Ya ce, ""Wallahi ba lafiya kalau ki ke ba, sabida ita soyayya barin rayuwa ce, kuma halittar Allah tsakanin Adamu da Hauwa'u."

ABRAHAM MASLOW (1970) (psychologist) wanda ya samar da %’o heory of Self-Actalization. Ya sanya ta cikin

"jerin rukunin bukatun rayuwar dan adam guda bakwai, wadanda ba zai iya rayuwa babu su ba (HIERARCHY OF NEEDS THEORY OF MOTIVATION)."

MASLOW ya ce;

"""As long as the more urgent and pressing need is satisfied, another urgent need will emerge and become operative, and a currently satisfied need will become unimportant and underestimated and no longer controls or dominates behaviour...""."

"-(Abraham Maslow, 1970)."

"Dariya ta yi cikin matsanancin nishadi, kace ka tashi da 'Hotel Administrator' ka koma malamin %’vi sychology""."

"""Ko daya, ni ba ni da alaka da psychology amma na san wannan, na kuma kawo miki misali da theory din ne don ki san cewa, bayan self-actualization din ki ya gamu, dole ki dawo daga baya ki nemi soyayyar miji da ta 'ya'ya (Love and Belonginess Need). Wannan a rubuce yake, sai dai kuma idan Rahinah waliyya ce ba mu sani ba""."

"""Yanzu ka bar maganar Maslow a gefe, na yarda da kai with no temptation, amma don Allah me ya sa ka aure ni a yadda ka aure ni a Jamus?"""

"Ya rausayar da kai ya yarfar da hannu ya ce, ""Only men in mid - twentieth can relate. I have no option a wancan lokacin, in ba so ki ke in kare da raping din ki ba kuma in kare (behind bars) ban da babbar azabar Allah da za ta jiraye ni ranar gobe kiyama""."

"Ta kai kyawawan yatsun ta ta rufe fuskar ta, ""Habeeeebu you are too much""."

"""Har na kai ki? My sweet sixteen my Bafulatana Rahinah Omar Girei. Duk da na sha wahala, ina kuma kan shan ta har yau ina alfahari da wannan gantalallen auren."

Ga kyautar Allah wadda bani da tamkar ta (Abdallah).

"And by so doing, i then came to realized the worth of a WOMAN, inda na gane abubuwa da dama a kan mata, na gane ba duka mata suka taru suka amsa suna daya ba na cewa su duka raunana ne a kan soyayyah, akwai masu kare%’šj elf esteem %’ din su koda soyayyar zata yi ajalin su, wadanda basu dauki soyayya da namiji shine rayuwar su ba, a typical example of my Bafulatana Dr. Raheenah Omar Girei. I salute!!!."

(Ya fada yana yi mata gaisuwar sojoji). Kan ta yayi gingirin-gin. A fili ta ce (cikin shauki). Baban Abdullahi kana fasa mun kai!

"Ba maganar fasa kai bace maganar gaskiya ce. Wanda hakan ya kara sawa na girmama ki, na kara daga darajar ki a zuciyar Nahuche."

Amma don Allah ina rokon alfarmar daga yau dinnan in tashi daga HABIBU in koma HABEEBEE.

"Rahinah sai dariya ta ke. Cikin matsanancin nishadin da bata taba tsintar kanta ba. In wani ne ya gaya mata watarana irin wannan na zuwa, da Habibu Nahuche zai tsaya a gaban ta ya bude baki yayi mata magana mai tsayi har haka za"

"ta karyata. Sabida karancin maganar sa. Habibu ya mike daga durkuson da yayi a gaban ta ya koma jikin gadon ya jingina, tare da harde hannayen sa a kirjin sa."

"%’ím o yanzu dai kin gane ko Maam? Ke da Dan ki ku gyara min waje in kwanta, yanzu zaki ji an kira asubahi bamu runtsa ba, barci nake ji sosai""."

"""Ai gadon ya mana kadan mu uku Habeebi. Ba ka ganin ba shi da fadi?"""

"""A haka za mu yi maneji, rayuwa sai da maneji da abunda ka samu. A baya ina na samu wannan alfarmar?."

"A hakan suka kwanta. Rahinah a barin dama, Habibu a barin hagu, Abdallah a tsakiyar su, %’n uch is life my dear wife, yadda ta zo wa bawa a haka ya kamata ya karbe ta"". Ya fada yana gyara wa Abdallah kwanciya, suka sanya shi a tsakiya suka rungume, suna fuskantar juna suna kuma kashe juna da ravishing smile."

"""This is pure contentment of my life"". Habibu Mustapha Nahuche, ya fada a ran sa yana sarke yatsun kafar sa cikin na Rahinah, wani irin jin dadi na tsirga masa. Rahinah ta rungume Junior da hannu daya, hannun ta daya cikin na Habibu, idanun ta cikin nasa suna yi wa juna kallo na kauna da soyayya."

"Da zasu iya, hakika da, sun rike wannan moment din daga motsawa kada gari ya waye, wani abu ya zo, ya gifta a tsakanin su."

"Sai ya mika hannu ya latsa makunnin fitila shudiya ta maye gurbin mai haske (dim light), ta cikin dan hasken shudiyar fitilar suke hango kyallin hawayen da ke kwance yana tsatstsafowa cikin idanun kowannen su."

"Hawayen so da farin ciki, wanda kwanciyar hankali kadai ya yi sanadin sa cikin idanun Habibu da Rahinah."

Tun tana tsammanin Habibu zai yi kalar wani motsi bayan wannan (ya nemi taba ta ko kissing din ta) har ta ji saukar numfashin sa a hankali mai nuna ya yi barci.

"Da ace wani ne ya gaya mata za ta kwana gado daya da Habibu watarana ba za ta taba yarda ba. Da dai wani ne ya gaya mata Habibu zai iya kwana gado daya da ita bai nemi komai daga gare ta ba, ba za ta taba yarda ba."

"Da asubah shi ya fara tashi sakamakon kiraye-kirayen sallah a masallacin asibitin. Junior ya motsa ya ji an matse shi a gadon sa, sai ya bude ido a hankali ya gan shi tsakiyar iyayen sa biyu. Wani abu da bai taba faruwa ba tun dawowar Rahinah cikin rayuwar su."

"Sai ya sa hannu daidai ya rungume kowannen su, ya ci gaba da barcin sa a haka."

Habibu da dabara ya zame daga rikon da Junior ya yi masa a hankali ya sauka zuwa toilet wanda ke makale a cikin aminity room din.

"Motsin sa ne ya tada Rahinah ita ma, ya fito daure da alwallah. Lokacin ta tashi ita ma ta kunna fitilar dakin. Suka dubi juna sai ta sunkuyar da kanta cikin jin kunya."

"""Dauro alwallah mu yi jam'i kawai, sai in wuce gida in yi wanka""."

"Ta bi umarnin sa, shi ya ja su jam'in suka yi raka'atainil fajr, sannan suka bada faralin asubahi. Suka kara da sallahr nafilah."

"Suka yi addu'o'i masu yawa a kan su da zuri'ar su, iyayen su da suka rasu da wadanda ke raye har ma da masoyan su, sannan Habibu ya mike don tafiya gida yin wanka, har ya kai bakin kofa ta ce."

"""Ka dauko min wani bedsheet din in canza wannan, da man shafawa ta a kan mudubi na"". ""An gama Habeebty, me ku ke son karyawa da shi?"""

"""Kada ka damu da wannan, Nene da Sahura duka za su kawo"". ""Kwalliya kuma fa? Wace iri za'a yi min? Kalli idanun ki, duk sun jeme""."

"Yar dariya ta yi ta ce, ""kai kuwa dan kwalli daya kwal ya tsoka daya a miya aka ce min kwakwalwar sa ta tabu fa! Ai in da akwai abinda yafi jemewa da ramewa duk zan yi su. Allah shine shaida. This the terrible moment of my life bayan na sace shi da kayi %’."

"Habibu ya gyada kai ya ce umh. I can relate, sai son dan kawai aka sani, baa san ta ya zaa nuna masa soyayyar ba. Mu bar wannan zancen. Ka zabo duk kayan da ka ke so in saka a wardrobe dina, ka dauko min turare Yves Saint Laurent a kan mudubi na""."

"Ya ce, ""Da kuma mascara da wet-lips ko? Bakin duk ya bushe"" Dariya ta yi ta ce,"

"""Anything that will beautify me Habibi""."

"Sai kuma ta rufe ido ta ce, ""kai ma yau ka sako kananan kaya, don in gan ka dan saurayin ka yadda ka ke a Jamus, dan saurayin nan nawa na cikin jirgin 'Boeing' da na rungume cikin rashin sani, wanda ya sanya wa Rahinah Omar, rigar kubuta daga hadarin jirgi""."

"Dariyar da Habibu ya yi sai da ta fiddo fararen hakoran sa, ya kada kai ya sumbuci Junior da ke barci. Rahinah ta saki baki da kunci tana jiran tata sumbar har da lumshe idanu, sai ta ji shiru, wayam."

"Kafin ta ankara ta ji shi ya kai bakin kofa yana fadin, ""Sai na dawo!""."

"Wai kuma sai ta ji duk babu dadi, Habibu na nufin ya daina kai hannun shi jikin ta kenan ko me? Tun zuwan sa ban da a ofishin likita da ya kankame ta saboda razana, ko sau daya bai kai hannu shi jikin ta ba."

"Da gaske yake kenan da ya ce ta jika komai nata ta shanye, he is going for a second wife ko me?"

"Wani abu da a halin yanzu ta san ko sama da kasa za su hade ba za ta taba yarda ba, (kara auren Habibu) don yanzu ne ta san tana son mijin ta uban dan ta! Tana kuma hakikanin kishin sa."

: HAJ. KALTUME HAJIYAR NAHUCHE

B

"a da sanin Habibu ba, Aunty Badiya ta kira Hajiyar Nahuche ta zayyana mata halin da Habibu da Rahinah suka sanya Abdallah. Lokacin sun yi sati guda a asibitin saura sati a sallame su."

"""Ki duba ki ga Hajiya, wautar su ta janyo wa karamin yaro lafiyayye irin Abdallah mental instability. A da ina blaming Rahinah ne ita kadai, amma wallahi yanzu na gane Habibu ya fi ta laifi, don shi yake biye mata a matsayin sa na namiji, mai hankali kuma babba sama da ita."

Karfe daya ba ya amo. Don haka zan maida yaron hannu na da zarar an sallame shi daga asibiti in ya so su je su haukata kansu su kadai.

"Na yi nadamar sa wa ki ba su yaron, ban san shirmen da suke aikatawa cikin gidan su kenan ba sai da na je na gani da ido na""."

"Hajiya Kaltume ba ta iya ta ce komai ba, bayan, ""Allah ya kyauta. Allah ya ba shi lafiya""."

"Amma can kasan ranta abun ya dame ta sosai, domin tana tsananin son Abdallah. Abdallah dan lelen Hajiya ne. Wunin ranar zungur da abun ta wuni yana damun ta a rai, tana ta sake-sake, ba ta yi niyyar zuwa gidan Habibu nan kusa ba, sabida rike girma da dattijantaka irin nata, amma ta yanke shawarar gobe dole ta je ta gano lafiyar Abdallah."

"Ga Hajiya Kaltume ba ta iya sa abu a rai ba, in ta sa abu a ran ta ya yi ta damun ta kenan, wannan damuwar ce ta tada hawan jinin ta ba tare da ta sani ba. Wuni ta yi kwance a daki."

"Ta shiga bayan gida da asubahi ta daura alwala duk da yadda ta ke jin jiki, ta dawo kenan za ta shiga daki sai kawai ta zame ta fadi bisa kofar dakin ta. Faduwar da sai gadon asibiti aka nufa da ita gari na dan yin haske da taimakon masu aikin ta."

"Habibu da Rahinah, wadanda a ranar ma sun yi kwanan zaune ne cikin rayuwa ta %’‹j eart to heart talk %’, wadda"

"ita suke kwana yi duk dare a gadon asibitin Abdallah, wadda a yanzu ta samar da mashahurin kusanci da aminci ga zukatan su. Hatta sallahr asubahi kullum tare suke yin jamin ta a dakin asibitin, sai gari ya waye ne Habibu ya ke zuwa gida ya yi wanka ya dawo."

"To yau ma kamar kullum, dawowar sa daga wanka kenan ya shirya cikin babbar shadda getzner mai hasken sararin samaniya, suka tsinkayi wannan mummunan labari na faduwar Hajiya da kwantar da ita a babban asibitin Zamfara da sanyin safiyar ranar a bakin mai aikin Hajiyar wato Larai, wadda ta dau wayar Hajiya ta kira Habib din, bayan ya dawo asibitin daga wanka da ya je ya yi."

"Rahinah dai ta ji Habib yana salati, sai kuma ya mike ya hau neman takalman sa da mukullan motar sa bayan ya sanya hular sa a gicciye, ya dau makullin mota, Abdallah na barci lokacin bai tashi ba."

"""Lafiya Habibi?"" (Sabon sunan da ya farlantawa Rahinah kiran sa madadin Habibu). Ta tambaya cike da damuwa cikin sanyin murya."

"Habibu na takawa zuwa kofa ya ce ""Hajiya ce wai babu lafiya, zan wuce yanzu, ki kula da Abdallah please, zan tsaya Kaduna in dauki Maman Musaddik mu wuce Zamfara""."

"Cikin damuwa sosai ta yi wa Hajiya addu'a, sannan ta yi masa addu'ar sauka lafiya. Har ya kai bakin kofa zai fita, ta ce, ""Habibi""."

"Sai ya dakata, sannan ya juyo yana duban ta da manyan kyawawan idanun sa."

"Ta taka a hankali zuwa gaban sa, ta sanya hannu a wuyan rigar sa tana sanya masa maballan da rudewa tasa bai balle su ba, a hankali Habibu ya dan rufe idon sa jin sanyin hannun Rahinah a wuyan sa, sannan ta makala masa links din hannun rigar shi da shima yake a bude. Ta yi kamar za ta sumbace shi, ko me ta tuna? Sai ta ji kunya, ta fasa. Ta yi maza ta ja da baya."

"Murmushi Habib ya yi, sannan ya sa kai ya fita daga dakin, ba tare da ya yi mata abinda take so din ba, ya fice yana fadin."

"""Sai na kira Ummu Abdallah, ki zauna da waya a kusa da ke don in ke jin lafiyar ku""."

"Bayan fitar Habibun, Rahinah kasa komawa ta zauna ta yi har sai da ta ga fitar sa, ta ci gaba da safah da marwah a dakin, tana kallon dan su Abdallah da ke barcin sa peacefully. Idan ta tuna kwakwalwar Abdallah yanzu ba daidai ta ke ba, duk sai ta ji ta daina jin dadin komai na duniya."

A wani gefen tana jajanta rashin lafiyar Kakar sa don ma ba ta san musabbabin sa ba. Bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login