Showing 87001 words to 90000 words out of 117287 words

Chapter 30 - Na Huce Sabuwar Rayuwa BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

afford to lose such a golden Doctor like her, inda ya sanar da su ba shi da masaniya a kan barin ta aiki, amma zai yi wa mijin ta magana, mai yiwuwa ne shi ya dakatar da ita."

"Ko da ya kira Habibu yana tambayar ba'asin maganar, sai ya yi shiru. Wannan ya tabbatar wa Uncle Usman zargin sa na cewa shi ya hana ta din, kuma ba abin da za'a iya yi wa Rahinah barazana da shi ta bar aikin ta na likita a yanzu in ba dan ta ba."

"Uncle Usman ya yi wa Habibu fada sosai ya ce,"

"""Aikin ta bai da alaka da rigimar ku Habibu, ko da ka gan ta da karatun ta ka same ta, kuma ta sanadinsa ne har ka samu damar auren ta, har ku ka haifi Dan da ka ke mata barazana da shi Habibu."

"Don haka ka bar ta ta yi aikin ta tunda aiki ne na taimakon al'umma. Bana son zuciya ba ne ko na rashin godiyar Allah""."

"Habibu ya yi mamakin jin Rahinah ta bi umarnin sa ta bar ayyukan ta duka, shi iya na Nizamiye ya ce, wannan ya kara tabbatar masa Rahinah ta fara canzawa daga kafaffiyar da ya san ta a baya, kuma da gaske ta ke za ta yi wa Abdallah goyon da ya kubuce mata na shekaru goma ba da laifin ta ba, sai ya ji tausayin ta ya kara ya tsirga masa."

"Amma ko da ya dawo gidan a washegari daga PH, bai nuna mata hakan ba. Bai nuna mata cewa ta fara karya lagon sa ba. Ya sha tura mata %’―i ext masseges %’ yana PortHarcourt amma ba ta taba replying ba, ko tana gani ko ba ta gani? Allah masani."

"Ko da ma ba masu bukatar reply ba ne, yawanci na ban hakuri ne kawai da alkawari kala-kala, a kan ya yi alkawarin zai canza, zai zama miji abin alfahari a gare ta. Zai koma irin yadda duk take son shi. Zai zame mata Mijin marainiya kuma loving and caring husband."

"Bai tsammaci da ma za ta kula shi ba, kamar ya san a duk lokacin da ta gani ba ta bata lokaci ta ke share su daga fuskar wayar ta duk da a lokuta da dama kalaman suna taba ta, suna sassauta fushin da ke zuciyar ta."

Amma still ta kasa sakewa da shi wholeheartedly. Ta kasa yarda duk abinda yake fadi haka yake har zuciyar shi. A ganin ta he needs time wato yana bukatar lokaci.

"Ba tare da ta san cewa yau zai dawo ba, tana kicin tana juya lafiyayyar miyar Talo-Talo (Turkey) da ta ke soyawa mai yawa ta saka a firji. Sai jin takun sa ta yi ya nufo kitchen din. Kasancewar shi mijin ta, Habibu Mustapha Nahuche, mutum ne mai takun kan sa (duk inda ta ji takun sa sai ta gane), yana ta hayaniyar cigiyar Abdallah cikin gidan bai san yana can bayan gidan yana fama da dirkeken 'Bike' din sa ba."

Abdallah where are you? Im here now!

"Daga bakin kofa ya tsaya hannayen sa biyu zube cikin aljihu yana kallon bayan ta da wata irin siga, yana jin wani irin contentment da wata nutsuwa ta musamman suna baibaye shi. Samun mace kamar Rahinah kadai matsayin matar aure is a BLESSING da bawa domin sai wanda Allah ya zaba ya ga damar ba shi, a ganin sa ko da ba za ta amfana wa mijin ta komai a shimfida ba, kallon kyakkyawar fuskar ta kadai da fararen idanun ta sun isa sanya shi farin ciki kullum."

"Ga shi ta yi wani abu da ya tsaya masa a rai, ya kuma lankwasa zuciyar sa yau, wato ayyukan ta da aka ce da gaske ta bari saboda Abdallah."

"""Good afternoon Dr.\Mrs NAHUCHE""."

"Habibu ya fada da lallausar muryar da Rahinah ta kasa amincewa tasa ce. Sabida a kullum yana mata magana ne harshly and loudly da sigar tonon rigima, amma yau ba abin da muryar sa ke dauke da shi sai lislama, ni'imtacciyar soyayya da kulawa tsantsa."

"Banza ta yi da shi ta ci gaba da soya miyar ta, sai ya tako a hankali tamkar mai tausayin kasa zuwa inda ta ke. Ba ta yi aune ba ta ji ya rike ludayin, ya kuma kashe cooker din."

"""Ki ba ni attention daga tafiya na dawo. Kuma kin san cewa I missed you ko?""."

"Ta daga ido ta dube shi a fusace ta ce, ""Ina ruwana da tafiyar ka? Na aike ka? Ko na ce ina bukatar dawowar ka? Na bi I missed you din da gudu na tattake da takalmi mai tsini a kafa ta!"" Ta fadi tana tattaka kafar ta a kasa."

"Dariya ya yi. Rahinah ko tsufa ta yi baya jin zata bar ki-fadin ta da tsiwa. Amma kwayar idanun ta sun fallasa cewa ta ji dadin %’Ϊm missed you %’ din, ita haka Allah ya halicce ta son soyayyar miji."

"""Ba ki ce ba, amma kin iya kai kara ta gun Baban ki ki ce na hana ki aiki, kin manta cewa yanzun ba ikon Baban ki ba ce, iko na ce (ya nuna kirjin sa da dan alin sa) To na hana din, ki yi duk abin da za ki yi, tunda na ce zan biya scholarship din da aka biya miki ga duk wanda ya bukata""."

"A kufule ta dube shi, sabida kalaman sa sun bata mata rai matuka. Shi da ya ke neman shiri amma ba zai bar gadara da fadin rai ba. Hausawa sun yi gaskiya da suka ce Mai hali ba ya fasa halin sa don shi hali kaman zanen dutse ne. ""Ba ka da arzikin da za ka fanshi ilmi na, domin shi ilmi ba a sayen shi da dukiya, wadannan kudin naka da babu tabbacin ba na haram ba ne sun yi kadan su fanshi karatu na""."

"Ba zan kara cewa ka sake ni ba, don I'm now matured enough ga bukatar hakan, amma har abada ba za ka samu zuciya ta tare da amincewar gangar jiki na ba. ""."

"Sai juyawa suka yi su duka suka ga Abdallah a bayan su, hankalin sa a tashe da fadan da ya tarar suna yi kamar za su tada kicin din."

"Kafin Habibu ya yi masa magana Abdallah ya juya da sauri, da sauri ya sakar mata ludayin ya bi bayan sa, sai kuma ya juyo yana kallon ta a kaskance. Domin kalaman ta sun masa ciwo ba dan kadan ba. (Cewa da tayi ba zai taba samun zuciyar ta da amincewar gangar jikin ta ba)."

"""Ki jika komai naki ki shanye don Allah Rahinah, I'm going for a second wife, wadda ta fi ki duk abin da ki ke takama da shi. Za ki ga ranar da kudin haram za su yi wa dan halal""."

"""Ka dade ba ka yi ba! Tunda ka kwashe shekaru goma ba ka yi ba sai yanzu, in ka yi yanzun gaskiya zai fi zama fashionable, sai ana son mutum a ke kishin sa""."

"Ta karasa cikin karkarwar murya da ita kanta ta ba ta mamaki. Da gaske yake? Ko kuwa barazana ce irin wadda ya saba? In ma da gaske ne bai kamata ta ji faduwar gaban da ta ji a kan maganar sa ba, in har da gaske sai da so ake kishi."

"Duk abin da suke fadi a kunnen Junior wanda ke bakin kofa ya kasa tafiya daki yana ta tsuma, zazzabi ne ya zo ya rufe shi sabida a rayuwar sa ba ya son fada, kuma ya tsani hargagi da tashin hankali. Amma dukkan su are talking bitterly to each other ba tare da sun san ya dade tsaye yana jin komai ba."

"A daren wannan ranar an yi drama ba 'yar kadan ba, hakurin Habibu ya gaza, yayi lallashin duniya Rahinah ta ki, musamman tunda yayi maganar gatsen zai kara aure, hakan ya kara fusata ta, ya kara gishiri akan danyen gyambo, bayan a da ta fara dan sakkowa."

"Shi kuma Rahinar sa yake son kasancewa da, anyhow, wanda abinda ya sanya shi dawowa daga PH kenan ba tare da ya gama abinda ya kai shi ba, ba don alkawarin da ya yi wa kan sa ba, na har abada bazai kara ba, ba akan Rahinah kadai ba, akan kowacce diya mace, sabida tunanin nasa yaya matan da zai iya Haifa a gaba, (after knowing the consequences of marital rape), da babu abin da zai hana shi maimaita laifin sa a yau, sai dai ko me zai faru ya faru."

"Ya yi kwanan bacin rai ba dan kadan ba, yau ko gafarar bai roka mata ba, bacin ran da ya sa da asubahin washegari ya buga wa Aunty Badiya waya."

"Wayar sa a daidai wannan lokacin ta fadar mata da gaba, idar da sallahr Asubar su kenan ita da Uncle, sai ta fito daga inda Uncle Usman yake zuwa dakin ta, ta amsa wayar tasa a nitse, don ba ta san ko me ta kunsa ba."

"Suka gaisa shi da Badiya, amma ba'a kai karshen gaisuwar ba Habibu ya ce, ""Maman Musaddiq aure nake so zan kara. Ina neman taimakon ki""."

"A zaune Aunty ta ke, amma sai ga ta tsaye a kan kafafun ta."

"""Amma ba karamar yarinya ba, bazawara nake so wayayya ba mai karatun boko ba, wadda ta doshi shekaru arba'in haka""."

"Aunty ta nisa, kafin ta ce,"

"""To Habibu za a bincika, amma ba yanzu ba. Duka-duka yaushe wannan ta koma? In ka kasa zama da guda daya zama da biyu ba naka ba ne. Find the root cause of the problem first, tackle it then, I'm sure ba dadi ne ya kawo bukatar karin auren ba sai akasin sa."

"Daman ina da niyyar zuwar muku cikin satin nan in ga lafiyar ku, amma yanzu gobe zan zo insha Allah."

"Ka ba ni sati biyu zan gana da Rahinah tukunna. Bayan nan in karin auren shi ne solution na tabbatar maka zan mara maka baya""."

Da wannan suka yi sallama.

Kamar yadda ta alkawarta masa a washegari Musaddiq ya dauko ta zuwa Abuja.

"Ba ta gaya wa Rahina za ta zo ba, yau din ma suna tsaka da rikicin su a falon kasa, wanda duk rikicin Habibu da Rahinah kashi tamanin cikin dari in ka bincika a kan Dan su ne""."

"""Ni na ce ki dinga kai shi makaranta? Ko ko salon samun hanyar gantali a kan titi? Ban ajiye masa direba ba?"" Cikin tsananin zafin rai yake magana. Wanda kin sa da ta yi daren jiya shi ne sila."

"Rahinah ta ce, ""Ka ajiye, kaishin da nake yi ganin dama ta ne. Wai me ka ke nufi da ni ne Malam a gidan nan?"

"Auren kulle za ka koma yi min? Ka ce aiki, na bari, sannan ka ce ba inda zan je don in mike kafa ta sai dai kawai in zauna in sharba kiba a cikin daki?"""

"""Za ki rantse da Allah sabida ki motsa kafa ki ke kai shi ba don ki yaudare shi ba? In motsa kafa ne ina gymnasium din gidan? Kawai so kike ya saba da ke, ya so ki, ya so ci gaba da rayuwa da ke, ki zo ki sake guje masa!"

"Ai mumini maciji ba ya saran sa a rami guda. Mun dade da sanin wace ce ke, mayaudariyar Uwa, muguwa, azzaluma. !"""

"Fushin nasa ba a kan kai yaron makaranta da ta keyi bane kawai, har da kwalelen talalar data yi masa daren jiya."

"""Habibu!"""

"Ya ji muryar Aunty Badiya daga bayan sa cikin fushi. ""Me nake gani haka? Me nake ji haka? Ku kalla nan...""."

"Ta nuna Abdallah da ke mannewa a bayan labule jikin sa yana ta rawa da karkarwa, ko kadan ba ya son fadan nan da suke yi kullum, ba abinda ya tsani gani irin sa'in sar su, da sunan nan da Habibu ke kiran Rahinah a duk sanda ya bushi iska; muguwa-azzaluma."

"Don a dan zaman sa da ita su biyu a cikin gidan ya fahimci abubuwa da dama a kan ta, tana son shi ita ma, kwatankwacin yadda Baban nasa ke son shi, har ya fi jin dadin kulawar ta a kan ta Baban sa."

"Bai ga mugunta ba, bai ga zalinci a Maman nasa ba!"

Daga shi har Rahinah ba su san yaushe Abdallah ya zo gurin ba. A tunanin su sun kaucewa idon sa tunda yana dakin sa yana barci.

"Aunty ta karaso cikin falon tana cewa, ""To tunda kalar rayuwar da ku ke yi kenan, ni a ba ni yaron in tafi da shi, da ma ba ku san kalar kashin sa ba balle na fitsarin sa, bayan na haihuwa. Kada ku bata masa tarbiyyah a banza""."

Aunty Badiya ta fadi a hassale tana janyo Abdallah jikin ta daga bayan labulen.

"Rahinah sai ta haye sama da sassarfa. Tana ji Aunty na ta yi wa Habibu fada, ta inda ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba."

"Ga shi kuma yana jin nauyin ta, yana kuma kare sirrin auren sa, ba don haka ba da ya gaya mata dalilin da ke tunzura shi a kan Rahinah ba Abdallah ba ne, the more mace ta yi denying husband dinta in bed, the more zuciyar sa ta ke a kusa, the more ya ke zama frustrated, duk wata kyautatawa da zata yi masa ba ya gane ta in ba wannan ba."

"""Ki yi hakuri""."

"Kawai ya ce kan sa a kasa, sannan ya ce cikin sanyin murya, ""Ni zan fita, ina fatan a nan za ki kwana?"""

Badiya sai ta ji kanin nata Habibu ya bata tausayi. Ta ce.

"""In kwana gidan da babu fahimtar juna da kwanciyar hankali cikin sa a kan me? Ka san dai ina da masauki na, me zai kai ni kwana gidan ku alhalin har gobe ba ku gama sanin ciwon kan ku ba? Ba ku iya rike amanar Da guda daya da Allah Ya ba ku ba sabida wautar ku?"""

"Kan sa a kasa ya ce, ""Hakurin nan dai nake kara ba ki Maman Musaddiq, ba za ki gane ba ne. Kuma maganar aure da na yi miki I'm very serious yanzu nake son sa ba gudu ba ja da baya""."

"Aunty ta ce, ""Tau! ai ka san inda zawarawan suke sai ka je ka bincika da kan ka. In ji dai Rahinar ma ba ni na gano maka ita ba?"""

"Ta haye sama ta barshi a nan tana fadin, ""In ka so ka bai wa Musaddiq daki ya huta yana waje yana fidda kaya a boot""."

"Ta kama hannun Abdallah suka bi bayan Rahinah zuwa dakin ta. Sai ta same ta ta hada kai da gwiwa a gefen gadon ta, ita ba kuka ta ke ba, amma idanun ta sun kada sun yi jajir."

"Abdallah ya ce, ""Mummy, ki yi hakuri""."

"Sai ta yi dan murmushi ta gyara zaman ta, ta ce, ""Aunty sannu da zuwa, ya hanya?"""

"Ta mike don ta dauko mata ruwa a firjin gefen gadon ta, Aunty ta ce, ""Bar ruwan ki Rahinah. Yau tafiyar nan tawa takakkiya, taki ce. Na rantse ban barin gidan nan sai na ji tun farko mene ne matsalar ku ke da mijin ki. Me ya hada ku kuma me ya raba ku shekara goma?""."

"Ta dubi Junior, ta ce, ""Junior maza tafi wajen Musaddiq yana dakin baki, ga choculates din ka na zo maka da su. Har da kelloggs""."

"Ga mamakin Aunty Badiya, yaron bai nuna zumudi ko farin ciki ba, kamar yadda ya ke yi a duk lokacin da ta bashi chocolate ko kelloggs din, jikin sa a sanyaye ya ke idon sa sai kallon Rahinah yake yi wani iri, domin ba ya son ganin ta a irin yanayin nan da ta ke ciki tun dawowar Baban sa gidan."

"Hatta fara'ar da ta ke wuni ciki yanzu ta dauke, koyaushe cikin yanayin da ta ke kenan; ido jajir babu fara'a."

"""Maza je ka Abdallah, ka ce ina gaida Yaya Musaddiq""."

"Da wannan ya juya ya fita jikin sa duk a sanyaye, ko ledar tsarabar da Mummy ta kawo masa bai dauka ba."

"Aunty ta maida hankalin ta kan Rahinah, ta ce, ""Rahinah, ba komai ya sa na ce ina son sanin hakikanin matsalar ku ba sai don Habibu da ya kira ni jiya yana batun yana so ya kara aure, shekara goma da ba kwa tare bai yi auren ba sai yanzu da ku ke tare Rahinah? And he sounds serious ban ji alamun wasa yake yi ba, don na fi kowa sanin sa."

"Idan ki ka bari Habibu ya auri irin matar da yake nufi, kin kade har ganyen ki""."

"""Aunty ko kyankasassar 'yar bariki yake so ku aura masa don Allah ku aura masa..."". Sai kuka ya kubuce mata. Aunty ta ce, ""Rahinah may I know your problem as a mother not an inlaw? Na yi alkawarin ko Baban ki ba zai ji ba, ba zan saka third party a tsakanin mu ba."

"Ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, na tabbata rashin SO ba shi ne matsalar ku ba, akwai wani boyayyen dalilin amma ba shi ba."

"Ko ban kawo solution ba ko ban hana shi kara aure ba zan taimaka miki da shawarwari matsayi na na mace yar uwar ki wadda ta fi ki yawan shekaru da sanin halin maza, wadanda insha Allah in muka bi su za mu yi maganin matsalolin komin yawan su. Hausawa suka ce barin kashi a ciki baya maganin yunwa Rahinah""."

"Lokaci na farko da Rahinah Omar ta ji zuciyar ta ta amince ta fada wa wani abin da Habibu ya yi mata. Wanda ya sanya mata tsanar sa, ya kuma lullube soyayyar sa wadda ta zo ta same ta bayan rabuwar su. Ko babu komai ita wannan shakikiyar sa ce, 'yar uwar sa ce ta ciki daya,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login