Showing 81001 words to 84000 words out of 215481 words

Chapter 28 - Ƙaunar Da Ta Zama Azaba by 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

ba har gurin motarsa ya bude min na shiga sannan ya zagaya ya shigo ya kunna motar sai kuma ya  kalleni.

“Bari na tambaya Madam ko za a siyo mata wani abu”

“Tohm”

Yana fita na fara daukar kaina hoto a motar, be jima ba ya dawo ya ja motar muka kama hanya. Na yi zaton zamu tafi Kareem Restaurant ne sai na ga ya faka a wani restaurant da ban sani ba, ko'ina na gurin wuta ce mai calar blue da ja daga waje. Ciki kuma farin haske ne irin wanda ko allurarka ta fadi zaka iya gani. Sai da ya fara fita sannan ni ma na fito muka jera a tare muka shiga.

“Me kike son ki ci?”

“Ice Cream”

“Ice Cream ai ba abinci ba ne”

“Ni idan na ci shi ya ishe ni, sai kuma nama”

Muna tafiya ina fada ina rabon ido, katon guri ne aka yi kowa bangare abu dabam ne, idan zaba sai ka tafi gurin biya ka biya sannan ka fice. Gurin masu pizza ya fara zuwa ya daukar mana daya, ya nufi shawarma ya dauki biyu, sannan muka nufi gurin masu kaza dake cikin gilashin tana juyawa kawar wata karuwa.

“Ba mu daya”

Ya fada sannan ya kalleni ya ciro wayarsa aljihu da hannu daya ya matsa can gefe yana amsawa. Mutumem ya gama yanka kazar ya saka a leda sai ya miko min, na waiga na kalli saitin da yake tsaye yana wayar da murmushi a fuskarsa da alama da Madam yake waya domin ita ce kadai zata iya saka shi irin wannan murmushi kuma ta dauke masa hankali. Ban bi ta kansa ba na nufi gurin masu ice cream ina duba wanda ya fi girma a jikin hoton dake gaban box din, domin sai ka zaba sannan za a dauko maka.

“Wane ya fi dadi?”

“Kowane ne yana da dadi yan mata, amman dai ki dauki vanilla ice cream mata sun fi son shi”

Na ji an fada daga gefena, na juyo na kalleshi sai ya sakar min murmushi.

“Can i pay”

Na girgiza masa kai alamar no, sai ya bata fuska kamar mai magana da yarinya.

“Why? Baki son na samu lada?”

“Kai Malam Lafiya”

Hafiz ya fada tun kamin ya karaso ni da shi muka juya kallon Hafiz din da ya daso gurin da saurinsa.

“Waye wannan? Yayanki ne?”

“Mijina ne”

Ya matsa nesa da ni ya kalli daga sama zuwa kasa.

“Duk kyaun nan naki, wannan ne mijinki”

Ban ce masa komai ba, shi ma kuma be sake cewa komai ba ya nufi gurin biya ya bar shi a gurin tsaye.

“Waye wannan?”

“Ban san shi ba, yau na fara ganinshi ni ma”

“Amman ai magana na ga kina yi da shi”

“Tambaya yayi zai iya biya na ce aa ni matar aure ce”

Hafiz ya kalli gurin da mutumen nan yake tsaye, shi ma kallonmu yake kamin ya karbi katinsa a fara saka masa kayan a babbar leda.

“Mu tafi...”

Na wuce gaba yana bayana muna isa gurin Mutumen ya karbi kayansa ya fara tafiya.

“Oga Abdull ga canjinka”

Daya daga cikin masu karbar kudi a gurin ya fada yana mika masa canjin 750.

“Keep the change”

Ya fada ba tare da ya juyo ba. Hafiz ya ciri Atm dinsa ya biya kudin aka fara saka mana a babbar leda, a nan na samu damar satar kallon mijin na wa, ni ban taba lura da yanayinsa kyau ko muni ba dress ko yanayinsa, gaba daya babu ko daya a gabana sai yau da mutumen nan yake mamakin ni din matarsa ce. Kuma gaskiya ya fada Hafiz ba shi da wani kyau na azo a gani, ba laifi dress dinsa na zamani riga da wando, kuma yana ta kamshi ba laifi ba zaka kira shi baki ba haka kuma ba fari bane.

“Muje”

Ya rika duka ledodin gaba ya saka ni sai da na fara fita sannan ya fito. Kamin mu isa motar na hango yarinyar nan da Zafeer yake yi ma gyaran mota tana doso gurin, ita ma kallona take kamar yadda nake kallonsa da alama ita ma dai ta gane ni kamar yadda na wayance ta.

“Noor ko?”

Ta fada yana nuna ni a lokacin da ta karaso kusa da ni. Na daga mata kai ina murmushi Hafiz ya kalleta.

“Wacece wannan?”

“Waye wannan Yayanki ne?”

Ita da shi kusan a lokaci daya suka yi tambayar kowanensu yana kokarin sanin abun da ke tsakanina da daya.

“Mijina ne”

Na fara amsa mata jiki a sanyeye ina jin babu dadi domin ta san alakata da Zafeer. A take na ga yanayinta ya sauya kamar mai mamaki kamar kuma bata jidadin amsar tawa ba.

“Zafeer...”

Sai kuma ta yi shiru...

“Allah be yi da shi ba, Noor shiga mota mu tafi”

Hafiz ya fada rai a bace yana ba ni umarni. Na nufi motar ina jin wani abu marar dadi ya tokare min zuciya. Kamin na isa gurin motar hawaye ya cika idona har ya fara zubo domin ta tuna da abun da nake kokarin mantawa da shi a kankanen lokaci, mutumen da ba ya kunyar nuna soyayyata a gaban kowa. Tsaye ta yi tana kallonmu har sai da muka bace mata. Kaina a kasa yake har muka isa gida na ki yarda na dago dan kar Hafiz ya ga hawayen dake min zuba, sai dai hakan be hana shi fahimtar kuncin dake zuciyata ba, domin yanayina ya sauka ba kamar yadda muka fita ba.

“Mutumen nan kamata yayi ki fada masa kina da miji tun farkon da yayi miki magana, kin san kina burge maza for no reason me ya ba zaki kama kanki ba? Ke komai sai an fada miki sannan zaki yi? Aisha tana da gaskiya be kamata na baki wayar nan a yanzu”

Ban ce masa komai fadansa sai kara min zafin hawaye yake.

“Ba ni wayar...”

Ya miko min hannunsa yana kashe motar. Sai da na hade yawu sannan na mika masa wayar.

“Zan baki amman sai nan gaba idan kin yi hankali, yanzu ko na barki da ita hankali ba zai kwanta ba, ai na ga darasi gurin abokina mata ba ku da amana if not taya kina tare da ni zaki zubar da hawaye saboda da wani da ba zai iya zaman aure da ke ba, ba zai iya miki rabin abun da na yi miki ba”

Na kalleshi.

“Amman zai ba ni farinciki, irin wanda ba zan taba samu a gidanka ba, da baka bar ni tsaye ba ka je kana waya da munafukar matarka ta ya wani zai min magana? Ko kuma an rubuta a goshina na ne cewar ni matar aure ce? Wayarka kuma ka aje bana so ko da nan da tsufa ne, idan ba ka yarda da ni a yanzu ba ba zaka taba yarda da ni ba har abada”

Na bude motar na fita a fusace na bar masa kofar a bude ba tare da na rufe ba. Falon na shiga na zauna kan kujera gaba daya na rasa me ke min dadi. A kan kujerar da nake zaune ya watsar siyayyar da muka yi.

“Noor For the very last time karki sake kiran Aisha munafuka, ko ba komai ta girme ki, ta cancanci girmama daga gurinki, balle kuma tana matata, ba zan yarda ki shigo gidana ki rainata ba, babu kalar soyayyar da bata nuna miki ba, idan baki gode ba karki zage ta ba zan yarda a raina min uwargidana ba uwar yayana, ki tsaya matsayinki...”

Uffan ban ce masa ba na tashi na shiga daki na kwanta kan gadona ina kallon OPO dake dakin hawaye na zubo, haduwata da matar a nan ya tuna min da waye Zafeer a gurina, abu da duk wanda ya san alakarmu zai yi mamakin ace ba shi na aura ba.

“Miye wannan?”

Ya tambaya a tsawace dagowar da zan yi ya watso min wani abu mai kamar magani a fuska da wata roba. Na tashi zaune na dauki maganin mai kananan yaya na duba, sai wata roba da ban gama sanin ta miye ba guda biyu, roba na fi duba domin ta yi min kama da balloon sai dai ta banbanta da ballon sosai, ba kuma zan iya fadar ko ta miye ba domin ban san amfaninta ba. Na sake duba maganin shi ma wani kalar magani ne mai 2 colors da ban taba ganin irinsa ba.

“Miye wannan.?”

Ya daka min tsawa har sai da hankalina ya tashi, gaba daya fuskarsa da hallitarsa sun canja jikinsa har rawa yake kamar zai doke ni.

“Ban san ko miye ba...”

“Karya kike munafuka, a jakarki na ganshi yanzu waya baki ina kika siya?”

Na girgiza kai amman na kasa magana domin tsoron fushinsa da nakr gani a yanzu ya cika zuciyata. Furta cewar a jakata ya gani ya saka na sauka da sauri da zimmar na tafi na duba jakar tawa da na bari a falon sai na ji ya fisgoni iyakar karfinsa na wulgar da ni kan gadon.

“Ina zaki je? Ba zaki fada min ba? Uban waye ya baki wannan maganin? Ina kika siya? Mi ya kawo condoms a jakarki?”

“Wallahi ban sani ba... Ba.. Ba.. Ban saka.. Magani ba... Ni ban...”

Na kasa magana tsoro da kuka suka ci karfina, ban san me yake fada ba maganin ne condoms ko kuma robar, ko ma duka? To miye illarsu? Miye kawo su a jakata? Taya? Ya hauro saman gadon da talkaminsa ya riko ni da duka karfinsa.

“Ina kika siye Noor? Saboda me kika siya?”

“Ban saya ba, ban san amfaninsa ba, ni ban saka komai a jaka na ba, ban san maganin miye ba, ban san robar ta miye ba, ba nawa ba ne Wallahi”

“To ina aka samu ya aka yi na ganshi a jakarki?”

Na rike hannunsa daya jikina na rawa.

“Wallahi Wallahi ba nawa ba ne, ban san miye ba”

“Da na aje ki gidanku ina kika je?”

“Ban tafi ko'ina ba Wallahi”

“Amman kin yi magana da Zafeer?”

“Ban yi ba, Wallahi ban ga Zafeer ba”

“To wannan abun su suka kawo kansu a jakarki kenan?”

“Wallahi ban san na miye ba, Hafiz sai idan saka min shi aka yi a jaka..”

Fwauuu ya buge min baki.

“Ban ce ki daina fadar sunana ba? Ke gaba daya kanki babu tunani babu tarbiya babu hankali? Gaba daya baki da lissafi? Waya saka miki maganin to? Waye? Ko ki fada min ko na ci ubanki da duka Wallahi”

“daga gida ban je ko'ina ba, kanwata kuma ba zata saka min wannan abun ba, ni da ita duk ba mu taba ganin wannan abun ba”

“To waya saka miki? Ina kika samu? Ni zan dauko na saka miki a jaka?”

“Sai idan Aisha ce ta saka min saboda ta yi min sheri, Wallahi ban san na miye ba”

Ina fadar hakan sai ya sake ni, ya sauka daga kan gadon ya fita daga dakin. A nan an samu damar daukar maganin na duba na sake duba balloon din har biyu sannan na nufo falo na duba jakata da ke kasa sarka da yan kunne da na cire na saka a ciki tun a gida suna watse a kasa. Naira biyar ma ba ni da ita a jakar to a ina zan siye magani? Kuma maganin miye zan siya, wane chemist bayan cikin gidan mu ban san na taka ko'ina ba. Ban gama shiga tashin hankali ba har sai da Aisha ta shigo falon tare da Hafiz.

“Noor ni na saka miki magani da condom a jaka? Ta ina? Da zaki fita na karbi jakarki ne? Kuma ai tare kuka dawo da Barrister idan na saka miki wani abu a ciki zai gani, Kuma na rantse da Allah bayan fitarku ban shigo dakin nan ba, me zai saka ma na yi haka?”

Ta juya gurinsa da sauri ta zube kasa.

“Na shiga uku kar ta kashe min aure, daman burin yan matan yanzu kenan, Wallahi ba ni na saka, idan ni na saka mata shi a jakarta kada Allah ya ba ni abun da nake so Wallahi ba ni ba ce Barrister Innalillahi Na shiga uku...”

Ya rika ta ya mikar da ita tsaye, gaba daya sai suka daure ni na rasa ya zan zarga ita ko kanwata? Ko kuma shi da ya saka min jakar a lefe? Yanzu ta ya zan wanke kaina.

“Tafi bangarenki”


Ta kalleni tana kuka.

“Allah ya saka min gareki, na barki da Allah saboda kar a zarge ki shi ne zaki maida laifin a kaina? Ba ni ba ke Noor daga yau kowa ya tsaya bangarensa....”

Na kasa cewa komai sai kallonta nake hawaye suna sauko min kamar ba gobe. Ta rufe fuska tana kuka sosai ta fice daga falon, kamar fitarta yake jira ya juyo kaina.

“Ta rantse ba ita ta saka miki ba, daman makasudin kiran kenan, fada min ina kika samu wannan? Yanxu kika samu ko kin dade?”

Na yi shiru kamar wadda kalamai suka karewa.

“Ba magana nake miki ba?”

Ya sake daka min tsawa. Still ban iya ce masa komai ba, domin babu wasu kalmomi da zan hada na wanke kaina.

“Shiyasa auren mace mai mutunci mai tarbiya da natsuwa yana da dadi, ka aureki saboda na rufa miki asiri amman kullum matsala kike ba ni, ni ban taba samun matsala da matata irin wannan!”

Yana matsowa ina matsawa baya jira kawai nake ya kai min duka a jiki domin alamar hakannta bayyana a jikinsa da fuskarsa. Kwafa yayi ya nufi ledodin da muka shigo da su ya kwashe gaba daya ya fice daga falon. Ranar kwana ne amman be kwana a dakina ba sai ya kwana a dakin Aisha, ni kuma na kwana a falon cikin kunci da rudani mai tsananin daure kai.
A haka muka kwashe sati biyu be shigo bangare na ba, da girkina da ba nawa ba duk baya zuwa gurina, sai dai na hango shi ta window idan zai fita ko ya dawo. A lokacin damuwa ya fara shiga raina, na tabbatar Zafeer ba zai iya min haka ba, gashi Baba ya aurar da ni ga wanda bana so kuma be iya zama da ni ba. Kukan safe dabam na rana dabam da dare ma idan zan kwanta dabam ga abinci amman bana iya sarrafawa na ci saboda damuwa sai ruwan sha yi babu bread domin ya daina kawo min komai, wani lokacin kuma na dafa taliyar yara kadan na ci.

Idan na zauna da tunani sai na rasa wa zan kaiwa kukana, Baba zan je na fadawa ko kuma Mama ko kuma dai Kareem zan fadawa shi da yake abokinsa? Ko kuma gidan iyayensa zan bincika na fada musu ko kuma na zauna a haka? Na zuba masa ido? Gashi babu wani dan'uwa da ya sake zuwa gurina na balle na bude masa ciki na fada masa damuwata. Amman har zuwa yaushe zai yi ta fushin da Ni? Zuwa yaushe zai sauko? Agogon dakin na duba karfe biyu da mintuna na rana, tashi na yi na dauki green hijab dina na saka na dauki jakar nan da na yi fitar farko da ita na sake dauka na bude marfin madubina na dauko balloon din nan da maganin na saka a jakata na saka talkamina na fito falon na leka windows din waje ban motarsa ba hakan na tabbatar min da baya cikin gidan kenan. Bude kofar falon na yi na fita sannan na janyo kofar ba gabana na faduwa na sauka entrance din na nufi gate. Kamin na fice har wani gumi ke karyo min domin idan ya tare ni a kofar gate din ko hanya ban san me zan fada masa ba. Mai gadin ne ya bude min na fita dama ko hagu sai na rasa ina zan dosa can wata zuciyar ta raya min dama domin ta nan muka bi lokacin da zamu tafi gida tare da shi.








#KhadeejaCandy
PAID PAGE 7️⃣


©KhadeejaCandy
©®Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....


You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153


_______•••_______


Na yi tafiya mai nisa kamin na samu Napep na tara ya fada masa inda zai kai ni na shiga. Sai da ya fara tafiya sannan na fara sake saken idan na tafi gida me zan fada? Na nuna musu abun da ya gani a jakar tawa ko kuma dai na fada ma Baba cewar ya daina shigowa bangarena? Gidanmu zan tafi ko kuma na su gidan? Idan ma na ce zan tafi gidansu ina zan bi domin ban taba tafiya ba be kai ni kamin auren ba, bayan aure kuma ba mu samu kwanciyar hankalin da zai kai ni gidan ba. Wata zuciyar kuma na raya min na tafi gurin Mama kai tsaye sai dai kuma ita ma zan iya shafa mata laifi. Ya mace bata da gidan da ya fi na mahaifinta saboda haka na fada masa unguwarmu kai tsaye.
Har kofar gidanmu ya faka Napep din na fita na shiga gidan da sallama. Yaya na fara cin karo da shi yana wanki sai kuma Hana dake gaban murhu tana girki har yanzu da sauran kuna a jikinta domin na same ta babu riga a jiki.

“Yaya dan Allah dari biyar zaka ba ni zan sallami mai napep”

“Lafiya?”

Ya tambaya yana kallon yanayi na, domin na shigo gidan ne cike da damuwar da ta kasa boyuwa a fuskata. Na yo shiru be sake ce min komai ba ya tashi ya shiga dakinsa ya dauko dari biyu da naira dari ya miko min.

“Su kenan suka rage min, nawa ya kawo ki?”

“Ban yi ciniki da shi ba, bari na tambaya”

Na juya na fita, ta inda na yi sa'a ina tambayar mai Napep din nawa ya ce min dari uku sai na mika masa na dawo cikin gidan na nufi kofar dakin Mama na zauna.

“Noor kin rame? Ko baki da lafiya?”

Hana ta fada satar kallon Yaya na yi dake kallona sannan na ce.

“Har yanzu konan be warke ba?”

“Eh da saura, kin san wuta bata warkewa da wuri, kowa ma cewa yake na yi sa'a jikina yana da kyau ne”

“Ina Baba?”

“Dazun ya kawo cefa ne ya fita, anjima na san zai dawo cin abinci ai tun da yace ya gama da wuri”

Na sake kallon Yaya sannan na kalli rufin kwanon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login