Showing 171001 words to 174000 words out of 215481 words
ne? Ko dai yayi losing mind dinsa ne?
Zan aure ka Kareem!!
Zan aure ka Kareem!!
Zan aure ka Kareem!!
Haka yake ta jin sautin muryata mai dadin sauraro da taushi a kunnesa. Kallonta yake kamar be fahimci yarenta. Mikewa ta yi tsaye sakamakom shigowar da kanwarsa Khadija ta yi ba tare da sake furta masa komai ba ta fice daga dakin. Ya kasa motsi ya kasa numfashi ya kasa yarda idonsa na ne kawai suke kanta har ta fice, Khadija ta juyo ta kalli kofar da Noor ta rufe ta kalli Yayanta dake kallon kofar ta sake duban kofar ta dube shi har lokacin kofar yake kallo.
“Big Bro...”
Ta tara masa hannunta tana motsa domin gani idan ya san abun da yake.
Sai ya lumshe ido ya koma ya kwanta a hankali numfashi ya dawo da karfi kamar zai fasa huhunsa zuciyarsa ta buga da karfi ya jimke hannunsa yana sauraren sauti daya na Noor Zan aure ka Kareem!! A yau kalaminta ya fi na kullum dadi, muryarta da fi ta kullum zaki.
NOOR POV.
Na aminta har a zuciyata na ji cewar zan iya auren Kareem a yanzu, i was afraid to lose him, a broken heart ce ta rage min yanzu, and i need someone who can fix it ba wanda zai saka broken heart dina into piece ba. And if Safeena zata min duk wannan saboda Kareem to akwai bukatar na aure shi saboda ta fahimci ni na ci gasan.
If Kareem zai bata lokaci kudinsa wajen ba ni kariya ko farinciki, to ya kamata na ba shi abun da yake so a gareni in har zan iya kuma ba tsabawa addini ba. I saw my future in his eyes.
Mun fara da kamar abota ne when we fell in love not knowing what it was. A yanzu dai yana fahimtata ina ji kamar zai iya rike ni. Ina tafe ina tunani kala kala har na iso gida, na ga bakuwar mota a kofar gidanmu ban kawo tunanin kowa ba, na shiga dakin Mama sai na samu mijinta a ciki tare da Yayanta suna magana. Waje na fito na zauna ina ji zazzabi zai rufe ni jikina yayi zafi ga ciwon kai da ya rufe idona, zuciyata na daukar abubuwan da suka fi karfinta.
Wani karamin cousin dina ya ce ana kirana a waje.
“Waye?”
“Ban sani ba, da mota ya zo yana waje dai”
“To je ka ce ina zuwa”
Na fada masa ma my mind was telling me Aaryam ne ya zo daukata kamar yadda Kareem ya fada, wata kila kuma ya turo shi ne ya fada ma Mama da kansa, ko kuma ya zo daukar mu ne gashi kuma ban fadawa Mama ba domin na same ta da baki, haka dai nake ta sake sake, gudun barinsa a waje ya saka na fita domin sanar masa cewar ban riga na fadawa Mama ba ya dan jira su kare magana tukuna.
Zatona ya sha banban da abun da na gani, idanuwa suka yi arba da abun da zuciyata ta dade tana kauna, rashin tsammanin dawowarsa ya haddasa min faduwar gaba. Na taka na isa gurin da yake tsaye na rumgume hannayena kaina a kasa.
“Baby Noor”
Sai da ya rufe ido na bude a lokacin da ya furta min sunan da yake kira na da shi a lokacin da muke abokan rayuwa. Ya matso kusa da ni, matsawowarsa ya masar d bugun zuciyata towards him.
“Ya kike ya hakuri ya gida ya Mama ya kowa?”
“Kowa lafiya kalau”
Na kasa daga ido na dube shi, kunya da nauyinsa sun baibaiye ni. Ya saka hannunaa daya a aljihu yana kallon unguwarmu.
“Kawai dai na zo na duba ki ne, ina fatar babu wata matsala”
Na girgiza kai na amsa murya can kasa.
“Babu”
Mun dauki tsawon lokaci a haka be sake magana ba ni ma ban sake cewa komai ba. Can kuma sai na ji ya kira sunana.
“Noor”
“Na'am”
Na amsa jikina na karkarwa.
“Daga ki kalleni mana, ko dai har yanzu tsanata kike?”
Na girgiza kai alamar Aa sannan na dago a hankali na kalleshi, shi din dai Zafeer mutumen da Baba ya cilasta min juya masa baya a lokacin da yake tsananin kaunata, ashe har yanzu ina da kimar da zai biyo ni ya tambayi lafiyata, hawaye suka sauko min, shi ma kallona yake idanuwansa da rauni kamar yadda fuskarsa ma ta nuna.
“Na zo ne na dubaki, no matter what happen kina cikin raina ina tausayinki”
“Na gode, na ba ni abun da ban cancanta ba”
“Mu bar abaya ta wuce baby Noor abun da ya wuce ya wuce, mu fuskanci gaba”
Na daga mishi kai sai ya sauke ajiyar zuciya.
“Zan tafi akwai abun da kike bukata?”
“Aa bana bukatar komai”
“Take care of your safe, sai na sake zagayowa”
Na yi baya baya sai ya bude motarsa ya shiga ni kuma na juya na shiga cikin gidan. A zauren gidan na jingina na lumshe ido ina maida numfashi a hankali, na sani Zafeer ya zo duba ni saboda karfin zuciya irin nasa, ba dan yana nufin dawowa ba, domin ban cancanci haka ba. Kuma na yarda wata soyayyar bata nufin aure, wani auren kuma baya nufin zama. Na dade a gurin dafe da kirjina har sai da na ji na samu salama sannan na share hawayena domin yanzu kuka ya zama abinci na, na shiga cikin gidan, ban shiga bangaren da Mama take ba sai na zauna a dayan bangare da kanenta da yake da Amarya na shiga falonta na kwanta jikin kujera na rufe ido kamar mai bachi.
Ban san me suka tattauna ba, Mama ce dai ta shigo ta kawo min wayata da Abdull ya karba tare da sim din da komai a ciki amman babu recording din an goge shi har ma da wanda na yi ma Safeena. Kiran da na ga ya fi yawa a wayata har an hada da sako na mayar domin jin dalilin kiran da kuma sakon da aka turo min _ki kira ni_
Ina kira sai ya daga muka gaisa ya gabatar min da kansa.
“Sunana Alhaji Sule unguwa Uku”
Har lokacin ban fahimci waye ba har sai da ya fada min shi ne wanda ya karbi number kwanan baya ina hanya.
“Na kira sai wani ya daga, yace kar na sake kira wai ke matar aure ce”
Na dan yi murmushi na san Kareem zai aikata abun da ya fi wannan ma.
“Amman zuciyata bata aminta ba, domin matar aure ba zata yi irin shigar da kika yi ba, wata kila dai shi ma yana cikin masu neman auren ne kamar yadda ni ma zan shigo yanzu, shiyasa ban yi kasa a guiwa ba na sake kira tana ringing ba a dagawa daga baya wani lokacin kuma sai na jita a kashe”
“Eh wayar tana hannun Yayana ne”
“Yayanki ko saurayinki? Ko dai karbe abarsa yayi saboda shi ya siya?”
“Aa yanzu ta dawo hannuna ai”
“Hakan yayi kyau, ya kamata na shigo mu gaisa ko ba haka ba? Mu fahimci juna kuma tattauna abun da ya kamata, ba mu san abun da Allah zai yi ba, ni dai na ga abun da ke min”
Na cire wayar a kunne na kalli screen na sake mayarwa, ashe dai uban Aisha nan haka yake da son zuciya shiyasa ita ma take da son zuciyar ta hana ni zaman lafiya a gidan Hafiz. Idan ba son zuciyata ba ta ina zai kalli mace kamar ni yace wai na masa, yarsa Aisha ma yayata ce ta uku balle kuma ni.
“Ba yanzu ba gaskiya sai nan gaba”
“Saboda me baki son na san gidanku ne? Ni fa da gaske nake babu alamar wasa”
“Yanzu ba gida nake ba, yanzu ina family house din mahaifiyata ne saboda Babana ya rasu tare da kanwata”
Ya tausaya min sosai yayi min gaisuwa sannan ya fada min zai zo yayi gaisuwa gurin Mama da ni. Na amsa masa da okay ne kawai dan babu yadda na iya, amman na kudiri aniyar idan ya zo zan fada masa gaskiya cewar ni ina da wanda zan aura wato Kareem... Minti goma da kare waya da shi airtime na 10k ya shigo wayata...
Alhamdullahi Allah ya maimaita mana. 🤲
*** *** *** *** *** *** *** ***
Sauka na yi daga kan kujerar na zauna kasa ina kallon Kareem dake shigowa bayan na Alhaji Sule unguwa uku ya sauka. Tun kamin na amsa wayar na samu kaina da murmushi.
“Hello”
“My heart beat, my life, my happiness...”
Ya fada murya can kasa kamar mai gudun wani ya ji.
-Uhm hmm-
“Kawai na kira ne na fada miki ina kaunarki”
Na yi murmushi ina shafa fuskata.
“I love you so much, my Beb my one and only”
“Hey... Ya isa haka”
“Be isa ba, i love you i love you i love you i miss you i need you, Noor jin nake kamar ba ke ba ce a yau, gani nake kamar ranar yau mafarki ce, after this fever i will survive komai zai zama kalau”
“Haha”
Na yi dariya.
“Amsa min mana ki ce min ke ce Noor maybe zan yarda”
“Ni ce Noor noor ta Kareem”
Na fada ne da zolaya sai na ji ya sauke ajiyar zuciya yayi shiru na wasu dakiku sannan ya ce.
“Noor da kin san yadda nake son ki a zuciyata wata kila da kin tsorata, ina masifar sonki Noor, irin son da ban taba mafarki ba”
Na yi shiru kamar wadda ta rasa abun fada, ajiyar zuciya na ji ya sake saukewa.
“Ta ya wayarki ta dawo hannunki? Kawai na rike number ki ne ina kallo sai kuma na gwada kira ashe zai shiga”
“Mama ta shigo ta kawo min, na dawo na tarar da mahaifin dare da Kawuna da Mama ban san me suke magana ba, kawai Mama ta shigo ta ba ni wayar”
“Okay, zan aiko a karbe ta a canja miki wata, ina son zuciyata ta natsu kina cikin aminci Noor”
“Okay”
“I love you”
Ya furta sannan ya kashe wayar, na mike tsaye na fice daga falon na shiga bangaren da Mama take, kamin na shiga dakinta Kareem ya sake kiran wayar.
“Hello”
“Noor, na ce tun da kin amince da ni me zai hana a daura mana aure kamin na tafi?”
Na yi baya baya na fasa shiga dakin Mama juyo ina rufe baki.
“Kareem yayi wuri ai, kwana biyu ya rage ka tafi fa, ni kuma ban fadawa kowa ba, babu wanda ya san da alakarmu”
“Zan aiko neman aurenki ne, albashin idan suka zo sai su sanar cewar sun zo ba tare da izininki ba”
“Aa ka bari sai ka dawo Kareem”
“Noor what if ban dawo ba fa? Ina tsoron kar ki canja shawara kamin na dawo, ina tsoron rasaki Noor”
“If we mean to be zaka samu sauki zaka dawo Kareem, kaddara ce ta hada mu ai ka fada”
“Noor ina tsoron rasa ki”
“Ta ya? Babu kowa a gabana yanzu sai kai Kareem”
“Na gode da kika sanar min wannan, thank you anjima Aaryam zai zo ya dauke ki, ki sanar da Mama”
“Okay”
Sai da ya sake fada min yana kaunata sannan ya kashe wayar, ni kuma na juya na sake komawa bangaren na shiga dakin Mama, babu kalar tambayar da ban yi mata ba akan zuwan mahaifin Abdull da kuma yadda aka yi ya ba ni wayata amman Mama bata amsa min tambaya ko daya ba.
Daga karshe sai na sanar mata Kareem yace zai aiko kanensa ya dauke mu domin yin sharadi a gurin DSS.
Jimm Mama ta yi da alama hakan kamar be mata dadi ba, sai dai bata ce min komai ba, cewar na tafi ko kar na tafi, kuma bata amsa da cewar zata tafi tare da ni ko akasin haka ba.
“Mama baki ce komai ba”
“Noor ki yi taka tsantsan da yaron nan, ba zan yanke alakarku kai tsaye ba, amman dai ki yi taka tsantsan da shi, izuwa yanzu ya kamata ace kin dauki darasin rayuwa, auren biyu kenan kika yi da kurciyarki da kananen shekarunki, duk yadda zai zubar da mutuncinki ko nawa to ki yi kokarin tsare shi, kin ga a yanzu hannuna kike mahaifinki baya raya dawainiyarki da tarbiyarki a kaina take, bana fatan ki aikata wani abun ko wani abun ya same ki da za a furt cewar ke yar mace ce”
“In Shaa Allahu Mama zan kiyaye”
Jikina yayi sanyi zuciyata na raya min akwai wani abu da Mama ta sani amman bata son fada min.
“Mama ko dai na fada masa ba zamu samu damar tafiya ba?”
“Aa abun da yake bukatar a aikata abu ne mai kyau, ko da be kawo shawarar ba, ni zan kawo aikawatar da haka saboda tsaron lafiyarki domin gujewa gaba, za mu tafi”
Na yi shiru na wani lokaci sannan na daga kai na kalleta.
“Mama ko wani abu kika ji akan Kareem ne? Domin mutumen kirki ne”
“Ba a gane mutumen kirki a fuska ko a furuci, ba a fuska ake zanawa ba Noor, Abdull ma ba mu yi zaton zai aikata ba sai da muka gani”
“Haka ne”
Daga wannan ban sake furta komai ba. Da yamma Kareem ya aiko da mota kamar yadda ya fada aka dauke mu ni da Mama da Babban yayanta da kanen mahaifi da mama ta aika masa ya zo jar gida aka tafi tare da shi. Office din DSS aka kai mu kai tsaye, ko da muka isa mun tararda Safeena da mijinta a can a ranar na fara arba da mahaifin Kareem suna kama da Aaryam sosai fiye da Kareem wata kila Kareem din ya fi kama da Mamansu ne.
Ban ga alamar maraba a fuskar mahaifinsa ba, zuwansa sai yayi min kama da wanda aka tirsasa ya aikata abun da ba shi da ra'ayin akai, hakan kuma ya saka ni jin wani iri.
“To ni me ya shigar da ni cikin lamarinta? Ina ce Abdull ta aura ni miye nawa a ciki da za a zo nan da ni?”
Aaryam ya dan tabe baki kadan irin na mai mamaki
“Ni ma na yi tunanin haka, but Kareem ya ce da ita za a zo”
Abdull ya kalleshi.
“Wait Waye ya taramu a nan to? Ni fa d aka aika min da takardar gayyata cewa aka yi mahaifiyar Noor take nema”
“An fada maka haka ne kawai, Yayana ne ya taraku a nan saboda a dauki matakin da ya dace”
Abdull ya sake daga ido ya kalli Aaryam sannan ya sauke kansa ba tare da ya sake cewa komai. Har aka yi komai aka gama Mama ce take magana da yawuna, wani abun kuma Kawu ya saka baki ko Baba Kamilu. Motar da ta kawo mu ita ta dawo da mu gida. Bayan na shiga gidan Kareem ya kira wayata ya ce na fito waje Aaryam yana tsaye yana jirana. Ban bata lokaci ba na fito sai na same shi a gurin da na bar shi, sabuwar waya ya bude a gaban idona ya karbi ta hannu ya cire sim din ya saka min a sabuwar wayar sannan ya mika min ya tafi da tsohuwar.
Rayuwa ta cigaba da tafi min a yadda ubangiji ya tsara min ba a yadda ni na tsara ba, Alhaji Sule unguwa uku ya zo gidanmu yayi min gaisuwa kuma yayi ma Mama da yan gidan ya kawo mana alheri na abinci da kudi, wata matar Kawuna har tsokana ta take wai Noor mai kwashe kwashe, iyakaci murmushi bana cewa komai amman ni na san ba aurensa zan yi ba. Wannan ya saka ban yi kasa a guiwa ba zuwansa na biyu na fada masa cewar akwai wanda yake neman kuma nake saka ran aurensa nan kusa idan Allah ya amince.
“Ai ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare, ita mace allura ce cikin ruwa mai rabo ka dauka”
“Haka ne”
Na furta ina gyara mayafina.
“Dan haka karki yi saurin yanke hanzarina, ni ma zan gwada sa'ata kuma ko da ban aureki ba ni na ci riba domin na tsaya da ke kuma kin min tarba ta mutumci na jidadin haka”
Na yi murmushi na sauke kaina kasa.
“Kuma kar haka ya saka ki ji nauyin tambayar wani abu a gurina ko bukatar wani abu, ni ina taimako ma ko a banza balle kuma akwai dalili, daga naira miliyan daya har miliyan dari zan iya kashe miki Khadija kashewa mace kudi ba asara ba ne, musamman macen da kake fatan ta zama Matarka kuma uwar yayanka”
Mamaki ya kamani ashe dai su ma tsofi sun iya kalaman soyayya, bawan Allah nan sai kokarin daure ni yake da kalamansa. Sama sama muka yi hira sannan ya dauko leda motar ya aje min a gabana.
“Ban gama sanin komai akan sarauniyar ba, amman dai ina fatan abubuwan da na zabo za su burge ki”
“Na gode, amman ba zai ka yi min dawainiya ba, bana bukatar komai a yanzu”
“Sakamakon rashin bukatar da kike da shi ne ai, bukatar take nemanki ke dai ki bar ni na gina miki sabuwar rayuwa kawai”
Na yi murmushi na sunkuya na dauki ledar.
“Na gode”
“Toh sai mun yi waya, bye bye”
Ya dago min hannu ni ma na daga masa. Ina shiga dakin na samu Mama bata ciki sai dariyar da na riko a waje ta subuce min, shi fa dattijon ya dage a bakin gaskiyarsa yaki yake yi ma soyayyarsa a gurin. Kayan tande tande ne da lashe lashe a ledar sai turaruka da bandir din 200 sabi. Na bude ice cream din na fara sha ina lumshe ido sanyi yana kai min har cikin zuciya.
Kiran Kareem ne ya shigo wayata sai da na daga na gane ashe video call ne. Na fara isar masa da murmushi sai dai shi tasa fuskar kamar yana cikin damuwa.
“Ya kike?”
“Lafiya kalau, sad face?”
“Me kike sha?”
Na daga na nuna masa robar.
“Waya kawo?”
Na yi shiru ina kallonsa i kNow if i lie zai gane domin ya san ba zan fita na siyawa kaina ice cream ba but me zan ce? Ban gama tunanin amsar da zan ba shi ba na ji ya ce.
“Wannan baban Aisha Alhaji Sule unguwa uku nan ba aurenki zai yi ba Noor, matansa hudu kuma yayansa duka manya ne, kuma yadda kike fresh and young me zaki yi d tsoho?”
Na yi dariya.
“Ni ma na aurensa zan yi ba kuma na fada masa ina da wand nake so