Showing 180001 words to 183000 words out of 215481 words
mu ba. Wata kila har yanzu mahaifiyarsa da kannesa ba su gama da hukuncin Allah ba, domin komai kaddarrawar Allah ne, ya rubuta ba zan auri Zafeer a wacan karon ba sai a yanzu.
Na sha huduba na sha nasiha na sha gargadi tun daga kan Mama har zuwa kanenta da yayye fa kuma yan'uwan mahaifina, ba laifi kawata Zainab na ta yi ta min nasiha akan aure da zaman aure ta nan na fahimci har yanzu wasu ganin suke kamar ni nake kashe aurena dan ra'ayin kaina, ko da yake dole ne na musu uzuri domin ba kowa ya san dalilin mutuwar auren ba, ba kowa ya san abubuwan dake faruwa ba.
Tsofi biyu ne suka zo daukar amary sai kanwarsa daya da wasu yan mata da ban waye su waye ba. Mun yi tafiya sosai kamar zamu bar gari kamin mu isa gidan da ya kama haya, kaina a lullube aka shiga da ni gidan amman hakan be hana ni ganin kyau da gidan yake da shi ba. Sai karnuka biyu dake ta haushi ganin Shigowarmu. Anty Larai na rike da ni har cikin dakin Farincikina. A gafe gadon ta zauna da ni ta sake yi min nasiha yan'uwanta ma suka min sannan suka tafi aka bar ni da cousins dina sai Zainab da wasu kawaye biyu, domin ban gayyaci kowa ba sai wanda ya ga dama ya zo dan kansa.
Bayan iyaye sun tafi na daga mayafina na kalli dakina idanuwa dauke da abun da ya zame musu ibada wato hawaye. Akwai farinciki akwai jindadi akwai kwanciyar hankali da sakewa a auren wanda kake kauna, masoya ne kadai za su iya labarta haka. Ban taba samun kaina a yanayi da na samu kaina a yanzu ba, farincikina na ninku, samun cikar buri ba abu ne mai sauki ba. Take a gurin na sauka kan gadon na yi sujadar godiya ga Allah.
“Awwww finally yau dai buri ya cika Noor ta zama matar Noor halak malak”
Cewar Zainab tana tsokanata. Sai na yi murmushi na shafa fuskata, for the first yau na yi aure na shigo gidan mijina ina mai farinciki da jindadi, kuma ina mai fata aure ne sai idan na mutu na bar shi domin bana fatanya mutu ya bar ni, bana sha'awar rayuwar zawarci bana burin aurena ya sakw mutuwa a yanzu. Mun kusa awa biyu a gidan sannan ango ya shigo tare da rakiyar abokansa biyu Mansur da Yusuf daman na san su tun muna tare da Zafeer.
Kusa da ni ya zauna ya kama hannuna ya rike yana dariya, Mansur na tsokanarsa wau tsohuwar soyayya yau ta tabbata daman hausawa sun ce da tsohuwar zuma ake magani.
“Noor muna muku addu'a Allah ya ba ku zaman lafiya da zuri'a dayyiba, kuma Allah ya hada kanku da abokiyar zamanki, dan Allah ku yi zaman lafiya ta yadda hankalinsa zai kwanta, kin san dai irin gwagwarmayar da aka sha kamin buri ya samu cika, to ki yi ma mijinki biyayya dan Allah”
Na ji dadin Shawarar Yusuf, Mansur ma ya kara da nasa yana tsokanar Zainab wai ba A su siya baki ba domin ba ba su ni lokacin da suka bukata ba, kuma ni din a yanzu ba budurwa ba ce ba sai an yi sayin baki ba. Wannan kuma haka yake a iya sanina budurwa ake yi ma siyen baki ba bazawara ba.
“Aa za a siya bakin Matata mai tsada ne ko aure dari ta yi sai an siya”
Zafeer ya amsa da kansa yana murza hannuna a hankali. Sai duk suka saka dariya, abokansa suka ciro kudin da zai kai 100k suka mikawa Zainab, ba sai sun fada ba na san Zafeer ne ya bada kudin domin cikinsu babu mai arzikin da zai iya kyautar 50k ma balle 100k. Zainab ta karba tana ta ihu da murna kamar ba matar aure ba, gaba daya ta cire auren ta aje a gefe sai sha'aninta take saboda bikina ne, abu ne da ta so ta yi tun auren farko amman be samu ba sai yanzu.
Sallama suka min suka Zainab na rada min lalata a kunne tana dariya sannan suka tafi tare da abokansa da za su sauke su gida, bayan sun yi mana addu'a tare da fatan alheri. Zafeer ya saka hannu ya yaye mayafina gaba daya ya kalleni, ni ma kallonsa na yi cike da farinciki duka auren da na yi ko wane ina tafiya da soyayyarsa da tunaninsa ne a gidan wasu, amman yau a gidansa na tare, tare da soyayyarsa to mi yafi wannan, ni ma dai na ji farincikin da masoya suke ji.
“Alhamdullahi, shekara da shekaru sai yanzu Allah ya cika mana burinmu, ko ma nace burina domin ni cutar ta fi kamawa”
Ya shafa fuskata da hawaye ke zuba.
“Ranar da aka daura aurenki da Abokin Kareem Hafiz ko? Na yi kamar na mutu na ji kamar ban taba samun farinciki a rayuwata ba, na wahala sosai domin ban yi zaton soyayya zata kai mu ga haka ba, ban yi zaton rashin imanin mutanen ya kai haka ba, musamman ma Kareem ya raba ni da ke ne kawai saboda yana jin cewar ya isa kuma yana da kudi, ba dan zai aureki ba, aurenki na biyu ma ba zan iya misalta bakinciki ba, har sai da na tambayi kaina miyasa kaddara take hada ni da ke bayan ko wane aure na ki, ashe akwai abun da kaddara take saka mana da ba mu sani ba”
“Wani abun a nesa yake, kamin a samu cikar buri akan wahala wani lokacin”
“Haka ne, domin na wahala kamin na same ki Noor, talauci ya cutar da ni ya nesanta ni da ke, amman Alhamdullahi gashi a yanzu arziki ya sadamu”
“Kaddara ce ta raba kuma ita ta sake hadawa yanzu, ba talauci ba, ba Kareem ba, kuma ba arziki ba”
Yayi murmushi mai sauti, da alama amsata bata gamsar da shi ba, tun a daren na san zama ba zai mana dadi a gidan ba, domin yana kallon na guje shi ne saboda talauci yanzu kuma na aure shi saboda arziki. Shi kadai yayi alwala domin ni na yi tawa tun a gida, raka'a biyu muka yi muka gode Allah muka yi addu'a sannan ya juyo ya rike goshina yayi min addu'a. Sai da na cire tufafin jikina an saka na bachi kamar yadda ya bukata kuma ya saka sannan ya dauko mana abun tabawa. He feed me, i feed him cikin soyayya da kauna, sannan kwashe kayan ya rufe kofofin gidan ya rage hasken dakin ya kwanta bayana.
A wannan daren na tsammaci abubuwa da yawa daga gurin Zafeer, kamar hugging, kissing romanced, da ma uban gayyar, ba dan ina da bukata a sai dan sani ba, kowane masoya suna raya darensu da soyayya ne. Wata kila akwai gajiya a tare da shi, domin be dade da kwanciyar ba na ji bachi ya dauke shi sai ninshari yake irin na wanda bachi yayi masa dadi. A haka muka kwana ni a karshen gado shi kuma a farkon gado fili mai yawa a tsakaninmu.
A tare muka yi sallah asuba, bayan mun gama na gaishe shi na kwantar da kaina a
cinyarsa, sai ya dora hannunsa a fuskata yana shafa fuskar a hankali.
“My beautiful Wife Good Morning, how was your night”
“Alhamdullahi ya naka daren”
“Alhamdullahi ni ma na kwana cikin farinciki, wannan ne karo na uku da abun farinciki mai girma ya same ni”
Na juyo kaina da kyau saitin fuskarsa na kalleshi.
“Fada min biyu, na san na uku”
Yayi murmushi ya lakaci hancina.
“Na farko, Auren Fanna, yarinyar nan ta yi kokarin ganin ta dawo da ni hayyacina a lokacin da kika guje ni, ta nuna min kauna ita da iyayenta, na jidadin da Allah ya hada ni da ita, a daren da aka daura aurenmu ta mantar da ni dukan wata damuwa”
“Ta ya aka yi ta san mun raba?”
Na tambaya ina jin kishi a raina, domin a yanzu na sani ba ni kadai ba ce a zuciyar Zafeer.
“Waye ma be sani ba, gaba daya fa rayuwara ta canja Noor da na rasa ki, na kusan na yi hauka, Allah ya sani na kaunace ki sosai a lokacin, kin san tana kawo gyara ta zo ta same ni wani iri ta tambaye ni me ya same ni na sauya haka, ban fada mata ba amman oga ya fada mata, a lokacin da ta sake zuwa na bar garin nan ne saboda ina jin ba zan iya zama idan ba same ki ba, a lokacin ina jin kamar ba zan iya rayuwa idan babu ke ba Noor”
Ya sauke ajiyar zuciya.
“Ta samu number wayata ta gurin oga, ta kira ni ta min nasiha sosai kuma tunatar da ni abun da na manta iyeyena da karatu wanda su suka fi muhimmanci sama da soyayyata da bata samu cikar buri ba, na fada mata ba zan iya zama a garin ba saboda makiya za su min dariya kin yi aure kin bar ni, sai ta bukaci na tafi Sokoto gurin wani dan'uwan mahaifinta na zauna a can, na zauna a can har sai da na samu sukuni na dawo hayyacina ni da mazan gidan muka zama kamar abokai, a lokacin da na dawo sai ta yi min ta yin kaunarta bayan ta ba ni gata na kwantar min da hankali da yin magana da iyeyena, kuma ta gabatar da ni a gurin iyayenta suka min nasiha. Na amsa soyayyarta amman bata bar ni na kashe naira ba, bayan sadakinta da na biya ban san wani abun wahala da na yi ba su ma kuma kudin sadakin ta gurinta na same su, bayan aure kuma takarduna suka fito na yi service sai mahaifinta ya ba ni babban gurbi a ma'aikatarsa”
Na tabe baki ina jin zafi a zuciyata.
“Mai arhace ma, ashe ita ta yi maka tayin kanta, kuma ta yi maka komai, wata kila dan bata da masoyi ne”
Da gatse na yi maganar domin na lura bara mana soyayya yake, a cikin labarinta da yake ba ni akwai kauna da soyayyarta a zuciyarsa, sai dai ina da tabbacin be kai nawa ba, wata kila ma dai kimarta ne kawai yake gani domin ta cancanci a yaba mata.
“Noor duk zaman da zamu yi dake karki yarda ki fadi wata magana marar dadi akan Fanna, ban ji babu dadi kuma bana son abun da zai kawo tsabani a tsakaninmu, idan Allah ya hada ku ina son ki yi mata biyayya fiye da yadda zaki yi min”
“Zan dai maka biyayya kai da kake mijina domin kai na aura kuma kai nake aure ba ita ba, ita dai matsayinta ba zai canja a matsayin matar ka ba, kuma abokiyar zamana”
Yayi murmushi ya dauke idonsa akaina.
“Na ji farko fada na biyu”
“Na biyun aikin da mahaifinta ya ba ni, already na fada a cikin na dayan ai, daren fa ban iya bachi ba, saboda farinciki, gashi ya sake ma iyayena muhalli kuma bana da su za ayi hajji da yardar Allah, na ukun dai nw baki sani ba”
“Na sani mana aurena ko?”
Yayi shiru for seconds tare da kai hannunsa a kunnena.
“Eh haka ne, aurenki ne farinciki na uku amman makasudin jiyar da wanda ya jiyar da ni bakinciki ne”
Kamar ya san zan tambaya waye sai ya ba ni amsa tun kamin na bukata.
“Na ji farinciki jiya na kwana a farinciki, yau kuma na farka a farinciki wanda ya raba ni da ke kuma na san jiya ya kwana da bakinciki ya farka da shi, zai ji kwatankwacin abun da na ji a lokacin da ya raba ni da ke saboda kawai yana jin yana takama da kudi, kuma ba ma aurenki zai yi ba ya aurawa abokinsa, manufarsa ta yin hakan ne ban gane ba har yau”
Gaba daya sai jikina yayi sanyi, zuciyata ta karaya saboda me Zafeer zai aikata abun da zai hana Kareem farinciki? A da can ni ma ban fahimce shi ba, amman a yanzu na sani ba shi da burin da ya wuce ganin farincikina. Na tashi zaune daga kan cinyar Zafeer na kalleshi.
“Bana jin ya raba mu ne saboda isa ta kudi, kuma abokinsa shi ya amsa cewar yana sona a lokacin da alakarmu ta lalace, Baba ne silar komai na sani Allah ka yafe masa”
“Me yasa shi be aure ki ba idan har sonki yake?”
“Saboda na fada masa na sake nanata masa cewar kai nake so, shi kuma yana tsoron ya auri macen da bata son shi”
“A yanzu ya fahimci kina son shi ne shiyasa yake ta shirye shiryen aurenki ko kuma dai yana son ya aureki a haka ne ko da baki son shi, ko kuma dai yana son ya maida ki kamar tsohuwar budurwarsa ne saboda yana ganin kamar baki da wayo...!!”
Na kasa sake furta komai na kasa fahimtar gurin da kalaman Zafeer suka dosa, maganar sai ta juye min upside down. Daga haka kuma wata maganar bata sake fitowa daga bakina ba. Shi ma kuma tashi yayi ya fita waje yana amsa wayar matarsa ko ma na ce uwar dakinsa.
Tea ya hada mana daman tun da dare ya siyo kayan tea da komai, ni dai ban ma iya cin biredi ba sai tea kawai na sha, duk inda ya juya kallonsa nake kalamansa nake tunani, na kasa hadewa har sai da na tambaye shi.
“Zafeer idan na canka daidai kamar ka aure ni ne saboda Kareem ya ji babu dadi ba dan kana so na ba?”
Ya kalleni.
“Idan na ce bana sonki zaki yarda? Ina sonki mana Noor har gobe, amman dai makasudin na dandana masa abun da ya dandana min ne”
Tun a kalamin na yi kuskure, ban kuma sake sakin jikina ba, farinciki da ya kamata na samu a gidansa sai na gagara samunsa. Wata kila ni dai kam ba ni da rabon dacewa a cikin aure wata kila tawa kaddarar a cikin aure take.
Har na gama cin amarci yan'uwan Zafeer ba su taba takowa gidana ba, duk wanda zai zo ko ya zo to daga dangin mahaifiyata ne ko mahaifina ko yan unguwa. A tsawon sati biyu da na kwashe a gidan Zafeer be taba kissing dina ba, be taba kai hannunsa a jikina da nufin jiyar da ni jindadi ba, idan har jikina ya hadu da nashi, to ni na kwnatar da kaina ko jikina a nasa, ko kuma na shiga jikinsa da dare idan zamu kwanta sai ya rumgume ni mu yi bachi, hana rantsuwa idan ya dawo daga aiki yana taba fuskata ko hannuna ya tambayi ya nake.
Tun ina hakuri har zuciyata ta fara raya min ba daidai ba, ko dai Zafeer yana kyamata ne ko kuma yana ganin kamar na yi tarayya da Kareem ne, ta ina ma ya san Kareem yana da tsohuwar budurwa? Ta ina ya san Kareem yana shirye shiryen aurena? A duk lokacin da zai amsa wayar matarsa sai ya tashi ya fita a falon ko dakin, idan kuma yana jin kuiyar fita ya kan umarce ni da na yi shiru ne ko kwararan motsi baya son na yi. Yau ma kamar jiya tana kira yayi min alama da na yi shiru sai na tashi na fice daga dakin na shiga kitchen dina domin duba girkina.
Shimkafa da miya na girka domin ita na fi kwarewa kuma ita ce favorite dina. A plate daya na zuba mana na kawo na aje a gabansa sannan koma na dauko mana lemu da ruwa da spoon na dawo na zauna ina facing dinsa, a rayuwata ban taba tunanin zan auri Zafeer na yi irin wannan zaman auren da babu soyayya a ciki ba.
“Ruwan miyar nan be tsane ba Noor kuma gishiri yayi yawa a miyar nan”
“Hannuna ne ya subuce”
Na amsa cikin rashin jindadi daman na san ban iya ba, kuma abu ne da na cutar da kaina da shi tun a kurciya hauka da rashin natsuwa ba su bar ni na tsaya na koyi girki kamar kanwata Hana ba.
“Ki maida hankali mana, babu abun da namiji yake so irin mace da ta iya girki, haka jiya kika girka tuwo be tuku ba shimkafa a tsaye a ganinta. Kin ga Fanna Wallahi duk gatan ubanta ta iya girki, ban tana siyen abinci ba tun da na aure ta, komai fa maida hankali ne aurenki biyu kina nufin kullum siyen abinci suke ba zaki girka ba? Idan baki iya ba sai yaushe zaki iya Noor?”
Ba da fada yayi min maganar ba, amman ambatar Fanna ta fini iya girki ya saka na ji raina ya bace.
“To ka kirata ta zo ta girka maka mana, ai ni ka san ni tun kamin ka aure ni, kuma a haka ka ji zaka iya zama da ni, ba kai kace babu wanda zai iya da ni sai kai ba? Me yasa tun yanzu ka kasa?”
Kallona kawai yake har na ci na tsude be ce uffan ba. Sai ma tashi da yayi ya dauki wayaarsa da makullin motarsa ya fice daga gidan. Ni kuma na kwanta a gurin ina hawaye, a yanzu kam na yarda 100% rayuwa bata nufin jindadi a gareni, indai har Zafeer zai aureni na kasa samun farinciki to ba zan same shi ba har abada. A dole kuma haka zan yi hakuri domin ba ni na tsarawa kaina komai ba.
Ni ma ban iya cin abinci ba saboda kuka da bakinciki, bayan fitarsa sai fargaba da tsoro suka kama ni, idan na cigaba da fusata akan wata zan yi ta samun matsala da mijina ne, wata kila har hakan ya zama silar mutuwar aurena wanda bana fata, domin mutane sun min shaidan bana zaman aure, alhalin mai daki shi ya san inda yake masa yoyo. Be dawo ba sai dare a lokacin kuka har ya sauya kamanin fuskata, abu ne da ya kamata ace idan da sabo na saba da shi kukan amman na kasa a lokacin da ya kwankwasa kofa sao na bude.
“Sannu da zuwa”
“Sannu amayar ya kike fatan an gama fushin yanzu”
Yana cire rigarsa yana amsa min, sai na shiga gabansa na durkusa har kasa na bashi hakurin abun da na yi masa a dazun kuma na roki yafiyarsa. Da sauri ya rika