Showing 33001 words to 36000 words out of 215481 words
yana shiga ya samu matarsa zaune a tsakiyar falon tare da yaransa, suna ganinsa suka taso da gudu suka tarbe shi dai ya daga su sama ya subance su sannan ya rika hannayensu.
“Baku tafi Islamiya ba?”
“Yanzu za mu je, idan mun gama cin abinci direba zai kai mu”
Tine ta fada tana tsalle ya fadada murmushinsa.
“Yayi kyau, Allah ya muku albarka ya tsareku ya shirya min ku”
“Amin Daddy, anni Daddy”
Tine ta amsa sannan Areef ma ya amsa, sai ya mike tsaye ya nufi inda suke cin abincin ya zaunar da su ba tare da ya kalli Yusura ba ya ce.
“Madam sannu da gida”
Ta yi murmushin dole saboda yaranta suna kallonta amman amsa masa ne take jin be zama dole ba. Shi ma dai yana yi duk abun da yake ne saboda yaransa kuma saboda ya bata hakkinta. Sama ya nufa ya shiga dakinsa rigar jikinsa ya fara cirewa sannan ya nufi bandakin ya cire wandon yayi wanka ya fito ya sake shiryawa ya saka wasu tufafin sannan yayi sallah. Yana kokarin mikewa tsaye Noor ta fado masa a rai, sai yayi murmushi yana mamakin yadda bata yi surutu ba a yau, wata kila saboda tana tsoron Babanta ne ko kuma dai ta shiryu din ne kamar yadda ta yi ikirari, amman yadda ta natsu nan babu surutu sai ya ji duk ta ba shi tausayi kuma sai ya ga kamar ba ita ba. Kwantawa yayi saman gadonsa ya dan taba chat for like 30min yana ganin Safeena ta hau online sai yayi saurin kashe data ya sauka ba tare da ya bude sakonta ba, ba kuma dan be bukatar hakan ba, domin be saka nuna mata rashin kulawa ba, amman a yanzu yana kokarin ganin ya gujewa wasu abubuwan ne kamin ya san matakin da zai dauka a gaba, so yake ya saba mata da wasu hayyarsa da bata san da su ba, shakuwar dake tsakaninsu ta ragu.
Saukowa yayi ya dauki abubuwan bukatarsa ya fice daga dakin cikinsa na kukan yunwa, domin ya san ko yunwar zata kashe shi a gidan nan Yusura ba zata shigo dakinsa ta kawo masa abinci ba sai dai ta aje masa a dinning, shi tun da suka yi aure yau shekara bakwai be san wata rana da Yusura ta taba shigowa dakinsa yana ciki ba, ko gyara dakin da take takan gyara ne kawai idan baya ciki sai dai idan ya dawo ya tarar an share ko'ina an gyara. Sai dai shi yana leka nata dakin sau daya a wata idan zai sauke mata hakkinta, ya sauko downstairs da kuzarinsa ya nufi kofar fita falon.
“Ga abincinka a dinning”
“Yarana sun ci ya wadatar, ni zan ci a waje”
Ta tabe baki ta dauke kai ta cigaba da kallon da take daman yaran suna gama cin abinci suka wuce Islamiya. Cikin motarsa ya shiga ya zauna yayi shiruuuuuu yana nazarin rayuwa, kamin kira waya ya katse masa hanzari. Ganin number Nabil ya saka shi murmushi domin baya kiransa sai da wani babban dalili, a yanzu kuma ya san dalilin ba zai wuce Noor ba kawar nishadinsa.
“Hello”
‘“Ranka ya dade barka da wuni”
“Bakar Nabil ya kake?”
“Lafiya Kalau ranka ya dade”
“Ina fatar kun samu fahimtar juna tare da mahaifinka”
“Komai ya wuce ina godiya Oga”
“Toh Alhamdullahi ina Noor”
“Eh daman saboda ita na kira, dubata da kace zaka yi nace kana asibitin yanzu mu tafi”
“Ba sai kun je asibiti ba ka kawo ta, restaurant zan zo da abun daurin a nan idan na daure mata sai ku tafi”
“Toh Oga”
Ya kashe wayar sannan yayi ma motarsa key, Asibitin ya fara zuwa ya dauko abun bukata sannan ya nufi restaurant dinsa. A reception ya same Noor zaune a kujera zaune tana raba ido da alama shi take jiran bullowarsa. Suna hada ido ta sakar masa murmushi shi ma yayi mata murmushin yayi tsammanin zata taso ta tare shi ne ko kuma ta bi bayansa sai be ga ta yi ko daya ba sai binsa da ta yi da kallo har sai da ya kirata.
“Noor”
“Na'am”
Ta amsa sannan ta mike tsaye ana ta kallonta ta nufi inda yake tsaye yana jiransa har sai da ta iso sannan suka jera suna tafiya.
“Ya aka yi na ganki yau kamar ba ke ba?”
Ta kalleshi murmushi har zuci.
“Ka karramani...”
“Da na yi me?”
Ya tambaya da kamar mamaki sai ya washe masa hakora.
“Ka ce Noor a gaban mutane, kai ne fa mai gurin nan kuma ka kira ni a gaban mutane kuma ka tsaya ka jira ni har sai da na zo, ba ka ga kowa kallona yake ba sun dauka ni ma wata ce”
Ta yi tsalle kadan ta dire tana jindadin da ya haifarwa da Kareem jindadi.
“Oh just? Abu kadan ke faranta ranki baki da matsala yarinya i like your style”
Ya fada sannan ya saka key ya bude office din ya bude mata ta fara shiga sannan shi ma ya shiga.
NOOR POV.
tsayawa na yi har sai da yayi min izinin zama sannan na zauna, ina kallon yadda kananan kayan jikinsa suka karbe shi yayi kyau da har na kasa boyewa sai da na fada.
“Ka yi kyau, kayan ya maka kyau”
“Thank you”
Ya fada yana murmushi tare da aje ledar dake hannunsa sannan ya janyo kujera ya zauna, a yadda na lura yanayinsa kamar ba a yadda ya saba ba, na lura akwai damuwa a tare da shi, sai dai ban ce komai ba domin damuwarsa ba tawa ba ce.
“Zaki ci wani abu a kawo miki? Yunwa nake ji zan ci abinci sai na daure miki hannu”
Har zance aa sai kuma na tuna wannan abincin fa Free ne idan ma ban ci ba ni nayi ma kaina.
“Eh amman ba zan ci gabanka ba”
Yayi murmushi.
“Me za'a kawo?”
“Zan iya fada da kaina?”
Ya daga min kai sai na ce.
“To ka kirata na fada mata da kaina ba zan iya fada maka ba, kuma idan ta shigo ka rufe kunnenka karka ji dan Allah”
Cikin saukin kai yayi min yadda nake so ya kira matar a lokacin da ta zo sai yaja kujerarsa baya ya ce.
“Face her”
Matar ta fuskance ni shi kuma ya saka yatsa ya rufe kunnensa. Dadin da na ji a lokacin da yayi abun da ya bukata ya fi dadin da na ji a lokacin da ya yi min tayin abincin. Sai da na gama fada mata sannan ya dauke hannunsa ya fada mata abun da zata kawo masa, bayan ta fice na kalleshi na ce.
“Ka ji me na fada mata?”
“No kin ce ai kar na ji”
“Ce Wallahi baka ji ba”
“Wallahi ban ji ba, ai kin ce kar na ji i respect that”
“Ya aka yi ka gane na gama fada to?”
“Ina karanta bakinki ne”
Na yi murmushi ina kallonsa.
“Kana da sauki babu ruwanka kamar ba kai ne mai gurin nan ba”
“I wish people knew”
Ya furta ya kalli agogonsa.
“Kareem daman ina son zuwa saboda ina son magana da kai, na jidadi da ka ce a kawo ni”
“Daman na lura akwai magana a bakinki ai, fada min Minene?”
Na dan yi shiru na sosai kaina da dayan hannuna ina dan jin nauyin maganar.
“Daman akan gidan da zaka siyama Baba ne...”
Sai a lokacin ya dago ya dube ni.
“Uhmm hmmm”
“Cewa na yi me zai hana kudin ka bawa Zafeer idan dai taimakon dan Allah ne zaka yi? Zai jidadi kuma zai siye gida, amman Baba shi yana da gurin zama ai”
Murmushi yayi.
“Shi kuma Baban fa?”
“Shi shi fa yana da gida, kuma idan ka ba shi kudin aure zai yi, amman Zafeer zai aure ni ne da kudin ya siye gida ko ya kama haya”
“Sai a bar Babanki yayi ta haya kenan? Kuma fa ba ni ne zan siye gidan ba”
“Ni dai daman ina son na fadi gaskiya ne, kuma ina son na roke ka dan Allah ka taimaka masa, Wallahi Babana ya boye muku ne amman gidansa ba haya yake ba, ban fada gabansa ba ne saboda kar ya yi fushi ya ce zai koreni ko ya dake ni”
Dariya ya fara yi kadan kadan kamin ta fara yin yawa ni dai na san a cikin labarina babu abun dariya amman sai kyalkyalar dariya yake har sai da na dan ji tsoro.
“Sorry”
Ya daga min hannu sai kuma ya sake tintsirewa da dariya ya mike tsaye ya nufi teburinsa sai da ya fara aje wayarsa dake hannunsa sannan ya dafa teburin yana girgiza kai.
“Wallahi ban taba haduwa da yarinya kamar ki ba, ke duk yadda nake misaltaki da ex dita kin fita, amman da babanki ya san kin zo nan kin fadi haka sai ya yanka ki ko Noor”
Na yi dariya na sauke kai kasa kamar wata wadda ta yi abun arziki.
“Amman kar kace ka ji na fada kace mutanen unguwa ne suka fada, ko kace Malam Sani ne ya fada maka, abokin Baba ne na san Baba ba zai rasa fada masa ba”
Ya sake yin dariya har da saka hannu ya tare kwalla da suka cika masa ido.
“Ya Allah Wallahi na dade ban yi dariya haka ba, ina cikin damuwa amman kin mantar da ni komai ina son mutane masu gaskiya sai na ji kin kara burge ni”
Mamakin jin cewar yana da damuwa ya saka na manta da banbarar da na yi.
“Yanzu kai har kana da damuwa? Kana da kudi fa, kana da mata da yara kana da aiki kuma zaka shiga mota mai kyau ka saka tufafi mai kyau kuma ka shigo nan ka ci abincin da kake so a haka kuma kana da damuwa? Daman masu kudi suna da damuwa sukan? Ai damuwa sai talaka ko?”
“Ke dai babu ruwanki, yadda rayuwa ta nuna miki haka kike tafi da ita i wish i was just like you”
Ya fada har lokacin dariya yake. Matar da ta karbi order ta kwankwasa kofar office din yayi mata izinin shigowa sai ta shigo. Sai da ta fara aje min plate uku sannan ta aje manya ledado biyu a gabana.
“Gashi, zan dauko lemu yanzu”
“No need akwai lemu a nan”
Ya fada sai ta amsa masa da Okay Sir sannan ta fice daga office din.
“Karka ji babu dadi daman ina son na kai ma Zafeer ne, shi ma idan ya ci abu yana kawo min”
Yayi murmushi kawai ya nufi kofar office din ya bude.
“Zan je na ci abinci ke ma ki ci na ki”
Ya fice, aiko a nan na samu damar saka hannun hagu na sauka kasa na zauna na ci yadda raina yake so da hagu sai da na koshi sannan na nufi fridge na dauko kalar lemun da nake so na sha. Na dawo da ragowar zan zauna kenan wayarsa da ya fita ya bari ta yi ringing ban kula wayar ba, sai dai da alama mai kiram be san rashin samu ba, sai ya kara kira. Na nufi wayar na dauka babu suna babu number a jiki sai wasu dot dot dot da aka jera kusan guda hudu.
Na amsa wayar na kai kunnenta.
“Kareem”
Na ji muryar ta fada.
“Baya kusa ya aje wayar ne ya fita”
“Wacece ke?”
Na yi shiru domin na ji mai tambayar ta tambaya ne da tsauri gashi kuma ni din ban san me zan ce ba.
“Ke ce yar iskar yarinyar nan ko? Wato ba zaki cire kanki a lamarin Kareem ba, karya miki hannu da na yi be zame miki darasi ba ko?”
A take na gane ko wacece.
“Eh ni ce, kuma yanzu ma na zo ne ya daure min hannu bayan wadda yayi min, kuma ya kawo min abinci mai kyau na ci, kuma ina cikin office dinsa ni kadai saboda na isa, kuma hannu na ni be karye ba Wallahi arziki kika ce saboda Kareem ya fada min ke daman haka kike baki da hankali ba dan haka ba da dai Babana ya kulleki gidan yari, dan Babana ya fi ki bala'i, ke din banza Kareem dai ni zai aura na fada miki kuma ki cire da shi, ballagaza kawai mai karyar ciwo, ai ciwon zuciya sai ya kashe ki, azzalumar banza da wofi”
Na yi hanzari sauke wayar na aje a inda na ganta ina jin tana magana amman ban saurara ba, ina ta kallo har sai da gaji da haushinta ta kashe wayar. Na koma na zauna na natsu sosai dan kar ya gane na yi wani abu, amman hakan be hana shi fahimtar na taba wayarsa ba, domin wayarsa ce farko abun da ya fara dauka a lokacin da ya dawo dakin.
“Ya aka yi wayata ta samu maiko?”
“Fadowa ta yi na dauke maka”
Ya kalleni kamar be yarda.
“Noor fada min gaskiya dai kirana aka yi kika daga kuma baki son na san kin daga haka ne?”
Mamaki ya kama ni jin yadda yayi saurin gano gaskiyata.
“Halam kana da aljannu”
Yayi murmushi kawai ya zari tissue ya goge wayar.
“Na manta da ita sai da na fita na tuna, kuma na yi tunanin kar na dawo na samu kina cin abinci ki ji babu dadi”
“Na gama zaka daure min yanzu zan tafi”
Ya saka wayar aljihunsa sannan ya janyo kujera ya zauna ya dauko ledar daya shigo da ita ya bude ya dauko abun daurewar ya daure min a hankali ba tare da ya matse na ji zafi sosai ba.
“Kareem me ye tsakaninka da matar da ta karye min hannu”
Ya daga kai ya kalleni.
“Me ya kawo wannan maganar?”
“Har yanzu ina mamaki me yasa ta yi min haka ne, amman dai ko miye na barta da Allah ba zata ga alheri ba”
Be sake ce min komai ba har ya gama sannan ya kalli plate din da na ci tsutsusar nan da nake ta kwadayi.
“Ke kika ci? Daman zaki iya cin wannan?”
“Tana da dadi, baka taba ci ba?”
Ya girgiza kai.
“Bana cin sea food, bana cin English breakfast”
“Ni kam na ci, akwai dadi ai”
“Idan ba ki ci ba ai ba ke ba ce”
Ya nuna ni yana murmushi.
“Wannan ce Noor din da na sani daman wacan da gani a gidanku shiru na san ba ke ba ce, this is the real you”
“Na gode Kareem, dan Allah ka fadawa abokinka gaskiya idan yana son taimako to ya taimaki Zafeer”
Ya amsa min da kai yana lumshe ido ya bude.
“Zan fada masa”
Na mike tsaye na dauki ledodin da hannun hagu. Sai ya mike tsaye shi ma ya karbi ledodin ya aje ya matsa da ni kusa da teburinsa ya zari tissue ya goge min yatsuna dake da maikon naman da na ci, domin abinci dai da spoon na ci.
“Haka nan kake yi ma matar ka ko Kareem? Ni ma Zafeer zai iya min haka yana ririta ni kamar sarauniya”
Yayi murmushi ya kalleni.
“Irinku haka ake tafiyar da ku sai a samu yadda ake so, ita mace awaza ce idan kace zaka lankwasa sai ta karye sai dai a lallaba, duk yadda mace yake ni ina iya zama da ita da zarar na karance ta, rayuwar duniya sauki ne da ita sai wadda ya so wahalar da kansa”
Na mayar masa da murmushin sannan ya ce.
“Zauna bari na kira Nabil ya zo ya kai ki gida”
“Bana son ya kai ni gida da kaina zan tafi”
Na fada masa saboda na san fada Ya Nabil zai min akan ka karbi takeaway.
“Ai be san kin shigo nan ba, ya kamata ya sani”
Ya dauki wayarsa ya taba sai na ga ya dago ya kalleni da fuskar mamaki amman be ce min komai ba ya maida idonsa kan wayar ya kira Yaya. Babu bata lokaci Yaya Nabil ya iso suka gaisa sannan ya fada masa ya kai ni gida.
“Toh ranka ya dade an gode Allah ya saka da alheri, ban ma san ka shigo ba sai da na neme ta aka ce kai ka kirata”
Ya daga masa kai, ni kuma na mike tsaye
“Ko ka saka ta Napep tun da aiki kake”
“Okay Oga”
Ya amsa sannan ya daukar min ledodin ni dai ban yarda na kalleshi ba har na fice office din. Na yi zaton ko Yaya zai yi magana yace ka karbi takeaway amman be ce min komai ba har muka isa titi ya tari Napep ya saka ni ya fada masa inda zai kai ni. Mai napep yaja mota ina jindadin yadda be tsangwame ni ba, na kalli ledodin na yi murmushi daman leda daya ta Zafeer ce daya kuma ta Baba saboda plan din da nake da shi. A bakin hanya ya sauke ni, ban shiga gida ba sai da na fara biyawa gidan da Mama take zubin adashe na yi mata karya cewar Mama tace a bata dubu goma a ciki tana da wata lalura zata maido zuwa gobe, na yi sa'a Talatu ta ba ni dubu goma bayab ta gama karanta min na fadawa Mamarmu kar ya wuce gobe. Na karba na fito gidan na nufo gidanmu cikin natsuwa ni kaina na san na samu canjin rayuwa daga jiyan nan zuwa yau na natsu sosai.
____________________
Gashi nan na yi long page na biya bashin na jiya 😆
Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*
✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧
𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆
*Talla👇👇👇*
https://chat.whatsapp.com/GY1W0qJiFbJD5A5J6F0fqA
*INA MATAN DA SUKASAN DARAJAR GYARA❓DAKU NAKE MACE MAI GYARAN BATA ZAMA BORA❌*
*KUZO GA INGANTATTUN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI💪BA MUNA KAYABA❌ HAJIYA KIZO KISAI KAYAN MATA WURIN DA BAZAKIYI ASARAR KUDIN KI BA*
*INA MASU CEWA NI KO NASHA KAYAN MATA BASAMIN AIKI HMMM HAJIYA BAKIDAI SIYA KAYA MASU INGANCI BANE, KAYANMU SUNA KARA NI'IMA, TAYARDA SHA'AWA, DADI, TIGHTENING (MATSI), CIKO DA GABAN MACE (DUK BUDEWAR SA), DUMIN GABA GA, KAMSHIN GABA GA KUMA NA KARA DANDANO OVER 💃💃💃💃💃👉 GA KUMA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI DAGARGAZA SANYI KODA YA SHEKARA 10 A JIKINKI* 09038090328
*A DAYA BANGAREN KUMA MUNADA SABAYA MAI GYARAN NONO DUK LALACEWAR SA KO KIN HAIHU GOMA SABAYAR MU ZATA CIKO MAKI DA BREAST SUYI GIRMA SOSAI MADAME*
*GA KUMA TA HIPS (MAZAUNAI)SU CIKO SUYI BULBUL NONO YA CIKO SOSAI HJY KIYI KIBA YAR DAIDAI SKIN DINKI YAYI KYAU KI KOMA TAMKAR TARWADA*
AKWAI KUMA NA GYARAN NONO WANDA BAYA SAKA KIBA💃💃💃
GASKIYA NA YARDA DA INGANCIN KAYANTA👆👆👆
*Chapter