Showing 75001 words to 78000 words out of 215481 words

Chapter 26 - Ƙaunar Da Ta Zama Azaba by 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

yaransa ne suke tashinmu daga bachin safe da muke komawa, yau kuma yana bangaresu wata kila shiyasa be leko nan ba, ko kuma dai fushi yake ne har yanzu be sauko ba? Domin jiyan nan na bata masa rai sosai, to me ya kamata na yi na bashi hakuri? Ko kuma na share shi idan ya gaji ya zo? Ni kadai nake ta sake sake na na rasa makama. Shiru shiru be shigo ba matarsa ma bata leko ni har azahar gashi yunwa sai cini take daman na kwana da ita. Sai kusan uku na rana sannan ya fita ina ganin haka na jikina ya mutu kuma na gane kuskuren abun da na aikata. Falon na dawo na zauna ina jin wata azzababiyar yunwa gashi babu kudi hannuna balle na siya wani abu kuma kitchen da rufe balle na saffara wani abu. A wani taimako na Allah sai ga matarsa ta shigo da sauri bangarena da far'ata kamar kullum ni kuma na dube irin duba na yar'uwa.

“Kanwata ya kike?”

“Lafiya kalau”

Ta yi fuskar tausayi.

“Wallahi ina can amman zuciyata na tare da ke ina tausayinki sosai, na san kin sha yunwa yau ko?”

Na daga mata kai.

“Ya ji haushina jiya ko? Ina son na bashi hakuri amman ban san ya zan yi ba, na ga har ya rufe kitchen din ya tafi da key din haka na kwana da yunwa”

“Allah sarki, gashi ya rantse kar na baki abincin da na dafa, saboda na fada masa da ke zan dafa”

Na ji babu dadi kamar na yi kuka kuma dai na daure kar na zubar da hawaye a gabanta.

“Aisha ki ce yayi hakuri”

“Zan fada masa amman ke karki yi saurin ba shi hakuri ki zubar da ajinki, yanzu kin san yadda zamu yi ga kudi 5k ki tafi ki siyo abinci a waje ki dawo ki ci”

Na zaro ido da sauri gabana na faduwa.

“Aa ba zan iya ba, jiya fa a gabanki na ce zan fita kin ga yadda yake fada shi ne sanadin ma duk wannan abun balle kuma ace na fita be sani ba”

“To zaunawa zaki yi yunwa ta kashe ki Noor? Ya tafi da keys din kuma ya rantse kar na baki abincinsa kuma ya fita ya fada min sai bayan Isha'i zai dawo saboda gurin Hajiyarsa zai tafi na bashi abinci ya tafi mata da shi”

Na kalli kudin sannan na girgiza mata kai.

“Ba zan iya ba, be kamata na fita be sani ba balle kuma ace siyen abinci zai yi fada idan ya ji”

“Taya zai ji? Ba zan fada masa ba”

Na girgiza kai na lake kafada.

“Ni dai ba zan je ba”

“Shikenan ni daman saboda ina tausayinki ne, bari na aje kudin”

“Sai idan ba a bawa mai gadi ya siyo min”

“Maigadin kuma? Ai ba zai yiyu ki aike shi ba, ba zai ma tafi ba saboda gadi yake yi kuma zai iya fadawa Barrister”

“Ni dai ba zan iya tafiya ba, sai dai ko ke idan zaki siyo min”

“Ni kuma? Da ciki dako dako na tafi siyo miki abinci.? Ina laifina na tausaya miki Allah ya baki hakuri”

Ta mayarda kudinta ya fice daga falon, ni kuma na koma na kwanta ina jin yunwar na min yawo a cikin, haka na kwana da wahala da kuka da bakinciki wata zuciyar na cewa na tafi na karbi kudin na siyo abinci domin ba ni da wata mafita bayan wannan, wata zuciyar kuma na fada min na tafi kawai na bashi hakuri kuma na fada masa ina jin yunwa ya ba ni key na dafa abinci domin alama ta nuna ba zai shigo bangaren nawa ba ya duba ni tun da gashi har dare yayi be shigo ba kuma ya dawo. Na tashi ina jin jiri na fita daga bangaren nawa ina sanye da atamfa riga da zane na shiga bangaren Aisha na samu yaranta suna ta wasa a falon ita kuma tana bare giďa. Da far'a ta tarbe ni ta dakawa yaranta tsawa wai su gaishe ni haka suka gaishe ni jikinsu na rawa na amsa ina zaunawa, kana ganina ka san yunwa ta ci ni har ta gaji.

“Lafiya Amarya?”

“Hafiz yana nan?”

Yaransa duk suka kalleni jin na fadi sunan mahaifinsu kai tsaye.

“Eh yana nan? A kira Miki shi?”

“Eh ina son na yi magana da shi”

“Toh”

Ta aje plate din giďar ta tashi ta shiga dakinta, bata wani jima ba ta fito ta ce min.

“Yace ki jira shi zai yi wanka”

“Tohm”

Na amsa idanuwana kamar za su yi magana tsabar yunwa dake matsa min lamba. Haka suka bar ni a gurin tun ina jiran fitowarsa har na fara bachi....
Ko da na farka babu kowa a falon sai ni kadai, tashi na yi na kamar zan fadi na fice daga falon na dawo bangarena ina kuka. Indai har horo ne Hafiz ne Wallahi na horu daga jiya zuwa yau kawai...




**** **** ****

Yusura na kokarin aje remote din hannunta akan Center table ta dago tana amsa sallamar da Safeena take yi.

“Wa'alaikusalam”

“Sannu da gida”

“Yauwa sannu dai”

Safeena ta maida kofar falon ta rufe ta shigo cikin falon ba tare da an yi mata izini ba ta zauna a kujera.

“Kin gane ni kuwa?”

Yusura ta yi murmushi yake.

“Ta ina fuskarki zata bace min? Safeena Right”

Safeena ta yi murmushi.

“Haka ne, na ga kamar ba jiya ba ne abun, ya gida ya karin hakuri? Na zo gaisuwar Momy ne”

“Gaisuwa...? Ko dai murna?”

Cewar Yusura babu alamar wasa a maganarta.

“Ah haba Subhanallahi ana murnar mutuwa ne? Hana dai Yusura sai kace wata kafura”

“Na ga abubuwa sun yi ta faruwa ba ki taba zuwa ba, kamar haihuwata sau biyu ina haihuwa da Kareem amman baki zo mana barka ba, sai yanzu?”

“Ban ji ba ne, amman ita mutuwa kin san ba a sanarwarta ni fa gaisuwa kawai na zo, ba fada ba ina tunanin yanzu duk mun girma mun zama manya har da yara”

Yusura ta yi murmushi.

“Haka ne, baya gida amman ki jira shi ba jimawa zai shigo sai ku gaisa”

Ta mike tsaye ta haye dama Safeena ta bita da harara tana jin wani masifaffin kishi na cinta. Yusura na shiga dakinta ta fara safa da marwa tana cizon bakinta gaba daya ta ma rasa gane hikimar zuwan Safeena gidan, ko bata rantse ba ta san Safeena ta yi farinciki da mutuwar Momy domin tana cikin manyan makiyanta da suka hana Kareem aurenta. Kasa zama ta yi har sai da ta hango tsayawar motar Kareem a gurin da ya saba tsayuwa sannan ta nufi kofar dakin ta fita, ta san be kamata ta nuna kishi ba domin ba son Kareem take ba, but abun da Safeena ta yi a yanzu kamar cin fuska ne da mutuncinta, kuma idan har Momy zata tsani Safeena ita kuwa bata san dalilinta na kaunarta ba, zuwanta kuma ya nuna ta jidadin mutuwar Momy if not ai tana da number wayarsa sai ta kira shi ta yi masa gaisuwa ko kuma ta same shi a wani gurin.



KAREEM POV.

A lokacin da ya faka motarsa ya lura da wata bakuwar mota fake a kusa da Entrance din shiga falonsu. Be raba dayan biyu ba ko dai yar'uwarsa ko kuma yan'uwan Yusura ta bangaren uba ne suka zo gaisuwa ko ziyara, ba tare da fargabar komai ba ya shiga falon. Yana rufe kofar Falon Yusura na saukowa ta karaso gurinsa ta karbi Keys din hannunsa da ledar hannunsa tana murmushi kamar ba ita ba, sai kuma ta sumbanci bakinsa.

“Sannu da zuwa...”

Safeena na kallonsu ta ji kamar ta kama da wuta, Kareem kam be lura da Safeena sai kallon matarsa yake yana mamakin inda wannan ya samo asali.

“Ga Safeena ta zo gaisuwa”

Ya juya ya kalli saitin da Safeena take zaune tana ci da wuta. Ya tako ya karaso gurin da take zaune da mamaki a fuskarsa.

“Safeena? Me kika zo yi nan?”

“Gaisuwa...”

Ta amsa daker numfashinta na gargada. Ya kalli Yusura sannan ya sake kallon Safeena

“Ashe Momy lokaci yayi”

“Haka Allah ya so”

“Allah ya mata rahama, ya bada hakuri zan tafi”

Ta dauki jakarta ta mike tsaye ta fara tafiya kamar wadda ta rikice.

“Ka rakata mata, amman karka dade ka ji Babyna... Bari na hada maka ruwan wanka”

Kareem ya kalleta sai ta sakar masa murmushi tana masa alama da ya amsa da gira.

“Okay...”

Ya amsa With so many questions da yake bukatar amsarsu. Sannan ya juya ya bi bayan Safeena da ke tsaye jikin kofar tana jin komai. Rufe kofar falon yayi suka sauka kasa.

“Wannan ya zama na farko kuma na karshe da zaki sake tako kafarki a gidana, ba zan daukar miki wannan ba”

“Me yasa ka yi min karya? Kace kai da Yusura baku zaman lafiya, kalli yadda ta tarbeka a gaban idona? Da far'a da soyayya, shiyasa gaba daya ka canja min, tun kamin Momy ta rasu daker na samu kanka yanzu kuma baka amsa kirana baka mayar min da amsar sakona”

“Safeena ina cikin jimami na rashin Momy a yanzu, bana bukatar wata maganar, abu na biyu kuma ki natsu ki fara tunanin yayanki da mijinki ki cire ni a rayuwarki... Na gane baki da hankali shiyasa har kika tunanin kashe aurenki ki bar yaranki ki dawo gareni, yanzu kuma abun ya wuce da har kin kai ki tako kafarki a gida? Ba zan daukar miki wannan ba, ban hada iyalina da kowa ba”

“Idan na ce zan aikata wani abu akanka Kareem baka ganewa, baka amsa kirana kana ta kokarin kauce min a lokacin da nake da tsananin bukatar saka ka farinciki, da kana kula ni da ban zo gidan nan ba, na riga na sabu da kai, na cutu da soyayyarka ba zan oya warkewa ba amman a haka a mahaukaciya kake kallona?”

“Taya mahaifiyata zata hane ni da abu na aikata? Taya tana raye zata hana ni aurenki yanzu kuma bayan ta mutu kike tunanin zan iya cigaba da wani mu'amala da ke? Safeena wake-up ki cireni a rayuwarki and i mean it....”

Ya bar ta tsaye a gurin ya rufe kofar falon ya shige ciki.

“Aurenta ya mutu ne?”

Ita ce tambayar da Yusura ta fara yi masa a lokacin da ya shigo falon. Be tunanin ta yi labe ta saurari abun da suke tattaunawa sai idan zuwanta a gidan ne ya bata mamaki.

“Me ye ma'anar abun da kika yi?”

Ta mike tsaye tana kallonsa.

“Irin abun da muka saba yi ne, a duk lokacin da baki suka zo, nuna cewar muna cikin soyayya da kaunar juna. Aurenta ya mutu ne ko kuma kashewa zata yi ta aureka saboda macen da ta yi mata karan tsaye ta bar mata duniyar?”

“Miye matsalarki da hakan?”

“Kana tunanin zan so abun da Momy ta ki? Har abada...! Ka fada mata kar ta sake zuwa gidan nan ba saboda ni ba saboda yaranka”

Ta aje masa keys dinsa da ledar dake hannunta a kujera ta nufi stairs, binta yayi da kallo har ta haye sannan ya zauna yana kai hannunsa ya taba hancinsa.

“Kai Mata kuna da wuyar sha'ani”

Ya sauke ajiyar zuciya ya mike tsaye ya dauki ledarsa da keys din ya haura sama ya shiga dakinsa...



#KhadeejaCandy



PAID PAGE 5️⃣


©KhadeejaCandy
©®Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....


You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153


_______•••_______


Tsananin yunwar da nake ji bata bar ni na yi bachi ba, haka na zauna a falon ina kuka jikina na rawa ga kuma tsoro da ya baibaye ni. Misalin shabiyu na dare na ji an murda kofar dakin an shigo, na zabura na tashi da sauri ina kallon kofar sai na yi arba da Hafiz sanye da kayan bachi fuska ba yabo ba fallasa ya shigo.

“Baki yi bachi ba?”

Madadin na amsa sai na duka a kasa ina kuka.

“Ka yo hakuri dan Allah, na daina ba zan sake ba, karka min horo da yunwa ina wahala sosai kuma ina jin tsoro”

Be ce min komai ba ya nufi kitchen din ya bude, ni kuma na zauna a gurin ji nake ko kallonsa ba zan iya sake yi ba idan be min izini ba, domin na lura babu imani a tare da shi. Shayi ya hada min ya kawo min, sannan ya sake komawa ciki ina jin kamshi yana tashi, ni dai ban yi komai ba ina zaune a gurin da ya bar ni har sai da ya gama abun da yake ya fito da plate din indomie ya aje min.

“Taso ki ci”

Na taso na dawo kusa da shi na zauna na fara cin indomie yana kallona har na gama ya kawo min ruwa na sha.

“Na gode”

“Zaki iya kwana ke kadai?”

Na girgiza kai.

“Ina jin tsoro”

“Zan kawo Ikram da Yayarta ta kwana tare da ke, amman Noor ki zama mai tsananin biyayya da gudun bacin rai please, ina da tsananin fushi da fada, amman idan ka iya zama da ni, ba wahala mun saba, kamar yadda yayarki take yi yanzu”

Na daga mishi kai. Sai ya kai hannunsa ya shafa fuska yana murmushi.

“Ki yi hakuri, be kamata na yi haka ba, amman na yi ne saboda ki gane kuskuren abun da kika aikata”

Ya sumbanci kumatuna sannan ya mike tsaye.

“Muje ki saka kayan bachinki”

“Nan zaka kwana?”

Na tambaya ina kallonsa.

“Aa yau ai ba girkin ba ba ne dakin Yayarki zan kwana sai nan da kwana biyu zan dawo”

Gaba ya saka ni na har cikin dakin na dauko kayan bachina yana kallona na canja arzikina daya ina da zanen dake daure tare da tare da shi na samu na yi dabara har na canja na saka riga da wando na bachi. Cak na ji an dauke ni daman ba wani jiki da ni ba kuma ya fi ni girma nesa ba kusa ba, saman gadon ya aje ni kwance ya kwanta da jikinsa ban gama fahimta ba na ji bakinsa cikin nawa. Na daure ne kawai saboda babu yadda zan yi ba dan ina so ba, ya dauki dakiku a haka sannan ya cire bakinsa ya daga ni ya sauka daga kan gadon.

“Ko ke fa amman da ba ni da ikon taba ki sai ihu, kamar budurwar kauye”

Na yi shiru ina kallonsa zuciyata na bugawa da karfi kamar zata cire, murmushi yayi min ya juya ya fice. Da gudu na tashi na shiga bandaki na fara korawa bakina ruwa na wanke shi tasss sannan na saka mai goge baki da buroshi na fara goge bakin ina jin kyankyami. Kamar daga sama na ga an turo kofar dakin ta jikin madubi nake kallonsa har ya fito murmushi yake kamin ya kai hannunsa ya cire brush din ya debo ruwa ya wanke min bakin sannan ya sake hade bakinsa da nawa wannan karon da ya cire sai da ya cilasta min hade yawun bakina.

“Na hade”

“Toh muje ki kwata, kar na sake kissing dinki ki wanke baki daga yau”

Na kalleshi kamar na ce wani abu sai kuma na kyale na bi umarninsa. Saman gadon na hau na kwanta ya lullube ni sannan ya fita be jima ba Ikram da Walida suka shigo suka hauro gadon suka kwanta tare da ni. Bachin yayi min dadi sosai domin ban kwanta tare da shi ba, babu fargaba ko tsoro a kusa da ni. Washe gari bayan na yi sallah ban koma bachi ba na fita falon na gyara kitchen na gyara falon na wanke na wanke na goge na goge sannan na dawo na zauna. Zamana babu wuya Aisha ta shigo falon kiran yaranta da sai a lokacin suka tashi bachi.

“Amarya ya kwanan kadaici?”

Na yi murmushi.

“Yara na zo kira, ko sun tashi”

“Eh sun tashi bari na kira su”

Haka ta bini da kallo har na shiga dakina na taso yaran suka fito, ta kama hannunsu suka fice tare. Dakin na gyara sannan na shiga na yi wanka na fito jikina na ciwo domin ban saba aikin wahala haka ba, mai na shafa na dauki riga da skirt material na saka sannan na shiga kitchen din na dafa shayi da gass na soya kwai biyar na soya dankali na fito na zauna. Ina tsaka da ci Hafiz ya shigo falon rike da biredi ya aje min.

“Good Morning”

Na amsa da murmushi sai ya gutsuri kwain dake gabana ya ci.

“Ashe kin iya soya kwai”

Na yi murmushi, ya mayar min da murmushin sannan ya tashi ya fice. Ina gama karyawa na hau bachin wahala idona cike da kwalla indai haka auren yake ba shi da dadi ni dai a gurin, ba zan fita ba ga aiki kullum ga wahalar kyautatawa miji ko baka so... Na yi wannan tunanin na yi wacan har bachi yayi gaba da ni ban farka sai azahar shi ma saboda Aisha ta shigo har dakina ne ta tashe ni daga bachin.

“Ke bachin rana kin yi sallah ma tashi mu yi hira”

Na tashi ina murza ido, bayan na yi sallah na dawo muka zauna da ita falo tana min hira mafi yawan hallayar Hafiz take fada min marar kyau, tana kara tsorata ni akan mijinta, sai dai abun da ya bani mamaki kuma ya daure min kai shi ne yadda take zaune da shi lafiya babu wani tashin hankali sai soyyayah da kaunar juna. Ba ita ta bar bangaren ba sai biyar na yamma a lokacin ne na shiga kitchen na sarrafa shimkafa da miya da naman kaza na ci, na bar ragowar kamar yadda na kasa cinye kwan da na soya a dazun. Da dare Hafiz ya shigo ya duba ni sannan Yaransa suka shigo muka kwana tare, washe gari ma haka ya na gyara komai na yi wanka na girka shimkafa da wuri, kamin na kwanta bachin kanwarta ta shigo kirana wai yau tana son na shigo bangarenta mu yi hira.

Kwasar fafauwana na yi na shiga bangarenta tana ta bani labarin irin soyayyar da suka yi, ashe aure ta yi bata dace ba ta fito shi kuma ya ganta ya nuna yana sonta iyayensa suka amince kasancewar ba masu matsala ba ne, shi yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login