Showing 168001 words to 171000 words out of 215481 words
na gane gaskiya, idan har ta tabbatar Abdullahi ya aikata abun da ake zarginsa, to ina baki tabbacin zan hukunta shi, domin ya zalince ki ya zalinci yar'uwarki, zan zame miki uba Noor zaki same ni mai kaunarki kamar mahaifinki, sai dai ina son na fada miki ki aje sirrin nan a cikinki domin bayyanarsa zai rusa abubuwa da yawa ciki, hakan kuma ba yana nufin zan bar maganar ba zan yi abun da ya dace In shaa Allahu”
“Shi ya kashe min Babana Abdull ne silar mutuwarsu, shi ya saka a kona gidan saboda na yi recording muryarsa yana fadar abun da ya aikata, kuma yayi hakan saboda kar kowa ya san abun da ya aikata”
Ina maganar ina hakki sai ya kura min ido yana kallona kamar mai nazari.
“Ki shiga ciki, ki samu natsuwa”
Na mike tsaye na nufi gurin da Mama Aisha take tsaye tana jirana, domin na fahimci ba da gaske yake ba daman ta ya zai hukunta dansa. I'm such a fool again. Na kama hannunta na rike muka shiga cikin gidan, wannan karon na samu zama akam tabarmar da aka shimfida ina kallon Mama dake rusar kuka, ni da ita duk mun fahimci Hana da Baba sun yi tafiyar da Baba dawowa.
“Na yafe ma yata duk abun da yake tsakanina da ita, Allah ka yafe mata, ka isar mata, mahaifinku ma na yafe masa duk wani abun da yayi min, Allah ya jikansa da rahama”
Wani kukan be tashi ba sai da Yaya Nabil yayi mana saukar bazata, rirrike shi na yi ina karkarwa saboda kuka, shi ma kukan yake Mama haka, kusan sai da muka saka kowa kuka a gidan. Duk wanda zai ji mutuwar Hana be kai ni ba, domin muna tare da juna ni da ita a koda yaushe she's been with me for my life. A tare muka tafi da Mama a family house dinsu, duk yadda Anty Larai ta so a bar mata da ni Mama bata yarda ba. Domin yanzu mu biyu kawai muka rage mata, daga ni sai Yaya.
A dakin empty room din Yayanta muka tare har ita, ita da Yaya suka raya dare da hirar Hana da Baba ni kuma na raya shi da kuka da nadama. Washe gari na yi yaki sosai kamin na samu kai abu a cikina. Ina shan furar ina jin Yaya yana hirar Kareem ne ya siya masa masa ticket din jirgi saboda ya zo ya yi gaisuwa. Mama na ta saka masa albarka. Dakin yayi kamar zai kama a lokacin da Yaya ya samu labarin abun da ya faru, har fadar yake Wallahi da zai ga Abdull sai ya kashe shi sai dai shi ma a kai shi gidan yari.
“Haka Allah ya kaddara, ni yanzu ko sunan yaron bana son ji, shiyasa na ce ba zan koma gidan Ubansa ba, babu wanda ya fi mu ku yanzu”
Duk hirar da suke bakina a rufe yake gum bana furta komai sai kallonsu nake idan hawaye suka zubo min sai na share. Da yamma Zafeer ya zo min gaisuwa ina cikin dakin ya shigo yayi ma Mama gaisuwa sannan ya dube ni ya ce.
“Noor ya hakuri?”
Kallonsa kawai nake kai kace bana jin yaren da yake magana da ni.
“Ai ita bata uhm bata uhm uhm, tun da aka yi rasuwar nan bata iya amsa gaisuwar kowa”
“Ki yi hakuri kowa yana da tabon mutuwa, kuma idan lokaci yayi ba a tsayawa Allah ya musu rahama ki yi ta musu addu'a kin ji?”
Na daga mishi kai sai ya mike tsaye yana kallona cike da tausayi da damuwa ya fice, Yaya Nabil ya tashi ya bi bayansa, Yaya Nabil ya dawo mana da tsaraba mai yawa buhun shimkafa uku da cefa ne da kudi 100k daga Zafeer, Mama ta karba tana ta yaba masa da yana hallayensa...
Daidaikum mutane suna ta zuwa mana gaisuwa bayan an watse sadakan uku ciki har da manema auren Hana. Sai dai duk wannan ban ji daga Kareem ba har na tsawon kwana biyar, wata kila ya hakura da ni ne kamar yadda na fada masa, but no matter what ai mutuwa ta fi gaban wasa ya kamata yayi min gaisuwa ko fa yake na ji Yaya dake shirye shirye komawa a yau yana zancen Kareem ba shi da Lafiya har yana fadar Mama ta je ta duba shi.
Ranar da Ya Nabil zai bar garin mun kashe adashen kukan da muka zuba, ni da shi da Mama muka yi ta tunanin Hana musamman wacan bankwana da ta yi masa lokacin da zai tafi ashe na karshe ne ko gawarta ba zai sake gani ba. Haka ma Baba ashe ba zai ga karshen karatun dansa ba, kudin da yake kwadayi ashe ba zai ga dansa ya fara rikawa ba.
“Amman wai Mama haka za a bar maganar nan shikenan ya tafi a Free?”
Ya tambayi abun da yayi fi masa ciwo a yanzu fiye da komai. Ni kaina ba ni da wata damuwa a yanzu kamar Abdull.
“To ya za'ayi, babu wata shaida ai, kuma ita wanda za ayi domin ita bata duniyar, wutar ma sai dai mu ce zargi muke domin ba mu da tabbacin komai”
Yaya yayi kwafa ya girgiza kai ya cije baki. Kwana biyu da tafiyarsa Mama ta tafi asibiti duba Kareem, bayan ta dawo take ta bada labarin yadda ya rame ciwon ya taba shi sosai. Ni dai ban ce komai ba, domin damuwata yanzu ta ishe ni riga da wando bana bukatar damuwa ko tunanin kowa a yanzu. The following day kanensa Aaryam ya zo family house dinmu, ban san wanda ya kwakwanta masa ba domin be san gurin ba. Sai da yayi min gaisuwa sannan ya isar min da gaisuwar Kareem kuma ya fada min ba shi da lafiya sosai jibi za a fitar da shi waje domin yi masa aiki.
Ban san miyasa ba, na ji ina bukatar ganinsa duk kuwa da ina jin kamar be cancanci haka ba.
“A wane daki yake?”
Na samu kaina da tambaya, wata kila na je duba shi domin ina gudun kar shi sai ya mutu na dawo nadamar rashin duba shi kamar yadda nake nadamar abubuwa da yawa a yanzu. Sai da Aaryam ya tafi sannan na koma cikin gidan na fadawa Mama ina son zan tafi na duba Kareem ance jikinsa da tsanani sosai.
“Karki ce ke kadai, ku tafi tare da Asma'u”
“Toh”
Na fita na nufi bangaren su Asma'u wacce ta kasance Cousin dita, sai dai ban same ta bangarensu mahaifinyarta ta fada min bata gidan ta fita, ban damuwa da na koma na nemi wani dan rakiyar ba na kama hanya ni kadai. Ba asibitin na nufa kai tsaye ba, zango na yada a unguwarmu ma shiga gidan da ya zama kofai, domin komai ya kone kurmus.
Bakin kofar dakinmu na zauna ina kallon cikin dakin, Hana kawai nake tunawa yadda muke rayuwa a ciki, da kuma ganina da ita na karshe na fita na barta tana rashin lafiya. Umman su Zainab ce ta shigo gidan ta fitar da ni tana ta ba ni hakuri har da addu'a take min tana tofa min a kai. A gidanta na zauna har sai da na samu sakewar zuciya sannan na fita daga unguwar na nufi asibitin da Kareem yake aiki kuma yake ciki.
KAREEM POV.
Yana ganinta sai ya ji kamar an zare masa ciwon dake kirjinsa, kusan daman ita ce energy sa a yanzu, da kuzari ya yunkura ya tashi daga kwance da yake yana kallonta, be tsammaci zuwanta ba ko da kuwa ace yana gangar mutuwa ne.
“Noor shigo mana”
Ta kalli Kareem sannan ta kalli Hajiya Hassana dake tsaye tana kankare masa kwai, ta maida kanta kasa ba tare da ta shigo cikin ba kamar yadda ya bukata.
“Wannan Hajiyar mu ce, mahaifiyarmu karki ji komai shigo”
Hajiya Hassana ta juya ta kalleta ganin ta tsane kanta gurin kofar kamar mai tsoron mutane.
“Shigo yarinya ni fita zan yi yanzu nan”
Ta aje kwan da bata gama barewa ba ta nufi kofa, sai a lokacin Noor ta kauce daga jikin kofar kuma ta gaisheta.
“Lafiya Kalau, sannu”
Hajiya Hassana ta fice daga dakin ta ja musu kofa duk kuwa da bata san wacece ba a gunsa. Noor ta tsaya a jikin kofar yatsun hannunta sarke da juna, fatar idonta da fuskarta kawai ya kalla ya fahimci irin kukan da ta sha, ta rame kamar ba ita ba ta zama so innocent.
Ji yayi kamar ace yana da iko da damar da zai sakata a kirjinsa ya rarrasheta da kalamai masu dadi, ina ma ace idan yayi mata alkawarin farinciki zata yarda da shi, ta ina zai fara rarrashin rabin rayuwarsa macen da ta hana shi ganin kyaun sauran matan duniya.
“Shigo ki zauna ko na taso ne Noor?”
Ta dago ta kalleshi da raunannin idanuwanta a take ya ji kamar ba shi da wani gata a duniya sama da ita.
“Daman na zo dubaka ne”
Tana maganar tana hawaye
“Baki son mu tattauna akan rayuwa? Wata kila idan aka tafi da ni aikin nan ba zaki sake ganina ba, shigo ki zauna Noor”
Ta fara takowa ta isa gurin kujerar dake facing din gadonsa ta zauna.
“Ya kike?”
Ta share hawayenta.
“Lafiya kalau”
“No ya kike?”
Ta dago ta kalleshi sai kawai ta fashe da kuka, rumtse ido yayi yana yawo da kansa a lokacin da sautin kukanta ke sauka kunnuwansa, be taba jin tausayinta a irin wannan karon ba, be taba kewa da kaunarta irin na yau ba, kamar ana cire kunnuwansa da zuciyarsa haka yake jin kukanta na kona masa rai.
“Na ji fiye da yadda ka ji a lokacin da ka rasa mahaifiyarka Kareem, na rasa miji na rasa uba na rasa kanwata saboda sakarcina da sha sha shanci”
Ya bude idon ya kalleta
“Babu laifinki a mutuwar kowa cikinsu”
“Akwai ni na aikata abun da ya zama silar mutuwarsu”
“Me ya faru Noor dita fada min me kika yi”
Ya cika da mamaki a lokacin da ta fada masa abun da ta aikata tana kuka.
“Me yasa haka Noor?”
“Because i was so stupid, ni sakarya ce ai daman bana tunani irin na mutane, bana ganin dacewa da rashin dacewar komai sai bayan na aikata, bana da tunani irin na mutane ni mahaukaciya ce kawai mai tarin shashanci”
Ya kara jin tausayinta ya rufe shi, zaunawa yayi da kyau yana kallonta, kaunarta ma figarsa.
“Kina da hankali da tunani irin na mutane Noor, zuciyarki da kwakwalwarki masu kyau ne, ke kawai mafita kike nema kokarin kare kanki da iyalanki kike, irinki kadan ne a duniyar nan, idan har abun da kike zargi ya tabbata to akasi ne aka samu a lokacin da kike kokarin neman mafita”
Ya sauke numfashi a hankali yana kallon yadda hawaye sauko mata ta daga kanta tana kallonsa irin kallon nan mai cike da tsoro da fargaba.
“Rayuwa bata da sauki Kareem, abubuwa da yawa basa nufin samuwa, burika da yawa basa cika, kaddara ta zama babi babi, idan wata ta rufe kofa sai wata sabuwar ta bude, farinciki ya zame min kamar lu'u lu'u mai wuyar samu”
Ta yi murmushi mai kone zuciya.
“Me yasa duk nake fada maka wannan? Kai ma kana cikin mutane da suka jefa ni a matsala, wata kila da Safeena bata samu labarin cire cikin ba, da duk haka be faru ba, da bata zuga Baba ya kai maganar kotu ba, da yanzu Hana tana raye”
“Ban fada mata komai ba Noor, Safeena shu'umar mace ce da zan iya kira da mummunar kaddara, Wallahi ban fada mata komai ba, idan har zan fadi sirrin wani, to sirrin wani zan fada ba na ki ba Noor, ta hanyar Nurse din da ta yi mata wanki ciki ta samu labari, a ranar da kika ji muryarta a wayata na je na same ta mun yi magana kuma ta fada min yadda ta tsara komai, amman baki saurare ni ba Noor shiyasa baki fahimce ni ba, bana da wata alaka da Safeena, zuwan da na yi ma domin ke ne”
Ya hade wani abu da ya tsaya masa a wuya.
“Na yi nufin baki farinciki Noor, na yi nufin maye miki gurbin abubuwa da yawa da kika rasa you're my only hope, ke ce cutata kuma ke ce magani, amman ba zan samu damar haka ba, domin na yi making mistake da zai yi ta hurting dina for the rest of my life, shiyasa duk abun da Allah yace kar a aikata a cikin hanin akwai alheri da nasara”
Ya lumshe ido.
“Ko yaushe zan huta ni? Ko yaushe zan samu salama na samu kwanciyar hankali? Yaushe damuwa zata bar ni? Ina jin tsoron duniyar nan mai fadi Kareem”
Ya kalleta idanuwansa cike da kaunarta.
“Nan gaba kadan Noor idan kin kwantar da hankali kin fahimce ni, kuma idan Allah ya ba ni aron domin ina tsakanin mutuwa da rayuwa ne a yanzu”
Me yake damunka Kareem?”
Ta tambaya tana share hawayenta.
“Tun a lokacin da na yi hadarin a baya, kirjina ya bugu amman ban dauka zai zo da matsala ba, shiyasa ban zafafa a gurin bincikar gurin ba, sai kawai na cigaba da harkokina, na kan ji yana min ciwo wani lokacin amman ba kamar yanzu ba, idan zan tashi sai na yi daker, ranar da muka yi waya dake na karshe a ranar na fadi, aka kawo ni asibitin nan ban san an zo ba, zuciyata ta yi kasa ta bar muhallinta dole sai an yi min aiki, aiki ne mai matukar hatsari wata kila na rayu wata kila kuma ba zan rayu ba”
Ta sauko daga kan kujerar ta zube kasan guiwoyinta ta kama gadon ta rike tana kallon fuskarsa, duk yadda take tausayin kanta take cikin damuwa sai ta ji kamar ta Kareem ta dara tata. Shi ma kallonta yake yana jin tausayinta fiye da kullum ta shiga taskon rayuwa ta fuskanci kalubale tun tana karama har yanzu, a zuciyarsa yake ayyana yadda take ji a nata zuciyar, a yanzu bata da kowa sai Mamanta sai Nabil su kuma ba za su iya samar mata gatan da yake jin zai iya samar mata ba.
“Zaka rayu Kareem, zaka rayu ko dan ni da yaranka we need you”
Ta kwantar da kanta saman gadon hawaye na sauko mata, Kareem ya kai hannu kamar ya shafa fuskarta sai kuma ita din ba halalinsa ba ce a yanzu. Jimke hannun yayi ya kwanto da kansa saman fuskarta tazara kadan ya bari a tsakanin fuskarsa da nata, lumshe ido yayi yana maida numfashi a hankali kamar yadda take yi, hawayenta na sauka a jikin gadon na idonsa kuma suna sauka a fuskarta.
Dif dif dif ta ji wasu ruwa masu dumi suna jika gefen fuskarta, har suka gangaro suka hade da nata hawayen suka sauka a kan gadon. Bude ido ta yi ta dago kadan ta kalleshi sai ga ta fuskarsa so cool very calm and innocent kamar ba daga idonsa hawayen suke fita ba.
“Kuka Kareem...”
“Ina sonki Noor, ina son rayuwa da ke, ina kewar mahaifiyata ina son na rayu da Yayana, ina kewar abokina ina jin rashin abubuwa da yawa I'm hopeless now... Every one is lonely sometime”
Ya furta ba tare da ya bude idon, kamin ya kai hannunsa ya share hawaye da be isa ya hana su zuba ba. Ba shi kadai ba kusan duk namiji da zai zubar da hawaye kuma ya bari a ga hawayensa tabbas yana cikin tsanani damuwa ko bukatar da abun da zuciyarsa take so. Ya bude idon ya kalleta yana maida numfashi a tare da ita zuciyarsa da nata suna bugawa at the same time something very deep inside their heart ya saka zuciyoyinsu nauyi.
“Idan wani ya sake nuna miki yatsa, Noor ki kaddara bana raye, idan wani ko wata ya saka ki zubar da hawaye i will show him the other side of me, as long as you're with me you're not alone and you will never be, you're not alone we're family. Ki fadawa Mama da duk wanda ya kamata ya sani, anjima Babana zai zo tare da Aaryam za ku tafi gurin DSS za'ayi yarjeje ni tsakanin ke fa Safeena da kuma ke da Abdull cewar idan wani abu ya same ki su ne”
“Why?”
“Duk wanda zai kona gidanku gaba daya, to rayuwarki yake nema ba ta iyayenki ba, an kashe su ko kuma an kone saboda tunanin ke ma kina ciki, kuma bana raba dayan biyu Abdull ko matarsa”
“Na fi zargin Abdull saboda case din gaba daya akansa ne, kuma shi ya karbe min wayar ai”
“Safeena ma zata iya, zuciyarta bata da kyau kuma ta san yadda nake sonki, a fada mata idan har zan sake yin aure a rayuwata to mace daya zan aura kuma ke ce Noor, idan har ban same ki ba, ba zan sake aure a rayuwata na hakura, idan ma na rayu hakan kuma ba zai hana na yi miki fatan auren wanda kike so ba kuma zai rike ki amana Noor ina son farincikinki a duk halin da zaki samu kanki i love you unconditionally, i never knew it could be so much, ina rokon Allah ya ba ni aron rayuwa i will spend every hour of every day keeping you safe, you're my favorite girl, na san wata rana zaki tuna da ni zaki so ni, sai dai babu tabbacin ina raye, but i will wait to capture your love, i will not give up”
Ta baki yake furta kalaman amman ta ido yake zuba mata su, ta kasa dauke idonta akan nashi, zuciyarsa ba isarwa na ta zuciyar da sakonsa, sanyin jikin daga numfashinsa ya fito ya shiga nasa sai ya saukar mata da natsuwa da take jin da kamar ta rasa. Kalamansa sun yi nasara gaskiyarsa ta yi tasirin sanyaya zuciyarta a yanzu kwakwalwar ta bude zuciyarta ta karbi sakonsa.
“Zan aure ka Kareem!! Ka tafi jinyar zaka same ni a yadda kake son na kasance, zan aure ka kuma na maka alkawari zan rike ďan da ka haifa da Safeena i will save you, i will make your life complete 100%, dan Allah Kareem na roke ka cutar da ni please don't let me down...”
Mafarki yake? Gaskiya ne? Ko dai suma yayi? Kuma tsananin kaunar Noor ta fara saka masa abubuwa