Showing 30001 words to 33000 words out of 215481 words
hanya, kamin su isa Kareem ya bi ta wani pharmacy ya siya mata magani ciki har da na zafin kafa saboda tafiyar da tace masa ta yi a jiya.
NOOR POV.
Ban kwanta ba sai da na rama sallah magariba da ban samu yi ba saboda tafiyar da na yi a kafa zuwa gidan Kareem sannan na kwanta a dakinmu tare da Hana, washe gari na farka da asuba, da kaina na warware hannuna saboda alwalar da zan yi na ji azaba sosai amman a haka na daure daman karfin hali rayuwata ce, Hana ce dai da bata saba da wahala ba ta tashi da zazzabi saboda dukan da Baba yayi mata. Mama ita ta yi shararta da safe bayan ta gama hada mana abun karyawa. Ina zaune dakinmu ina ji sallamar yaro Mama ta amsa Baba dake daki kwance yana sauraren redio kuma ya kashe radio yana sauraren abun da yaron yana fada.
“Wai Zafeer ya ce a ga sako a abawa Noor kuma yace yana waje yana sallama da ita”
“Toh shiga ga dakinta can ka kai mata”
Na ji Mama ta fada, sai yaron ya iso bakin kofar dakinmu yayi sallama, na mike tsaye na amsa sai ya shigo rike da katon kwando ya aje min.
“Gashi Wai Zafeer yace a kawo Miki kuma yace yana waje yana sallama”
“Toh”
Yaron ya juya ya fita ni kuma na dauki hijab dina na saka sannan ya bude kular dake cikin kwandon na duba kwai ne soyayye da plantain sai kamshi suke. Na rufe na fita ina jindadi na nufi waje cikin natsuwa, tsaye na same shi rike da wata ledar da ban san meye a ciki ba.
“Baby Noor ya jikin?”
“Alhamdullahi, kai ka aiko min da sako?”
“Eh na yi tunanin ko ba zaki iya cin abun da aka girka ba a gidan na saka aka shirya miki wannan”
“Na gade”
“Never mind, jiya na kwana da tunaninki a raina, na zo Mama tace kin kwanta, jiya ya bani kamar wani abu ya faru dake, sai na kasa natsuwa”
“Lafiya Kalau”
“Kin ji sauki? Ya hannu mu gani”
Na bude masa ya duba cike da tausayawa.
“Noor dan Allah ki daina wannan rashin jin nan bana jindadi yadda abubuwa suke faruwa dake, kuma bana son yadda Mama ko Baba suke miki hukunci, kuma Noor please bana son na sake ganinki da mutumen nan, bana son na sake jin wata alaka tsakaninki da shi”
“Bafa komai tsakanina da shi, kawai shi yace abokina ne wai, na fada masa ina da saurayi ina da wadda zan aura”
Ya daka min tsawa.
“Wane irin aboki? Abota ake mace da namiji ne? Kar na sake jin sunansa ma na fada miki ko?”
“Eh na daina”
“Good karbi wannan magani ne na siyo miki na sha da shafa”
“Toh na gode Sosai Zafeer ina sonka sosai”
“Ina sonki Noor, ina sonki irin son da baki taba tunani ba, irin son da idan na rasa ban san wane hali zan shiga ba”
“Ni ma idan ba kai ba ba zan auri kowa ba”
“Ko ma kin yi auren ba zaki zauna ba, babu wadda zai iya dawainiya dake Noor sai ni kadai, da zaki auri maza dari Noor ba za su iya dake ba sai Zafeer ke tawa ce har abada!!!”
Na yi murmushi ina jindadi shi kuma ya mika min ledar na karba yayi min murmushi sannan yace.
“Allah ya baki lafiya, shiga ciki kar ace kin jima a waje”
“Toh”
Na masa waving na dawo cikin gidan, a tsawon shekara uku da muka yi tare da Zafeer ba zan iya fadar ranar da kaunarsa bata karuwa a zuciyata ba, kamar yadda ba zan iya bayyana yadda yake kaunata ba. Soyayyarmu da shi wani abu mai rikitarwa, duk yadda iyaye suke gajiya da ni shi be taba gajiya da ni ba. Ko da na shiga dakin na samu Hana ya bude wasu abubuwa tana ci, ban ce mata komai ba na dauka ka kasa na cirewa Mama da Baba na su sannan na zubawa Hana na ta na fara cin biredin kamin na fita waje na dauko kofi na zuba tea dake cikin karamin flask na fara tsomawa kamar mai cin tuwo da miya. Ina gama cinyewa wani yaron ya shigo yana sallama da Baba, ina jin lokacin da ya fita be dade ba na ji ya shigo da baki yana kiran a dauko tabarma. Tashi na yi na fara lekawa waje a hankali ashe sara na yi kan gaba, idona ya sauka akan na Kareem dake kallon kofar dakinmu kamar ya san a nan nake rayuwa. Murmushi ya sako min sai na yi saurin komawa na zauna gudun kar Mama ko Baba su ce na yi laifi.
“Noor... Fito ga Alhaji ya zo ganinki”
Na dauki Hijab dina na saka na fito waje n zauna. Na gaishe su cikin natsuwa suka amsa mutumen da ya kira ni da Amarya a office din Kareem ya amsa yana murmushi kamar ya san ni.
“Lafiya Kalau Noor ya jikin?”
“Lfy kalau”
“Waya ce ki warware?”
Kareem ya tambaya cike da kulawa yana kallon hannun nawa kamin ya koma kallon fuskata.
“Idan zan yi sallah ruwa be tabawa”
“Noor..”
Sai yayi shiru wata kila yana gudun Baba yayi min fada ne. Murmushi yayi min sai na sauke kaina kasa ina murmushi.
“Noor me kika ci haka bakinki duk maiko”
Abokinsa ya tambaya sai na kai hannu na taba bakin cike da kunya domin ban san maikon ya bata min baki ba.
“Ai kazamar Budurwa ce nan”
Cewar Baba yana kokarin kunyata ni. Abokin da ban san sunansa ba yayi dariya ya ce.
“Aa Baba mantawa ta yi dai da alama, gashi nan ta gyara muku gida ko'ina an share fes”
A nan kam na yi sa'a Baba be tona min asiri ba, yayi dariya kawai yayi shiru.
“Ni sai nake ganin kamar na sanka, amman dai ba zan iya tunawa ba ashe nan ne gidanka”
“Ikon Allah zai iya yiyuwa ka san ni Wallahi, ai da yake ku masu arziki ba tuna talaka kuke ba, amman na yi mamaki”
Mutumen yayi murmushi yana cigaba da fadar.
“Haba Baba wadda ke da irin wannan gidan za a cewa talaka sai dai mai rufin asiri”
“Yaro ai haya nake a nan ba gidana ba ne, tukuna na dai”
Mamaki ya saka na kalli Baba da sauri jin yana fadar gidan da muke ciki ba gidansa ba ne.
“Allah yayi budi, yanzu kuna biyan nawa a wata kamar wannan?”
“Toh da dai talatin ne, amman wannan shekarar na ji yana fadar zai maida shi dubun hansi, saboda halin rayuwa”
“Allah ya bada yadda za'ayi”
Baba ya amsa da Ameen, duk abub da ake idon Kareem yana kaina, idan muka hada ido sai ya sakar min murmushi. Sai daf da za su tafi sannan ya ba ni ledar magani ya bude ya nuna min yadda komai yake.
“Baba ka bincika, mu ji gidan idan be fi karfinmu ba sai mu siya zai fi biyan haya”
Cewar Abokin yayin da ya kai tsaye, Kareem ya kalleshi da sauri ni ma na kalleshi baki sake ina mamaki Baba kuma ya mike tsaye.
Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*
✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧
𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆
*Talla👇👇👇*
KINADA DAYA DAGA CIKIN WADANNAN MATSALOLIN ❓👇👇👇
To kiyi saving numba ta ki danna wannan link👇 https://wa.me/message/N2S6DQEPETKQO1 Idan kinyi saving ki fadamun zanyi SAVING TAKI😍ko Baki Siya yanzu ba WATARANA zatayi maki AMFANI👇👇
1.INFECTION CIWON SANYI 👉LALACEWAR BREAST👉RASHIN HIPS & BUTT👉KIBA TAYI MAKI YAWA KINASO KIYI SLIMMING👉TUMBI YAYI MIKI YAWA KINASO KI RAGE ?👉 AKWAI KUMA INGANTATTUN KAYAN MATA APHRODISIACS MASU KYAU DA INGANCI GA kUMA SABAYA ASALIN MAI KYAU 3500 only 👌
KIZO KI GWADA KAYAN AMNOOR INA TABBATAR MAKI BAZAKIYI NADAMA BA 👉 KIYI SAVING NUMBER TA DM ME https://wa.me/message/N2S6DQEPETKQO1
*Chapter - 10*
“Dan nan? Kai kam uwar da ta haifo ka ta iya haihuwa, Allah mai iko na gode na gode Allah ya saka da alheri”
Baba ya kai kasa yana masa godiya har da kuka, ni kam mamaki ya hana ni rufe bakin sai kallon ikon Allah nake. Muna hada ido da Kareem na sauke kai kasa na bata fuska, domin abun da Baba yayi be min dadi ba, ina jin yin haka ba daidai ba ne. Sai dai ba babu bakin yin magana baba ya dafa ni danya ya cinye. Kareem ya sauke hannunsa a hankali kasa yayi yana motsa agogonsa har sai da na dago na kalleshi sai ya daga min gira daya irin na wadda ke tambaya a boye. Ban ce komai ba daman ni me zance a gaban Baba ko ba a gabansa ba ne na riga na daina duk wani abu da be shafe ni ba.
“Baba anjima Nabill zai kawo Noor asibiti a sake daure hannu saboda ba son a kwance har sai ta ji sauki, kuma kar ayi wasa da maganin da na kawo”
Na ji Kareem yana fada, sai na lake kafada daya bacin ran nawa ya kara bayyana na saka kuka a take.
“Aa Wallahi ni bana so, akwai zafi sosai”
“Aa ba sake taba hannun za'ayi ba, daurewa kawai za'ayi”
Ya amsa min hakan be canja kudurina ba na girgiza masa kai.
“Ni dai bana so a bar shi a haka”
Baba ya juyo kaina kamar mai jirana.
“Aiko sai kin so, ka ga sakaryar yarinya ko? Haka ta da sakarci, ba da zafi ake cire zafi ba, shashashar yarinya kawai”
Kareem ya kira sunan Baba a hankali sannan ya ce.
“Baba dan Allah ku daina kiranta da sunaye marasa kyau, kamar yanzu kace mata sakarya, su iyeye kamar wani bakin tabo ne a jikin farin tufafi duk yadda ya diga sai ya bayyana, shiyasa ake son a rika taka tsantsan da kalami, yara basa jin magana mun sani dukanmu muna da su, amman a haka muke kai zuciya nesa idan ba haka ba, sai mu yi barna kuma a karshe dai mu din ne za mu wahala, misali yanxu kana kiranta mahaukaciya to ba zata taba yin hankali ba, ko da kai mutanen unguwa ne suke mata wannan ikirarin balle mahaifi. Amman fa ka yi hakuri na shiga tsabgar da ba tawa ba”
“Aa ai gaskiya ka fada, haka ne Wallahi ai bakin ne ya saba kuma ita wannan Noor din idan ka zauna da ita na wuni daya, In Shaa Allahu sai ka ji ta gundureka saboda bata jin magana sam, shiyasa ma nake so na aurar da ita na huta”
Na kalli Kareem sai na rufe idona ina jin kunya ta rufe ni, ta dayan bangaren kuma ina jindadi, ni kaina ai na fi son ayi min auren ma na huta domin na san Zafeer ba zai min abun da ake min a gida ba, shi ba zai taba gajiya da ni ba.
“Baba yanzu, Noor tana da wadda zata aura kenan?”
Abokinsa ya tambaya. Sai Baba ya ce.
“Shekara uku da yin baikonsu kuwa, amman har yanzu be shirya ba, ni ai idan be gama shiri a cikin lokacin nan ba to sai dai ya hakura da ita domin so nake na aurar da ita In Shaa Allah, Yaya yayyuna da suke kauye sa'aninta duk an musu aure”
Na bude ido ina kallon abokin da ya kalleni yayi murmushi sannan ya juya yana fadin.
“Gaskiya kam idan ka aurar da ita hankalinka zai fi kwanciya, ita daman ya mace gidan aure aka santa”
“Shiyasa ai nake son ayi komai na huta ta huta”
Allah ya gani ni dai sai na ji na tsani abokin Kareem din nan ko ma dan'uwansa ne oho domin ya bawa Baba shawarar da ba zata taimaka wajen gyara soyayyata da Zafeer ba sai dai ma ta bata abun.
Suna daf da ficewa Kareem ya juyo ya dago min hannu kasa kasa. Ni dai kallonsa kawai na yi ban yi wani Yunkuri ba har ya fice. Fitar ke da wuya Mama ta fito daga dakinta da ta boya ta zauna a inda suka tashi tana fadin.
“Malam an samu hanyar kudi ina jin suna magana, baya ko tunanin gaskiya ta bayyana ya ji kunya”
Hana ta fito daga dakinta ita ta zauna kusa da ni tana fadin.
“Mama ai kara da yayi haka wa zai bari wannan damar ta wuce shi haka”
Mama ta tabe baki.
“Kudin me za su amfana mana Hannatu? Ai ba za su wuce ya bamu na cefane, sauran kuma idan be kara aure ba, su kare a gurin zaurawansa tun da Allah be raba shi da ganin mace ya ce yana so ba, ko ba shi ko sisi kuwa balle wata hanyar ta bude”
“Shi ne kawai abun da yake bata min rai da Baba, wasu iyayen idan suka samu sai ka ga iyali sun wadata amman shi babu ruwansa da mu”
Ni dai ban ce komai ba gudun kar na saka baki na fadi wata maganar ace na bata ran Mama ko Hana. Can na ji Mama ta ce.
“Ni ko wannan mutunen sai na ke jin kamar da biyu suke mana wannan dawaniyar”
Na kalli Hana dake tambayar Mama
“Kamar Yaya Mama?”
“Ta ya mutum zai shigo cikin gidanku haka nan kawai yace zai siye muku gida? Ko dai yana son ya bukaci auren Noor ne ko kuma wani abun dabam haka siddan kace zaka siyawa mutum gida daga zuwa? Kalli yadda yake kyautar kudi kamar tsintarsu yake”
Na kalli Mama.
“Ya san ina da Miji na fada masa ina da Miji, kuma ya san Zafeer har ya kira min a waya lokacin da wannan abun ya faru”
Mama ta bude baki ta sake magana sai ga Baba ya shigo baki har kunne.
“Kai kai kai Noor yau dai rashim jin maganar nan naki ya janyo mana alheri, gidan nan zai siya min, Allahu Akbar masu arziki na inda suke, ina ma ace ďana ne wannan yaro”
Mama ta ce
“Shi ma danka ba mu cire rai ba, wata rana inda rai da rabo zai maka komai Malam”
“wannan Nabil din ko ya samu ai sai dai ya bawa uwarsa, ai baya kaunata sam bana saka rai ma”
Ban yi furucin Baba ba, daman shi be yarda yayansa za su iya kawo masa abun arziki ba musamman ma ni.
“Yanzu Malam yarda ka yi ka karbi kudin gidan da yake naka? Wannan abun da ka yi zubar da girma ne be dace ba”
“To... Wato na bari rabo na ya wuce ni kenan? Amman dai Hajara ba ki da hankali garabasa ce fa wannan sai kuma na bari ta wuce ni?”
Mama ta sauke ajiyar zuciya.
“Indai domin Noor yake yi Noor tana da miji, ba za mu watsar da zancen shekara uku mu zama kananan mutane ba, be kamata ba Wallahi, yaron nan yana sonta kuma yana iya kokarinsa akanta”
“Kokarin me yake da ita? Tun da nake da shi ya taba daukar dubu goma yace Baba gashi ka siya wani abu? Shi dai yana sonta kawai amman babu wani hidima da yake, kuma na zancen aurenta da yaron nan kika ji na yi ba har kike wannan maganar ke dai kam Hajara ba dan ina mijinki ba sai na ce hassada kike min, ke dai baki farinciki da samu na, ba ki son jin alherina, ina zaton ganin farinciki a fuskarka sai ki tare ni da wani zancen banza karuwa da zane! Ai da har ina cewa ko zane daya ne ya kawo ayi musu aure to yanzu na fasa yayi mata komai kamar yadda ake yi ma kowa, yau din nan zan kira shi na fada masa na shirya aurar da Noor, kudin gidan nan da za a bani ai sai na tsakuri wani abu a ciki na yi mata hidima sauran kuma na yi lalurar dake gabana, ba a bori da sanyin jiki kuma ice tum yana danye ake tankwara shi idan ya shirya ya fito kawai kamin kudin su kare”
“Malam ina fada maka gaskiya ne kawai bana adawa da samunka, duk mace ta gari tana burin samun Mijinta musamman idam yana kyautatawa a gidansa”
“To ni bana yi, Wallahi ba dan yau ina cikin alheri ba babu abun da zai yana na bata miki rai yanzu nan, shashashar mata kawai”
Ya ciro wayarsa yana fadin
“Bari na kira dan iskan yaron nan ko yanzu sai da Alhaji yayi min maganarsa, kuma duk laifinki ne ke kike goyo masa bayan yi min rashin kunya”
Ni dai ba zan iya cigaba da sauraren jin tsabani da sa'insa tsakanin uwa da uban da suka kawo ni duniya ba, dan haka na tashi na shige dakinmu na kwanta ina kallon ceiling, wata zuciyar na fada min idan ma taimako Kareem yake son yin to ba Baba ya dace yayi ma.
KAREEM POV.
Sai da suka shiga mota sannan Kareem ya kalli Hafiz ya ce
“Miye dalilinka na yin haka?”
Hafiz ya kalleshi kamar be san abun da yayi ba.
“Me ba?”
“Siya masa gida mana”
“Oh taimako ne, after ma na siye zan gyara masa shi, ina da halin yin haka ya kamata na yi”
“Me yasa baka yi ba tuntuni sai yanzu”
“Saboda Noor ne”
Hafiz ya kure tambayarsa dan haka yayi shiru ba dan ya gamsu ba.
“Wai ni kam ya aka yi kace a kawo maka Noor?”
Hafiz ya tambaya yana taba agogonsa.
“Na ga alamar kamar tana son magana ne, kuma tana tsoro, and gaskiya ne ai dole za a sake daure gurin saboda kai ya ki warkewa”
Hafiz yayi murmushi. Sai Kareem ya ce.
“Ba abun da kake tunani ba ne Hafiz, ba zan iya neman aure a cikin aure ba, Annabi ya hana, na san yadda ake ji idan ka rasa wadda kake so, ba zan yi kuskuren aikatawa wani ba, na auri wadda bana so ban ci da dadi ba, na bar wadda ke so na hakan ya jefa ni a matsala ba zan so hakan ya faru da kowa ba, indai saboda ni kake yi dan Allah ka daina Hafiz”
Hafiz yayi kamar ba da shi Kareem yake magana ba ya kawar da kai dayan gefen yana jin haushin yadda abokinsa yake fadar Amnabi ya hana amman shi yake aikata abun da kisan kai da shirka sai yi da wani ne ya fi shi zubuni. A gida ya sauke Barrister sannan ya kama hanyar zuwa gurin aikinsa. Be fito asibitin ba sai karfe biyu, gidansa ya nufa kamar yadda ya saba