Showing 99001 words to 102000 words out of 215481 words

Chapter 34 - Ƙaunar Da Ta Zama Azaba by 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

aurenka da ita a yau Hafiz...”

“Amman kansan bana gari ina hanyar dawowa, na maka alkawari Kareem ina dawowa gidansu zan sauka zan daukota mu tafi gida tare, hakan ya maka..?”

“Yayi, thank you my friend”

“Ka fi karfin haka, amman ban taba jin ranka ya bace irin haka ba, baka taba bani umarni ko rokona wata alfarma irin wannan ba”

Kareem ya sauke ajiyar zuciya shi kanshi ya san he's too harsh for his friend, abun da be saba ba.

“ABun ne naka ya daure min kai Hafiz, na rasa gane ma kake nufi fa yarinyar nan, kuma a rasa wanda zai fada maka abun da ka aikata ba daidai ba ne ko Mama ko Baba”

“Babu wanda ya san ya sake ta sai Aisha ita kuma na gargadeta kar ta fadawa kowa, Mahaifinta kuma na fada masa zan waiwaye shi, tun daga lokacin ban sake amsa wayarsa ba”

“Ka bar abun da ya wuce ya wuce, a fuskanci gaba ita kanta a yanzu na san ta yi sanyi ba zata yi maka laifi ba, sai dai hakan ba zai saka na kasa fada maka ka yi hakuri da Noor ba, ba zan ce ka daina bawa matarka yarda 100% ba, na san maya suna sa wuyar fahimta wuyar sha'ani, but still ka rika bincike kamin ka aiwatar da abu, ka daina compare Noor da AISHA Noor yarinyar kuma bata san komai ba akan aure, Aisha kuma ta waye ta san komai ka tuna ba kai ne first husband dinta ba, kuma Aisha ta yi karatu har degree ba zaka hada ta da Noor da bata ma son zuwa makaranta ba, bawa ta irin wannan wayewar da duniyancin da yan matan yanzu suke da shi, and kishiyace ta koro Aisha daga gidan mijinta na farko, abu ne da ka san shi na san shi, har abada na zata taba son kishiya ba, babu ma macen da zata so kishiya you should think about it Hafiz”


“Hmmm...”

Kawai Hafiz yace, hango soyayyar Noor da yake a zuciyar abokinsa ne ya hana shi walwala da bude mata nata shafin soyayyar a zuciyarsa, yana rayuwa da matar da ba shi ya kamata ya aureta ba, kuma matar da abokinsa amininsa wanda ya zama dan'uwansa yake sonta, kuma a haka ita kuma a zuciyarta tana son wani dabam ba shi ba.

“Sai na dawo...”

Ya fada sannan ya kashe wayar. Kareem ya sauke ajiyar zuciya ya yi ma motarsa key ya karasa restaurant. Yana shiga office dinsa Cashier ya shigo suka fara lissafin abubuwa da suka kamata. Be fita ba sai 6pm Kareem ya saka aka kawo masa coffee ya sha saboda ya samu sauki stressed, domin jin yake jikinsa ya mutu gaba daya har wani abu yake ji kamar bachi kamar ba bachi ba.
Be bar office din ba sai da aka fara kiran sallah magariba. Yana fitowa sallah kira ya shigo wayarsa, yana ciro wayar ya duba. Number Hafiz ce ba tare da wani dalili ba gabansa ya fadi, babu tsoro ko fargaba amman haka zuciyarsa ta rika bugawa da mugun karfi yana ta kallon wayar tana ringing har ta katse ya kasa amsawa. A karo na biyu da aka sake kiran sai hannunsa da zuciyarsa suka hau rawa.

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un”

Ya furta domin be taba jin yanayi irin wannan ba, haka kuma Hafiz be taba kiransa ya gagara amsa wayar ba a yayinda take rike a hannunsa sai yau. Sai da aka sake kira a karo na uku sannan ya iya amsa wayar.

“Hello”

“Assalamu Alaikum... Barka dai”

“Barka ina mai wayar?”

Ya tambaya yana jin kirjinsa na masa wani irin nauyi.

“Wayar ya samu hatsari a hanyarsa ta shigowa garin Kano, mun samu wayarsa a motarsa sai muka bude da fingerprint dinsa, da muka shiga log calls na sa sai muka samu number ka ne da yayi waya da ita last”

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un... Yana ina?”

“Mu sami'an kula da hadarukka ne, yanzu haka muna hanyar asibitin Malam Aminu Kano ne tare da shi”

Kareem ya yanke wayar da sauri ya nufi motarsa da gudu ya hau motar ya taka titi kamar wanda baya son rayuwarsa. Kamin su isa asibitin har ya rigasu ya fitowa motarsa ana fitowa da shi daga motar Road safety. Da gudu ya nufi abokinsa dake numfashi daker jini na fita ta cikin kansa.

“Hafiz... Hafiz...”

Haka ya bi gadonsa da aka dora shi akai aka wuce da shi ICU, Kareem ya dora hannu saman kai kamin ya sauke ya nufi motarsa, wayarsa ya dauko ya kira mahaifin Hafiz, yana dagawa ya ce.

“Hafiz din ya rasu ne?”

“Aa yanzu suka shigo da shi, Baba kar a fadawa Mama dan Allah”

“Tohm ni ma ai sun kira ni, gani nan hanyar asibitin”

Ya sauke wayar ya kira mahaifinsa ya fada masa. Yana sauke wayar wani likitan da ya san shi ya fito ya dafa Kareem.

“Doctor Kareem, Mutumen yana son magana da kai, ka shiga ka ganshi ka yi abun da ya dace...”

Kareem na jin haka gabansa ya tsinke ya fadi, domin shi ma likita ne ya gama fahimtar yaren na su. Cikin rashin kwarin guiwa ya shiga sai ya samu likita uku da Nurses suna kokarin tsayar da jini dake ta zuba amman sun kasa, not because of ba su iya ba, sai dan lokacin tafiya yayi mai ajiya zai karbi abarsa, dabara bata tare damuwa.

“Kareem... Allah yayi ba zan samu cika maka burinka ba, ba zan samu dawowa na tafi da Noor ba, ka gyara inda kake ganin na bata, ka san son yarinyar nan Kareem na ga haka a idonta da aikinka, na so ka da farinciki ne shiyasa na so ka aureta, ko yanzu lokaci be kure ba, dan Allah ka auri Noor Kareem ka samawa kanka farinciki, ga Iyeyena nan na bar mana amanarsu, ga Yayana ka ce a kula min da su, na yafewa kowa ka ce kowa ya yafe min, ba zan tashi ba, na san me nake ji na san me nake gani lokacin yayi babu tsayawa...”

Magana kawai yake ba dan yana ganin kowa ba domin an yanke ganin, ana saka masa oxygen yana cirewa yana magana daker. Kareem ya rike hannunsa yana kuka.

“Yaushe Momy ta tafi, ban gama warkewa daga ciwonta ba zaka tafi ka bar ni Hafiz?”

Hafiz ya cire Oxygen din zai yi magana bakinsa ya cika da jini. Sai ya fara kalmar shahada yana tari jinin yana koma masa yana sake fitowa. Mahaifinsa na shigowa wa'adin yana cika rai yayi halinsa Hafiz ya amsa kira...

PAID PAGE 1️⃣3️⃣


©KhadeejaCandy
©®Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....


You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153


_______•••_______


Wani abun da Kareem be sake yi ba shi ne hawaye. A gaban idonsa ran abokinsa amininsa abokin shawararsa ya fita. Ya saba ganin mutuwa ya saba sanar da ita ya saba jinta but this one is different mutuwar Hafiz ta yi hitting dinsa in a different way, na farko a lokacin da be yi tsammani ba, kuma a gurin wanda be sakawa ba, mutuwar Momy ta zo masa da sauki domin ta yi ciwo kamin ta rasu, and ko da yaushe tana yawan fadar zata mutu zata mutu tana kan tunatar da su idan sun manta. Amman abokinsa da yake lafiya kalau suka yi waya a hanyarsa ta dawowa har yayi masa alkawarin dawowa da Noor, ta yi hitting dinsa so so so bad. A hanyar da be yi tsammani ba, what a lost, this is a great lost to him ya rasa RAI BIYU within a year...
Ya rasa uwa ya rasa babban amininsa.

Har kara ma mutuwar Momy ya samu zubar da hawaye yayi kuka a lokacin da ya kebe kansa amman mutuwar Hafiz ta yi hitting dinsa in a way da ta tare hawayensa ta tare zuciyarsa daga kuka tun daga asibitin da mahaifinsa yake kuka har aka dauko gawarsa aka dawo da ita gida gurin iyayensa yan'uwa da matarsa suka rufe gawar da kuka shi kam ko kadan hawaye be kusanci idonsa ba. Kuma ta hana idanuwansa runtsawa a lokacin da ya kwana tare da gawar abokinsa domin yin masa sallama ta karshe.. Da kansa ya wanke abokinsa yayi masa sutura sannan aka jira wayewar gari domin kai shi gidansa na gaskiya.
Suna fitowa daga sallah azuba ya shiga cikin gidan ya tambayi mahaifiyar Hafiz ko an sanar da Noor.

“Aa ba a fada mata ba, jiya na tambayi Aisha ya ba su zo tare ba sai tace wai tana gidansu ta tafi kusan sati uku bata gidan”

“Ya kamata a sanar da ita, hakki ne a fitar mata da shi...”

“Aisha tace sakinta yayi, amman be fada mana ba, ko ka sani”

“Haka ne, amman tana da hakkin a sanar mata... Mama ki aika a daukota”

“Toh ko zaka tafi tare da Raliya sai ku taho da ita, tun da kai ka san gidan”

Yayi shiru kamar yace a a sai kuma ya amsa mata da kai ya ce Raliya ta tashi su tafi. Karfe 6am daidai suka faka a kofar gidan.

“Shiga ki musu magana”

“Tohm...”

Ta amsa tana kuka sannan ta bude motar ta fita.



NOOR POV.

Muna tsaka da tafiya sai na ga sun yi nisa sun bar ni, yana rike da hannun uwargidansa Aisha ita kuma tana rike da hannun yaranta. Gajiya ta saka na zauna a gurin da suka bar ni mai tsananin turbaya da jar kasa, sai dariya nake sun yi nisa sosai kamin Hafiz ya juyo ya kalleni a lokacin ne ya hankara bana tare da su sai ya rugo a ruje ya nufo inda nake yana rike da hannun Aisha ya karaso kusa da ni yana numfashi daker.

“Noor taso mu tafi...”

Ya miko min hannunsa sai na daga kai na kalleshi sannan na mika masa nawa hannun zai kama kenan kasar da yake tsaye akanta ta bude ta rusga da shi ya fada, sai ya bar mu a gurin ni da Aisha muna kallon ramen da ya fada, ita tana rike da yaransa ni kuma ina daga zaune a gurin domin be kai ga riko ni ba ya fada. Dariyar Aisha ce ta dawo da hankalina zuwa gareta kamin ni ma na fara dariyar sai na mike tsaye. Ban lura ba ashe saman wani tsaye nake tsaye mai tsananin tsawo da saka jiri. Tangal tangal na fara kamar zan fadi sai na ji wani ya rike ni ta dama, yana sakina ya fara tangal tangal wani ya rike ni daga hagu, yana sakina na sake komawa yar gidan jiya, sai kuma na ji an rike ni ta baya, kamin na ji wani dabam kuma ya rumgume ni a kirjinsa, a chest with full of hairy chest har yana shiga min baki.

.....Firrrrrrr gigit na farko daga bachin wahala da kuma mafarkin da na tabbatar ba na kwarai ne, domin mafarkin dariya yana nufin bakinciki ga mai yinsa sai dai ta inda ban fahimta me yasa ni da Aisha muke dariyar? Kuma su waye suke rike ni? Waye wanda na kwanta a kirjinsa. Tashi na yi na alwala na rama sallah sannan na gabatar da sallah asuba ina jin fuskata na min yaji saboda dukan da Yaya yayi min ya ji min ciwo a kumatu da gafen ido har ma da saman bakina. Na jingina kadan ina lazimi da hannuna na ji an buga gidanmu, Yaya ne ya bude bana jin me ake cewa amman tabbas na ji yana fadin.

“Eh tana nan”

Sannan ya kwala min kira na tashi da sauri da kuzari na fita gudun kar na yi laifi. A tsakar gidan na yi arba da kanwar Hafiz, domin Aisha ta gabatar min da su a lokacin da suka zo ina amarya haka ma a burin Walima mun hadu da juna. Hawayen da na gani a idonta ne suke min magana ba bakinta.

“Yaya Kareem yana waje ya ce ki zo mu tafi”

Na nufi kofar babu talkami a kafata na fice daga gidan zuwa kofar waje. Kareem ya na samu jingine jikin wata bakuwar mota ya rumgume hannayena yana kofar gidanmu.

“Hafiz ya rasu...!”

Na fada domin a yanzu na gama fahimtar mafarkina.

“Ban fada mata ba”

Na ji kanwarsa ta fada daga bayana. Juyowa na yi na kalleta.

“Na sani, na gani a mafarkina na gani jiya ya saki hannuna ya zo zai kama ni sai wani rame ya bude ya fada da shi, ya saki hannuna da na Aisha, ya tafi ya bar ni ina tangal tangal, wayyo Allah na, na shiga uku wayyo Hafiz...”

Na ruka zan kai kasa sai kanwarsa ta rike ni ni da ita muka fashe da kuka mai karfi.

“Karfe 8am za ayi masa sallah, you need to be there kamin a tafi da gawarsa”

Kareem ya fada ganin kukan na mu ba mai karewa ba ne. Yaya ya leko yana ganin Kareem ya gaishe shi, sai Kareem ya ce.

“Ka fadawa Baba Allah yayi ma Hafiz rasuwa jiya da dare, sakamakon hatsarin da yayi a hanyarsa ta dawowa daga Kano”

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un”

Yaya ya fada ya juya ya koma cikin gidan, Kareem kuma ya bude mana mota ni da ita muka shiga baya. Yanzu ta ina zan roki gafararsa ya tafi be fahimce ni ba, ina jiran tsammanin zuwa ko aikowa a dauke ni sai labarin mutuwarsa ya riske ni a yanzu.

“Ni ma tawa rayuwar ta kare...!”

Wannan kawai na iya furtawa ina kuka bayan haka ban sake fadar komai ba har muka isa gidan. Gidan ya cika tam da mutane amman ba cikar farinciki ba domin kowa kuka yake da jimami. Haka na fito motar babu talkami a kafata kanwarsa ta ja ni ta shiga da ni har gurin da gawar take. Sai ta ja ta tsaya daga bakin kofa ta ni kuma na kwance, yana kwance cikin kagara an masa sutura amman likkafaninsa yana jike da jini. Ban taba arba da gawa ba sai a ranar domin ban taba rasa kowa ba, ban rasa uwa ba ban rasa uba na ban rasa yaya ko kanwa ba. Ban san ya zafin abun yake ba, ban taba zauna a daki daga ni sai gawa ba sai yau. Ashe mijina ne farkon abun da zan fara rasawa a kananan shekaruna... Ban taba sanin idan mutum ya mutu abubuwan da kake masa marar dadi ne suke zuwa su tsaya maka a rai ba sai yau.

Yadda yayi ta kokarin kaiwa ga jikina ina hana shi da ihu da kokawa ne ya tsaya min a rai, ya saka ni fasa ihu ya saka ni rawar jiki, me yasa ban bari ya kai ga abun da yake halalinsa ba? Me yasa na biyewa Aisha da tsoro har abubuwa suka zo mana a haka? Ashe zaman ba mai tsawo ba ne ko da na zauna a gidansa ne. Wasu matane ne suka shigo suka fitar da ni, ina wani irin kuka da ban san ina yi ba, sai hakuri suke ba ni suna rarrashina amman ji nake kamar suna cewa bude baki ki yi kuka sosai Noor yau ranar kukanki ce.

Ni dai na san bana son Hafiz amman kuma ba kinsa nake ba, amman a ranar na ji tausayinsa kuma na ji tausayin kaina, ban gane haka ba sai da aka fito da gawarsa za a fita da ita domin yi masa sallah. Ban san ya aka yi ba na isa gurin na ratsa cikin maza na rike makara, ina kiran sunansa kamar ance zai iya amsa min. Daker aka banbare hannuna daga jikin makarar su kuka ni kuka ana rike ni aka fita da gawar mijina wanda shi ne duniyata a yanzu.

Ban kara raina kaina ba sai da aka kai shi gidansa na gaskiya aka dawo, maza suka shigo cikin gidan domin yi mana gaisuwa, ashe wata kalar azaba ake ji idan aka yi maka gaisuwar wanda ya rasu. Allah ya jikansa yayi masa rahama ya raya abun da ya bari haka kowa yake ta fada. Cikin taron masu yi mana gaisuwa Mama ta kutso ta shigo ta iso inda nake ta zauna sai ta saka hannunta biyu ta rika fuska.

“Yi hakuri Noor yi hakuri”

Ta fara karanta ayatul kursiyu ta tofa min a kai ta busa ido. Ban sani ba ashe ba daidai nake kallon mutane ba, idanuwan nawa juyewa suka yi ina kallon mutane a baibai. Ta rumgume ni tana kuka, sannan yan'uwanta da na Baba suka shigo suka zauna suna gaisuwar kamar yadda yan'uwan Aisha ma suke cike a gidan, ita ma kuka take tana gurnani ko'ina ana jinta sai hakuri ake bata wasu na addu'ar Allah ya sauke ta lafiya. Ni kuwa a zuciyata ba ni da makiyiya irin Aisha domin ita ce silar duk wata fitina a gidan Hafiz, ashe ma ba dadewa zai yi tare da ni ba, me yasa ta zuge min kunne bata bar ni na yi zaman aure kamar ita ba? Amman laifin ba nata ba ne nawa ne miyasa na dauki zugarta? Why?

Har aka yi addu'a uku ban daina ganin laifin kaina ba, kuma ban daina fargabar yadda rayuwa zame min ba bayan tafiyar Hafiz, na san kowa zai dora min laifi ne a gidanmu, kuma na cancanci haka ya kamata ayi min kowane kalar hukunci a yanzu. Na gane ba laifin kowa ba ne nawa, ni ce wawuyar da ban fahimci duniya ba.
Wani irin nauyi na ji an dora min ashe haka ko wace mace take ji idan ta rasa abokin rayuwa, ni kenan da ban dade da shi ba kuma ban haihu da shi ba ina ga wandanda suke da yaya kuma suka dade a tare? Wani abun da zan iya cewa tsana ce ko tashin jindadi na ga ganina fuskar iyayen Hafiz bayan sadakan ukun ita ce ta mutuwar auren.

Ina da tabbacin a cikinsu babu mai iya bada shaidar abun da ya faru indai ba Aisha ta fada ba, domin sun ce ba su san da sakin ba har sai da ta fada, amman sai na ga nuna min wani kallo, mahaifiyarsa na tambayar me ya hada mu har tana fadan danta mutumen kwarai ne mai mutunci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login