Showing 177001 words to 180000 words out of 215481 words

Chapter 60 - Ƙaunar Da Ta Zama Azaba by 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

Kareem ya lakawa Hafiz kin kashe shi da bakinciki, domin na san tunanin abun da kika masa ne ya saka shi hatsari, kika maida ni bazawar karfi da yaji kika maida yarana marayu duk hakan be miki ba sai kin kulla soyayya da ubana? So kike yi ki karashe shi ma? Kuma ki shirya masa karya”

Na mike tsaye ina murmushi.

“Na yi kishi da ya na ji yadda ake ji, shiyasa yanzu nake son na yi kishi da uwarta, kuma dole ace da mijin Iya Baba”

“Karya kike Wallahi, kin yi kadan ke a su wa? Har abada ba zaki taba wannan matsayin ba Wallahi, kuma ubana matansa hudu cif ba shi da gurin saka ki”

“Zaki gani idan zan yi matsayin ko akasin haka, mata hudu kuma ba matsala ta ba ne, uwargidan zai fitar ya saka ni, kuma da kike zance na saka ki a zawarci ai kin saba zawarci domin Hafiz ba budurwar ya aureki ba, shiyasa kika yi duk yadda zaki yi dan ki hana mu zaman lafiya saboda kar ya san banbancin dake tsakanin auren budurwar da kuma bazawara, ni ba ni na ga mahaifinki na ce ina so ba, ubanki ne ya ga abun da yayi masa ya biyo sawu kamar yadda mijinki ya biyo”

Farat kanwar ta yi ta fado dakin ta rufe ni da duka sai Aisha da dayar kanwarta da matar da suke tare suka fado suma suka fara min duka sai ihu nake ina maida martani a duk inda na samu, abun da ban sani ba ashe Mama ma tana nan tana min yaki a waje dukansu take ta ko'ina, wata cousin dita yar sister Mama ma ta shiga aka yi ta fafatawa da ita, sai da manyan gida suka ankara aka kawo mana dauki aka raba fadan. Kawu ya rufe Mama da fada wai madadin ta raba sai ta shiga ana yi da ita.

“Yaya ta ina zan tsaya su kashe min ita? Daga ita sai Nabil suke rage min, ina zan yarda su yi mata illa su bar ni da jinya da hannu a kai, kana ganinsu manyan mata da su sun fi karfinta ta ina zan tsaya raba su?”

Mama na fadan tana rika ni da duba hannuna da suka kusa karyawa.

“Wai ke ina kika janyo wadannan mutanen? Ke dai Noor Allah yayi ki da rashin jin magana Wallahi, ya aka yi suka san gidan nan kuma su waye su?”

Kawu ya rufe ni fada shi ma kamar zai min duka. Mama ta ce

“Aisha ce fa da kanenta Aisha matar margayi Hafiz”

Kawu ya rike baki, Mama Asiya ma mamaki ya shaki wuyanta.

“Ai ni ban gane ta ba, ya aka yi ta san gidan nan kuma me ya kawo ta? Ina ce mai rabawa ta raba? To miye na duka kuma?”

Mama ta fada musu komai kamar yadda na fada matan tun farkon fara zuwan Alhaji Sule unguwa uku a gidan. Kawu ya nuna ni da tsaya hannunsa na rawa kamar zai dakeni

“Ke yanzu ina ke ina tsoho? Ina ke ina kishi da uwarta? Ashe ke ce marar gaskiyar ma, kina girma hauka na shiga kanki? Ai duk abun da suka miki ke kika ja”

“Kawu ba fa ni na janyo shi ba, shi ya tare ni a hanya ya karbi number wayata kuma ban san mahaifinta ba ne sai daga baya, kuma Wallahi na yi blocking number shi ma”

Na fada cikin kuka Mama na ja min hannun. Sai bayan da komai ya laba sannan na dauki wayata na cire number shi daga blacklist na fita daga gidan gaba daya na shiga makota na kira wayarsa, ringing daya ya daga sai na fashe masa da kuka sosai.

“Ni ban ce ka je ka fadawa uwargidanka abun da yarka ta fada min ba, shiyasa na ce ba zan aureka ba saboda gidanka ya fi karfinka”

Yayi shiru irin na manya masu nazari, ina jin haka sai na kashe wayar. Ga ayi second biyu ba kiransa ya shigo na ki na daga, sai da ya sake kira sannan na daga na kara fashewa da kuka.

“Me ya faru Khadija?”

“Matakar ta aiko yarka Aisha da kanenta biyu sun zo har gida sun min duka, ni Mamana har Aisha na fadar wai ba Mamansu ta ce a fada min ba zaka taba aurena ba matanka hudu baka da gurin jefani, wai kuma so nake na koya maka zaman banza domin ba ta inda zaka aure ni daman na san ba aurena zaka yi, gashi ma ashe gidanka sun fi karfinka akan me uwargidanka zata aiko ayi min duka? Mi miye nawa a ciki? Ai kai ka gan ni kace kana so na ko?”

“Khadija”

Ya kira sunana a natse sai na kara narke masa da kuka.

“Ki yi hakuri, kuma ina son na fada miki ni Alhaji Sule gidana be fi karfina ba, kuma ban zo gurinki domin shashanci ba, aure nake sonki kuma shi ya kawo ni, abu daya zaki min a yanzu ki burge ni, ki amsa cewar zaki aure ni!”

“Na aureka taya? Mata hudu fa haka uwargidanka ta aiko a fada min, kuma idan ma na aureka na je matanka su rika min duka”

“Wallahi Wallahi babu wanda ta isa ta saka miki hannu Khadija, kuma zan tabbatar miki da haka, ki bawa Mama hakuri zan zo yanzu da kaina na ba su hakuri, kuma ki jira matakin da zan dauka”

“Amman da gaske zaka aure ni? Ni tsoro nake karka cutar da ni ba ni da kowa sai Allah sai Mamana da suka yi ma duka dazu, har kusan karya min hannu suka yi”

“Wallahi Wallahi zan aureki Khadija, idan ma kin amince cikin satin nan sai a daura mana, ni bana bukatar komai daga gareku, zan zo yanzu nan na bawa Mama hakuri”

“Toh sai ka zo”

Na kashe wayar ina murguda baki, daman bahaushe yace idan ka san me zaka fada baka san me zai dawo maka ba. Ba a jima ba Alhaji Sule ya zo gidanmu tare da abokinsa ya bawa Mama da yan gidanmu hakuri ya aje mana kudi mai kauri sannan ya tafi, ko be bani labari ba na san ba za'ayi mai kyau ba. A daren ne Zafeer ya sake sallamawa a gidanmu sai dai wannan karon ba da ni yai magana ba sai da ya shiga ciki yayi magana da Mama ban san me suka tattauna domin fita na yi na bar musu dakin.
A dakin Anty Amarya ina amsa facetime with Kareem. Fada yake few hours suka rage ya shiga da shi tiyata.

“Da dare za'ayi maka?”

“Mu nan safiya ce, akwai banbanci lokaci”

“Na maka addu'a sosai da dare, a kowace sallah ma ina maka, Allah ya baka lafiya Kareem”

“Amman baki min addu'a ki ce Allah ya ba ni ke, idan ni din alheri ne a gareki?”

Na dan yi shiru ina jin wani iri domin kudirinsa akaina ba zai ga ci ba, kuma ban san taya zan buda masa littafin ya karanta har ya fahimta ba.

“Babyna”

Kallonsa nake ba tare da na amsa ba.

“Zafeer ya sake dawowa ko? Kuma Baban Aisha ya zo?”

“Taya kake sanin duk wannan Kareem”

Yayi murmushi daya kara bayyana ramarsa.

“Karki da wannan, i just hope idan an yi min tiyata na tashi zaki min albishir mai dadi”

A kokarina na karfafa masa guiwa domin samun yin aiki a cikin nasara na daga masa kai na jadda masa zan tarbe shi da labari mai dadi.

“Ina fatar hakan, zan huta na tsawon kwana hudu, ba lalle na sake facetime dake ba sai na ji an samu results din da ake bukata, but what so ever dai i love you i want you to know that i know you”

Na yi murmushi ina jindadin furucinsa har cikin raina, for the first time na ji ina sha'awar kwantawa a jikinsa na rumgume shi mu yi bankwana amman babu dama, na shafa screen din wayar.

“Hey... No more tears, bana son na ga idonki da kuka, i love you so much”

Na share hawayen wasu na zubo min.

“Allah yasa ayi aikin cikin nasara Kareem get well soon please”

“I will”

Ya laka yatsunsa biyu a screen din wayar, ni ma na lika nawa a saitin nasa, ni da shi aka rasa wanda zai dauke ido daga barin kallon dan'uwansa, tausayin halin da yake ciki a yanzu da kuma wanda zai shiga idan ya tasa ni, ya saka ni zubar da hawaye kamar babu gobe. Ya maida hannunsa gurin bakinsa ya sunbanci yatsun ya sake lakawa saitin da nawa suke.

“Idan har na rayu na aure ki Noor, sai na mantar da ke duk wani daci da bakinciki da yake cikin duniyar nan, sai na saka kin gamsu cewar wata mace bata fiki gata da samun soyayya ba a gurin miji, zan so ki har abada Noor”

Na lumshe ido na maida lips dina na kaaa tsakanin hakorana ina tauna zafin rabuwar da ba mu riga mun yi ba.

“Noor ta so ana kiranki”

Na kalli Anty Amarya sannan na kalli wayar dake aje gabana.

“Zan tafi Kareem ana kirana”

“Okay Love... Fada min wani abu mai dadi kamin ki tafi”

“I love you”

Na fada with no hesitation, murmushi yayi ya shafa fuska ta jikin wayar sannan ya daga min hannu.

“Bye”

“Bye”

Mun dade muna kallon juna ni da shi, kewaraa ta hana ni kashewa shi ma kuma baya son ya daina ganin fuskata. Sai da na yi da gaske sannan na iya aje wayar na share hawayena na fita daga dakin Anty Amarya. Bangaren da Mama take na koma na shiga a wani yanayi kamar ba ni ba, gaba daya Mood dina ya canja.

“Ki tafi Zafeer yana waje yana jiranki”

Na cire hijab dina da ya jike da hawaye na dauki wani na saka, sannan na fita na tsaye a kusa da motarsa har muka gama gaisawa ban kalli fuskarsa ba.

“Noor na yi magana da Mama na tambaye ta ko akwai wanda kike so da har ya hana ki amsa aure na a karo na biyu bayan duk wulakancin da kika min? Ta fada min babu ta tabbatar min har yanzu kina kaunata kawai dai kina wasu hange hange ne da ba su da amfani”

Ya gyara tsayuwarsa.

“Ni kuma na san akwai mai wasa da hankalinki har yanzu, wannan Kareem din ko? Ba aurenki zai yi ba Noor kawai yana wasa da hankalinki, ya raba ni da kw farko Noor ban yi tunanin zaki sake kula shi ba, balle har ya zama dalilin da zai saka ki amsa cewar zaki aure ni”

“Ba shi ne dalilin ba, kai da Mama kun yi kuskure fahimta ne kawai”

Na fada domin a zatona Mama ta yi masa maganar Kareem ne. Sai ya tari numfashina

“Mama bata min maganar Kareem ba, kuma bata fada min komai akansa ba Wallahi, amman kin san ba zan rasa sanin halin da makiyina yake ciki ba ko?”

Na yi shiru ina jin babu dadi, na kasa sakewa zuciyata na raya min zan ci amanar Kareem ne, amman kuma. Zafeer ya cancanci komai a gurina, ba ni da masoyi irinsa, ya nuna min so iyakar so.

“Ina hango yadda kake kallona a idonka nw Zafeer”

Ya sassauta muryasa.

“Ki bar wannan maganar, ni dai babu abun da na iya kuma na sani sai kaunarki, zan iya yin komai saboda na aureki, na so ki Noor kin sani, na kusan mutuwa a lokacin da na rasa ki, ba ni fa wani buri a yanzu da ya wuce na aureki, rayuwar da muka sha alwashin ginawa a baya ba mu samu dama ba nake son mu gina a yanzu, shin kina so na har yanzu?”

A nan kam na daga kai na kalleshi da idanuwa dake hasko min irin rayuwar d muka yi a baya.

“Ina sonka har gobe har jibi har gata Zafeer”

Yayi min murmushin da na manta rabon da na ganina fuskarsa, ya matso kusa da ni cikin wata siga da ta fi kama da rada ya furta min.

“Zaki aure ni Noor?”

Na daga mishi kai.

“Zan aureka Zafeer”

Wani kuka mai karfi ya zo min. Tun daga ranar sai soyayya tsakanina da Zafeer ta dawo sabuwa ya karbe liyi na ya siya min wata wayar da sabon layi, kowa a gidanmu sai da ya san Zafeer ya dawo gareni, domin ya hanani kula kuwa ciki har da mahaifin Aisha da ya saki uwargidansa saboda ya aureni, kamar yadda ta sake zuwa har gida ta yi min cin mutunci ta fada min na kashe auren uwarta ni kuma na jira nawa sakamakon. Duk wani shirye shiryen aurar da ni Mama ta fara domin Zafeer ya fada min ba zai bata lokaci kamar yadda yayi a wacan karon har ya rasa ni ba.

Dawowar Zafeer ta min dadi, musamman da ya sanar min an kori Abdull a kamfanin da yake aiki, sai dai bana jinsa a yadda nake jinsa da farko, idan kuma na tuna Kareem ba da masaniyar komai akaina babu ta inda zai same ni sai hankalina ya tashi, lokuta da dama na kan so gwada kiransa a sabuwar wayar da Zafeer ya siya da sabon layi domin na haddace number sa, sai kuma na tambayi kaina me zan fada masa idan ya amsa kiran nawa. Na san an yi nasarar aikin a satin da aka amsa aikin na ji a gurin Yaya Nabil an masa aiki kuma anyi a nasara, amman na kasa kira na tambayi jikinsa ko na yi magana da shi.



Ya miko min zobe daya ya saka daya.

“Wannan na ki ne”

Na karba ina murmushi na yi saka a yatsana, soyayya sabuwa ni da Zafeer kamar ba mu taba shiga damuwa a baya ba.

“Dukanmu mun taba yin aure, ni na yi aure na farko ke ma kin yi har biyu, so ni a yanzu bana son ayi wani biki ko taro, ba zan yanke hanzarinki ba, na san mata kuna da son biki wata kila zaki yi walima ko?”

Na dan yi shiru ina nazarin abun da zan yi, domin Mama ce take ta shirye shiryen auren, har yanzu ban yi wani yunkuri ba.

“Bani ba ko Mama zata yi, amman dan ta ni bana sha'awar wani shirye shirye”

“Good, zan fi jindadin haka, ba sai an wahalar da ke ko Mama ba”

“Babu wahalarwar a ciki, ba za mu bukaci komai ba”

“No ba ina nufin kudin da zan bada ba no zan baki kudi enough ki yi hidimarki, kawai dai dauaniniyar ce wahala ai, kuma ina son na fada miki na kama gida a bypass ba laifi gida ne mai kyau sosai kuma yana da tsari mai kyau sai dai ba ma kusa da mutane”

Na dan kalleshi da mamakin jin furucinsa domin a tunanina yana gidan kasansa ko da yake gidan ba zai amfana min komai ba. Yayi murmushi yana kallona.

“Ya na san zaki yi mamakin na fadi haka ko? Gidana da nake zaune wanda nake tare da Fanna ne, kin ga yadda muka sha soyayya ni da ke kamata yayi ace mun tare a gidanmu mu kadai babu sa ido babu ganin laifi ko?”

Abun da ya fada haka ne, za mu fi sakewa idan muka tare mu kadai.

“Wai ni kam taya ka lallabata ta amince ka kara aure?”

“Ban gane ta amince ba, ni ne fa mijin ba ita ba! Tun kamin na aureta ai ta san ina sonki kuma at any chance zan iya aurenki, abu na biyu Fanna ba mace ce mai matsala ba, kuma bata cika zama ba, saboda ita ce tabbar yar mahaifinta yawancin abubuwan da suka shafi kasuwancin mahaifinta ko kamfaninsa ita take tafiyarwa, yanzu haka bata kasar ma”

“Amman me yasa baka bita ba?”

Ya daga fadunsa.

“Ra'ayi, tana son muna tafiya a tare sosai saboda tana son na zama ďa namiji da mahaifinta ya rasa, na maye gurbin ďa namiji da ba shi da, so nan din ma akwai abubuwa da nake kula masa da su”

“Amman ance ta tsofe ka wai haka ne?”

“Ko ma dai minene ai ta taimaka ta aure ni a lokacin da kika zubar da ni a kasa ko? Ita ta rarrashi zuciyata na samu sukuni har na rayu”

Na ji wani abu ya soki zuciyata.

“Daman tun a farkon zuwan da take na lura da sonka take yi, shiyasa take baka kudi mai yawa har ta taba tambayata wai kai saurayina ka tuna?”

Yayi murmushi ya shafa kansa.

“Manta da duk wannan, yanzu dai ya maganar tufafinki? Ina tunanin kudi zan baki ki siya duk abun da kike so”

“Me yasa ba zaka hada min da kanka ba?”

“Kawowar ne nake tunani kamar zai fi dai ki hada da kanki”

Bana masa jayyaya akan abubuwa daman can ni ba mace ce mai son ja'in ja ba, balle kuma shi da bana son ya ga laifina a yanzu ko da kuwa kan akaifa ne. A yadda ya tsara a hakan na bi sai ya kawo min kudi mai yawa da sunan siyen kayan lefe, Mama ta siya min kadan sauran kudi kuma ta kara gurin siyen kayan daki da na kitchen domin komai sabo ta yi min kamar auren fari. Yan'uwan Mahaifina sun yi kokari matuka, sun hada kudi mai yawa suka kawo gun Mama a matsayin gudunmawarsu.

Mama ta hada da wanda ta samu a danginta da kuma kudin da Zafeer ya ba ni na lafe ta siya min kayan daki fa kayan Kitchen masu kyau irin na mai rufin asiri. Ba ayi walimar ba kamar yadda Zafeer ya bukata, saboda Mama tace ta fara gajiya da shidawa mutane aurena a yanzu, gwara kawai mutane su ji an daura. A iya cikin gida muka yi bikinmu ba tare da tara makota ko kawaye ba. Iyana yan'uwan mahaifina sai na Mama da suke gidan kawai suka san da daurin auren da aka daura a ranar Jumma'a. Jikina ya sha gyara ta ko'ina ba a taba yi min gyaran jiki ciki da waje mai kyau irin wannan ba, Mama ta kashe kudi sosai gurin gyara yarta mace da ta rage mata daya tilo wato ni kenan.

Ni kaina na san na gyaru domin fatar jikina har wani tsantsi take kamar auduga. Ranar assabar aka yi wunin biki bayan an yi jere ranar alhamis, na yi zaton ganin yan'uwa da dangin Zafeer amman ban ga ko daya ba, daman tun da aka fara neman auren bayan iyayensa maza da suka kawo sadaki, wani daga familynsa be sake leko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login