Showing 42001 words to 45000 words out of 215481 words

Chapter 15 - Ƙaunar Da Ta Zama Azaba by 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

ita tun ina da rai”

Na kalli Baba da sauri hawayen da ban san yaushe suka taru a ido ba suka zubo min. Sai dai wani kyauta da dadi sai na kasa cewa Uffan ba kamar da ba, wata kila da zan iya daka tsalle na rantsewa Baba na kunyata shi ko a gaban waye nace Zafeer nake so domin shi ne zabin raina... Amman a yau sai na kasa furta ko da kalma daya ne.

“Baba Noor tana son saurayin nan nata, kuma shi ma yana sonta, be kamata ka shiga tsakaninsu ba, da dai zaka duba ka ba su damar zai fi, inda aka fito be kai inda za'aje ba”

Kareem ya fada sai na juyo ina kallonsa da kamar damuwa a fuskarsa.

“Ba wai bana son ta aure shi ba ne, samarin ne na yanzu sai a hankali ni har na fi sha'awar Noor ta auri mai mata sun fi rikon aure, kuma ita Noor ai ba wani so ta sani ba, ita dai barta ga shirmenta mu lokacin da muna yara ai ba wani soyayya muka sani ba, sai dai kawai ace an maka mata kuma sai ku yi zaman aurenku lafiya lau, zamani ne ya lalace har aka san wani lobe lobe, kuma ita Noor ai kawai dai ayi sha'ani...”

Baba ne yake maganar ya karasa da dariya irin wadda ke nufin Noor bata san abun da take ba. Abokin Kareem ya ce.

“Gaskiya, kuma ance abun da Babba ya hango yaro ko hau tsauni ba zai hango shi ba, to Allah yasa hakan ne mafi alheri, kuma kana da gaskiya ba Baba idan yarinya bata karatu babu inda ya fi dacewa da ita irin gidan aure, ko da ma tana karatun balle kuma irin Noor cikin kankanen lokaci zata fara son wani ma”

Shi ma dai kallonsa na yi wata kila ya manta da ina zaune a gurin yake wannan zancen, kamar Kareem ya san abun da yake zuciyata sai ya dubi abokin nasa ya ce.

“Hafiz dan Allah karka zuga Baba ya aurawa Noor wadda a shi take so ba, baka san komai game da auren wadda baka so ko baya sonka ba, idan ba zaka lurar ba, to karka lalata”

Mama ta tashi ta shige dakinta, ni kuma na mike tsaye ina jin Baba na fadar.

“Ai gaskiya ya fada babu wata zuga, Noor ai tana da saukin kai sosai kowa ya same ta ya zamu mata ba dan tana ƴata ba, sai dai ace bata jin magana amman tana da saurin sabo sosai”

Daga haka ban sake juyo me suke tattaunawa ba, har suka ci suka shude suka fita ban san anyi ba, domin hankali ya karkarta a gurin Zafeer ina ta hararon dalilinsa na rashin zuwa, Allah kadai ya san me Baba yace masa ko yan'uwansa, amman me yasa Mama bata fada min hali da ake ciki ba? Shim ba ni da hakkin sani ne? Ko kuma ita ma din bata sani ba? Ko kuma saboda sun mayar da ni wawuya marar hankali da tunani ne? Tun da na yi alwala azahar ban sake fita ba dakin ba har aka yi Isha'i da ita na yi sallah, abinci ma da Mama ta kira tace na zo na dauka na dare sai na kasa fita na ji kamar bana bukatar abincin.

Misalin karfe tara da yan mintuna yaro yayi sallama ya ce Zafeer yana sallama da Noor, kamar ina jira ba tashi da sauri daman akwai hijab a jikina na fito waje na saka talkamina zan nufi kofar sai Baba dake kishingide yana sauraren redio ya ce.

“Ina zaki?”

Na yi shiru na rasa me zance, domin na san ya san dalilina na fita a yanzu.

“Na fa fada masa zan miki miji tun da shi be shirya ba, na san halin wasu yaran yan iskan unguwa sai su nemi lalata yarinya ma idan suka ga ba su samu damar aurenta ba, gashi ke ba wayo ba balle na ce”

Mama dake zaune gafensa ta ce.

“Haba Malam.. Ai ko da ka fada masa haka be kamata ka hana ta fita ba, baka san me ya zo da shi ba, kuma ba san abun da Allah zai yi a gaba ba, ko rabuwar za'ayi ai ta mutunci tafi, Wallahi Allah kadai yasan zagi da za'ayi maka a unguwar nan saboda kin dagawa yaron nan kafa da ka yi”

Baba ya juya ya kalleta a fusace.

“An dade ba a zage ni ba, a cikin masu zagin akwai mai wani mudu daya na shimkafa? Ko akwai mai ba ni dari biyar na kara na yi chefane? Ni fa ban hana shi aurenta ba, amman na fada masa muddi be shirya ba to kar ya batawa yarinya lokaci kuma ni na gaji da halayarta ina son na aurar da yata, ai Annabi S. A. W ma cewa yayi idan wadda kuka yarda da addininsa da mu'alamarsa ya zo son yarku to ku aura masa, addinin musulunci ya bawa iyaye damar zabar wa ƴaƴansu mazajen aure, daman can ni ban wani yarda da tarbiyar yaron nan ba, waya sani ma ko zuwa yayi ya hure mata kunne ta bishi su gudu?”

“Zafeer din Baba?”

Na furta da kaina kuka yana cin karfina. Sai ya zabura ya tashi zaune.

“Zafeer din fa, ko ubanki ne shi ko kanen uwarki ne? Dan'adam babu abun da ba zai iya aikatawa ba ai, ke kuma kwakwalwar kifi ce dake gaki sokuwa sai ya tsara miki ki yarda ki hau ki bi, to daga yau sai yau kar ya sake sallamawa ki fita, ke ban ma yafe miki ba ki kula shi ko a hanya, ban yafe miki ba wata magana ta sake shiga tsakaninki da shi”

Mama ta tashi tsaye dukan kirji.

“Malam kana lafiya kuwa? Wane irin abu ne wannan? Saboda wani ya bullo ya nuna yana son Noor cikin kankanen lokaci ya siye bakinka da zuciyarka da dukiyar da baka san hallaci ko haramcinta ba zaka yarda ka rusa soyayya da baiko shekara uku dake tsakanin yaran nan? Duk irin iya shegen da Noor take haka Zafeer ya ganta yace yana so sai kuma ka shiga tsakani yanzu da yake hararo gaba? Haba Malam kar ka yi abun kunya mana kar kasa hakki ya bibiyemu”

Baba ya mike tsaye ya dauke Mama da mari.

“Duk wata doka da zan saka a cikin gidana ke kike rusa ta kuma ke kike ba su damar rusawa, ko a addinance ba ni da laifi tun da shi yace be shirya aurenta ba a yanzu, kuma wannan yaro da kike zargi Allah ya isansa domin har yau be fito yace min yana son Noor ba, dan haka ya barki da Allah da zargin lalata alaka da kika masa, kuma bari ki ji na fada miki idan yaron nan ya sake yin sallama kika bar Noor ta fita abakin aurenki....! Wato yan unguwa su yi da ni, na shigo cikin gida ki dora min tukunyar masifa, to ba zai yiyu ba, daman can Allah yayi ba matarsa ba ce”

Ya saka talkaminsa ya dauki radio ya fice babu ko hula akansa. Mama ta dube ni ta kara min da wani bakincikin.

“Allah ya kara, duk abun da ya faru ke kika ja, shegen shishigin tsiya da iyayi da yawo da shashanci shi ya ja miki, kuma ni ba zan bari aurena ya mutu ba saboda ke, domin ba zan koma neman gurin zama ko rabawa ba kuma zan yarda rayuwar Hannatu da Nabil ta shiga wani hali ba saboda ke, kadan ma kika fara gani, hawayen da kika yi ta saka ni ina fada miki gaskiya kina bijirewa yau ga sakamakon kin fara gani, kuma wannan so min tabi ne baki san me zai biyo baya ba, sai ki zuba ruwa kasa ki sha...”

Tana maganar tana nuna ni ta muryarta nake karantar kukanta domin nawa hawayen sun hana ni ganin fuskarta. A kananen shekaruna na fara dandana zafi da bakincikin rabuwa, Baba ya sauya tunanina ya rusa burukana, ya wargaza shirina, ya saka ni a wani gidan kurkuru da ban isa na fitar da kaina ba, ban san ma ya kofar fitar take ba....

Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*


✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧


𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆


*Talla👇👇👇*

https://chat.whatsapp.com/GY1W0qJiFbJD5A5J6F0fqA
*INA MATAN DA SUKASAN DARAJAR GYARA❓DAKU NAKE MACE MAI GYARAN BATA ZAMA BORA❌*

*KUZO GA INGANTATTUN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI💪BA MUNA KAYABA❌ HAJIYA KIZO KISAI KAYAN MATA WURIN DA BAZAKIYI ASARAR KUDIN KI BA*

*INA MASU CEWA NI KO NASHA KAYAN MATA BASAMIN AIKI HMMM HAJIYA BAKIDAI SIYA KAYA MASU INGANCI BANE, KAYANMU SUNA KARA NI'IMA, TAYARDA SHA'AWA, DADI, TIGHTENING (MATSI), CIKO DA GABAN MACE (DUK BUDEWAR SA), DUMIN GABA GA, KAMSHIN GABA GA KUMA NA KARA DANDANO OVER 💃💃💃💃💃👉 GA KUMA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI DAGARGAZA SANYI KODA YA SHEKARA 10 A JIKINKI* 09038090328

*A DAYA BANGAREN KUMA MUNADA SABAYA MAI GYARAN NONO DUK LALACEWAR SA KO KIN HAIHU GOMA SABAYAR MU ZATA CIKO MAKI DA BREAST SUYI GIRMA SOSAI MADAME*

*GA KUMA TA HIPS (MAZAUNAI)SU CIKO SUYI BULBUL NONO YA CIKO SOSAI HJY KIYI KIBA YAR DAIDAI SKIN DINKI YAYI KYAU KI KOMA TAMKAR TARWADA*

AKWAI KUMA NA GYARAN NONO WANDA BAYA SAKA KIBA💃💃💃

GASKIYA NA YARDA DA INGANCIN KAYANTA👆👆👆




*Chapter - 13*

Babu kowa a tsakar gidan balle na ce wani ne ya rika ni ya isa da ni kofar dakinmu, haka kuma ba zan iya fadar cewar kafafuwana sun kawo ni ba, domin samun kaina na yi tsaye a tsakiyar dakinmu ina kallon hudun daren da ya cika daki. Can ka na ji an dafa ni muryar Hana ta fara isa kunnena.

“Da ni ce ke, zan auri mutumen nan ko dan na samu rabuwa da Baba lafiya, kuma zaki huta da duk wata masifa tashi da tashin hankali ko fada, idan kika yi aure zaki huta Noor”

Na juyo na kalli ta saitin inda take tsaye. Amman na kasa ce mata komai sai hawaye ne suke min zuba, a rayuwa ban tana jin wani abu tashin hankali ba irin wadda na ji a yau din nan. Sai na ke jin kamar sanarwar mutuwa aka min cewar Zafeer ya mutu ya bar ni a raye.

“Noor ki yi addu'a kawai, kuma karki bari so ko shashancin da ake ganinki da shi ya zama silar lalacewarki saboda bakin da Baba yayi cewar be yafe ba idan kika kula Zafeer”

Na sulale kasa a hankali na zauna a gurin, na rasa me zan yi ko na ce, kalamaina kamar sun kare, duk wani kuzari a yau ba ni da shi. Me yasa Baba zai min haka? Anya ya san yadda nake son Zafeer kuwa ko kuma yadda shi Zafeer din yake so na? Mama ta yi gaskiya tace ni ce na janyowa kaina kuma haka din ne, domin ni na yi silar zuwan Kareem da abokinsa a gidanmu gashi sun lalata baiko ba tare da na san waye mai so na a cikinsu ba, ba ma nuna suna so na ba, kuma ba su furta ba ban taba ganin wata alama dake nuna soyayyata a garesu ba.  Gaba daya sai na ji kamar mafarki nake wunin ranar sai ya zame min kamar ba gaske ba, ni dai na san ina matukar kaunar Zafeer irin kaunar da nake jin idan ba shi ba ba zan iya zaman aure ba. A inda na zauna ban tashi ba har garin Allah ya waye kuma bachi be kusanci idona ba, haka kuma ban bude baki na ce da kowa komai ba ban kuma ihu ko kururuwa ba, saboda ina jina a wani yanayi na dabam da ban saba jina ba.

Bayan na yi sallah asuba na nemi gurin kwanciyata na kwanta sai idona suka ce firr ba dai bachi ba Nooriyya, karyarki ba a wannan wunin ba, haka na tashi zaune na kurawa kofar wajen ido, na dade a zaune kamin na iya bude baki na fara ambaton Allah, Ban yi wani kwakwaran motsi ba har Hana ta gama shirinta na makaranta ta fita ta zuba kunu sannan ta kawo min nawa har inda nake kallo daya ta yi min ta fahimci a tsorace nake ga idona yayi wani Ja kamar wadda ta shekara bata yi bachi ba.

“Ga kununki in ji Mama...”

Na kalli kunun na dauke kai ina jin ba zan iya kai komai a cikina ba yanzu. Ni dai ba wani sanin damuwa na yi ba amman ina jin dakinta na daf da ni domin kokarin rabani da Zafeer da Baba yake ko ma yayi wani abu da ban taba mafarkin faruwarsa ba.

“Wa'alaikusalam”

Muka ji Mama ta amsa sallamar Zainab dake sanye da uniform din makaranta, Hana ta jiya ta fice daga dakin kamar dai babu wadda ya damu da halin da nake ciki, wata kila ba su yi zaton soyayya ta ta kai haka ba, ko kuma ganin suke wani abu ne da zan iya mantawa a take. Ko kuma dai saboda ni na janyowa kaina ne shiyasa lamarin ya zo min ta haka.

“Noor... Lafiya kike kuwa?”

Kamar an bude min kofar sassauci tana tambayar haka sai na fashe da kuka na kwanta jikinta amman na kasa fada mata damuwata har ta gaji da tambayata ta koma rarrashina.

“Allah dai yasa lafiya, Zafeer ya je gidanmu shi ma cikin damuwa yace na fada miki ya zo jiya amman be samu ganinki wai yana son ku hadu a gurin aikinsa ko kuma kwanar dan musa mai itace anjima da karfe goma”

A sirrance take fada min sakon na Zafeer, abun da hausawa ke cewa ga bikin zuwa babu zanen daurawa, domin ban isa na tsallake umarni da furucin mahaifina na je na ganshi ba, kuma a yau bana jin zan iya budewa kawata cikina balle na fada mata damuwata da babu mai min maganinta sai Allah.

“Noor akwai wata matsala ne? Fada min ko minene dan Allah”

Na girgiza mata kai na matsa baya na kwanta ina maida numfashi daker.

“Wai fada kuka yi da shi ne ko kuma me?”

Nan ma dai ban ce mata komai ba. Har ta gaji ta tashi ta fita ta barni rumgume da bakincikina. Ban iya fitowa na yi komai ba har Mama ta gama aikinta na gida, Yaya ya dauko ruwa sannan yayi wanka ya fita, a nan na samu mikewa tsaye ina jin kaina na masifar ciwo ga wani jiri jiri da nake ji yana dibata yana yawo da ni. Ruwa na zuba na shiga bandaki wai saboda na samu na yi wanka amman sai na saka yin wanka na zauna a bandakin ina ta kuka. Hankali be kara tashi ba sai da wani almajiri ya shigo ya ce Zafeer na sallama da Noor Mama tace masa yaje yace bana gidan. Rumgume kaina na yi ina ta kukana babu mai rarrashina har sai da na gaji na tashi na daura zanena na fito ba tare da na yi wanka ba na aje ruwan a waje sannan na nufi dakin Mama na zauna daga bakin kofar dakin ina kuka na ce.

“Mama Wallahi duk na daina abun da nake, ba zan sake kin jin maganar kowa ba, Mama ki yafe min kuskurena, kuma dan Allah ki roka min Baba yace ya yafe min yayi hakuri ya bar ni na auri Zafeer dan Allah Mama”

Kaya take ninka amman haka be hana ta kalleni ba ta ce.

“Kin fi kowa sanin halin Babanki ai, yanzu ya ga mai kudi ba zai yarda da soyayyarki da yaron nan ba, kuma ni ban ga laifin ubanki ba, daman tsuntsu da ya ja ruwa ai shi ruwa kan doka, tun abun nan be yi nisa ba ya kamata ki gane gadar zare kike yi ma kanki amman ina, hankali yayi yamma ke kin yi gabas, idan kika ga Babanki be hada aurenki da wannan mutumen ba to sai idan shi din ne yace baya sonki ko kuma wani ya gani wadda ya fishi”

“Ba so na yake ba Mama Wallahi wata kalmar soyayya bata taba shiga tsakanina da shi ba”

Na fada da muryar kuka wani kukan na cin karfina.

“Wannan kuma ke kika jiyo, ga dubu biyu nan tashi ki kai gidan mai adashe, bashin da kika ci ne ban gama biya ba”

Ta jego min kudin ni kuma sai na kai hannu na dauka, na kalleta sannan na tashi na fice daga dakin ina hawaye. Dakinmu na koma na zauna gaba daya sai na rasa abun da ke mini dadi. Na kusan minti talatin a dakin ina kuka har sai da Mama ta yi magana sannan na yunkura na tashi idona a kumbure na saka rigata da hijab na riko kudin na fito na saka talkamina na fice daga gidan. Kamar wata marar lafiya haka nake tafiya har na isa gidan mai adashen na bata kudin na juyo na fito ta babu wani kuzari a tare da ni. Daf da zan isa gida na ji muryar Zafeer yana kiran sunana amman na kasa waigawa saboda bana son na yi arba da fuskarsa kar rauni ya saka ni karya doka da mahaifina ya saka min, amman hakan be hana shi shan gabana ba.

“Noor magana fa nake miki kina tafiya kamar baki gan ni ba, me ke faruwa ne?”

Na dauke kai na kauce daga gabansa na cigaba da tafiyata.

“Noor... Noor.. Ni ne fa, Noor”

Na kasa juyawa kuma na kasa amsa masa sai hawaye suka zubo min. Ya sake shan gabana.

“Jiya na tafi gidanku ban samu ganinki ba, idan har Baba zai juya min baya ya ki sauraren uzurina ban yi zaton haka daga gareki ba Noor, kin san ina sonki sosai zan iya jure komai ban da rashinki Noor, na roki Baba jiya na ce ya yi hakuri ya ba ni wata biyu zuwa uku zan yi na yi duk yadda zan iya, zan aureki Noor ko haya ce zan kama mu zauna kamin na samu aiki, amman me yasa kike kokarin canja min? Ko wani abu aka ce na miki? Ko kuma an fada miki wani aibuna ne...?”

“Babu wani aibunka da za a fada min da zai saka na tsane ka Zafeer, babu wadda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login