Showing 90001 words to 93000 words out of 215481 words

Chapter 31 - Ƙaunar Da Ta Zama Azaba by 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

zauna ya rufe sannan yaja motar muka fara tafiya, be kalli inda nake ba ni ma ban kalleshi ba sai sake saken nake a zuciyata ina zai kai ni? Me Kareem ya fada masa? Ina son na tambaya amman na kasa saboda bakinnya rufe min gam. Unguwarmu ya nufa yana ratsa gidajen dake ciki har ya isa kofar gidanmu, a nan na fahimci so yake ya hada ni da iyayena. Na kalleshi hawaye na min zuba.

“Fita ki shiga gida, ki zauna sai na neme ki...”

Ya fada ba tare da ya kalleni ba, na juyar da kaina dake rawa na bude motar na fita sai na yi tsaye na kasa daina kallonsa na kasa juyawa na shiga cikin gidan. Mun dauki mintuna a haka sannan ya miko hannu yaja gambun motar ya rufe yayi mata key ya bar ni a gurin tsaye cikin ruwan hawaye. Me kuma aka ce na ce? Yanzu kuma wane kalar laifin na aikata? Na zauna sai ya neme ni ya sake ni kenan ko kuma yaya?




#KhadeejaCandy

PAID PAGE 9️⃣


©️KhadeejaCandy
©️®️Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....


You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153


_______•••_______

Na kusan minti talati tsaye kofar gidanmu kamar wanda aka cewa shiga ki tararda hisabinki haka tsoron shiga gidan ya kamani, domin na san waye mahaifina. Amman ba ni da wani gurin da ya fi gidan ina zan je? Ai ba ni na kawo kaina ba shi ya kawo ni. Cikin kasala da fargaba irin na wanda ya rasa makoma na saka kafata a gidan, duk yadda nake son hana hawayena zuba kasawa na yi. Sai kuma na yi rashin sa'a Baba na tsakar gidan yana alwala, ban yi sallama ba domin bakin har lokacin a rufe yake. Baba ya hasko ni da fitilarsa mai haske.

“Wa nake gani kamar Norriya?”

Tafiya kawai nake cikin gidan na kasa Cewa komai.

“Lafiya?”

Na durkusa a gabansa.

“Wani abu ne ya samu Hafizun?”

Na girgiza kai.

“Toh me ya faru?”

Hana ta fito daga daki tana kallona cikin tashin hankali.

“Cewa na zauna sai ya neme ni”

Fitilar dake hannun Baba ta subuce ta fadi kasa.

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un, daman ai sai ba ke ba Noor, yanzu duk irin abubuwan da mutunen nan yayi min yayi miki sai da kika kai shi makura? Tafiya kika yi kina masa shashanci da sakarcin na ki ko? Har ya gaji yanzu ya koroki gida”

Na matsa baya da sauri jikina na rawa domin fadan da Baba yake min irin na son duka ne.

“Yaushe aka yi auren da zaki biyo dare yanzu ki ce wai yace ki zo gida?”

Na bude baki zan yi magana ya daka min tsawa ya cire talkaminsa ya jefani da shi.

“Ban son jin komai daga bakinki, marar mutunci daman ai na san sai kin masa shashanci, kina kallon yadda rayuwa take a gidan nan kin samu mai rufa miki asiri ne shi ne kika fara masa rashin kunya ko? Saboda ya sake ki ki auri Zafeer ke ga ki shim mai ruwa uku shashasha, sakinki yayi?”

Na girgiza kai.

“To tashi maza ki koma dakinki, ina nan ina jindadi na samu suruki mai dauke mana komai shi ne zaki fara watsa mana kasa a ido? Ni daman sai da zuciyata ta raya min anya ba kina masa rashin mutunci ba ne, in ba haka ba da yanzu ya gyara mana gidan nan amman shiru, ashe kina can kina nuna masa rashin tarbiya, mai kashin tsiya so kike mu koma rayuwarmu ta baya ko? Ke yar zamani, minti biyar ban yarda ki kara yi a gidan nan ba, koma dakinki gobe zan zo na ji me ke faruwa amman Wallahi ba zaki kwana gidan nan ba, wato halin uwarki zaki dauka na rashin hakuri ko? Ko kuma so kike ya sake ki ki dawo ki sake zaunawa ke da kanwarki a daki daya? Wawuya marar hankali, wato ki zaki nunawa wai ba zaki yi zaman aure ba ko? To na fiki zama dan tasha... ”

Ya karasa yana daukar butar da yake alwalar da ita ya jefa min. Na tashi da sauri na fice daga gidan ina kuka, Baba be saurari izurina ba ya koroni daman na san hakan zai faru, da na fito sai tashin hankalin yayi min yawa na rasa ina zan je, na koma gidan Hafiz din da ya kawo ni gida yace na zauna sai na neme ni ko kuma na tafi gidan Mama? Ita ma koroni zata yi. Haka na bi hanya ina tafe ina hawaye har na isa titi, wata zuciyar na ce min na tafi gidansu kawata Zainab na kwana, domin ba ni da kudin abun hawa ma balle na koma gidan na san kuma ba zai ba ni ba, wata kila ma na samu ya fadawa mai gadinsa cewar kar a bar ni na shiga cikin gidan. Juyowa na yi na dawo cikin unguwarmu na shiga gidansu Zainab, Umma na ganina ta san ba lafiya ba, kamin Zainab tace min komai Umma ta fara tambayata lafiya.

“Umma Hafiz ne yace na zauna a gida sai ya neme ni, na zo kuma Baba ya kore ni, na san idan na tafi ma Mama ba zata saurare ni ba, ban san inda zan je ba”

“Wani abun kika masa?”

“Ban masa komai ba Wallahi ban masa komai ba”

“Aa Noor ba zai yiyu haka nan kawai yace ki tafi ki zauna a gidanku ba, sai kin masa laifi, Allah yasa dai ba Zafeer kika saka a zuciyarki ba, kar soyayyarshi ta hana ki zaman aure, ki kama kanki Noor ki natsu, yaushe aka miki auren da har za ace an fara samun matsala irin wannan?”

Na yi shiru domin ba kowa zai yarda da ni ba.

“Kin ga ni ba zan baki mafaka ba, mahaifinki ya koreki wace ni na baki gurin zama? Ai zai ma iya ci min mutunci ko kuma a ce saboda ni ba uwarki bace yasa na yi haka, ki yi hakuri ki koma dakinki ki bawa mijinki hakuri ku zauna, shiyasa ma na hana Zainab tafiya gidanki kar wani abu ya faru ace ita take hure miki kunne, ki yi hakuri ki koma dakinki Noor”

“Tohm...”

Na amsa kana na juya domin bata bar ni na zauna ba ma, haka na fito daga gidan ina hanya Zainab ta tarar da ni ta ba ni 500.

“Mama tace ki hau Napep, kuma Noor idan ba zaki iya komawa gidan kai tsaye ba, ki tafi gidan iyayensa ko kuma wani dan'uwansa wanda kika san yana jin maganarsa, sai a kira shi a yi masa magana kinji”

“Ban san gidansu ba, be taba kai ni ba”

“Ko gidan wani abokinsa ba kisa ni ba?”

“Na sani amman hakan zai iya bata masa rai, jiya naje can na fada masa amman be yi komai ba, wata kila shiya saka yau na ce na dawo gida na zauna”

“Idan kin tafi kice ya fada miki gidan iyayensa ki tafi, ba wai dole shi zai masa magana ba, kuma Noor na san halinki da rashin jin magana dan Allah ki zauna lafiya”

Na yi murmushi ina jin ina ma ace ni ce a matsayinta.

“Na gode Zainab”

Ta tsaya a gurin har sai da na samu Napep na hau sannan ta juya. Kuka ne abun da nake yi har mai napep din ya isa kofar gidan Kareem.

“Allah yasa lafiya kike wannan kuka ko mutuwa aka yi?”

Ban ce masa komai ba na mika masa dari biyar din na fita Napep din ina kallon gate din gidan ban san me zan sake ce masa ba. Ina ta zuwa masa da matsalata, waya sani ma ko hakan ya zama sanadin mutuwar auren nawa gaba daya. Sai dai ba ni da wata mafitar bayan wannan, a gaban gate din na duka ina kuka sosai. Da rarrafe na isa gate din na kwankwasa, babu jimawa mai gadin ya bude ya leko.

“Waye?”

Na share hawayena na mike tsaye.

“Ni ce wadda na zo jiya, Kareem yana nan?”

“Eh yana ciki”

Ya bude na shiga ido a kumbure hancina n yaji saboda majina da gugar da ya sha, fuskata ta yi ja sosai. Kai tsaye na nufi cikin gidan cikin rashin sakewa da tunani kala kala a raina, damuwa ta saka na manta waye matar Kareem, na manta cewar huruminta na shigo domin mijinta. Na kwankwasa kofar falon ta bude min ni da ita muka tsaya kallon juna.

“Ke ce?”

Na daga mata kai.

“Kareem yana nan?”

“Eh yana nan shigo”

Na goge gudun hawayena na shiga falon na tsaya daga gurin kofar ina kallonta.

“Ina son magana da shi ne dan Allah”

“Okay ina zuwa bari na kira shi”

Ta juya ta nufi wani gurin da nake kyautata zaton kitchen ne. Bata ji ba ta fito nufo gurin da nake tsaye.

“Ki shigo ki zauna mana bari na kira shi”

Ba tare da tunanin komai ba na shigo kamin na zauna ta ware hannunta ta buga wani abu mai mugun karfi a kai, ban gama tantance miye ba na sake jin saukarsa a wuyana, wani irin jiri ya dauke ni na soma ganin ta zame min biyu kamin idon ya rufe...




*** *** ***

Babu ihu babu kokarin kare kai Noor ta yi kasa idon suka rufe, gefen da ta buga mata mociyar kuma jini ya fara jika hijabin har ya zubo kasa. Da sauri Yusura ta saki muciyar ta matsa baya jikinta ya fara rawa, me ya kaita? Me yasa ta aikata? Ina tunaninta ya tafi haka? Sai kuma ta matsa ta taba Noor ta ji bata motsi ta sake matsawa baya ta zauna kan kujera hankalinta a tashe jikinta na rawa. Kaminnta tashi da sauri ta haura sama. Dakin Kareem ta shiga yana sanye da multicolours din Pajamas dinsa hannunsa rike da books din Rules of the Journey. Daga kishingiden da yake ya dago kai ya kalleta ko'ina na jikknta rawa yake tashin hankali a fuskarta karara.

“Ya.. Yarinyar da ta zo jiya ce ta dawo yau”

Kareem ya rufe littafin yana kallonta hankalinsa kwance.

“An samu akasi na buga mata abu ta fadi”

Wani irin tsalle ya daka ya sauko daga kan gadon.

“What.... Me yake damunki? Why?”

Ya fice daga dakin da sauri sai ta bi bayansa kamar zata yi kuka. Kareem ya sauka kasa ya karasa gurin da Noor take kwance cikin jini.

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un, Me kika aikata haka Yusura? Baki san me ya kawo yarinyar nan gidan nan ba, ban san halin da take ciki ba kawai ki kara mata da wannan?”

“Ta mutu ne?”

Yusura da ta kasa karasa saukowa ta tambaya cikin kuka. Kareem ya saka hannunsa ya cire Hijab din Noor ya taba wuyanta ya cire dankwalin kanta ya daure mata kan dake zubar da jini sannan ya tashi ta sauri ya haura sama ya dauko keys dinsa ya fita ya janyo motarsa ya kawo kusa da entrance din ya shiga falon ya dauko Noor da bata san inda take ba ya saka ta bayan motar ya shiga driver side ya ja motar sai asibiti.

Gado aka bata shi yayi mata duk wani treatment da ya kamata, ya saka mata drip sannan ya lalaba aljihunsa ya sai a lokacin ya tuna be zo da wayarsa ba.

“Oh nikan matan nan son hada min wuta...”

Ya fada yana kallonta.

“Me ma ya sake fito da ke Noor?”

Tambayarta yake kamar ance masa zata iya amsawa. Dakin ya fita be bar asibitin ba sai da ya tsabtace kansa sannan ya shiga motarsa ya koma gida. Yana shiga falon Yusura ta mike tsaye tana kallonsa.

“Tana raye?”

Wani mugun kallo ya watsa mata.

“Kusan wannan ne karo na biyu da kike kokarin illata yarinyar nan, wannan ya zama na karshe, wacan karon kamin ta yi aure ne har ina fada mata kawai dai an samu akasi ne, ba wai dan kishi ba, yanzu kuma ban san me ya zo kanki ba...”

Ta matsa kusa da shi.

“Yanzu din ma akasi ne, gobe da jibi din ma akasi ne matukar bata dauke kafarta daga gidan nan ba, kusancinta da kai yana kusanto maka da mutuwa ne kai da ita”


“Idan kika kasheta zai ba ni mamaki, domin baki da wani dalili na aikata hakan. Kashe ni ba zai bada mamaki ba, tun da na san ba ki so na, ko akwai abun da ya canja?”

“Babu Kareem babu, babu abun da zai canja har gaban abada...!!! Ko a mafarki bana fatan ko a lokacin da kake da natsuwa balle yanzu da kake bibiyar matan aure ciki har da matar amininka...”

Ta fada da karfi sannan ta juya, fisgota yayi ya dawo da ita.

“Babu wata alaka tsakanina da Noor, idan har zan kulla wata alaka makamanciyar wadda kike zargina da ita, to da zan aureta ne na aje ta a gidan nan under the same roof mu rayu har abada ni da ita, sai dai kuma babu irin wannan sha'awar tsakanina da ita”

“An fada min ai, kun yi soyayya sai kuma ka saka abokinka ya aureta deal ne?”

Sakinta yayi yana murmushi.

“Haba ke kuwa taya Kareem zai yi soyayya da wata yarinya, yana da damar aurenta kuma sai ya ki aurenta ya saka abokinsa ya aure ta? Daga baya kuma ya zo yana bibiyarta? Wane irin ƙidahumi ne ni? Ai da abun da aka fada miki ne ya faru to sai dai na aurota na kawo nan mu sha soyayya”

Abu ta hade da karfi ta juya ta haura sama ta barshi a gurin tsaye. Ta wani bangaren baya ganin laifin abun ta aikata domin gidanta suka shigo kuma neman mijinta, ta gurin da abun zai daure masa kai ace tana kishinsa domin abun da ake so ake kishi, shi kuma be saka ran samun haka daga gurin Yusura. Isakar bakinsa ya busar ya nufi dakinsa ya wayarsa ya dauka ya kira Hafiz.

“Hello...”

“Barrister kana gida?”

“Ina gida lafiya?”

“Zaka iya fita waje mu yi magana”

“Okay....”

Shiru na 2 minutes ne ya shiga tsakani kamin Hafiz ya amsa daga dayan bangaren.

“Ina jinka”

“Kun sake yin fada da Noor ne?”

“Daman ba fada muke ba, kawai dai na turata gidansu ne yau?”

“Saboda me?”

“Tana bukatar a koyar da ita zamantakewar aure Kareem, ba zan Boye maka ba na fara nadamar auren yarinyar nan!”

“Subhanallahi, to maybe wani abun ya faru a gidansu ko kuma bata tafi gidan ba, ta zo gidana by mistake Yusura ta fasa mata kai yanzu haka dai tana asibiti”

Hafiz yayi shiru kamar ba zai ce komai ba.

“Dan Allah kaje ka sameta kuma ko miye a tsakaninku ka yi hakuri mana Hafiz, hankalin Namiji baya zama daya da mace, kuma san halin mahaifin yarinyar yana daga cikin dalilin da ya saka ka aureta saboda ka tsamota daga kunci, to miyasa ba zaka jure ba kana lurar da ita har ta fahimta, ba mamaki mahaifinta korarta yayi ta rasa gurin zuwa ta zo nan, ni kuma ban ma sani ba sai fitowa na yi na samu Yusura ta yi mata aika aika, kuma kai ya kamata na kira domin responsibility dinta yana kanka as her husband don't misunderstand the issue please”

“Tana ina yanzu?”

“Tana asibitinmu, emergency room 44, please ka sassautawa yarinyar nan Hafiz duk yadda kake tunanin hankalinta be kai can ba, a yanayin yadda na fahimta ta tashi a wani yanayi ne na rashin dace da iyaye shi ne musabbabin komai, idan ka hada mata zafi iyayenta suka hada ma za ku iya sakawa ta kamu da depression domin bata da mai rarrashinta bata san gurin da zata tafi ta ji sanyi ba, ta yi kankanta ace ta fara samun matsalar aure tun a yanzu, and idan bata samu kwanciyar hankali a gidan ka ina zata samu? Already ta rabu da wanda take so, idan ta rabu da kai iyayenta za su iya juya mata baya, idan a gidanka bata jin sanyi kashe kanta kuke son ta yi? Kai da kanka ka ce za a iya koya mata son wani, to ka koya mata mana, ka nuna nata gurin da illar abu yake da sannu zata gyara”

Hafiz ya ki ce komai ba, sai wani cika zuciyarsa take duk abun da Kareem yake fada shi wani abun yake hangowa can dabam.

“Good Night”

Kareem ya kashe wayar ya jefar kan gado ya sauke dogon numfashi.

“Poor girl”

Ya furta, ya zauna bakin gadon yana jinjina kai.




NOOR POV.

“Good Morning...”

Na ji wata matar da ban taba arba da kalar fuskarta ba ta fada tana yi min murmushi. Yunkurin tashi na yi zaune sai ta rika ni na zauna na sake dubanta da idanuwa da ba su gama budewa ba.

“How are you feeling now?”

Na daga mata kai ina jin kamar an dora min wani dutse a gefen kaina saboda nauyin da yayi min. Hannu na kai na taba sai na ji an daure gurin, gefen wuyana ma an saka min wani abu a gurin sai ciwo yake min.

“Ya jikin na ki?”

“Da sauki”

Na amsa ina kallon dakin da ban san lokacin da aka kawo ni ba. Gashi babu kowa a kusa da ni sai wannan nurse din da ba musulma ba domin sakar cross ce a wuyanta sai gashin doki da ta dora. Ta taba jikina ya cire robar ruwan da be kare ba sannan ta yi rubutu akan files din dake hannunta tana min tambayoyi, sunana umguwata ina da aure ko babu sai kuma number wayar Mijina ko ta mahaifina, da alama dai sabon file take bude min a yanzu. Sai da ta gama sannan ta saka hannunta aljihu ta ciro wata takarda ta miko min.

“Ga wannan mijinki yace idan kika tashi a baki”

Na mika hannu na karba, a gabanta na fara warware takardar har na bude.

“A yau 2 ga watan 6 ni Hafiz Abdullahi na saki Matata Noor saki daya”

Shi ne a rubuce, gashi sunana da nasa ne a rubuce balle na ce kuskuren fahimta aka yi aka ba ni abin da ba nawa ba.

“Wayyo Allah.. Na shiga uku na lalace, wayyo ni Allah me yasa Hafiz zai sake ni yanzu na shiga uku, yanzu ina zan je? Wayyo Allah... Baba kashe ni zai yi, yanzu korata za su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login