Showing 105001 words to 108000 words out of 215481 words
Kano gurin Yayarta bayan rasuwar mijinta na farko, tana sana'a har Allah ya kawo mata Baba ya aureta a yanzu.
Bata taba haihuwa ba a wacan auren nata kamar yadda take labarta masa wani lokaci ni da hana, ba wata babbar mace ce be domin Mama ta yi kanwa da ita ta biyu, sai dai tana da irin jikin nan sosai da zata iya daukar Mama da irinta uku ta goya ta gudu, domin ni da Mama jikinmu daya, ita ba kiba ni ma babu kibar, ba mamaki ma kibar ce ta burge Baba ya aurota.
Wani sabon salo da ta kirkira shi ne na dorawa Hana tallar awarar a titi tana siyar mata kullum zata bata 500 naira, ita kuma tana yin kunun waken soyar a gida, ana shigowa ana siya sai dai ba sosai kamar yadda take fada mana ba.
Dole ce ta saka Hana yarda tana soya mana awara a waje ba dan tana so ba, domin ko a lokacin da Mama take gidan kuma muke cikin tsananin shan wahala bata taba gwada dora mana talla ba, amman ita wannan da ba uwarmu ba ta fara dora ma Hana talla daga zuwanta.
Ko da yake ba laifinta babne laifin Baba domin shi ya bata dama Hana kuma bata isa tace ba zata yi ba, duk kuwa da kasancewar bata so ko kadan. Domin fita tallar ya kashe mata tafiya makarantar yamma, ya zama boko kawai take iya tafiya da safe.
Ni kuma aka bar ni da wahalar aikin gidan, shara wanke wanke da hura wuta tun ban iya ba har na iya, girkin ne kawai bata bari na yi domin na gwada girkanwa ta ji be yi mata yadda take ba. Idan zata hada kunun wanken soyan ni nake wanke goruna ni nake mata komai har tacewa, awara kuma ni zan gyara wake da dare da safe taje ta kanta ta kai nika, idan ta dafa a tare zamu natse ni zan yanka idan aka soya be wuce a ba ni da hansin ba ko saba'in.
Wani sabon shafin wahalar rayuwa Umma ta bude mana a idan, ni da Hana saboda sana'ar da take wai ai ba ita zata fita ta yi ba a dole hana zata soya mana wara a waje ni kuma na yi aikin cikin gida. Ta inda nake samun sauki shi ne takaba da nake bana fita, saboda haka duk wani aiki na fita ita zata fita ta yi, da safe kuma Yaya sai ya cika gidan da ruwa sannan yake fita.
Ta inda gurin da ta samu banbancin da Mama a zamanta gidan ita kam Baba yana bata abinci da cefane mai kyau, ba kamar Mama ba da wani lokacin zai ce be da shi ko kuma ya bada abinci ya hana cefane ko ma ya hana gaba daya. Wata kila saboda ita din tana da dan da sauran kurciya ba kamar Mama ba, wata kila kuma dokin amarci ne yake Allah masani.
Idan kuma aka yi girki ba a ba mu wani abun arziki Allah ma ya sa yanzu damuwa bata barina na ci na koshi kamar da, wani lokacin har ragewa nake na bawa Hana a da kam na fi kowa cin abinci a gidan, ranar da Hana ta tafi family house din Mama ta fada musu halin da ake ciki na dora mata talla, washe gari Kawu Garba ya samu Baba yana nuna masa hakan be dace ba, sai Baba yace kar wanda ya sake saka masa baki akan lamarin yaransa shi ya ga damar su yi, kuma babu mai ciyar masa da yara sai su.
A nan yake fadar ai tun kamin auren ya fada mata yaransa za su rika mata wani abun saboda ta fada masa ita fa tana sana'a kuma aure ba zai hana ta yi ba, shi kuma ba zai iya ganin matarsa da aure ta fita waje ta yi sana'ar wara ba, domin haka yarsa zata maye masa gurbi. Ni kam gaba daya na zama kamar ba ni ba duk abun da ake bana iya cewa komai sai ido, wani kalar canji ne ya same ni irin wanda ban yi zato ba.
KAREEM POV.
Da kansa ya shiryawa yaransa abun karyawa ya dauko lunch box dinsu ya raka su har gurin School bus suka shiga sannan ya juyo ya dawo, dakinsa ya shiga yayi wanka ya shirya ya fito ya shiga motarsa. Family house dinsu ya wuce domin fara gaisawa da iyayensa kamin ya wuce aiki kasancewar yau Monday.
Wani abun da ya sabawa kansa da shi ne, na kin kallon mahaifiyarsa a duk lokacin da ya shiga gidan. Kai tsaye ya wuce bangaren Hajiya Hassana wadda take step mom dinsa. Karyawa ya same ta tana yi tare da Khadija da Aaryam da sauran yaransa Aneesa da Kamla. Kanensa duk suka gaishe shi ya amsa, Yusura dake zaune gefe daya ta mike tsaye ta shige dakin Hajiya Hassana sai a lokacin ma Kareem ya lura da ita. Khadija ta kwashi kayan abincin ta bi bayan Yusura Kamla da Anessa ma haka, sai ya rage daga Step Mom dinsa sai kanensa Aaryam.
“Zaka ci abincin a zuba maka?”
Hajiya ta tambaya.
“Aa”
“Baka cin abinci yanzu, tun da Momynka bata nan, shigowa nan ma sai monday Monday kake yi ka duba mu, idan Momynka bata nan ni da mahaifinka ai muna nan kuma Kanenka suna nan be kamata kana haka ba”
A hankali ya sauke ajiyar zuciya.
“Hajiya Bana jindadin shigowa ne yana yawan tuna min da Momy kuma ina jin babu dadi”
“Tohm ya za'ayi haka tsarin Allah yake, kai kanka mutuwa zaka yi balle kuma wasu, sai hakuri rayuwa ta gaji haka, ni kaina yanzu gidan ba dadi yake min ba Wallahi, amman a haka nake daurewa saboda Khadija da Aaryam da kuma Aneesah, dole na yi walwala idan ba haka ba dukanmu sai mu taru mu takura mu yi ta bakinciki da kuka”
Yayi shiru be ce komai ba. Hajiya ta dauki tissue ta goge hannunta.
“Likita..”
Ta kira shi sai ya kalleta daman haka take kiransa tun Momy na gidan.
“Ni fa ba zan boye maka ba, ban gane manufar abun da ka yi ba, kuma ban gane inda kuka dosa ba”
“Na miye ba Hajiya?”
“Kai da Yusura mana, ta dawo gida kawai tace mana ka sake ta, saki daya biyu ko uku ba mu sani ba, Daddy ka ma fushi yake da kai shiyasa be maka maganar ba har yau, Khadija da Aaryam ma gashi a zaune kullum haushinka suke ji saboda haka”
Kareem ya juya ya kalli Aaryam kyakkyawan saurayi mai jini a jika, sai yayi murmushi.
“Saboda Yusura?”
“Eh mana, Daddynka cewa yayi ba zai maka magana ba, kuma kar wanda yayi maka a saka maka ido kawai, ita kuma ta so barin gidan ni na hana, saboda na san idan Momynku tana raye Yusura bata da gurin zama sai gidan nan, a nan ta girma nan ta saba yanzu kuma dan Momy bata nan babu wanda zan bari ya dauketa ko kuma ita ta tafi ta bar mu, sai idan na mutu, kai ma dan kana ganin Momy bata nan ya saka kake son ka wulakanta amanar da ta baka, to ka sani Yusura ta fika gata a gidan nan, kuma matukar ina raye ni ce gatanta ba kuma zata wulakanta ba”
Kareem yayi gutun murmushi ya girgiza kai, kana ya sake juyawa ya kalli Saurayin Kanensa ya ce.
“Fushi kuke ta yi da ni akan abun da Baku san komai a kai ba”
Aaryam ya ce.
“Haba Big Bro ko dai minene ai be kamata ace ta kai ga haka ba, kai fa Namiji ne, kuma ga yara tsakaninku, kawai dai ban maka magana ba ne saboda Daddy yace kowa ya saka maka ido, kuma ina kasa da kai be kamata na tsuma baki a irin wannan ba sai idan ka bukata”
“Gaskiya ne”
Kareem ya fada tare da aje numfashi sannan ya mike tsaye ya nufi bangaren mahaifinsu, sai a yanzu ya fahimci dalilin da ya saka har yau da suke wata biyu da sati biyu da rabuwa Daddy be taba kiransa ya tambaye shi miye ya faru ba, kuma be taba yi masa maganar ba a duk shigowar da yake gaishe shi a gidan.
A natse ya shiga bangaren kamar yadda ya saba sai bayan da ya zauna sannan ya gaishe da Daddy dake sanye da gilashi yana duba newspaper.
“Lafiya Kalau, Kareem ya gidan ya yaran?”
“Lafiya kalau Daddy”
“Maa Shaa Allah, yau Monday ko akwai aiki”
“Haka ne Daddy”
“Allah ya taimaka ya bada nasara”
“Ameen”
Kareem ya mike tsaye har ya fara tafiya sai kuma ya dawo ya zauna yana kallon Daddy. Daddyn ma ya kalleshi
“Allah yasa lafiya, akwai wata matsala ne?”
Kareem ya hade wani abun da ya tsaya masa a makoshi sannan ya ce.
“Daddy, ban ji kace komai akan dawowa Yusura gidan nan ba”
Daddy ya aje newspaper dake hannunsa.
“Oh wai Yusura, Mijinta ne ya sake ta kasan kuma bata da wani gidan da ya wuce nan, bata da gata a duniyar nan sai mu, zamanta a nan ya takura maka ne? So kake a koreta?”
Kareem yayi murmushi jin yadda Daddy yake fadar mijinta ne ya saketa kamar be san Kareem din ne mijinta ba.
“Aa Daddy ai ban isa na ce a koreta ba”
“Good kara dai da kasan haka”
Ya sake yin murmushi, a yanzu ne ya kara tabbatar Daddy fushi yake da shi.
“Kawai dai na yi zaton ko zaka bincike abun da ya faru ne”
“Abun da ya faru, tsohuwar budurwarka tana zuwan nemanka, amaryar abokinka tana zuwan nemanka ta yi magana sai ka mareta ka ce ka saketa”
Dif Kareem ya dauke wuta kamin ya kalli Daddy ya ce.
“Haka ta fada maka?”
“Ba gaskiya ba ne Daddy, Safeena ta zo gaisuwar Momy ne, kuma na gargade kar ta sake zuwa domin babu wata alaka tsakanina da ita, Noor kuma tana zuwa ne saboda tsabanin da suke samu da Hafiz a lokacin”
“Zan yarda da wannan, domin ban san ka da wani aiki na assha ba, shi ma wannan saboda Hassana ta matsa ne ya saka ta fadi wannan dalilin, amman bayan haka bata fada mana komai ba, ni kuma na auna abun a ma'aunin kishi ne, sai dai kai kuma ka yi kuskure na aikata saki a take”
Kareem yayi shiru kamar ba zai ce komai ba. Daddy ya cigaba.
“Shiyasa na yi shiru na zuba maka ido na gani shin kana da hankali kansan ya kamata ko baka sani ba”
Kareem ya sauke numfashi mai nauyi.
“Daddy, akwai abubuwan da ni da ita muka boye ba mu bar kowa ya sani ba, ban san ya zaka fahimta ba gaskiya ce mai matukar nauyi da daure kai, Daddy ni da Yusura ba mu taba son junanmu ba, ban taba jin ina sonta ba ita ma bata taba jin tana so na, wannan sakin ma ta dade tana bukatar na yi mata shi, saboda da nisanta da ni”
Daddy yayi murmushi mai sauki ya cire gilashin idonsa.
“Kareem karka maida karamin yaro mana, baka sonta bata sonka aka yi muku aure kuka zauna lafiya har kuka haihu ba a taba jin kanku ba sai yanzu da Mahaifiyarka bata raye zaka ce wai baka sonta? Wannan ba hujja ba ce”
Cikin tsananin damuwa Kareem ya ce.
“Wallahi Daddy bana son Yusura ita ma bata so na, kawai dai mun amsawa Momy ne kuma mun zauna saboda ita, ni da ita ba za mu iya bijirewa umarninta ba”
“Okay yanzu da bata raye mu ne abokan wasarka? Kai da ita? Ni ba zan ma yarda ba ku son junanku ba. Kareem zan baka shawara karka yarda ka rasa Yusura, na yi aure tun kurciya har yanzu na zauna da mata biyu a lokacin da mahaifiyarka take raye, mu kan samu tsabani mu yi dadi, wani lokacin har iyaye su sani, amman ban taba ganin matar aure da bata taba kuka da mijinta ba sai Yusura, bata fadin sherinka, bata kawo kararka, kai a gurinka ba abun kunya ba ne aji ka saki matarka? Kuna da yara biyu me kake fada musu? Idan aure kake son karawa you're free to do so ba sai ka saki matarka ko ka wulakanta ta ba, idan har kana fadar saboda Mahaifiyarka ka aureta to miye amfanin sakin a lokacin da mahaifiyarka bata raye? Ke nan ganin idonta kake yi ma biyayya ba saboda Allah ba? Yanzu da ban yi magana ba haka zaka zuba ido ta cika idda? Ko saki uku ka yi mata? Domin bata fada mana ko saki nawa ka yi mata ba, kuma ita bata zauna kamar kai ta kalli kwayar idonmu ta fada mana bata son dan mu ba, Kareem idan ka sake ka rasa Yusura ka rasa matar kirki kenan har abada”
Kareem yayi shiru be ce komai ba, domin ya fahimci Daddy ba zai yarda da duk wani zancensa ba.
“Saki nawa ka yi mata?”
“Daya”
Sai a lokacin Daddy ya sassauta muryarsa ya daina yi ma Kareem fada.
“Ka yi hakuri, shi zaman aure dan hakuri ne, duk can talkaminmu suka tsinke, dole sai an kai zuciya nesa, bana son na sake jin wata matsala a tsakaninku, ka maida matarka dakinta ku zauna lafiya dan Allah”
Kareem kamar zai fasa kuka ya ce.
“Daddy mai daki shi ya san inda yake masa yoyo...”
Be rufe baki ba Daddy ya rufe shi da fada yana masa tsawa.
“Get out Kareem, tashi ka dauki matarka ka aje ta gida sannan ka wuce aiki, wato Momy kake tsoro kana gudun zuciyarta mu kuma ka raina mu ko? Toh ka bari har bayan raina sannan ka saketa idan ka ga dama ka hada har da yayanka ka koresu gaba daya”
Da sauri Kareem ya sauko daga kan kujera yana bawa Daddynsa hakuri, domin idan akwai abun da yake gudu da tsoro a rayuwarsa to fushin iyayensa ne.
“Ka yi hakuri Daddy, na maida aurena saboda kai, kuma zan dauke ta mu tafi gida yanzu kamar yadda ka ce ka yafe min dan Allah”
Daddy ya dauke kai ya kai hannu ya dauki gilshinsa ya mike tsaye ya shige bedroom dinsa. Kareem ya dafe kansa ya rumtse ido, ya fi karfin minti talatin a haka sannan ya dago ya fito daga bangaren ya dawo bangaren Hajiya Hassana ya zauna a falon ya kasa yin komai har sai da Step mother dinsa ta fito sannan ya gabatar mata da abun da ya maido da shi bangaren nata.
“Na maida aurena Hajiya, a fada mata ta fito mu tafi”
Hajiya Hassana ta yi murmushin jindadi.
“Haba yanzu na ji magana, ko kai ba haka ake so, kuma dan Allah ayi ta hakuri karka ce zaka biyewa mace ita mai rauni ce, kuma duk matsala da za a samu a daina saurin saki, muna raye idan ya kamata mu ji sai ka sanar mana mu tsawatar mata yafi ayi ta saki ga yara”
“Tohm Hajiya”
Ya amsa irin amsawar nan na wanda ya rasa interes da mafaka da kuma gata a lokaci daya, daman tun farko yayi tsammanin haka shi ya hana shi sakinta a lokacin da Momy bata dade da barin duniya ba, da ace kuma ya sake a lokacin da take raye Allah kadai ya san irin fushin da Momy zata yi da shi. Ya mike tsaye yana jin wani fever na rufe shi ya nufi motarsa ya bude ya shiga ciki ya zauna yana jiranta bakinciki cike fal a zuciyarsa.
Ya bata awa daya a haka sannan Aneesah ta fito ta bude motar ta ce masa.
“Big Bro wai Hajiya tace ka tafi zata kawo ta da kanta”
“Toh ki fadawa Daddy haka idan na wuce”
Cikin tsananin damuwa Kareem yake maganar sannan ya ja motarsa ya fice daga gidan. Wunin ranar aiki kawai yayi dan ya zame masa dole ba dan jikinsa da zuciyarsa suna cikin dadi ba. Bayan ya gama yana kokarin hada kayansa ya wuce wata mate room ta shigo ta kawo masa takardar envelope.
“Maman Khalid miye wannan”
“Wallahi ban sani ba, wata ce ta zo dazun bata same ka tace bari ta ba ni na aje maka dan Allah kar na bawa kowa sai kai hand to hand”
Ta fada cikin hausarta da bata gama kwarewa ba, kasancewarta bayarabiya. Ya karba fuska ba yabo ba fallasa yayi mata godiya ya hada kayan saukinsa ya fice daga office din. Sai da ya shiga motarsa sannan ya bude envelope din wani kamshi mai dadi ya bugi hancinsa, flower ce farkon abun da ya fara cirewa daga takardar sannan wani sexy chocolate da kuma farar takardar mai rubutu red. Be yi tsammanin ganin romantic abu irin wannan ba sai a Safeena kuma ya canka daidai a lokacin da ya fara karanta sakon na karin shekararsa a yau.
“Happy birthday Love, barka da zagayowar ranar haihuwar mutumen da bana son zama da kowa sai shi, barka da zagayowar ranar haihuwar mai bani farinciki a zuciya da jiki, mai kwantar da min da hankali, mutumen da ke nisantarsa ke haukata ni ta hana ni sukuni, barka da karin shekara My future husband, my partner in crime, the father of my future kids, father to be... I know its your birthday today.. I am sure u will give me treat in a big house like we use to be.. so I shall talk to you in person there, because I don't know to express my feelings in paper, i love you duk yadda kake tsammanin za mu iya rabuwa da junanmu ba zamu iya ba Kareem saboda muna son junanmu, ba zan iya kyaleka a irin wannan yanayin da kake da bukatar wani a kusa da kai ba, i know how painful it's to lost a best friend and Mother. Please take good care of yourself for me...”
Ya girgiza after ya gama karantawa, so today is his birthday gaba daya ma ya manta, daman tun kamin su rabu tun tana girlfriend dinsa ita take tunawa da birthday sai kuma Momy, and even after break up bata daina wishing dinsa ba a duk lokacin da ranar zata zo. Wani gurin ya bude a motarsa ya saka takardar ya rufe ya yi ma motarsa key.
Kusan wannan ne karo na farko da yake jin kamar baya sha'awar komawa gidan all his thoughts is