Showing 159001 words to 162000 words out of 215481 words

Chapter 54 - Ƙaunar Da Ta Zama Azaba by 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

ba, tare muka tafi? Taya zaki tambaye ni”

Ya amsa min kamar da fada, gaba daya na lura daga jiya zuwa yau kamar dai haushina yake ji ko kuma baya son mu yi zaman lafiya. Ya bude motarsa zai shiga.

“Ni fa ba sim din na zo karba ba, wata matsala ce ta faru jiya bayan ka wuce shiyasa na zo nan, babu wanda ya san na fito ma”

Ya kalli ruwan da suka fara dauka ya kalleni.

“Shigo ciki”

Ya rufe motar ya koma cikin gidan ni kuma na bi bayansa muka shiga falon, ac ya fara kashewa sannan ya zauna a hannu kujera ya duba agogon hannunsa sannnan ya kalleni kallona.

“Zauna fada min minene?”

“Baba ne, wai zai yi karar mahaifin Abdull saboda abun da ya faru da Hana”

Mikewa yayi tsaye yana mamaki.

“Ta ina ya ji wannan maganar?”

“Ban sani ba, amman yace wata mace ce ta fada masa kuma har matar da ta zubar mata da cikin ya gani da idonsa, kuma idan maganar nan ta fita, rayuwarta zata lalace ni ma ba zan sake samun wanda zai aure ni ba”

Ya kalleni with so much effection.

“Duk yadda zaki zama Noor akwai wani yana nan yana jiranki, idan duniya da mutanen cikinta suka juya miki ba, shi yana nan tare da ke, babu wani abu da zaki aikata ko waninki ya aikata da zai saka shi gudunki, idan kika ga ba ki da kowa a duniyar nan hakan yana nufin ba shi a raye”

“Waye?”

A madadin ya amsa min sai ya sauke kai ya jefo min wata tambayar.

“Kin fadawa Safeena abun da ya faru da Hana ne?”

“Ban fada mata ba, ni ban ma yi magana da ita bayan faruwar hakan ba, sai dai idan shi ya fada mata, ko kuma kai!”

Ya girgiza min kai

“No ba ni da wata alaka da Safeena yanzu, babu yadda za'ayi wata maganar ta shiga tsakanina da ita, balle wannan sirrinku ne, ba zan iya cutar da ke ko wani na ki ba Noor”

“Me yasa ka ambaci sunanta? Kana ganin zata iya wani abu?”

“Saboda zata iya yin haka, zata iya tona wannan asirin ta hada wannan makircin saboda bakinciki rasa ni, saboda na fada mata ba zan sake dubanta ba, na san na yi kuskure a baya, amman yanzu na gyara komai ya wuce, ta fada min aurenta yana gad da lalacewa saboda kin fadawa mijinta cewar danta data haifa ba na shi ba ne, kuma ya dauki yaran yaje gwada jininsu, ta fada min idan aurenta ya mutu ba zata kyale ki ba, kuma dole sai na aureta ni kuma ba zan taba aurenta ba”

“Me yasa ba zaka aureta ba? Ya zaku yi da dan kenan?”

“Me zan yi da ita? Ko ba ita ba ba zan sake yin aure ba a rayuwata”

“Saboda me?”

“Ba zan auri macen da bana so ko bata so na ba, mace daya nake so a duniyar nan, idan har ba zan same ta ba, to zan hakura da aure ne har abada”

“Wacece? Hafsat”

“Noor... Noor ce...”

Ya amsa min tare da sautin fitar iska, fuskarsa kuma cike da rauni. Na mike tsaye ina kallonsa, sai ya tako ya matso kusa da ni, ya zuba min kalaman da na gagara mantawa.

“Babu wata Hafsat Noor ke ce, i love you so much, tun a farkon haduwata da ke na ka mu da sonki Noor, amman a lokacin baki ganin kowa a gabanki sai Zafeer, bana son na lalata alakarku saboda bana son ki samu rauni a zuciyarki, ni ne dalilin da ya saka Hafiz ya aureki, saboda ya fahimci ina sonki, amman ina tsoron na yi rayuwar aure da babu dadi a tsakanina dake, a kokarinsa na gyara tsakanin ginin da ya rusa na Zafeer da ke, mahaifinki ya Kyautar masa da ke”

Kallon juna muke daga ni har shi falon yayi tsif kamar babu kowa a ciki.

“Kamin ya rasu ya fada min na samawa zuciyata abun da take so, kuma ke zuciyata take so Noor, yarinyar da na baki labarin wani ya riga ni ke ce Noor, ke ce karshen bukatuna, ina son ki Noor”

Na sauke idona kasa hawaye suka sauko min.

“Ina jin zan iya kyautata miki Noor, na baki rayuwa mai kyau, gatan da kika rasa, zan sama miki, burina kullum na ganki a farinciki, but i know I'm not perfect, ban cancance ki ba, you deserve someone better da me, akwai wata kofa da ba zata bude ba a tsakanina da ke, na bata rayuwata na sani, kin fada min ba zaki iya zama da mazinaci ba, ko da ya tuba, kina da gaskiya Noor na girmama ra'ayinki”

Hannu ya saka ya cire hawayen da ya taru a idonsa.

“Ina son murmushinki, ina son dariyarki, ina damuwa idan kin damu, ina jin farinciki da farincikinki, idan na tunaki ina jin nishadi, ina son rautarki i love every about you Noor but I'm weak, ban cancance ki ba, ni ba mutumen kirki ba ne, taya nagartacciyar yarinya irinki zata auri namiji kamar ni wanda ya aje ďa ba tare da aure ba? Kuma da matar wani matar sunna?”

Yayi murmushi

“I'm so lonely, ina fatar kalamaina ba za su bata miki rai ba, i hope ba zaki yanke alaka da ni ba, ganinki ma yana saka ni jindadi, ina son na roki abu daya”

He take one step forward i take one step backward.

“Kawai ki bar ni na rayu da kaunarki, if you ever need someone you know I'm here, daga yanzu har zuwa karshen rayuwa, ina fatan duk wanda zaki aura nan gaba, zai rike ki amana ya baki kulawa irin wacce na so baki, ban miki fatan rashin dacewa duk da yake kaddara tana rabaki da su, tana kara kusancinmu, amman bayan nufin zan aure ki Noor, amman ina sonki Noor na mutu a kaunarki, i was waiting for so long ma fada miki yadda nake ji akanki, ba ni da sauran farinciki a yanzu sai ke sai yarana”

Ya saka hannunsa aljihu ya ciro sim din ya miko min, na daga kai ina kallonsa.

“Ba ni da wata dama na hana kowa rabarki, ina jin kishi saboda ina sonki, amman ba ni da wata hujja ta alakantuwa da ke, amman ko na mutu noor ina son ki sani KAREEM YANA KAUNARKI i wanna tell what i feel in million meaning...”

Juyowa na yi ya nufo kofar fita daga falon da nake jin yayi min kada a yau duk kuwa da irin girmansa.

“Ruwa ake Noor ki bari a dauke ruwan”

Ban juyo ba balle na amsa shi haka na fita cikin ruwan ina hawaye da ban san na miye ba, me yasa bake kuka? Me yasa Kareem ya fada min haka yanzu? Da gaske so na yake ko dai yana son yayi min irin na Safeena ne? Kalamansa sun yi min nauyi sun mantar da ni dalilina na tafiya gidan.
Ashe Zainab ta fadi gaskiya Hana ma ta fada cewar Kareem yana so na.

Tafiya kawai nake irin na wanda ya rasa gurin zuwa, ruwan saman da ake kama da bakin kwarya yana dukana, da na fara gajiya da tafiyar sai na samu wani guri a gafen wani babban gida dake unguwar na tsaya, ina matukar tsoron ruwa da tsawa ko walkiya amman a ranar gaba daya tsoron komai ya fice min a kai. Motar Kareem nake facing dake fake a daidai inda nake tsaye, abun da ban sani ba ina tafiya yana bina a baya har na samu gurin tsayuwa.

Front seat ya bude yana kallona, takawa na yi cikin ruwan na nufi motar na shiga na zauna, a bude na bar kofar har sai ya kwanto ya miko hannunsa ya rufe gambun motar. Wani yanayi nake ji na dabam shi ba tsoro ba, ba jindadi ko akasinsa ba, a yanzu na kasa sakewa da shi, kamar bako haka nake jinsa. A tsawon awannin da muka yi a motar ko kadan ban yarda na kalli hafen da yake zaune. Amman shi nasa idon suna kaina har aka dauke ruwan. Sannan ya tashi motar yana tuki yana kallona har muka isa.

A gaban gidanmu ya faka sai a lokacin na juyo kadan na kalleshi idanuwana suka sauka cikin nasa.

“I'm sorry i hurt your feelings, wata kila kin fi son abota da ni, wata kin fi sakewa idan ba soyayya ba ce, bana nufin bata ranki Noor kawai dai na fada miki ne saboda na samu sassaucin abun da yake zuciyata, dan Allah kar hakan ya saka ki canja min ina jindadin kasantuwata da ke”

Na juya na bude motar na fita, shi ma sai ya bude ya fito.

“Ki sanar da Baba ina waje”

Ban juyo ba kuma ban amsa bana shiga ciki, a zaurenmu na tsaya na rumgume kaina ina wani irin kuka mai karfi amman bana iya barin sautin ya fita, da za a tambaye dalilin kukan ni kaina ban sani ba, zuciyata ta yi min nauyi da bata taba min ba kamar ba zan iya daukarta a kirjina ba haka nake ji. Gefen hijabina na saka na share hawayena sannan na shiga cikin gidan da idanuwa da suka yi ja. Dakinmu na shiga na samu yar'uwata ita ma tana nata kukan.

“Hana me ya faru ina Baba?”

“Ya tafi yanko sammaci ya ce ba zai kyale maganar nan ba, shikenan rayuwata ta lalace”

Na tashi da sauri na fice daga dakin waje na fito na samu Kareem tsaye yana kallon kofar gidanmu.

“Baba ya tafi kotu zai saka karar”

Motar ya bude ya dauko wayarsa ya zagayo ya mika min wayar.

“Saka min number Baba”

Na karba na saka masa jiki na rawa na mika masa kasa ya sunkuya ya aje min sim dina ya juya ya wuce, ina tsaye a gurin ina kallon motarsa har ya bace min.





KAREEM POV.

Be yi nisa da unguwar ba ya faka motarsa ya jingina kansa yana ya runtse ido, wani azabben ciwo yake ji a kirjinsa da ya wuce misali, ya kusa minti talatin tsaye a gurin sannan ya dago ya kira number mahaifin Noor. Da farko be daga ba har sai da ya sake kira. Cikin mutumci Kareem ya gaisa da shi sannan ya gabatar masa da kanshi, sannan ya kora da dalilin kiransa.

“Baba na wani labari na ji marar dadi, cewar an yi ma Hana fyade abun ba dadin fada ma, ban jidadi ba gaskiya sai dai abun da ya fi daga min hankali shi ne cewar da aka yi zaka yi karar wanda ya aikata abun ko haka ne?”

“Haka ne mana, ta ya zan bar wanda ya keta haddin yata ya tafi a banza, dole na kai shi kotu hukuma ta hukunta shi, suna aikata hakan ne saboda suna ganin ba a musu hukuncin komai”

“Haka ne, kaiwa kotu yana da amfani musamman idan har za a musu hukunci, sai dai Baba ina son ka sani kotun yanzu ba irin ta baya ba ce, kuma mutumen nan yana da rufin asirin da zai iya komai dan ganin asirinsa ya rufu, mahaifinsa ma babban mutum mahaifiyarsa ma haka kuma ita ma babban mutum take aure, baka tunanin aikata hakan zai janyo ka jefa rayuwarka cikin hatsari?”

“Bana tsoron komai ni, Allah yana tare da mai gaskiya, tarin kudinsu ko ikon da suke da shi ba zai hana na kaisu kotu ba, shiyasa ma zan yi karar uban ai, domin shi yake gari ba dan ba, kuma ya san dansa ba ban kirki ba ne ya zo nema masa aure? Ko da lamarin nan ya faru ai ya kamata ya zo ya same ni ya ba ni hakuri kuma ya samu dan wani abu ya ba ni ko? Duk be yi ba sai ya zuba min ido yarinya ace har ciki aka zubar mata kamar wata karuwa, ai an fada min kai ka zubar da cikin, ashe kai ma zaka iya cutata Alhaji na yi zaton ai an zama daya yanzu”

Kareem ya shafa goshinsa ya sauke ajiyar zuciya.

“Duka mun yi wannan abun saboda kar kowa ya ji, idan maganar nan ta fita Hana zata rasa abubuwa da yawa, zata takura cikin mutane kuma abun zai zama abun magana ba lallai ta samu mai aurenta a haka ba, dan Allah Baba ka bar maganar nan ko dan mutuncin yaranka, kuma karar mahaifinsa be dace domin ba mahaifin ne ya aikata ba, hakan zai iya janyo alakar dake tsakanin Mama da mahaifinta ta samu rauni”

“Idan ta samu rauni ni miye nawa a ciki Alhaji? Daman ai an fada min Hajara ta boye wannan ne saboda uban wai kar aurenta ya mutu saboda yana da kudi ko, wato ta fi son rayuwarta akan rayuwar yaranta saboda kwadayi da son abun duniya”

“Ina da tabbacin ba dan haka ba ne Baba, saboda kar rayuwar Hana ta lalace ne kawai ba dan wani abu ba, dan Allah Baba karka shigar da karar nan ka tsaya ka yi nazari”

“Na yi iya nazarin da zan yi daga jiya zuwa yau, kuma na duba na ga abun da ya dace na aikata kenan, yanzu haka na biya kudi an yanka sammaci an aika wa ubansa zamu hadu kotu litanin mai zuwa rana irin ta yau”

“Baba zan biya duk wani kudi da ka kashe na kai sammaci kuma zan samu wani abu na baka, zan yi duk abun da ya dace zan dauki abubuwa dan Allah Baba ka bar maganar nan”

“Ka gani Alhaji Kareemu ina ganin mutuncinka sosai ina mutumta ka, dan Allah mu tsaya a matsayinmu kar abun ya wuce nan, ni ba makwadaici ba ne, ba irin uban nan ba ne da zaka ce ka dauki kudi ka ba ni ka rufe baki, wato saboda ka raina kuma ka maida wannan matsalar ba komai ba ko? Shiyasa kake son ka rufe bakina, ba dan na san ka da dadewa ba ai sai na ce Abdullahin ne ya aiko ka, ni ba zan bar maganar ba sai na kwaci hakkin yata”

“Ayi hakuri Baba”

Kareem ya sauke wayar tare da sauke ajiyar zuciya, wannan karon ya kasa shawo kan Baba yana mamakin me aka nuna masa haka da har ya dage dole sai yayi wannan karar, shi dai kam zai iya fada be taba ganin mutum mai zuciyar Baba ba, baya tsayawa tunani idan zai aikata abu.
Nurse da ya saka ta yi ma Hana wankin ciki ce second person da Kareem ya kira after Baban Noor.

“Hello”

“Juwairiyya ya kike ya gida?”

“Lafiya kalau Alhamdullahi ranka ya dade ya aiki?”

“Kwanan baya akwai wata yarinya da na kira kika mata wankin ciki zaki iya tunawa?”

“Eh ba a dade sosai ba ai ko?”

“Haka ne, kuma ina tunanin lokacin da na kiraki na fada miki cewar yarinyar kaddarace ta hau kanta, kuma tana da matukar muhimmanci a gurina shiyasa na kasa yi mata da kaina na saka ki yi, domin zan iya cire ciki ko ya kai wata takwas kuma mace ta rayu, abu da kika san na kwarai a kansa, amman na kira ki na bukaci ki mata ne saboda bana son na ga yarinyar a wani yanayi da be dace ba, abu na biyu duk mai aikin lafiya ya san aikin lafiya sirri ne cin amana ne ka dauko sirrin wani ka yada kin san da wannan?”

“Na sani, me ya faru?”

“Da wa kika yi hirar yarinyar nan? Saboda abun ya zagayo yana bibiyar yarinyar nan”

“Ban yi maganar da kowa ba gaskiya”

“Don't lie to me please, mahaifinta da bakinsa ya fada cewar har wadda ta cire mata cikin ya gani da idonsa”

“Ni Wallahi ban san na samu wani na yi wannan maganar da shi ba, me zai saka na yi haka? Gaskiya akwai dai yadda aka yi amman Wallahi ni ban yi magana da mahaifinta ba ban san ma mahaifinta ba ban san kowa nata ba, wata kila dai ita can ta fada har maganar ta juyo amman ni ban fadawa mahaifinta ba”

“Ba ki yi maganar da kowa ba?”

“Gaskiya ban yi maganar da kowa ba”

“Lokacin da na kiraki na fada miki ciki ne nake son ki wanke waye a kusa da ke?”

“Akwai kawayena guda biyu lokacin mun je barka kawata yar makarantarmu da ta haihu, amman ko su ban yi maganar da su ba?”

“Zan iya sanin sunansu?”

“Yeah Safeena Jafar Ishaq da Amina Alhassan”

Sunan farko da ta ambata ya sanyaya guiwar Kareem a nan ya gane gurin da maganar ta fita, wata kila bata son fada masa cewar ta sanar da Safeena ne, wata kila kuma gaskiyar take fada masa idan har zata boye wani abu ba zata ambaci sunan Safeena ba.

“Mi ya faru?”

Ta tambaya jin yayi shiru.

“Kawai ina tunani ne, wata kila ita ta fada ko yayarta zan bincika ta can na ji a ina maganar ta fita”

“Sai dai idan can domin ni ban yi maganar da kowa ba”

“Okay”

Ya sauke wayar ya bugi sitiyarin motar da karfi.

“Safeena...!!!”

Ya lalobo number Safeena yayi mata kira ya fi a kirga bata daga ba har sai da ya aika mata da sako.

“I need to talk to you abu ne mai muhimmanci”

Few seconds da delivery sms din kiranta ya shigo wayarsa.

“Magana nake son mu yi mai matukar muhimmanci, ki same ni a guest house, yanzu”

Yana fadar hakan ya kashe wayar ya hau titi ya dauki hanyar gidansa da suka saba haduwa.
Ya rigata isa domin shi yake son magana da ita a yanzu, a yanzu ikon a gurinta yake hakan ya saka ta bata masa lokaci na tsawon mintuna arba'in sannan ta shigo gidan. Yana tsaye ta window falon yana kallonta har ta fito motarsa ta turo kofar falon ta shigo.

“Lafiya kake son ganina?”

“Me kike so Safeena”

Kamar jira take sai ta sauke gyalenta ta aje jakar a kujera ta nufo shi tana nuna shi.

“Kai Kareem kai nake so!”

“To miye matsalarki da Noor? Miyasa kike cusata a cikin matsalarmu?”

Ya tambaya ba tare da ua juyo ba hannayensa duka biyu suna zube a aljihunsa.

“Saboda Noor ce ta raba ni da kai, Noor ce macen da ta cike gurbina da ita, kuma ita ce ta kashe min auren da takardar kawai ya rage Abdull ya ba ni”

“Ban cike gurbinki da na noor ba, wani gurbi na gina mata mai kyau mai tsabta, mai cike da kauna da soyayya, dan Allah ki cireta a cikin matsalarki”

Har lokacin da yake maganar be juyo ya kalleta ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login