Showing 114001 words to 117000 words out of 142992 words

Chapter 39 - GARGADA SO Gasar da Lokaci By M Shakur

M Shakur   

21 Sep 2026

261

taji amman saita daure ta mike tashiga hada abubuwanta tadauki car key suka fito tare ita tana rikeda platter Ni ima na rike da rose din har zuwa inda motar Hawwa yake, Ni ima sai kallon motar take tanaji kaman tahadiye zuciya ta mutu idanunta harsun kada sun chanza, abayan motan sukasa komi Ni ima na kallon motan irin wannan fa ba tokunbo car Hawwa ke dashi ba no, asalin sabuwa gal ce, komi na motan ba ariga an daye mata ledaba, maida kofan bayan Hawwa tayi tarufe tace  bye tawuce ta shiga gaba Ni ima na tsaye tana kallonta, Hawwa taja mota tabar wajen abinta, da kyar Ni ima ta iya wucewa zuwa wajen tata motar zuciyanta kaman an barbada busheshen barkono da danye tsabagen azaban radadi dayake mata, sai kawai ta tsaya tana kallon motan ta, motar Hawwa tada Toyota Camry ce 2006/2007 ita lokacin da Baban Yaseer yabata Camry nan na 2014 kaman zata haukace dan tafi na Hawwa kyau da tsada gata latest, but yanzu dataga motan da Hawwa keja benz datakai irin 150M sai taji ta tsani tata motar, saitaji ta rainata, wai tayaya ma rana daya Allah zai dauki miji mai bala in kudi yabama Hawwa ne? Eh? Within a blink of an eye rayuwan Hawwa ya chanza kakap, big phone iPhone 15 pro max, ita tana fama da Samsung S21 dinta da ada takejin dadi yafi na Hawwa S10, Hawwa ce big car, ga sadaki mai tsoka, ga gwalagwalai, Hawwa ko sisi taki bata, da dane da hala yanzu Hawwa tabata like 20M from that sadaki wlh dan Hawwa bata kyashin bata abu, Hawwa is going to big house now and yaron seems to love her alot, jibi yanda yake bata gifts, ranan su diamond agogo dasu turare yau abinci da flowers masu tsinannen kamshin dadi, he s so romantic, she thought babu miji that will be as sweet and romantic as Baban Yaseer yanzu taga wanda"

yafisa.

Hawwa ta hadu da irin gayen kan taki fadamata har sai bayan tayi hauka? The way suke soyayya

"hakan nan she can swear Hawwa tadan jima da sannin gayen? Wannan dayaketa bata gifts sunyi sex ne? Hawwa is so happy she wants her to be sad, tafison taga hawaye da bakin ciki da bacin rai da damuwa akan fuskanta, wannan gayen ya shigo rayuwanta yasa Hawwa ta chanza bata damu da itaba yanzu, imagine wai ita Hawwa ke shama kamshi, what will she do yanzu? Da kyar ta lallaba tashiga motan ta tada tabar wajen tana tana tafiya akan titi tazo ta wajajen banex ta kalli masu bara dake wajen, sai kawai tayi parking motan tafito taje wajensu tace  zan baku kyautan kudi sosai amman saikun bani wayanku na tura wani sako har rige rigen bata wayan ake, kakkarba tayi marasa kati har tana samusu ta bank dinta, sako tashiga turama number Khaleel da kusan duka number su sannan ta basu 5k suraba tawuce"

takoma mota tana murmushi taja abinta zuwa gida.

**

Khaleel na cikin mota tareda Sam wayanshi yayi kara daukan wayan yayi yaga messages guda 5

"from different numbers hardly unknown ke kiranshi ma talk more of sako, kaman bazai budeba saikuma yabude daya."

 _Hawwa is a whore! Tsohuwan karuwa ce she sleeps with everyman dayake zuwa yace yana sonta

saisa suke guduwa basa aurenta sabida tabasu abinda suke nema_

Chak Khaleel ya tsaya yana kallon messege din to be very very honest he doesn t care idan Hawwa

"sleeps around or not cus yasan tun zamanin da wato old days aka daina samin virgins, konji is real babu yanda za ayi yataso maka baka nemi wanda you will sleep with ba so what ai d ane tayi, baida right to judge her life is not easy takai this years 29 without a man, shi tun yana 24 yafara ai, but dudda haka saiyaji still zuciyanshi namai wani iri sai kawai ya ijiye wayan da sauri without opening sauran messages din ahankali yace  park the car Dasauri Sam yace  lafiya? We are not there yet dan murmushi Khaleel yamai yace  just give me a moment fita yayi daga motan yafara tafiya zuwa chan gefen titi baitaba sani akwai randa za a gayamai wata yar iska ce harma yaji abun yadameshi ba, ko yadingajin ciwo aransa ba, duk sai yaji wani iri, who even send the message? What if is Hawwa? He don t think she will ever defame kanta dudda yasan batason auren su but Hawwa is someone that value self respect and image nata, ko kadan batason compromising self respect and imagine nata saisa he even use that picture and threaten her with it, cus yasan she will not want him to expose that koda ba gaskiya bane dan she values her self respect, juyowa yayi yakalli Salman daya fito daga motan yana kallonsa da hannu yama Salman alamu daya daukomai wayansa amota daukowa yayi yazo wajen yakawomai dasauri ya karba yabude second"

message din.

 _Hawwa babe din boss dinta ne DIG she slept with him in order ya dauketa yasata a task force din

nan dan she was an ordinary police girl before without any star_

Sai another message.  _Officer Hawwa sleep with yaran office example Abraham data girmeshi da

"shekaru slept with Hawwa countless times_ ,"

Yanda zuciyan Khaleel ke bugawa kasa cigaba da bude sauran messages din yayi ya manna ma

"Salman wayan a kirjinshi yace  track those numbers all of them for me, track them! I need information uuughhhhh! Ya dunkule hannu yayi punching air yawuce fiuuuu yatafi mota ya shiga da kanshi yarufo da mahaukacin karfi akaja motan Sam yace  lafiya are you okay ? Lumshe idanu yayi yaki magana har"

sukakai party saukowa yana shiga yadauki about 5 shots na tequila yana sha Sam yace  Lee are you okay? Why are you drinking like that ko kallonshi baiyiba shaye shayen dayahau yi saida yabama duka abokanshi tsoro saida yay1 total out sannan Sam da Moh suka kaishi sama aka kwantar dashi agado Moh yace  kasan what s wrong with him ? Girgixamai kai yayi suka wuce suka fita daga dakin aka barshi

warwas agado.

"[10/6, 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE "

"Washegari Khaleel yafarka adakinsa da kyar ya lallaba yaje yayi salla wuraren 9, ko wanka baiyiba"

"yafito yasauko kasa Mommy na falo tace  good morning Son ko kallonta baiyiba Noor ta taho wajenshi da gudu tace  Daddy kanta yashafa kadan yace  go to grandma I m coming Noor yafice idanunshi sunyi ja duk sun nuna alamun bacci, yayi waje yana kallon Salman daya taho da sauri Khaleel yace  ya? Salman yace  we tracked the numbers duka numbers din beggars ne dake hanyar banex, da kyar bayan nabasu kudi suka iya sanar dani wata mace ce tazo tabasu 5k tayi amfani da wayansu dasauri Khaleel yace  did you ask them description nata? Salman yace  yeah wai batada tsawo sosai she s very fair and da Toyota tazo shiru Khaleel yayi kaman mai tunani, kawai yawuce wajen motar sa Salman yabiyosa ya shiga driver ma yashiga sukabar gidan, ahankali cikin muryan gajiya da bacin rai yace  my wife s house "

jan motan sukayi har zuwa unguwan su Hawwa.

Baba na kofar gida azaune da aswaki a bakinsa ya hango mota yasan Khaleel ne kawai sai yafara

"murmushi kafin ma abudemai Khaleel yabude da kanshi yafito Baba ya tsareshi da idanu ganin idanunshi adan kumbure hakama fuskanshi dasauri Baba yataso shima Khaleel yawuce wajen Baba kafin yayi magana har Baba yakai hannunsa kan fuskanshi cikeda so yace  bakada lafiya ne Ibrahima ?Baba Khaleel ya kalla dan ranshi abace yake yayi shiru yakasa magana sai dan huci da yasauke Baba sai kawai hankalinsa yatashi yace  meya sameka? Tell me ? Dan ijiyan zuciya yasauke yajuyo yakalli Salman da hannu yamai alamu yakawomai wayanshi wayan aka kawomai muryan Khaleel ba dadi yanunama Baba wayanshi yace  Baba wasu sakonni aka turamin marasa dadi bazan iya karanta maka ba kaima, nasa ammin tracking number yadanyi shiru Baba da gabanshi ke faduwa yace  ina jinka gayamin menene ke faruwa ? Cikeda jin zafi Khaleel yace  Baba matana ta batamin rai sosai, ina kyautata zaton har yanzu"

"tana tareda mahaukaciyan nan, so nazo na ganta ne "

Dudda Baba baiga sakon ba but ayanda yaga Khaleel yasan Ni ima tayi wani abu ranshi inyayi dubu

"yabaci tsabagen bacin rai yace  muje ka shiga gidan kacimata mutunci ba anan waje zan kiramaka itaba, ai gidana nakane ban maka iyaka da ko ina acikin gidannan ba, muje Baba yayi gaba Khaleel yabishi abaya suka shiga cikin gidan ko ina a gyare ta buga sallama gaban dakin Hawwa, Ammi ta amsa yace  da mijin Hawwa nazo Zainabu Hawwa dake zaune daga ita sai dan rigan bacci tana danna wayanta dasauri tadauki hijabi tasaka dark blue har kasa, ita dama Ammi da hijabi ajikinta Ramla kuma na kitchen tana aiki dasauri Ammi ta tashi da fara a tace  bismillah bismillah kushigo shigowa Baba yayi Khaleel biyeda shi abaya, kan Khaleel na kasa yace  ina kwana Mom  muntashi lpy Khaleel ahankali Baba yace  biyoni Ammi binshi Ammi tayi suka fice daga dakin tareda maido musu da kofan suka rufe, Khaleel yazuba hannu a pocket nashi yana kallon Hawwa dako dagokai batayi ta kalli inda yakeba, kaman ma batasan da mutum awajen ba, Babu wasa kan fuskanshi rai abace yace  wacece ke tareda ke jiya a office? Batare da Hawwa ta kalleshi ba tace  da wanda nake tare, ko wanda nai magana, ko wanda nagani a office is none of your damn business ran Khaleel abace ya daka mata tsawa da saida dakin ya amsa.  Nace dawa kike tare jiya an office! ? Dagokai Hawwa tayi adan tsorace sabida yanda yayi mata tsawa ta tabbata anji a tsakar gidan, tashi tayi daga gadon ta taho inda yake dasauri dan bataso su Ammi suji tanamai ihu suhau mata fada akanshi, hakan yasa tace  who do you think you are kanamin ihu aka? Ran Khaleel abace yanunata da hannu yace  dawa kike tare an office jiya?  My friend! Hawwa ta amsa kai tsaye ganin yadameta da tambayan, cikeda jin haushi tace  I was with Ni ima me akayi? Sabida an auramin kai saina tambayeka kafin naga kawata konai magana da kawata ? Wani irin fizgota Khaleel yayi yakai hannunshi zuwa wuyanta ranshi abace yace  what is so special about that witch of a woman da kin kasa"

hakura da ita? Are you a lesbian!? Are you really into girls?

Ja idanun Hawwa suka soma yi tafara dukan hannunshi hakan yasa yasaki wuyanta tadanyi tari

kadan sannan ta kalleshi tace  da aurenka gwara zama da Ni ima! At least ita bata living wayward life irin naka! Radadi zuciyan Khaleel yafara sai kawai yakara fizgo Hawwa yakama kafadunta ya matse yana kallon cikin idanunta zuciya yakaimai wuya da kishi kai da komi ma ganin yanda Hawwa ke son Ni ima yace  idan nakara ganin ki da yarinyar nan i will killl her! I will ruin her life! I will make her life a living

"hell you know me so well to know duk abinda nakeso nayi sainayi, stay away from that witch evil vile"

woman inba hakaba saina kasheta!

"[10/6, 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE "

"Ayanda yau taga idanun Khaleel saida Hawwa ta tsorata wlh, bata taba ganinshi haka ba, yanda"

"ranshi yakai ga baci yasa kawai ya turata yajuya yabude kofa yafito Baba da Ammi na tsakar gidan sunyi charko charko a tsaye, yama kasa kallonsu sabida baison suga kwayan idanunshi yawuce zaure da sauri Ammi tabiyoshi daidai ya shiga zaure tace  Ibrahim! Chak Khaleel ya tsaya batare daya juyoba, dasauri Ammi ta taho tazagayo ta gabanshi sai kawai Ammi tasa hannu takamashi ta zaunar dashi kan bench dake zauren ahankali yazauna sai kawai yakai hannayensa biyu yarufe fuskansa yafuzar da iska masu zafi kaman zai kama da wuta sakonnin nan nacimai rai, ahankali Ammi tace  it s okay ya isa Khaleel ya isa sauke hannunshi yayi ya gyadamata kai ahankali yace  thank you Mom anatse Ammi cikin hikima tace  can you show me sakonnin da aka turamaka game da Hawwa ? Araunane ya girgiza kai yace  Mom banso kowa yagani, sirrin matana ne I can t show you banso kumata wani kallo kirji Ammi tanuna tace  nine mahaifiyar Hawwa, show me Ibrahim idan akwai abinda yakamata namaka bayani zan maka, banso ku fara aure da zargi ko kokonto aranka, ayanda abin ke tafiya nan gaba hala za a iya maka sakonnin dayafi wayan nan daci ma da tada hankali ma, so show me Allah yasani sabida nauyin Ammi dayakeji ne yasa gently yamikama Ammi wayanshi daya bude mata message yace  5 numbers suka turo sakkonni, nasa anmin tracking akace lambobin wasu beggars ne, jiya danai magana da ita suna tare a office dinta, I believe somehow she took my number from wayan Matana batare datasan anyi ba duka sakon nin Ammi tabi takaranta ran Ammi yama Ammi badadi sai kuma takaraji ta natsu da Khaleel tama aminta dashi gabaki daya, dawani ne da yasaketa yace yafasa aure but shi yazo kawai yayi warning nata kan zama da Ni ima ne, ahankali tace  Khaleel wlh karyane kazafi akeso ama Hawwa! Babu wani abu na Hawwa daban sani ba, Ni ima so take takashe auren ku, wlh Hawwa bata taba soyayya da Oganta ba, Hawwa maza tsofaffi ma basa burgeta, sheri ne diyata ba haka takeba, sai kuma abokin aikinta Abraham tabbas ta sanar dani yaron na bibiyanta shima bawai ya iya yafurta da bakinsa yana sonta ba, ai bata bashi fuska, yana mugun shakkanta, Hawwa bazata taba iya soyayya da wanda ta girma ba Khaleel kuma wanda yake ba addininta ba, saikuma na karshe sauran samarinta anatse Ammi tace  Ibrahim Hawwa na can be everything, stubborn, mafadaciya da sauransu amman Hawwa na ba mazinaciya bace! Dudda ta dade batai aure ba bata taba kallon zina as solution na matsalolinta ba, duk ina maka bayanin nan sabida ni uwa ce bazanga ana so akashe auren y ata naja baki nai shiru ba, duka sakon nin nan karya ne"

"Khaleel koda bakai trusting Hawwa ba trust me ni mahaifiyarta, I will never lie to you kaji ."

Sosai Khaleel yake kallon Ammi natsuwan da tun jiya yakasa samu bayan yaga sakonnin nan sai

"Ammi tabashi natsuwan in just few minutes ya yarda and he believed her, gyadama Ammi kai yayi ahankali yace  I know! Deep down I know my wife is not like this, kawai bansan mesa zuciyana keta zafi yana radadi ba bayan na karance messages din yasan inda Hawwa yar iska ce da bazata taba tsanan halinshi ba, sabida batayi saisa she despise his way of life, dan murmushi kadan Ammi tayi tace  sabida kana sonta ne saisa kakejin haka! Tsare Ammi Khaleel yayi da ido jin tace yanason Hawwa bayan shi yasan baya sonta he just wants to show her he can have her idan yanaso, ahankali Ammi tace  Khaleel aure dole agina foundation da trust, you have to trust matarka, itama matarka have to trust you, ta hakan ne zaku iya strengthening bond naku ta yanda babu any makiyi dazai iya zuwa ya jijjigaku kaji "

gyadama Ammi kai yayi ahankali Ammi tace  tashi kaje gida kai wanka Ni ima zanje har gidansu naga

mahaifiyarta gyadama Ammi kai yayi baiso yagayama Ammi what he s planning dan zata iya hanashi

"but Ni ima zatasan she messed with the wrong person this time, tashi yayi yawuce haryakai kofa saikuma yajuyo hada ido sukayi da Ammi kai yadan sosa yana sauke idanunshi kasa ahankali yace  thank you Mom for guiding me yana maganan yawuce yafita Ammi tai shiru tana kallon inda yabari saiga hawaye ya sauko daga idanunta daidai Malam na zuwa zauren ahankali Ammi tace  Malam ina alfahari da wannan miji dakama Hawwa hakika Hawwa tai sa a! Hawwa tai dace ahankali Baba cikeda damuwa yace  nagode Zainabu da babu ke da bansan yanda zanyi handling issue din nan ba, me Ni ima ta turo a sakon ? Karantama Baba sakon tayi tass sannan suka tashi suka wuce dakin Hawwa tana zaune ganinsu yasa ta tashi ta taho wajen Ammi tace  Ammi wlh ita tazo wajena an off& & . Tassss! Ammi ta yanka mata mari mai kyau da lafiya Baba yace  nagode Zainabu! Hawwa ta dafe kuncinta dasauri, wani irin feeling Ammi keji aranta, irin after much struggles da wahala da kata katan rayuwa da gori, habaici maganganun banza, gulman makota da mutanen gari, kasamu ka aurar da diyarka wata yar iskan kawa na kokarin kashema yarka aure, cikin murya mai rauni Ammi tace  Hawwa magani Ni ima tabaki a abinci kikaci da bazaki iya rabuwa da ita ba ko me? What did I tell you about that girl ranan nan? Ni da mahaifinki nan mun gayamiki Ni ima bata kaunarki kona miskala zarratin, ta tsaneki, kukanta kukan mazuru ne, kukan karyane da yaudara, so tabiyoki jiya office kika bari tazo, kinsan cewa Ni ima ta dauki wayanki a sace ta kwashi number mijinki? Hawwa dake dafe da kuncinta tana kallon Ammi da mamaki tabude baki in disbelief, tace  Ammi karya yamiki kawai ya tsani Ni ima ne  kinci mai garinku Hawwa kaniyanki Baba yamata dakuwa yatsunshi kaman zasu shiga kwayan idanun Hawwa yace  mijinki kike kirada makaryaci ? Sauka kanta tayi kasa ahankali, Ammi tace  ta aikama Ibrahim sako cewa DIG oganki, Abraham da duk duka samarinki dasuka gudu jikinki kike basu suna amfani dake dawani irin sauri Hawwa takalli Ammi, Ammi tace  tayi amfani da wayan masu bara jiya at exactly 2:15

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login