Showing 66001 words to 69000 words out of 142992 words

Chapter 23 - GARGADA SO Gasar da Lokaci By M Shakur

M Shakur   

21 Sep 2026

250

wajen gadon yadan kalli Baba in very cute and dan shagwaba voice yace  Baba don t pay attention to whatever she says yashiga auna BP Baba duk Baba yana kallonshi, chan ya saurari pulse nashi da heartbeat sannan ya ciccire komi yace  jininka yahau kadan a little sleep da magani will help zansa akawo ma yajuya zai fita ahankali Baba yace  Ibrahima! Juyowa Khaleel yayi ahankali babu wanda yataba kiran sunanshi ahaka sai Baba, tsayawa Khaleel yayi gaban gadon gently Baba yace  kaima likita ne ? Ahankali Khaleel ya gyadamai kai yace  eh gyadamai kai Baba yayi saikuma ahankali yakai hannayenshi dake rawa rawa yakama duka hannayen Khaleel yarike Khaleel ya kalli yanda yarikemai hannu yayi shiru, baki Baba yabude ahankali zaiyi magana saiya fashe da kuka irin na manya dinnan, Khaleel yayi shiru yana kallonshi sai kawai yaji he s feeling bad, like really bad, he can t remember the last time he felt this bad for anyone in his life, cikin murya mai raunin gaske dan maganganun Ni ima sun taba Baba dudda bai nunaba yace  yau Ni ima ta goranta mini, ta zageni, ta zagi y ata duka agabana cikeda damuwa Baba ya tsagaita kukan saiya kalli Khaleel yace  Ibrahima zuciyata batamin dadi ko kadan banmasan mesa nake gayama ba amman har cikin jinina nake jinka wlh, Allah ya dauramin kaunarka kaman danda na haifa Baba yaja hanci yace  banda komi ko ada chan kaji nake gasawa da sauransu Hawwa tana around shekara 6-7-8 haka mukai hatsari mahaifiyarta tarasu nikuma nadawo haka saida aka guntulemin kafa daya, da kyar da wayyo Allah nasata tagama sakandire Allah yamata baiwan iya dinki kwandala nawa babu akaratunta na jami a ita tasa kanta hartai masters tace zata fara aikin yan sanda, Hawwa ke kula damu da kannenta komi na gidana Hawwa ne, wata kila inda bata daurama kanta dawainiyan mu ba ta takura kanta harta fara aikin yan sanda ba da hala by now tayi aure nima inada laifi ya goge hawaye yace  babu mai neman y ata babu maison ya aureta an tsani Hawwa na, bansan yanda zanyi ba, hawan jini yakama Hawwa sabida tunani da damuwan mesa batai"

"aure, kanninta hudu mata duk sunyi aure hadda yara, yaran unguwa dasuka taso tareda Hawwa wasu"

"yaransu hudu biyar ma, dudda bata nunawa dan tanada jarumta da taurin zuciya amman damuwa"

"yamata yawa, narasa yanda zanyi babu maison auren Hawwa na wayyooo Allah na kaico na amma y ata gorin aure Baba kawai yacigaba da kuka da zuciya daya, shi kadai yasan kalan damuwan dake zuciyansa, Khaleel yakai kusan 2min kallon Baba yake chan kaman mai koyan magana yace  inaso na auri Hawwa Baba! Dawani irin sauri Baba yadago kanshi yakalli Khaleel danjin zancen yayi kaman saukan aradu, bakinshi har rawa yake yace  Ibrahima kace zaka auri Hawwa? Gyadamai kai Khaleel yayi ashagwabe, bayan hannu Baba yakai ya goge fuskansa tass da sauri yana kallon Khaleel din yasake maimaitawa.  Ibrahima kace zaka auri Hawwa ? Gyadamai kai Khaleel yayi yace  eh Dasauri Baba yace  kasanta ne ? Gyadama Baba kai yayi sounding like sangartaccen yaro din nan yace  inada Baby her name is Noor antaba kidnapping nata shine Dady na yakira wajen aikinsu ita ta tayamu nemo Noor lokacin nafara ganinta kenan sosai Baba ke kallon Khaleel da yanda yaron ke magana kana ganinsa kasan dan gayu ne irin yaran masu kudin nan, yan gata he s so adorable, washe baki Baba yayi yay kosasshiyar murmushi saikuma ya dakatar da murmushin yace  Maza da dama sunsha zuwa suce sunason Hawwa dazaran nace su turo magabatansu shikenan bazaka kara ganinsu ba, bazan takura maka ba Allah yasani zuciyata ta natsu dakai idanhar da gaske kake kanason Hawwa kaje kazo da iyayenka zuwa layinmu da magriba, kome yasamu ka kawo zan baka auren Hawwa, idan yaso bayan ta warke sai ayi maganan tarewa da sauransu kaji, layinmu yana nan kayin gwadabe babu wanda baisan Baba gurgu ba kuzo ina jiranku ahankali Khaleel na kallonshi yace  okay Baba the way yake sounding whenever he talks kaman Baby yasa baba yace  shekarunka nawa Ibrahima? Ahankali yace  32yrs murmushi sosai Baba yamai sai kawai yakai hannunshi ya shafa kanshi zuwa gefen fuskanshi yace  Allah maka albarka yarona murmushi Khaleel yayi kadan saikuma kawai yahau gadon yazauna kusada Baba kaman dan yaro"

"yadaura kanshi kan kafadan Baba, shi kawai yanason Baba without any reason."

"[9/23, 8:59 PM] M Shakur: GARGADAN SO "

M SHAKUR

EPISODE

"Sundanyi nisa ahanya yasa hannu yadauki wayanshi yayi dialing number Babanshi, Musbahu PA"

Excellency ya dauka yace  Khaleely Babanka na kan chamber cikeda isa yace  I don t care kaimai waya cikeda lallashi Musbahu yace  Allah huci zuciyan yallabai bari na kaimai Khaleel na kan layin kusan 5min

sannan yaji muryan Babanshi a speaker yana excuse me sai chan Excellency yayi magana cikin so da

kewa yace  Khaleely na ya akayi? Ina tsaka da meeting? Meya faru bakada lafiya ne ? Dan kishingida

"yayi murya chan kasa yace  I will send you address na wani anguwa kasameni awajen by 6, kazo da trust friends naka dasauri Excellency yace  angama yarona zanzo, but meke faruwa lemme know wat I m coming there for shiru Khaleel yayi kaman bazaice wani abuba chan yace  I want to marry someone Pops dasauri Excellency yace  aure? Aure Son? Ba mamanka is the one handling all of that for you ba, an mata screening ne ita wacce kakeson auren? Why do I have to come our lawyers da Malamai can take care of the aure for you, is my presence necessary ? Kai tsaye Khaleel yace  ai nasan dasu nace kazo Pops dan tausasa murya Excellency yayi yace  I know, I know, karka bata rai I didn t mean to hurt you, zanzo kawai nayi mamaki ne this is the first person dakake neman aure da kanka batare da Mom naka ta zaba maka ba ta auro maka ba, wacece yarinyar? Kai tsaye yace  that police girl dan zaro idanu Excellency yayi yace  you mean officer Hawwa wacce ta ceto Noor? That criminologist ? Murya chan kasa Khaleel yace  uhmm dan shiru Excellency yayi sai chan yace  Khaleely are you sure about this decision? Cus naga yarinyar is hot tempered, bakaga yanda kuketa fada rannan ba, and you guys are almost age mate fa dan ba karaman yarinya bace, banson wacce zatazo tana baka ciwon kai ba tana wahalar da d ana fa, I dislike stubborn girls ahankali Khaleel yace  I can handle her Pops, I just wanna have fun with her Pops don t worry dan murmushi Excellency yayi cikeda kaunar yaron nashi yace  you know I will always give you kome kakeso ko? You have my support, see you by 6, I love you yarona Khaleelyn Babanshi dan smiling kadan Khaleel yayi ya katse wayan ya yar agefe yadago kanshi yakalli Salman yace  I want every info akan mahaukaciyan nan and that photo boy of hers gyadamai kai"

Salman yayi yace  yes sir kallon driver yayi yace  Sam s house .

Wani tamkeken estate suka wuce suna zuwa gaban gidansu gate yayi scanning motansu kawai

"yabude musu suka shiga, budemai kofa Salman yayi Khaleel ya sauko yawuce ya shiga flat din Sam dayake bangare daban aka budemai kofa, tundaga falo yake jiyo ihun Sam din tareda na mace, tsaki yayi yawuce wajen dinning inda yaga wine, wine cup yadauka yaje fridge yazuba ice sannan yazo ya tsiyaya wine din ya zauna yafara sipping yana jiyo ihunsu wlh sun isheshi, bacci yakeji, dan gajeren tsaki yayi ya ijiye wine glass din kawai yawuce sama kai tsaye yabude kofan dakin yashiga Sam yadago kanshi yana nishi kaman kwado yace  Hi cousin mugun kallo Khaleel yama yarinyar dayake abun da ita yace  get out! Dasauri yarinyar ta fixge jikinta ta duka tana kwasan kayanta ta wuce tafita Sam rai abace yace  wai kai mehaka ne eh? I m not done fa Dan iska kawai mai bakin hali tsaki Khaleel yayi yawuce abinshi"

ya shiga next dakin yafada gado yana lumshe idanu bacci yakeji sosai.

Kusan 20min Sam yadauka dan saida yayi wanka sannan yafito yashiga dayan dakin yana kallon

"Khaleel dake lumshe idanu yace  ya akayi Lee ? Da muryan bacci yace  wake me before 6 zamuje daurin aure Sam yace  wani daurin aure wazaiyi aure? Yana kulle idanunshi yace  me ? Dasauri Sam yazauna bakin gadon yana kallonshi yace  yaushe aka fara daura maka auren gayyatan jama a? I thought a seminar room na gidanku ake komi ? Hamma Khaleel yayi yace  this time is different  wazaka aura ? Sam ya tambaya da kosawa, Idanun Khaleel a kulle yace  that Police gurl fashewa da dariya sosai Sam"

yayi yace  Leee bakada mutunci shegen gari! Ai nasan after all that girl said you must find a way to show

"her who s the boss, there s nothing da zakaso da bazaka iya samun shi ba, and comfortably use it and"

"dump it murmushi kadan Khaleel yayi yace  starting tonight! She will belong to me! Sam na annashuwa yace  use her kayi BDSM kamata lilis, 50shade of Lee zakai da ita dan dariya kadan Khaleel yayi murya chan kasa da bata fita da kyau sabida bacci yace  she s sick I don t wanna hurt her now! Da sauri Sam ya kalleshi jin maganan dayayi which sounds so unlike him yace  Lee mekace? Cousin? Kai Khaleel? Yakai hannunshi yayi tapping nashi amman ina yayi bacci, dan murmushi Sam yayi yace  shegen yaro to ahaka zaka auren? Lemme call Balalau designer kiran designer yayi aka turamai bespoke manyan kaya dayawa na gizna ya zabanma Khaleel milk shiya dauki ash yatura kudi around 4 aka kawo musu kayan wuraren 5:00PM wayan Khaleel yahau ringing ganin Pops ke kiranshi yasa Sam yashiga tadashi da kyar yatashi wayan Sam yabashi karba yayi yasa a kunne yana lumshe idanu yace  gamu a hanya already gyadama Pops kai yayi yace  okay Dasauri Excellency yace  bacci kake ne Khaleelu? Ahankali yace  uhn cikeda so yace  okay tashi kashirya sannu stop stressing yourself katse wayan yayi yana kallon Sam dake shiryawa baiyi magana ba Sam yace  jekai wanka ga kayan ka nan my gift for ango dan tsuki yayi kawai yatashi yafada bayi yayi wanka yafito jallabiya mai kyau yasa ya shimfida dadduma yayi la asar yana idarwa Ga mamakin Sam saiyaga yawuce yana bude kayan without"

complain cus baison saka manyan kaya yafara sakawa Sam kawai ya tsaya yana kallonshi& & .

"Tun around 4 Baba yabar asibiti yakoma gida, yana kwalama Ramla dabata dawo hospital ba sabida"

"Ammi tacemata yazauna kawai an basu abinci kira, dasauri tafito tace  gani Baba murmushi yayi yace  dauko hijabi kibini kofar gida tabarmai zamu shimfida kaman zanyi baki da yamman nan biyo Baba tayi har dakin Umma data hadarai Baba ko kallon inda take baiyiba yashiga kwaso tabarmai daga dakinshi yana bata taba karba sannan suka wuce waje tare tashiga shimfidawa yace  bari na leka gidan Malam Sama ila Allah yasa yana nan yawuce yana kallonshi yashiga sallama a gidan dake just 2 houses daga"

nasu.

"[9/23, 8:59 PM] M Shakur: GARGADAN SO "

M SHAKUR

EPISODE

Fitowa Malam Sama ila yayi Baba suka gaisa sosai Baba yace  Malam Sama ila kai kadai nake

"sanarma da maganan nan sabida koda abun baiyuba kar kunyan duniya yakamani yadan sauke ijiyan zuciya yace  inasa ran wani yaro dake neman Hawwa zai kawo mahaifinshi da mangariban nan suna zuwa nakeso na daura musu aure shine nace bari nazo nafada maka tunda kaine Babban amintacce na kuma limamun masallacin mu cikeda farin ciki yace  Alhamdulillah, Alhamdulilah ubangiji Allah ya tabbatar da alkhairi, matar mutum kabarinsa inji hausawa, bakada matsala ina nan ai duk sanda suka zo sai nabada sanarwa a masallacin a tsaya gyadamai kai Baba yayi jikinshi narawa yace  akwai wani abun da ake bukata ne a masallaci kowani abu, kaga duk su test din nan ba matsala bace Hawwa wajen aikinta duk bayan rabin shekara 6month sukeyi, nasan AA ce Hawwa zata iya auren kowa, sannan Hawwa na batada wani cuta, banson tambayoyin nan suhanani auran da ita dan Allah kadama kayi Malam Sama ila murmushi Malam Sama ila yayi yace  kada kadamu bazan yiba Baba yace  yauwa bari nabaka kudade adan fefesa turare a masallacin asa yara su gyara cikin kudaden daya dauka dazu dazaije asibiti yazare 20k yamikamai Malam Sama ila ya karba Baba yawuce yatafi Malam Sama ila yabishi da kallon tausayi yace  Ya Allah kadubi zuciyan tsohon nan ka aurar da yarshi kada ka kunyatashi saikuma kawai"

yawuce masallacin nasu.

Zama Baba yayi a kofar gida sai kada kafafu yake itama Ramla tafito tazauna kusadashi dan cikin

"gidan ya isheta ganin yanda yakeyi yasa Ramla tace  Baba su waye zasuzo wajenka ne haka ? Dan kalle kalle Baba yayi saikuma yamata alamu da hannu datazo kusada shi dasauri Ramla tazo tana zama agabanshi akasa akan tabarma, dan dukowa yayi cikin whispering yace  Hawwa ce tayi miji sunanshi Ibrahima, bakiga yaron ba badai shiga rai ba, gashi kyakkyawa dan gayu tsaftsaf dashi son kowa kin wanda yarasa ga tausayi, inhar abun ya yuwa Kulu na tayi goshi zaro idanu Ramla tayi cikeda farinciki dan bakaramin addu a sukema Hawwa tasamu mijiba ba, Baba kaman yaro yace  banso asani, banson kowa yaji, daga Mamanki sai Malam Sama ila sai kece mutum ta uku danike fadamawa, hadiye murnan hadiye murnan kuwa Ramla tayi tana kallonshi kaman TV, Baba yace  nace suzo karfe shidda da mangariba dai kinga ana salla sai adaura auren kawai kai kasa daurewa Ramla tayi kawai saita tashi tahau tsalle sosai tana bude bakin ihun murna amman bata bari ihun ya fito, Baba ya tuntsure da dariya sosai yana kallonta yanajin dadin dabai tabajiba yace  wai bacewa nayi kidena murna ba, wannan yarinya bakiji yacigaba da dariya shima kaman yatayata tsallen, shi kanshi baisan murnan yakeba, zama Ramla tayi awajen sai hira suke da Baba farin cikin auren yama kore damuwan rashin lafiyan Hawwan dake asibiti akwance, wajajen 6:30 Ramla tawani zabura tace  Baba ga motocin yan sanda tare da wasu jeep suna shigowa, Baba wlh sune, sune Baba Da Ramla da Baba yar tsere tseren leke ake yakama hannunta yana hamdala yace  zauna zauna Ramla kada aga mun kosa kokuma imaza je kiramin Malam Sama ila maza dasauri Ramla tawuce tana kallon motansu dake shigowa ahankali yaran anguwa na binsu daidai ana parking motoci a kofar gidan Baba, shima Malam Sama ila tareda wasu dattawan unguwa da Ramla na zuwa wajen duk sukazo suka tsaya tareda Baba dudda maza ne Ramla jitayi bazata"

iya komawa ciki ba wlh agabanta za ayi komi abunka da yarinya.

"Gently aka bude motan Excellency yasauko yana sanye da Baban riga na gizna tareda Musbahu, aka"

"bude second car din, Mahe ne Baban Sam kanin Excellency shima sanye da manyan kaya, sai third car, Nigerian chief of staff da attorney general wayanda shakikan Excellency ne sai fourth car wanda gently Khaleel ya sauko yana sanye da milk na Gizna dake sheki ya kafa hula ta kusan 8million akai tana sheki yana zuba kamshi fuskanshi yayi wani kwarjini da annurin haiba, Ramla ta taushe bakinta sabida ihu na neman fitowa ganin mijin Ya Hawwa tace  Ammi mijin Ya Hawwa na da kyau, wayyyoo wlh bantaba ganin mutum me kyanshi ba, Ammi yahadu, Ya Hamza, Asiya wayyooo Sam shima yafito, anatse Malam Sama ila yace  Bismillan ku gaban Baba sai bugawa yake yaga Khaleel yasan dan masu kudi ne but bai dauka kudin yakai hakaba, duk zama sukai akasa Baba ne kadai zaune kan kujera dan zaman kasa namai"

wahala sabida kafanshi da guda daya ce.

Yan anguwa aka taru kaman ana wani abu but babu wanda ya iya zuwa wajen sabida jami an tsaro

dasuka tare wajen da bindogoginsu a hannu.

Malam Sama ila cikeda natsuwa yabude taron da addu a yace  ina muku maraba da zuwa faram

"faram su Excellency suka amsasu, anatse Excelllncy yace  to Masha Allah da farko dai sunana Alhassan Mangal senate president na Nigeria kaman ruwa ya cinye su Baba yana kallonsu yayi shiru, yanuna Mahe yace  ga kanina Uwa daya uba daya Mahe, ga yarona Ibrahim Khaleel, ga dan kanina Sameer, gakuma shakikai na yanuna kowa yace  d ana ya samemu da maganan yaga yarku mai suna Hauwa u yanaso, sun hadu ta sanadiyan kwato mana yarmu datayi daga hannun yan kidnapping Noor, munzo neman aurenta dafatan za a bamu murmushi sosai Baba yayi he s overwhelmed baisan cewa yaune rannan da zaiga auren Hawwa ba, today started so bad for him, ciwon Hawwa saikuma hatsarinta, saikuma Ni ima da abubuwan datayi, baitaba tsammanin ending na yau will be this good ba, lallai bahaushe yayi gaskiya dayace idan kasan mafitar rana bakasan mafadan ta ba. Gyaran murya yayi yanuna kirjinshi yace  harga Allah na yarda da Ibrahima! Na aminta da Ibrahima! Nakuma natsu da Ibrahima, danhaka ni mahaifin Hawwa nabawa Ibrahima auren y ata Hauwa u dayazo nema ayau! Malam Sama ila yace  Allahu Akbar duk akai Kabbara awajen, Malam Sama ila yace  idan ba damuwa ga masallacin mu nan, muyi sallan magriba tunda lokaci yayi sai adaura auren kai tsaye Excellency yace  bismillan mu duk aka tashi aka wuce out of respect

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login