Showing 18001 words to 21000 words out of 37595 words
wayarta akan kujera batare da ta lura ba.
Yana jin ‘karar tashin motarta ya isa kujerar ya d’auki wayan gamida zama, kan chat na Rafee ta tsaya inda tayi saving as *Baby*, haurawa sama yayi nan yaci karo da wasu pictures da aka tura ma mummy wanda yarinyar ta d’aukesu tsirara haihuwar uwarta, nan take kanshi yamishi nauyi, yama rasa wani irin tunani zaiyi, chats d’in ya fara karantawa daga daidai wajen, duk hirar batsa sukayi wanda har mummy take cewa tayi missing na laushin jikinta. Bashiri ya mi’ke yana nanata “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”, jirin da yaji yana faman kwasheshi yasa ya tsugunna akan guiwowinshi hawaye suna zubowa daga idanunshi, ajiye wayar yayi ya dafe kanshi da hannunshi duka biyun, ya dad’e ahaka yana kuka kaman ranshi zai fita, zuciyarshi ne yake raya mishi “Does this mean Mummy tana lesbianism??, nooo!!!, this cant be, innalillahi”, ya kasa gaskata abinda idanunshi suka gano mishi, wani irin takaici ne ya lullu’be shi har baisam time d’in da ya runtse idanunshi yace cikin kuka “Ya Allah!!!!, noooo!!!, ya Allah!!!, Allah…..”
A firgice ya bud’e idanunshi don ta’bashi da akayi, share hawayenshi yafara yi yana ‘ko’karin hana kanshi abinda zuciyarshi ke raya mishi yayi, ahankali yace “Mummy….”
Cikin razana da ganin halin da ya shiga daga fitarta yasa zuciyarta a ‘kunci balle da taga yana kuka tsakaninshi da Allah. Kama hannunshi tayi taja shi suka zauna akan kujera, bubbuga bayanshi tayi sannan ta tambayeshi “Meh ya sameka?”
Rinannun idanunshi ya d’ora akanta, danne zuciyarshi yayi, nan take ya d’au ma kanshi al’kawarin bazai ta’ba nuna mata yaga wani abu ba har sai yabi komai a hankali ya ‘kara tabbatar ma kansa zargin da yake mata gaskiya ne. Da wannan tunanin yayi murmushin ya’ke yace “Bakomai Mummy, kaina kawai ke ciwo… ”
Da sauri ta katse sa “Karka min ‘karya Abdul, nazo na sameka kana kuka kaman wanda aka aiko mishi da sa’kon mutuwa sannan kace min kanka ke ciwo?, ni fah uwarka ce, nafi kowa sanin halinka, tunda na haifeka baka ta’ba kuka irin haka ba sabida dauriya irin naka, ka gaya……”
“Mummy bani snacks nah naci, I’m starving” ya fad’i haka ne don guje ma conversation d’in. Mi’ka mishi tayi, yana kar’ba yayi hugging nata kad’an yace “Thank you” sannan ya saketa ya mi’ke yabar side d’in.
Haneefah.mywapblog.com
Stylishbichi.mywapblog.com
Munayshat.mywapblog.com
*REAL MHS*
Munay, Hanee and Stylish.
Skip to content
haneefahusman
SEPTEMBER 19, 2016
ABUN SIRRI NE 39-40
*ABUN SIRRI NE*
Na ‘yan uku
*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*
*NWA*
*39-40*
☆☆☆☆☆☆☆☆
**SUHAL**
Yana barin layin gidansu Leena yayi parking na motarshi, hannunshi ya aza dukka biyun ya dafe kanshi cikeda jin haushin kanshi. Tunani ya dingayi “Meh matsalana?, mesa before naje gidansu bakina yake cike da magana amma ina ganinta na nemi hankali nah narasa?, why?, or was i scared?.”
Buga kanshi yayi yace afili “No i’m not scared, toh wai ma tsoron meh zanji?, tsoron mace?, noo!!, ba girmana bane na kasa furta mata inasonta”.
Sa’ke-sa’ke ya dingayi yanason gano mesa ya kasa koda kallonta da kyau balle ma ya sanar da ita abinda ya kaishi. Ya dad’e yana soki burutsu har saida duhu yafara mamaye garin sannan ya kama hanya.
Ko gida bai ‘karasa ba yasamu nearby masallaci ya sauke farali don lokaci yariga yayi, addu’a ya dingayi kan Allah ya mallaka mishi Leena yakuma sauwa’ke ma Ilham sonshi da takeyi.
Bashi yadawo gida ba sai 8:30pm, sai sannan ya duba wayarshi da tunda yayi saving number Leena bai duba ba, nan ya tarar da missed calls na Ummi, Umma, Ilham da Fu’ad wanda sun kira ne daga magriba zuwa 4 minutes ago, yama rasa ya akayi yamanta da wayarshi a cikin motar yashiga masallaci.
Jiki amace ya kashe motarshi sannan ya nufi sashen su Ilham don achan zasuci abinci yau, yana shiga iyayen suka nufeshi fuskokinsu d’auke da d’imbin damuwar dad’ewar da yayi awaje, abinda bai ta’bayi ba gashi sun ta kiranshi bai d’auka ba. Tambayoyi suka shiga jero mishi:
Abba yace “Ina ka shiga haka?”
Baba yace “Lafiya kam dai ko?”
Ummi tace “Meh ya sameka kayi dare haka?”
Umma tace “Ina ka tsaya har warhaka ba tare da ka sanar damu ba, kasamu cikin damuwa”
Fu’ad yace “Suhal are you okay?, mesa bakayi picking na calls namu ba?”
Ilham kuwa rugawa tayi ta rungume shi, tana kuka tace “Ya Suhal ina fatan ba abinda ya sameka?, I was so worried, zuciyata ta kasa sukuni, i thought something bad happened to you”
Kallon Ilham yayi yana shafa kanta yana lallashinta “I’m okay kinji?, kibar kukan haka, ba gani ba?”
Jinjina kai tayi sannan ya janyeta daga jikinshi hannunsu sakale da na juna, kai sunkuye cikin ladabi yace “Kuyi ha’kuri nasan nayi laifi amma muzauna tukunna”
Ba wanda yace ‘kala acikinsu, haka suka ja jiki suka zazzauna akan kujeru suna sauraren bayanin da zai musu.
A raunane yasoma magana “Naje gidan wani abokina ne munata hira don mun dad’e bamu had’u ba, daf maghriba nabar gidansu, ganin in nace sai na iso gida zanyi sallar lokaci zai ‘kure shine na nemi wani masallaci a hanya nayi Maghriba da Isha sannan na taho gida. Rashin d’aukar waya kuma nabarshi a motar ne nikuma nashiga masallaci, sai da na iso gida ne ma na duba wayar naga missed calls naku, kuyi ha’kuri d’aga muku hankali da nayi”
Kusan atare iyayen sukayi ajiyar zuciya, nasiha suka mishi akan kar ya ‘kara kai dare awaje haka, in ma yakama dole toh ya kira ya sanar dasu. Ha’kuri ya ‘kara basu sannan yayi excusing kanshi don ya watsa ruwa, yana mi’kewa Ilham tayi saurin dam’ke hannunshi tace “Ya Suhal kaci abinci mana tukunna”
Shi sai sannan ma yatuna rabonshi da abinci tun 1pm don ko yunwar bai ji, murmushi yayi yace “Bari nayi wankan zanzo naci”. Bai jira cewarta ba ya sake janye hannunshi ya fice daga parlourn, iyayen duk sun lura da wata irin kulawar da Ilham take bama Suhal wanda hakan yana musu dad’i, saidai matsalar da suke gudu kaman yana shirin tasowa, hakan yana matu’kar fad’ar musu da gaba don in dai tunaninsu na Ilham tanason Suhal daidai ne toh abunda suka binne acikin zuciyoyinsu shekara da shekaru ne za a tono shi. Sha re maganar kowannensu yayi suka cigaba da hirarsu ta yau da kullum.
Fu’ad kuwa Suhal yana fita yabi bayanshi, lokacin da yashiga Suhal ya cire jumpa d’inshi ya rage daga shi sai farar vest da short nicker, towel ya d’auka da zummar shiga bathroom don bai san Fu’ad ya shigo d’akin ba sabida tunanin Leena da ya d’auke hankalinshi. Gyaran murya Fu’ad yayi, a d’an firgice Suhal ya juyo yana kallon Fu’ad da yake tsaye yana wani shu’umin murmushi, kallon “me ya kawoka?” Suhal ya mishi. Dariya Fu’ad yayi ya zauna akan sofa dake tsakiyar bedroom d’in sannan yace “Guy, zo kawai muyi magana”
Suhal yayi jim sannan yace “Maganar meh zamuyi?”
“Maganar wacce kaje wajenta d’azu”
Suhal a zuciyarshi mamaki ne ya cikashi ya akayi Fu’ad ya ramfoshi haka?, fuskewa yayi yace “Wata kuma?, wajen abokina naje ba wani waje ba, kaga Malam ni bansan me kake nufi ba, as u can see wanka zan shiga so excuse me”
Saurin shan gabanshi Fu’ad yayi ya wani tsare yace “Kabar ‘boyemin don nariga da na ganoka, whats there in ka gayamin?, snatching zan ma?” Ya ‘karasa maganar had’e da daga gira d’aya sama
Dafe kai Suhal yayi yana murmushi ya bugi kafad’ar Fu’ad yace “Okay you got me, naga wata yarinya inasonta shine naje gidansu, kai fah shege ne, wai ma ya akayi ka gane?”
Murmusawa Fu’ad yayi yace a gadarance “Ka manta waye ni ko?, duk ‘boye-‘boyenka saidai in banga daman ganewa ba don ganewar shine abu mafi sau’ki”
Harararshi Suhal yayi sannan yace “Ni bance ka tsaya kanamin bragging ba, just tell me, ya akayi kagane?, or nayi wani abu na rashin gaskiya ne?”
Zama sukayi sannan Fu’ad yace “Kai bakama iya ‘karya ba wallahi”
Had’e fuska Suhal yayi yace “Bangane ‘karya ba, waye nama ‘karya?”
“Dazun da yamma nadawo ina nemanka sai Ilham ke ce min ka tafi meeting, yanzu kuma kace kaje gidan abokinka saisa nagane ba kaje ko d’aya daga cikin biyun ba, wani waje daban kaje”
Tunani Suhal ya lula, shi har ga Allah ya ma manta yayima Ilham wani ‘karya, ahankali ya furzar da iska yace “Wallahi namanta ne, amma ai daga kai sai ni mukasan ‘karya nayi so please ka rufamin asiri”
Girgiza kai Fu’ad yayi yace “Ilham ma zata gane ai tunda ita ba yarinya bace”
Murmushi Suhal yayi yace “Bar maganar Ilham, zan san yanda zanyi da ita”
Wani kallo Fu’ad ya watsa mishi sannan yace “Kaman ya?, i hope dai ba toying da feelings nata kakeyi ba?”
“Feelings?, wani irin feelings?”
“Kabar yi kaman bakasan me nake nufi ba, kasan Ilham tana sonka ba tun yau ba so no need denying it, nidai dont break my sister’s heart, Allah zamuyi rikici sosai”
Had’e fuska Suhal yayi yace “What do you mean?, an gayama im heartless ne?, banyi toying da feelings na wasu ba balle Ilham da take da babban matsayi a wajena, inason Ilham but bazan ‘boyema ba, soyayyar wa da ‘kanwa nake mata ba na wani abu daban ba”
“Why?, mesa bakasonta?, meh kake nema da bata dashi?, ‘yar uwanka ce ta jini?, mesa?”
Dafa kafad’ar Fu’ad Suhal yayi yace “Im so sorry Fu’ad, zuciyata ta kamu da son Leena ba Ilham ba, I cant help it, karkaga laifina, narasa ya zan taushi zuciyata tasota, Ilham tacika mace, infact batada makusa, but…….”
Cikeda tausayawa ‘kanwar tashi Fu’ad ya katse Suhal, mi’kewa yayi yace “Fine, ni bazanyi forcing naka ka sota ba but bazan d’auki kayi hurting nata ba, i can do anything for her, if you dont love her kayi ‘ko’karin janye jikinka daga gareta har sonka yafita daga ranta, please just dont hurt her don zamu samu matsala” yana kaiwa nan yabar d’akin kaman yaje yakama Ilham yayita duka bisa son maso wani da takeyi.
Jiki sanyaye Suhal yashige toilet yayi wanka sannan yafito yayi shirin bacci cikin pyjamas. Parlour yanufa ya kunna tv amma ba kallo yakeyi ba don ya zurfafa atunani sosai, sallamar Ilham ne yadawo dashi hankalinshi, amsa mata yayi, ahankali ta shigo ri’ke da tray mai d’auke da warmers a hannunta.
Sorry lovelies, ku cigaba da biyomu.
Haneefah.mywapblog.com
Stylishbichi.mywapblog.com
Munayshat.mywapblog.com
*REAL MHS*
Munay, Hanee and Stylish.
Skip to content
haneefahusman
SEPTEMBER 21, 2016
ABUN SIRRI NE 41-45
*ABUN SIRRI NE*
Na ‘yan uku
*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*
*NWA*
*41-45*
Haneefah.mywapblog.com
Stylishbichi.mywapblog.com
Munayshat.mywapblog.com
☆☆☆☆☆☆☆☆
Gidan Hajiya Hafsat***
Binshi kawai tayi da ido don bakinta ya kasa furta ko da kalma d’aya ne duk da zuciyarta cike yake da tambayoyin da take bu’katar amsa daga wajen d’an nata. Jingina da jikin kujerar tayi, nan taji alamun ta zauna akan abu, tashi kad’an tayi gamida zaro abun, aiko tana ganin wayarta ne ta zaro ido cikeda tsoro, nan take zufa suka soma tsatstsafo mata, ba shiri ta danna home button wuta ya kunnu akan screen na wayar, tana swiping yayi unlocking, akan chat na Rafee da ta bari yake har yanzu, nan taji hankalinta ya kwanta don batayi tsammanin Abdul ya gani ba, atunaninta in ya d’auka ba chat na Rafee zai tsaya ba don zai shiga na wasu ma, da wannan tunanin ta saukar da wani nannauyar ajiyar zuciya gamida sakin murmushi ta tattara wayarta tayi d’aki tacigaba da hira da lesbians ‘yan uwanta.
Abdulyassar yana isa d’aki ya bud’e d’an madaidaicin fridge nashi yasaka leather da Mummy tashigo mishi dashi sannan ya hau tunanin mafita da hanyoyin da zai bi don ku’butar da uwar tashi daga mummunan halin da take ciki. Wani tunani ne ya fad’o mishi arai, dama MD na company da yakema aiki ya gwada mishi yanason Mummy amma da MD d’in ya mata magana sai mummy bata bashi fuska ba, alokacin yaji wani iri da mutumin ya tinkareshi da maganar don yaga MD’n kaman ya raina mishi wayo ne yazo yace mishi yanason uwarshi, yanzu dai baida choice don haka zai danne zuciyarshi ya yarda yafara cusa ma Mummy ra’ayin mutumin har dai ta amince a d’aura musu aure, sa’ka da warwara ya dingayi yana ambaton duk wata addu’a da tazo bakinshi yana kuma ro’kon Allah ya bashi ikon cin jarabawar nan da ya d’ora mishi na uwa mai mad’igo.
Da dare wani irin zazza’bi mai zafi ya ri’keshi, a daddafe yaje masallaci yayi sallah yadawo gida. Momy shiru-shiru har ‘karfe tara bataji d’uriyar d’an nata ba sa’banin kullum da yana dawowa daga Isha around 8pm zai shigo su ta hira suna kallo har 10pm ko 11pm, tunowa da yanayin da ta sameshi dawowarta daga siyan snacks da yace yakeso ta fara, nan fah tasoma WAS-WASI(Book by Mermue my grandmother) acikin zuciyarta “Anya Abdul baiga wani abu a waya nah d’azu da rana ba?”
Tsaki taja tana mai jin haushin kanta yanda akayi ta manta da wayarta agida ta fita, chan kuma tace ma kanta “Kai bai gani ba, Abdul da shegen bin diddigin shin nan bazaiyiwu yagani sannan yayi shiru bai min maganar ba”.
Mi’kewa tayi tanufi side nashi, sallama tayi har sau biyu bataji ya amsa ba sai kawai ta shiga. A ‘kasa ta ganshi sai wani rawa jikinshi yakeyi, dagudu ta ‘karasa wajenshi tana jijjigashi tana kiran sunanshi, kuka tasoma tana salati tana tatta’ba jikinshi da yayi zafi jau kaman wuta. Dagudu ta fita ta fara ‘kwala ma maigadi kira don ya taimaka mata su sa shi a motar, cikin ‘kan’kanin lokaci ta isa dashi asibiti sabida gudun da tayi, nan fah likitoci suka kar’be shi suka wuce dashi A&E(Accident and Emergency).
Awa biyu sukayi suka fito, wasu nurses suka turashi ward sannan Dr yace ma Mummy tabiyo shi office yanaso yayi magana da ita. Jiki asanyaye tabishi har office nashin gamida zama akan kujeran da yake facing nashi, batare da ‘bata lokaci ba yasoma koro mata bayani kamar haka “Meh relationship naki da patient nan?”
“D’a na ne” ta bashi amsa
Jinjina kai yayi yace “Ba wani serious abu bane, ciwon kai ne ya kamashi har ya kai ga sumar dashi sannan heart nashi is beating more than normal, ko akwai wanda ya ‘bata mishi rai ne ko yanason wani abu?”
Jim tayi tana tunani sannan ta girgiza kai tafara magana cikin rawar murya “Shi kad’ai ne d’ana, ba abinda ya nema ya rasa a duniyar nan, don Allah doctor save my son’s life, I cant afford to lose him”
“He’s out of danger saidai dole ki kiyaye abinda zai sake jefashi cikin hali irin wannan don kar abun yayi worsening”
Share hawayen da ya zubo mata tayi tace “In Sha Allah zan kiyaye”
Jinjina kai yayi yace “You can go”
Har ta tashi sai kuma ta juyo ta kalleshi tace “Zan iya shiga na ganshi?”
Batare da ya d’ago ya dubeta ba yace “Zaki iya shiga but no noise don ba ason ya farka sai alluran ya sakeshi”
Cikin rawan jiki ta fita daga office d’in ta nufi d’akin da Abdul ke kwance ga ‘karin ruwa a hannunshi.
Daf asubah ya farka, yana motsi Mummy ta mi’ke tana shafa kanshi don ko runtsawa ta kasa yi, cike da kulawa tace “Sannu son, ya jikin?”
Bin d’akin yayi da kallo, nan yagane asibiti yake, ahankali ya bud’e baki yace “Da sau’ki, meh ya kawoni asibiti?”
Murmushi ta mishi tace “Shhh, dont stress yourself, yanzu barin taimaka ma kayi sallah tukun, in kaci abinci sai muyi magana kaji?”
Ba don yaso ba yace “Okay mummy, zan iya tashi da kaina”
Mi’kewa yayi a daddafe ya bi gini ya shiga toilet sabida jirin da yake damunshi, cikin ‘karfin hali yayi alwala yazo ya tada sallah. Yana idarwa Mummy ta had’a mishi tea ta bashi sannan itama ta kabbara nata. Da gari yayi haske doctor ya shigo ya dubashi had’e da bashi shawarwari, aciki har yake tambayarshi meh yasa a zuciyarshi da har yake neman barazana da rayuwarshi, sai anan ne Abdul ya gane abinda ya sameshi, bai bama doctor amsa ba, ganin haka yasa dr d’in share zancen kawai yayi murmushi ya bar d’akin.
Da yamma aka sallamesu don jiki yayi sau’ki.
Bayan kwana biyu
Kwana biyun nan Mummy tayi-tayi da Abdul ya gayamata meh yake damunshi amma fafir ya’ki, yanzu ma rikicin da suke tafkawa kenan. Ta sa shi agaba har tana neman mishi kuka, shiru yayi yana tunanin ya zaiyi, shawara da zuciyarshi yahau yi har ya amince ma kanshi da shawara d’aya.
Kama hannun Mummy yayi yace “Im sorry Mummy, na rasa ya zanyi ne don bansan ya zaki d’auki maganar ba”
Idanunta jawur ta kalleshi tace “Abdul hankalinka d’aya kuwa?, kana wasa da ranka akan tunanin yanda zan d’auki maganar da kakeson gayamin?, you are my only son, ina sonka fiye da yanda nakeson kaina, ka gayamin ni kuma nama al’kawarin zanyi maka shi ko da kuwa it will cost me my life, Abdul kaine komai nah, don Allah ka taimakamin kabar wasa da lafiyarka, bazan iya jure ganinka cikin rashin lafiya da yake barazanar d’auke min kai ba”
Wani son uwar nashin ne ya tsirga mishi zuciya, yasan ko menene ya gayamata zata yarda balle yanzu da zuciyarshi ya d’an ta’bu saidai shakkar tunkararta da maganar yakeyi. Share mata hawaye yayi shima yana hawayen yace “Mummy kiyi ha’kuri, bazan sake ba, kibar zubda hawayenki akaina please Mummy”
Shafa fuskarshi tayi tace “Shikenan Son, gayamin meh kakeso”
Kawar da kanshi yayi daga kallonta ya maida kallonshi gefe don bai jin zai iya kallon idonta yamata maganar. Murya na rawa yace “Mummy aure nakeso kiyi, ganinki ahaka yana matu’kar damuna, i dont mean to disrespect you amma wallahi mummy k’awayenki sam ban yarda dasu ba don basu min kama da masu mutunci sannan inajin wasu maganganu akanki da suke ‘batamin rai, anguwan nan maganarki ake tayi wai kina harka da manya sabida yanda suke ganin abokan business naki suke yawan zuwa nan gidan(shi baisan tana harka da maza ba don bai ta’ba gani ba, da ya dawo daga london after graduating from college sai yaga yanda maza suke sintiri agidan ba dare ba rana, da ya tambayeta sai tace ai business partners nata ne, shikuma haka ya yarda har yau don daga baya kam ma sun rage zuwa gidan sai ‘kalilan nasu don guest house da Mummy ta gina achan suke zuwa suyi harkarsu ba tare da Abdul ya gane ba), aure shine only abun da zai sa subar maganganun da sukeyin duk da dai ban ta’ba yarda ba don nasan halinki, bakya haka, mummy aure zai siya miki mutunci har ma dani, please Mummy” ya ‘karasa maganar kanshi a sunkuye yana zubda hawaye.
Mummy da ranta yayi mugun ‘baci jin ya ambaci aure tuni