Showing 3001 words to 6000 words out of 37595 words
Hafsat ta amsa “Bud’e ki gani”
Tsaki Leena ta ja don ta gane mai muryar, bud’e ‘kofar tayi ta bata hanya don ta wuce sannan ta gaisheta, amsawa tayi tana wani ‘kare ma Leena kallo. Leena duk takaici ya cikata, dama ita sam batason Haj Hafsat d’in nan, tasha gayama mummy amma watarana har mari takesha sakamakon hakan, ita tama rasa mesa mummy take ‘kawance da matar da duk wani mai ilimi bazaiso huld’a da ita ba don kuwa a ganinta Haj Hafsat tana abu kaman karuwa.
Ta juya zata koma d’aki kenan Haj Hafsat ta jefa mata tambaya “Ke, ina mamanki?”
Ba tare da ta juyo ba tace “Tana d’aki, ai ba yau kika soma zuwa ba so ke ba ba’kuwar gidan ba ce”
Tsaki Haj Hafsat ta ja sannan ta nufi d’akin mummy. Rufe ‘kofa mummy tayi, ko gaisawa mai kyau basuyi ba suka afka duniyar da shaid’an ke buga musu gangarshi(Ya Allah ka karemu daga fad’awa halaka, Ameen).
Haj Hafsat ta fito daga wanka tayi combing na kanta sai ta nemi ribbon nata ta rasa. Cikin takaici tace “Ohh ni Hafsa, yau kuma ina ribbon nawa ya shiga?”
Haj Rahma tace “Inaga wajen cire riga ne kika ko’be harda ribbon d’in”
Neman duniyar nan sunyi amma ba ribbon ba alamarshi. Haj Hafsat ta nufi ‘kofa tana cewa “Bari naje d’akin yarannan su bani”. Bata jira cewar mummy ba ta fice.
Tana shiga daidai lokacin kuma Rafee ta fito daga wanka sanye da towel multicoloured wanda ko guiwarta bai kai ba, wani mayunwacin kallo Haj Hafsat ta bita dashi, nan take taji ta kwad’aitu da ita amma sai tayi ‘ko’karin danne maitarta, ‘kwa’kulo murmushi tayi ganin Leena dake kwance akan gado tana binta da kallon tuhuma.
Cikin wani irin yanayi tace “Rafee, bani ribbon naki mana don Allah, nayi neman sama da ‘kasa banga nawa ba”
Rafee sai lokacin ma ta lura da Haj Hafsat ta shigo d’akin, batace komai ba ta bud’e drawer ta d’auko sannan ta mi’ka mata. Tasa hannu zata ‘karba sai tayi magana kaman rad’a “Kinada jiki mai kyau, dirinki mai d’aukar hankali ne”
Rafee yi tayi kaman bata jita ba, ta’be baki Haj Hafsat tayi ta juya tabar d’akin cike da sha’awar Rafee.
Fitarta ya bama Leena damar yin tunani “Wai ma ya za ayi ribbon ya ‘bata a nemeshi a rasa daga zuwanta?, sai kace wacce ta cire tayi wasar ‘kasa?, toh ita dai ba wasa tayi ba tunda dai babba ce, amma a wani dalili yasata cire ribbon har ya ‘bata?” wad’annan tambayoyin tana neman ansarsu kuma tasha alwashin da yardar Allah sai ta samo su koma a ina ne.
Haj Hafsat kuwa tana komawa d’akin Haj Rahma ta d’auki jakarta ta sallameta tabar gidan. Da dare ma kasa bacci tayi sai juyi takeyi akan gado, chan sai ta kira wani layi, jin an d’auka ya sata magana “Inaso nasaka aiki ne, ka nemomin number Leena ‘yar gidan Haj Rahma”
Bansan me aka gayamata daga d’ayan bangaren ba, nadai ji tace “Ni nafika sanin wannan, kawai dai na kwad’aitu ne kuma ko ta halin ‘ka-‘ka ne sai na mallaketa, ka samomin, zaka samu tukwuici mai tsoka”.
Shin su wayene duk wad’annan mutanen?, ku biyomu don jin tushen labarin.
Sorry fans, kuyi ha’kuri damu, In Sha Allah zamuyi ‘ko’kari mu dinga kawo muku akai-akai. We love you all.
Haneefah.mywapblog.com
Stylishbichi.mywapblog.com
*MHS*
ABUN SIRRI NE 16-20
*ABUN SIRRI NE*
Na ‘yan uku
*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*
*REAL MHS*
*16-20*
TUSHEN LABARI
☆☆☆☆☆☆☆☆
Marigayi Alhaji Modibbo yanada ‘ya’ya guda biyu dukkansu biyu maza; Abdulaziz ne babba sai Murtala. Sun taso cikin soyayya da kulawa had’e da ingantaccen tarbiya daga wajen mahaifiyar su marigayiya Haj. Habiba.
Iyayen sun rasu ne a cikin had’arin jirgi na dawowar su daga India inda dama Haj Habiba ta raka Modibbo ne don annual check-up nashi, alokacin kuma Abdulaziz yana shekarar shi ta ‘karshe a jami’ar Bayero wato Bayero University Kano, yana karantar Business Administration, Murtala kuwa yana 300L don ba wani tazaran shekaru tsakaninsu, Abdulaziz ya bama Murtala shekaru d’aya ne kacal.
Cikin ikon Allah Abdulaziz ya gama makarantar shi ya cigaba da juya tarin dukiyar da babansu Modibbo ya bar musu. Kaman kiftawar ido aka wayi gari Murtala ma ya gama tashi makarantar inda ya karanci Infotech.
Lokaci d’aya Abdulaziz da Murtala suka tada zancen bikinsu, bappansu wato ‘kanin Modibbo shi ya jagoranci komai har izuwa ranar d’aurin aure. Abdulaziz ya auri Hasiya, Murtala kuma ya auri Maimuna, ba tare da ‘bata lokaci ba aka kai amaren dan’kararren gidan da angwayen suka gina, gini ne da yaci kud’i fiyeda tsammani don zana gidan ma daga ‘kasar waje suka d’auko architect, furnitures ma duk sunce sun hutar da iyayen amaren nasu amma iyayen sukace ina!!, bazai yiwu ba. Haka dai aka kawo furnitures kowanne daga gidan iyayensu aka jera musu, gida yayi kyau Masha Allah.
Zaman mutunci da girmama juna Hasiya da Maimuna sukeyi, sun sha’ku har suka zama tamkar ‘yan uwan juna. Bayan shekara d’aya Hasiya ta haifi d’anta kyakkyawa son kowa ‘kin wanda yarasa, ranar suna yaro yaci sunan Suhal. Suhal yanada shekaru biyu Maimuna itama ta haifi d’anta namiji mai suna Fu’ad, Fu’ad da Suhal sun taso cikin soyayyar junansu, ba wanda zai gansu yace ba iyayensu d’aya ba don iyayen nasu ma basu nuna banbanci tsakanin yara biyun, duk abinda Baba(baban suhal) da ummi(maman suhal) zasuyi ma Suhal to sai sun yi ma Fu’ad, hakazalika duk abinda Abba(baban Fu’ad) da umma(maman Fu’ad) zasuyi ma Fu’ad to tare da Suhal sukeyi.
Daganan duk matan basu sake haihuwa ba, mazan ma sam basu nuna damuwarsu ba don sun gode ma Allah da ya basu yara d’ai-d’ai, wasu mutane ko d’ayan Allah bai basu don haka basuda dalilin nuna matsawar su akan haihuwa.
Suhal yanada shekaru 9, alokacin kuma Fu’ad yana 7 kwatsam sai aka wayi gari Ummi tanada ciki, zo kuga murna, gaba d’ayansu sun d’ora son duniyar nan akan cikin. Wata tara cif ta haifi ‘yarta kyakkyawa wacce taci suna Ilham.
Ilham ta zamo musu hasken idaniya, komai Suhal da Fu’ad suka samu to akan Ilham yake ‘karewa, in sunga abu kuma sunada kud’in saya toh fah dole su sayamata. Itama Ilham komai Ya Suhal da Ya Fu’ad, abun nasu gwanin burgewa.
Dawowarsu gida yanzu Suhal yayi graduating inda yayi university a Turkey ya karanci Pharmacy, Fu’ad kuma saura mishi shekara biyu ya kammala had’a degree d’inshi a fannin Banking and finance.
Suhal kyakkyawa ne gashi yanada zubi irin na jaruman maza, baya shiga harkar mata ko kad’an don aganinshi yayi ‘karami da aure duk da yanzu he is 26, Fu’ad on the other hand kuma ya mafi Suhal kyau saidai matsalarshi shine-Shaye-shaye da bin abokan banza, abinda yake had’ashi fad’a da Suhal kenan don ba garin da zai waye har dare yayi ba tare da Suhal ya mishi wa’azi akan abinda yakeyi ba saidai kuma sam Fu’ad baya ji. Tohh gashi yanzu Suhal ya kammala ya dawo gida Nigeria, Fu’ad shi kad’ai zai zauna, ba mai sa mishi ido balle asan me yake ciki har anemi nutsar dashi, ko ya zai kasance??.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Alhaji Kabeer Mansur babban d’an kasuwa ne a jahar Kano. Auren saurayi da budurwa sukayi shi da matarshi Haj Rahma, afarko zaman nasu cike yake da tarairaya da kuma kula da ha’k’kin junansu, saidai fah tun lokacin da ta haifi ‘yarta na fari mai suna Rafee’at sai labari ya chanza don alokacin ya bun’kasa harkokin business nashi zuwa ‘kasashen waje, da yake shi mutum ne da sam bai had’a aikinshi da komai ba sai ya share watanni bai waiwayi gidanshi ba.
Zaman da dad’i ba dad’i har Mummy ta haifi ‘ya’ya biyu bayan Rafee’at masu suna Safiyya da Yaleena. Sun sha’ku da uwar tasu sosai amma uban kam gaba d’aya ma in yazo gida yin kwana biyu sam basu sakewa dashi, d’ari-d’ari zasu dingayi har ya tafi, shi ko daddy tun hakan yana damunshi daga baya kuma ya tattara su ya watsar. Tsakanin shi da yaran shine suce “Ina kwana?”, shikuma yace “Lafiya”, sam babu irin sha’kuwar uba da ‘ya’yanshi a tsakaninsu.
Daidai gwargwado yaran sun samu tarbiyya daga wajen uwar tasu saidai ba nan gizo ke sa’ka ba, mace ita kad’ai bazata iya tarbiyyar yara har uku ba, gashi dukkansu mata. Kowa dai yasan tarbiyyar namace sai da tsawatar war uba, anasu tasowar ina ma suka ga uban balle har ya tsawatar musu?.
Mummy macece mai matu’kar ha’kuri da juriya duk da ko wani dare da kukan rashin mijinta take samu tayi bacci amma ahaka take ‘ko’karin kare kanta daga fad’awa hala’ka. Kwatsam wata rana taje shopping sai ta had’u da wata mata inda suka gaisa har sukayi exchanging numbers, wannan shine kuskure mafi girma da tayi a rayuwarta sannan shine mafarin zubda duk makaman tsaronta.
Wannan matan ba kowa bace illah Haj Hafsat, Haj Hafsat gogaggiyar ‘yar duniya ce, tayi aure amma zaman auren ya gagara sakamakon bin maza da takeyi, tanada yaro guda d’aya namiji mai suna Abdulyassar.
Hafsat bata tsaya akan harka da maza kawai ba, ita d’in tana cikin manyan mata masu mad’igo. Tunda ta ‘kyalla ido taga Haj Rahma tsigar jikinta suka tashi, hakan yasa taje suka gaisa ta fake da cewar tanaso su zama ‘kawaye.
Had’uwar Mummy da Haj Hafsat ba ‘karamin ‘barna yayi ba, shige mata takeyi sosai, tun mummy tana shashshareta har dai ta sake suka soma zumunci. Bayan watanni sai ta soma nuna mata asalin halinta wato lesbianism, da farko mummy sam ta’ki amma da yake shaid’an yana nan yana wasa da zuciyarta sai ta yarda suka fara harka, ba a d’au lokaci ba mummy ta tsinci kanta dumu-dumu acikin harkar don tun asali dama mummy irin matan nan ne masu yawan sha’awa, acewarta Haj Hafsat tana rage mata zafi tunda mijin ba zuwa gareta yakeyi ba sai bayan watanni.
Da girma yazo ma ‘yanmata ukun ne kowaccen su tayi nata halin.
Rafee ita ‘yar hayaniya ce, abarta da harkar ‘kawaye, asa wannan kayan, a saya waya mai tsada, aje wani waje ahuta sannan tana d’an harkarta itama na lesbianism a ‘boye shiyasa ita tun tasowarta bata huld’a da maza, ko saurayi yazo saidai ta koreshi, tun mummy na fad’a har daga baya tayi tsammanin ko aljanu ne, malami ta kira don ayi ma Rafee ru’kiya. Malami yata zuba ayoyi amma Rafee ko gezau, bayan ya gama ne yake ce ma mummy ai lafiyarta ‘kalaw, ba aljanu bane so tabar damuwa, aure kaman mutuwa yake, in ya iso ba makawa sai an yishi, nan fah mummy ta zuba ma Rafee ido har halin yanzu da take da shekaru 29.
Sofy kuma ‘yar party ce da saka matsatstsun kaya, tana d’an d’aga kwalba irin na yanmatan zamani wato codeine saidai nata baiyi yawa ba, in tasha yau toh sai bayan wata d’aya zata sake sha. Duk iskancinta bata ta’ba zina ba, ba wanda zai ganta yace ‘yar musulma ce in tayi wani shigar. Saurayinta guda d’aya ne; Bash, sun dad’e tare kuma tun ba yau ba yakeson tabarshi su dinga aikata zina amma ta’ki bashi fuska, iyakacin abinda ke shiga tsakaninsu shine romance.
Leena itace wanda suke kira “Ustaziya”, Leena sam batayi halinsu ba. Tanada kamun kai, bata tara ‘kawayen banza sannan bata shiga harkar da ba nata ba. Itama dai batasan halin da Rafee take ciki ba, iyaka abinda tasani shine rawar kai da sukeyi wanda ba yanda ta iya dasu saidai ta zuba musu ido tunda duk sun girmeta, ta ma isa tayi magana?. Tsakaninta dasu shine addu’ar shiriya wanda bata gajiya da musu ba-dare-ba-rana.
Mummy daga baya ta tsiri fita yawo, sam bata zaman gida, hakan ba ‘karamin gudunmawa ya bayar wajen ta’bar’barewar tarbiyyarsu ba.
Tohh gashi yanzu Haj Hafsat ta ‘kwallafa rai akan Rafee sakamakon ganinta da tayi da towel, ko ya zai kaya???.
Ku biyomu ‘yan uku don jin cigaban labarin.
Haneefah.mywapblog.com
Stylishbichi.mywapblog.com
Munay, Hanee da Stylish.
*MHS*
ABUN SIRRI NE 21-22
*ABUN SIRRI NE*
Na ‘yan uku
*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*
*21-22*
☆☆☆☆☆☆☆☆
Cigaban labari
Washegari
Suhal ne zaune akan kujera a ‘karkashin shade na tree da ke tsakar gidan, ya d’ora ‘kafafunsa akan wani plastic chair, gefenshi d’an ‘karamin table ne wanda yake d’auke da glass cup da kuma juice. Sanye yake da black jean trouser had’e da farar riga, jarida ne a hannunshi yana d’an dubawa, sipping na juice d’in yakeyi cike da aji.
Ilham ce tafito daga side nasu da saurinta ta nufi side nasu Suhal. Yi tayi kaman bata ganshi ba, shi ko mamaki ne ya cikashi ganin yanda ta wani fuske tana tafiya kanta a sunkuye, a zuciyarshi yake rayawa tabbas ta ganshi ne yasa tayi hakan, toh amma me dalilinta?. Har tasa hannu zata bud’e ‘kofar parlourn Suhal ya ‘kwala mata kira, amsawa tayi sannan ta tura baki, idonshi ‘kyam akanta yace “Zo Ilham”
Kaman kar taje sai kuma ta fasa, fuskar nan ba ko murmushi sai ma bakin da ta tura ita adole wai tayi fushi. A gabanshi ta tsaya sannan tace “Gani ya Suhal”
Sau’kar da ‘kafafunshi ‘kasa yayi sannan ya nuna mata kujerar alamun ta zauna, juya kai tayi kaman bata san body language da yayi mata ba. Ahankali yace “Sit down mana”
Ba don batason mishi musu ba da bazata zauna ba, jan kujerar tayi tana wani tuttura baki ta zauna. Dariya ne ma ya kamashi wanda ya kasa dannewa sai da ya dara, nan fah Ilham ta kuma ‘kulewa, murya na rawa tace “Ya Suhal ni fah ba mahaukaciya bace da zaka kirani kasani a gaba sannan ka tsaya kanamin dariya”
Da ‘kyar yasamu ya tsaida dariyar sannan ya saita kanshi, in a serious tone yace “Lil sis, are we fighting?, jiya fah nadawo garinnan gashi yanzu kinganni sai kika wani kawar da kai kaman kinga ma’kiyinki, me na miki haka da ko sannu bazaki iya ce min ba?”
A shagwa’bance tace “Toh…toh…ba kaine kabar sona ba”
Zaro ido yayi had’e da nuna kanshi yace “Who?, me?, noo ba ranar da zan bar sonki, bansan dalilinki na tunanin hakan ba so inajinki, gayamin, wani laifi namiki?”
Gyara zaman ta tayi tace “In ba kabar sona ba toh mesa baka bani tsaraba ta ba?, ya Fu’ad kam tun jiya da dare ya kirani ya bani, kai kuma baka kawo min ba don baka sona wata’kila ma har fata kakeyi namutu” sai ta fashe da kuka
Tsayawa kallonta yayi cikeda mamaki, bakinshi ya kasa furta ko wacce irin kalma, ohhh Ilham akwai rigima, yasan ta d’ora mishi laifi ne kawai don rikici irin nata amma don dai bai bata tsaraba ba ai bai zama reason da zata ‘ki mishi magana ba kuma har tace mishi watakila yana fata ta mutu. Dafa hannunshi yayi a ‘kar’kashin ha’barshi sai ya ‘kura mata ido kaman yasamu tv, itako sabon kuka ta shiga rerawa kaman wanda aka mata mutuwa.
Fu’ad ne yafito da plastic chair don shan iska, ganin yanda Ilham ke kuka sannan Suhal ya zuba mata ido sai abun ya bashi mamaki, nufan wajensu yayi ya ajiye kujerar shi a tsakiya inda sukayi kaman triangle. Ya kalli Suhal ya kalli Ilham, chan dai yace “Kai lafiyarku wai?, ke kinzo kin zauna kina kuka, Suhal kuma ya wani saki agaba kaman yasamu tv, me ya faru?”
Share hawaye Ilham tayi ta maida dubanta wajen Fu’ad sannan tace “Ya Fu’ad kar kaji mamaki ko da wu’ka kaga ya Suhal yazo zai chakamin, ya Suhal yabar sona”
Suhal ya sake baki yana jinta, azuciyarshi yake rayawa lallai Ilham ta cika ‘yar duniya, tas ya kwashe komai ya gayama Fu’ad. Haba, meh Fu’ad zaiyi in ba dariya ba, yi yakeyi sukuma suka bishi da kallo.
Bayan yayi shiru ne sai yace “Ke fah wawiya ce ashe bansani ba, yanzu fisabilillahi Ilham don bai baki tsaraba ba shikenan yabar sonki?, ke dai kawai kina neman reason na kuka ne gashi kin samu, toh ko da yake zai iya yiwuwa yabar sonki ne sabida kin zama tsohuwar yayi, yau dai na ganku a rana, Ilham tana holding grudge against Suhal” ya ‘karasa maganar yana tafi harda bubbuga ‘kafa alamun yaji dad’i.
Ganin haka yasa Suhal cewa “Wai kai Fu’ad wani irin shed’an ne?, ganinka anan na tsamman zaka tayani lallashinta amma tsaba ka nuna kanada horns harda tail yasa kazo kana neman ‘kara ‘kwa’bawa kana ‘kara ma wuta petur, malam ka tashi ka kama gabanka tunda ba amfani zakayi ba”
Fu’ad gyara zamanshi ma yayi had’e da d’ora ‘kafa d’aya kan d’aya bai ce komai ba. Ba irin lallashin da Suhal baiyi ba amma atapir Ilham ta’ki ha’kura. Mi’kewa yayi yasa hannunshi a cikin aljihu yace “Tashi ki shirya nima barinje na chanja kaya sai nazo in kaiki shopping ki za’bi duk abinda kikeso”(ya fad’i hakan ne don yasan ko wani irin fushi tayi inhar ance za akaita shopping to za a nemi fushin arasa)
Nan take hawayen suka tafi kaman anyi ruwa an d’auke, murmushi ta fara yi, cikin jindad’i tace “Ai daman nasan kana sona ba kaman ya Fu’ad mai shegen ma’ko ba, ka ma san meh yabani as tsaraba?”
Girgiza kai yayi yana murmushin mugunta yace “Gwanda da kika gane da kanki, Fu’ad ai sai addu’a, ma’konshi yayi yawa, gayamin wani tsiyar ya baki?”
Cikin yatsina fuska tace “Wasu jewelleries ya kawo min wanda nasan ba masu tsada bane, ina tunanin ma irin masu fading nan ne da turare guda uku irin cheap ones wanda ‘kamshin su ba dad’in nan sai wani agogon M&S”
Suhal da kanshi ya jinjina ma Fu’ad don yasan kud’in da ya narkar ba kad’an bane amma gashi Ilham don tsaba iskanci wai kushewa takeyi. Jinjina kai Suhal yayi yace “Ohh ke kinji mamaki ne?, kad’an daga ma’ko irin na Fu’ad kenan ai, in gaya miki, ranar da ya siya miki abubuwan nan har zazza’bi sai da yayi”
Dariya Ilham tasa tace “Ya Fu’ad Allah ya shiryeka, inaga kud’inka sai sun ru’be wataran”
Duk maganan da sukeyin nan Fu’ad bai tanka musu ba don yagane manufar Suhal na son ya ‘kular dashi amma yanzu sai yace “Lallai Ilham kincika ‘yar air, yanzu kuma kaina kika dawo?, ba damuwa, gobe ma rana ne”
Murgud’a baki tayi tace “Koma me dai, ga ya Suhal mai sona wanda bai ‘kiuyan kashemin kud’i” sai ta juya wajen Suhal da ke ta faman danne dariyarshi tace “Mutafi ya Suhal kar ya ‘kara shiga tsakaninmu”.
Basu jima a d’akunansu ba suka fito cikin shirin fita, motar suka shiga sannan sukayi ma Fu’ad gwalo suka fice daga gidan. Sahad stores sukaje, shopping sosai tayi ya biya kud’i suka juyo gida.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Munay, Hanee and Stylish
Skip to content
haneefahusman
AUGUST 24, 2016
ABUN SIRRI