Showing 27001 words to 30000 words out of 37595 words
Leena, wancan had’uwan mu is a different case, karkiyi ma magana ta mummunar fahimta”
Share hawayenta tayi tana magana ita kad’ai “Its all my fault, da tun farko ban yarda da kai ba da ko da wasa bazaka fara d’aga min murya ba, tsawa?, abinda nafi tsana a duniya”
Nadama ne ya dirar mishi a zuciya, tambayar kanshi yakeyi meh yasa yayi ma Leena haka. Cikin lallashi yace “I sincerely apologize, raina ne ya ‘baci”
“Akan meh ranka zai ‘baci?, don na tsaya da wani?”
“Yes Leena, I got jealous wanda har nayi over-reacting na saki kuka” ya fad’a kai tsaye gamida cigaba da driving
Kallonshi tayi cikin rashin fahimta tace “Jealous?, jealous?, of what?, why?”
Murmushin gefen le’be kawai yayi yace “All this questions, reserve them, nan gaba zan answer miki all, yanzu dai tell me kin ha’kura”
Murmushi tayi tace “Na ha’kura amma sai ka min al’kawarin u will never shout at me again”
“Ohh ohh, wannan d’in ma I was mad saisa, will learn to control myself next time, sannan karki ‘kara tsayawa da wani don anything can happen in na ga hakan”
“Lafiyanka?, kar na tsaya da wani fah kace, kai zaka bani miji ne?”
Dubanta yayi sannan ya maida hankalinshi kan titi yace “Eh, zan baki miji that I trust, wanda nasan bazai ta’ba hurting naki ba, he will take care of your every need, wanda yake sonki fiye da kanshi”
Zatayi magana ya d’aura hannunshi akan nata yace “No more questions”.
Da haka suna hira har ya sauketa a gida ya kira maigadi yazo ya shigar mata da ledojin cikin gida, godiya sosai ta mishi har sai da ya gaji yaja hannunta ya kaita cikin gidan sannan yabar gidan da sauri ya shige motar ya tayar. Dagudu tafito kaman zatayi kuka tana d’aga mishi hannu, dariya yayi shi kad’ai yace afili “I love everything about you”
☆☆☆☆☆☆☆☆
Sofy ta farka daga bacci taji jikinta ba komai, gefenta ta duba taga Bash sai shar’ban bacci yakeyi. ‘Ko’karin mi’kewa tayi dafe da kanta sabida yanda yake sara mata kaman zai tsage biyu, gashi ta rasa gane meh ya kawota hotel da Bash har gata a tu’be.
Ihu sosai tayi wanda ya tayar da Bash daga wahalallen baccin da yakeyi, rarrafawa yayi ya isa ‘karshen gadon ya rungumeta ta baya yace “Baby kwanta muyi bacci”
Hankad’e shi tayi murya yana rawa tace “Bash meh ka min?, ina ka kawoni?, mesa ka kawoni nan?”
Sake rungumeta yayi yace “Baby you know I love you….”
Tureshi tayi da iya ‘karfin da ya rage mata ta fashe mishi da kuka tace “Bash tell me!!!, meh kamin?!!”
Jingina da jikin gado yayi yace “I had sex with you”
‘Kwalalo ido tayi duk da bataji mamakin furucin shi ba don tayi zaton hakan ne saidai tanaso ta gaskata saisa ta tambayeshi, saka hannu akai tayi tana kuka tana salati “Innalillahi, Bash ka kasheni, mesa kamin haka Bash?, sakayyar da zakamin akan irin son da nake maka kenan?, Bashi mesa?, mesa bazaka bari sai munyi aure kayi koma meh ba?, ka cuceni ka cuci rayuwata, yanzu meh zan gayama Momy in na koma gida?”
Kamo hannunta yayi ya jawota jikinshi yace “Dont you trust me?, zan aureki Sofy, inasonki, sonki ne yasa na aikata miki hakan, Momy kuma ba sai kin gayamata gaskiya ba don ma ba ganewa zatayi ba, yanzu tashi muje muyi wanka sai na maidake”
‘Kan’kame blanket da ke jikinta tayi tana kuka sosai tace “Mesa ka samin ‘kwaya?, sabida kasan ba yarda zanyi ba shine kayi drugging nah ko?”
“No baby, ki yafemin, ba wanda zai gane saidai in ke zaki fad’a”
Tashi yayi ya janye blanket d’in daga jikinta, kallonta da yayi ahaka sai ya ‘kara ji dole ne ma ya sake wani round, haurawa gadon ya sakeyi yafara shafata ahankali har yafara yi da sauri-sauri. Ganin abinda yake shirin yi yasa Sofy ta fara kokuwa dashi amma ‘karfin su bazai had’u ba, tanaji tana gani ya sakeyi har sau biyu, tana kuka har ta koma ajiyar zuciya tsaba azaban da takeji, ko motsi ta kasa yi har ya gama abinda zaiyi ya wuce toilet.
Bai jima ba yafito d’aure da toilet a ‘kugu, gadon ya hau ya janyota jikinshi yana faman lallashi da mayaudaran kalamanshi. Mi’kar da ita yayi ta tsaya da ‘kafafunta amma meh?, ta kasa sabida ba ‘karamin ciwo yaji mata ba. Cak ya d’agata ya kaita toilet, bai gasata ba baiyi komai ba don shi bai ma san ana wani gashi ba, wanka kawai ya taimaka mata tayi sannan ya dawo da ita d’akin. Sai sannan ta lura da yanda bedsheet d’in yazama jawur, tausayin kanta taji sosai da wannan yanayi da take ciki. Kaya yasamata ya bata wani pain killer sannan ya ri’ko hannunta suka fito daga wajen tana takawa a hankali.
Sai da suka shiga motar ne ta tuna da kashedin momy na kar ta kuskura ta kai la’asar. Jiki na ‘bari ta ciro wayarta taga 8:47pm, ga missed calls na Momy, Rafee da Leena sunkai tamanin, rufe bakinta tayi tana kuka don itakam yau tasan kashinta ya bushe. Da lallashi da lallamin SABON SALON D’A NA MIJI ya sa tabar kukan da take yin, yace mata tace ma Momy ta raka ‘kawartata gidan sistanta ne sannan wayarta ta manta yana silent.
A ‘kofar gidan ya tsaya, zagayowa yayi ya bud’e mata ‘kofa, fitowa tayi tana cije le’be, rungumeshi tayi tana hawaye tace “Bash, Momy zata gane, tafiyana nasan ya chanja, wallahi zata gane”
“Kiyi ‘ko’karin saita tafiyarki yanda bazata gane ba, zan kira wani friend nah likita ne sai na tambayeshi ko akwai abinda zai rage miki zafin, ko ma yaya dai zan kiraki”
Jinjina kai tayi tace “Toh zan gwada saitawa”
Kissing nata yayi yace “Wannan ABUN SIRRI NE a tsakaninmu, only the two of us, zakiji sau’ki so stop crying”
Sai da yaga ta shiga gida sannan ya shige motarshi yabar wajen, zuciyarshi cike da farin cikin yau ya kar’bi abinda yayi sha’awar kar’ba daga wajen Sofy shekara da shekaru amma ta hanashi, yau yayi yanda yakeso da ita, rayawa yakeyi a zuciyarshi tunda yanzu yasamu yayi disvirgining nata ai yayi mai wuyan, duk lokacin da yake bu’katar ta zai san yanda zaiyi yasa ta yarda ta hanyar mayaudaran kalamai.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Leena tashiga ta nuna ma Rafee da Momy abubuwan da ta saya takuma gayamusu cewa Suhal ne ya biya, ba ‘karamin mamaki sukayi ba, har Momy tace zata kirashi tace bai kamata ya kashe kud’i dewa haka ba amma Rafee ta dinga bata ha’kuri har ta ha’kura amma duk da haka saida ta kirashi ta mishi godiya takuma ce mishi bai kamata ya shiga wahala har haka ba, murmushi yamata yace bakomai.
Shiru shiru suna zaune har akayi maghrib ba Sofy ba labarinta, kiran duniyan nan sun mata amma bata d’auka, hankalinsu yayi mugun tashi, su tsoron su ma kar wani abu ne ya sameta a hanyar dawowa tunda tun La’asar ya kamata tadawo.
Ko abinci sun kasa ci, suna wannan halin ne har past 9, daidai lokacin Sofy ta bud’e ‘kofa gamida sallama a hankali. Rige-rigen isa wajenta sukayi, tambayarta Momy ta hau yi “Sofy, lafiya?, meh ya tsaida ke har yanzu?, ba abinda ya sameki?”
Hawayen da take ma’kalewa ne ya zubo mata, rungume Momy tayi tace “Kiyi ha’kuri Momy, ki yafemin, bazan sake ba”
Kama hannunta Momy tayi tajata suka zauna akan kujera sannan tace “Shikenan, ba abinda zan miki, ina kikaje sannan meh ya tsaidake har warhaka?, wayarki kuma mesa baki d’auka?”
“Da naje gidan ‘kawata d’in sai mamanta ta aiketa gidan sistanta shine tace muje tare, da mukaje kuma sistanta d’in tana son mutane sosai, ta hanamu tafiya wa sai mijinta ya dawo zai dawo damu, mijinta bai dawo ba sai wajen takwas, muka jirashi yayi wanka yaci abinci shine ya dawo damu, har yace ma zai shigo yabaki ha’kuri yakuma miki bayani don yanda yaga na rikice amma sai nace mishi yabari kawai, in namiki bayani you will understand. Wayana kuma bansan yana silent ba sai da muka kamo hanya ne nagani” Sofy ta fad’a cikin kuka
Rafee da Leena zuba mata ido sukayi suna jin labari, Momy ta sauke ajiyar zuciya tace “Shikenan, in zaki sake dare irin haka ki kiramu ki gayamana, kinsa duk hankalinmu ya tashi, na tsamman wani mugun abu ne ya sameki”
Jinjina kai tayi tana share hawayenta tana kuma godema Allah da ‘karyar ta ya kar’bu a wajen Momy.
*REAL MHS*
Munay, Hanee and Stylish
Skip to content
haneefahusman
OCTOBER 8, 2016
ABUN SIRRI NE 61-65
*ABUN SIRRI NE*
Na ‘yan uku
*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*
*NWA*
*61-65*
Haneefah.mywapblog.com
Stylishbichi.mywapblog.com
Munayshat.mywapblog.com
☆☆☆☆☆☆☆☆
Yana isa gida ya hango Ilham zaune akan kujera a tsakar gida ta sa ‘yar three quarter da top, kunnenta toshe da headphone, fuskarta saitin sama saidai idanunta a lumshe suke wanda hakan ke nuni da ko ma mene takeji a kunnentan yana ratsa jikinta sosai.
Har yayi parking bata ma san ya shigo gidan ba, a hankali yafara takawa yana dosan inda take. Cire headphone d’in yayi daga kunnenta, a d’an firgice ta bud’e idanunta, ganin shine yasa ta sauke ajiyar zuciya tace “Ya Suhal you startled me”
Murmushi yayi yace “Meh kikeji kika nitsu haka?” sawa a kunnenshi yayi yaji karatun Qur’an ne.
Gyara zamanta akan kujerar tayi tace “Daman meh kake expecting?, a song?”
“Yeah, na tsamman wa’ka ne”
“Na tuba ai ya Suhal, wallahi wani wa’azi naji inda ake cewa duk wanda yaji kid’e kid’e a ranar al’kiyama za a zuba mishi ruwan dalma a kunnuwa, bakaga yanda naji tsoro ba, tsoron azaban Allah”
Murmushi yayi yana mi’ka mata headphone d’in yace “Good girl, gwanda da kika bar ji, Allah ya shirya masu ji”
Tace “Ameen”. K’are mishi kallo tayi ta rungume hannuwanta a ‘kirji tace “Daga ina kake haka?”
‘Karya yamata yace “Na d’an je yawo kad’an ne” don yasan ko da wasa yace yakai Leena shopping ne ba ‘karamin rikici zasuyi ba
“Are you sure??” Ta sake tambayarshi
“Kina doubting ne?” Ya jefa mata tambaya batare da ya amsa mata wanda ta tambayeshi ba
Rau rau tayi da ido tace “Yeah, Allah ni tsoro nakeji ya Suhal, kar wata ta ‘kwace min kai, da zan samu ma ko fita hanaka zanyi don kar wasu matan su ganka”
Basar da maganar yayi don baison su ja conversation d’in. Jan hannunta yayi yace “Ni ba wannan ba ma, i have a gift for you”
“A gift?” Ta tambayeshi cikin murna
Bai ce da ita komai ba itakuwa sai faman sake tambayarshi takeyi, ‘kofar baya ya bud’e ya ciro teddy d’in ya mi’ka mata.
Wani irin ihu tayi wanda sai da ya toshe kunnuwanshi, tsalle tayi ta rungumeshi tana ‘kara ihun murna tanata zuba mishi godiya kaman ya bata aljannah. Da ‘kyar yasamu ta sauka daga jikinshi, murmushi yamata yace “You will never grow up naga alama”
Tura baki tayi tace “Kai fah ya Suhal kana son zagina wallahi”
“No ba batun zaginki bane, in ba yarinta ba yanzu wannan ihun da kikayin nan ba sai a tsamman saceki akazo yi ba?” Rufe bakinshi ke da wuya suka ga iyayen nasu a tsaye da gani aguje suka fito
Baba yace “Ya dai?, lafiya kam ko?”
Suhal yaja guntun tsaki yace “Wallahi lafiya lau Baba, kaga yanzu fad’an da nake mata kenan, ihun da tayi ko ni sai da na firgita”
Umma tace “Meh yasata ihun?”
Ilham cikin murna tace “Ihun murna ne fah umma, bakiga teddy da Ya Suhal ya bani bane?” Ta ‘karasa maganar tana rungume da teddy da yama fita jiki
Dariya kawai sukayi don shirmen Ilham sai ita. Ummi tace “Ni wallahi na tsamman ma wani abu ne ya sameta”
Dariyarsu suka dinga yi suna fad’an irin tunanin da yashiga ransu lokacin da sukaji ihun. Kiran sallah da aka fara ne yasa Abba, Baba da Suhal suka wuce masallaci, iyaye matan da Ilham kuma suka shige cikin gida.
Daga bayan Isha Ilham ta dami Suhal akan suyi game, sunkai sha d’aya da rabi na dare suna game sannan a gajiye suka kakkashe electronics na parlourn.
Suna cikin sallama da Ilham sai wayarshi yasoma ringing, dubawa yayi yaga Leena ce, satar kallon Ilham yayi ta gefen ido yaga ta ‘kura mishi mayun idanunta. Sakawa a silent yayi ya mayar aljihu yace “Goodnight”
Matsowa kusa dashi tayi da niyyar pecking nashi sai gyaran murya sukaji a gefensu, da sauri Suhal yasa kai yabar sashen. Ilham kuwa kunya kaman ta nutse ‘kasa ganin Abba ya kamasu ahaka, isa gabanta yayi ya kira sunanta “Ilham”
Batare da ta d’ago ba tace “Na’am”
“Meh ke tsakaninki da Suhal?”
Dubanshi tayi da sauri, wani abun da bata ta’ba gani ba yau ta ganshi a idon Abbanta, ‘bacin rai ne kwance ‘karara a fuskarshi, a rikice tafara in-ina “Ba….bu”
“Babu?” Ya maimaita
“Eh, ba…bu?”
Iska ya furzar yace “Kince min babu, karki kuskura na ga akasin hakan”
Jiki na rawa tace “Toh, In Sha Allahu”
“Je ki kwanta, sannan daga yau ban yarda kina yawan had’a jiki dashi da wata manufa ba, ki mishi kallon wan ki wanda kuka fito ciki d’aya kin jini?, ko da wasa karki fara tunanin sonshi don mun riga mun miki miji”
Zaro ido tayi tana kallon Abba, da ‘kyar bakinta ya iya cewa “Miji abba?”
Cikin tsawa yace “Eh!!, ko gardama zakiyi ne?!!”
Kuka tasa mishi tace “Amma Abba…..”
D’aga hannu yayi zai kwasheta da mari amma Umma da fitowarta kenan tayi saurin kama hannunshi tana girgiza mishi kai.
Kallon Ilham tayi tace “Ba komai, je kiyi bacci, baza amiki auren dole ba kinji?”
Dagudu ta nufi d’akinta tana hawaye. D’aki Umma da Abba suka shiga, ko zama yakasa yi, tunaninshi yana neman guje mishi, zama abakin gado Umma tayi tace “Abban Fu’ad, meh kake shirin yi?, ba dai sirrin da muka binne acikin zuciyoyinmu shekara da shekaru ne kakeson tonawa ba??”
Girgiza kanshi kawai yayi yace “Nafiki son abar sirrin nan arufe saidai inaga hakan bazai yiwu ba, dole nan gaba zamu tona”
“Mesa za a tona?” Ta tambayeshi tana shirin kuka
Zama yayi akusa da ita yace “Maimuna, yazama dole ne yin hakan, yaran nan ni da Yaya muna zargin soyayya sukeyi, ko ba ke bace kika kawo mana maganar tun farko?, ke kika fara lura don dukkanmu bamuyi tunanin hakan ba a lokacin da muka bar ABUN SIRRI a cikin zuciyanmu”
“Ehh, amma ai zargi mukeyi, ka bari sai mun gaskata hakan tukunna afara batun d’aukan mataki”
Murza hannunta yayi yace “Kinsan girman laifin hakan in ya faru, tun farko gwanda muyi ma tufkar hanci, kar sai abu yayi nisa mu rasa bakin zaren”
Kallonshi tayi tace “In Sha Allahu ma ba abinda muke zargi bane”. Tattaunawa suka tayi akan sirrin da suke ‘boyema yaran nasu, duk iya d’auko rahoton mu mun kasa gane menene wannan sirrin, ba abinda suke ce mana sai *”ABUN SIRRI NE”*
☆☆☆☆☆☆☆☆
Hira suka zauna yi kaman kullum, anan sukaci abinci, duk yanda akaso Sofy ta tashi ta rage kayan jikinta ta’ki, acewarta ta gaji abarta ta huta, gaskiyar magana dai batason Momy taga tafiyarta ya chanja ne.
10:15pm
Momy tashi tayi tace “Ni na shiga, sai da safe”. Amsa mata sukayi sannan ta nufi d’aki don call na Hajiya Hafsat da taga ya shigo wayarta. Fad’awa kan gado tayi had’e da picking, cikin wani salo tace “Hello”
Hajiya Hafsat daga d’ayan ‘bangaren tace “Yagida Hajiya?, wallahi sai kewarki nakeyi”
Momy tace “I miss you more, ina kika shiga ne kwana biyu bama had’uwa saidai muta phone call?”
“Hajiya abubuwa ne suka sha min kai, kinsan abu da business, rikicin wani kud’i nah naketa faman yi duk kwanan nan” Haj Hafsat ta bata amsa
“Allah sarki, in kud’i kike bu’kata ai zan iya baki ba sai kin dami kanki ba”
“A’a Hajiya, a harkarmu ba a haka, bazan d’auki liability nah na d’aura miki ba alhalin inada tawa business d’in”
“Toh shikenan tunda haka kike ganin yafi”
“Ya yarana?”
“Suna parlour, Sofy ne yau takai dare awaje sai yanzu tadawo”
Da sauri Haj Hafsat tace “Ina taje haka?”
Yanda Sofy ta gayamata haka ta mayar ma Haj Hafsat wacce kawai jinta takeyi, tariga tasan ‘karya Sofy ta shirga don taga fitowarsu daga hotel alokacin da take faman shiga da wani Alhajinta.
“Allah ya kiyaye, a dai cigaba da saka ido kar ta fad’a hanyar banza”
Murmushi Momy tayi tace “Abinda nakeyi kenan kullum tunda ubansu bai damu dasu ba”
Daga nan hirar tasu ta chanja zuwa nasu na ‘yan duniya, mudai MHS muka tattara biros namu muka bar d’akin
☆☆☆☆☆☆☆☆
Momy ta tashi ba da dad’ewa ba Sofy ta d’auki jakanta tafara takawa ahankali tana cije le’be ta shige d’akinsu, Leena dai bata lura da yanayin tafiyar Sofy ba don kallon TV da takeyi, Rafee ce dai ta lura. Bin bayanta tayi da sauri ta maida ‘kofar ta rufe, a firgice Sofy ta dubeta tace “Rafee lafiya?”
Jan hannunta Rafee tayi suka zauna akan gado sannan tace “Sofy meh ya sami tafiyarki?”
Sunkuyar da kai Sofy tayi tace “Nothing”
Tsaki Rafee taja tace “Kibar min ‘boye-‘boye”
“Babu nace miki”
Tashi tsaye Rafee tayi tace “Fine tunda kinfison Momy tasani, zanje na sameta na gayamata in yaso sai ta tambayeki, ita kam ai baki isa ki ‘ki gayamata ba”
Da sauri Sofy ta tsugunna akan guiwowinta tace “Don Allah karki gayama Momy, zan gayamiki”
“Ehen?, ina jinki”
Tashi tsaye tayi tace “Bash ne”
“Bash yayi meh?” Rafee ta tambayeta
“Yayi drugging nah sannan yayi raping nah, he did it more than once duk da yasan yajimin ciwo, ya rabani da virginity nah” ta ‘karasa maganar tana kuka
Kan Rafee ne ya sara sosai, duk iskancinta tafiso ya tsaya a ita kad’ai, kar ‘kannenta su fad’a iskanci kaman yanda ita tayi tsundum aciki.
Rungume Sofy tayi tace “Shhh, yi shiru kar momy ko Leena suji”
Shiru tayi sai sheshshekar kuka da takeyi, bubbuga bayanta tayi sannan tace “Shikenan, muje kiyi wanka ki gasa jikinki da ruwan zafi sai kizo kisha magani”
Jinjina mata kai tayi, toilet suka shiga, Rafee ne ta tayata gashin, Sofy sai kuka takeyi tana rufe baki don kar ajita duk da irin zafin azaban da takeji.
Tayi gashi sosai sannan Rafee ta kamo hannunta suka dawo d’aki, sallah ta rama tukunna tasa kayan bacci. Rafee ta ‘ballo wani capsule ta bata da ruwa akan tasha, duk da Sofy ta tsani magani haka yau tasha ba ko gardama, bata jima da sha ba wani baccin gajiya ya d’auketa.
Rafee zama tayi a bakin gadon tana hawaye, ita kad’ai tasan irin turirin da zuciyarta ke yi akan budurcin Sofy da Bash ya kar’ba.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Ku cigaba da ha’kuri, yau d’in kuyi managing don bai da yawa. Don nayi al’kawari ne saisa na dage nayi squeezing time nayi.
Love
*REAL MHS*
Munay, Hanee and Stylish
Skip to content
haneefahusman
OCTOBER 8, 2016
ABUN SIRRI NE 66-70
*ABUN SIRRI NE*
Na ‘yan uku
*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*
*NWA*
*66-70*
Haneefah.mywapblog.com
Stylishbichi.mywapblog.com
Munayshat.mywapblog.com
☆☆☆☆☆☆☆☆
Bari mu waiwayi ya Fu’ad yake all