Showing 15001 words to 18000 words out of 37595 words
ya shiga toilet yayi wanka yasa wani short sleeve shirt da three-quarter. Masallaci ya wuce don yin sallah, tare suka dawo da iyayen nasu as usual.
Ilham suka gani tana jera abubuwan da zasu bu’kata wajen cin abinci, sannu da shigowa ta musu sannan taje ta kira umma da ummi daga d’akunansu.
Dama wajen zamanta a tsakiyan Fu’ad da Suhal ne, tana zama ta d’an karkato da kai daidai kunnenshi tace “Ya Suhal ya headache naka?”
Murmushi ya mata yana wasa da cokalin hannunshi yace “Da sauki lil sis, thanks to you”
Fad’ad’a murmushinta tayi tace “Kafi ‘karfin haka a wajena”
Kallonta yayi ta gefen ido ya girgiza kai kawai ya cigaba da caccakula abincin yana ci bawai don yana jindad’inshi ba sai don kar iyayen su hau tambayarshi, shi kuma bai shirya answer da zai basu ba. Da suka gama suka zauna don kallon news amma Suhal ya musu sai da safe, cikeda mamaki Abba yace “Lafiya dai ko?”
“Lafiya lau Abba, nagaji inajin bacci ne kawai”
Baba yace “Toh Allah yasa hakan ne”
Bai son jan magana sai kawai ya sallamesu ya fice daga sashen.
10:20PM
Duk iyayen sun nufi d’akunansu don shirin bacci amma Ilham hankalinta yana wajen Suhal, sosai takeson sanin halin da yake ciki, tashi tayi tabar Fu’ad zaune yana chatting a wayarshi. Ba tare da knocking ba kawai ta bud’e d’akin, ganin wuta a kunne a bedroom nashin sai kawai ta kutsa kanta ciki. Kwance ta sameshi idanunshi suna kallon ceiling amma hankalinshi sam bai wajen don ta kira sunanshi sau hud’u ba tare da yasani ba. Ta’bashi tayi, firgigit ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula, baki wangale yake kallon Ilham, chan dai ya fuske yace “Yaushe kika shigo?”
Zama tayi a bakin gadon tace “Tun dazu, ya Suhal meke damunka?, tunanin me kakeyi?”
Daburcewa yayi yace “Amma meh ya hanaki yin sallama?”
Da mamaki take kallonshi don ita tun tashinta indai zata shigo d’akinshi bata damuwa da knocking ko wani abu, shiga kawai takeyi, hakan yasa tace “Naga kullum haka nake shigowa amma baka ta’ba magana ba, mesa sai yau kake ganin laifi na da banyi sallama ba?”
Murmushi yayi yace “Ba laifinki nake gani ba, ina dai gayamiki ne sabida nan gaba, daga yau ki dinga sallama ko knocking kinji?, its not proper ace gatsau kawai ki shigomin d’aki”
Jinjina kai tayi tace “Yi ha’kuri ya Suhal, bazan sake ba”
Zama yayi ya jingina da jikin gadon yana mai fuskantar ta yace “Ya wuce, akwai abinda kikeso ne?”
Girgiza kai tayi tace “Babu, nazo na duba ko headache d’in ne yasake dawowa saisa ka bar parlour dawuri sai kuma nazo nasamu kana tunani?, is something bothering you?”
Jim yayi yana tunanin me zai ce mata, daga baya yayi murmushi yace “Nothing to worry about, kawai sungullan bud’e pharmacy d’in nan ne ya hau kaina, im stressed out”
Cikeda tausayawa tace “Ayyah sannu Ya Suhal, ko na dinga rakaka in yaso sai na tayaka wasu abubuwan?”
Da sauri ya katseta yace “No dont bother, zai wuce kwanan nan”
Hayewa kan gadon tayi, shiko binta yayi da ido yana ganin ikon Allah. Baiyi aune ba yaji ta rungumeshi tana hawaye, bubbuga bayanta yayi yana tambayarta me ya faru. Cikin muryan kuka tace “I cant take it ya Suhal, bazan iya ganin kana wahala ba, zuciya na bazai iya d’auka ba, please let me help you”
Zuciyarshi ya hau dukan uku-uku don yanzu kam ya gama tabbatar ma kanshi inda Ilham ta dosa amma sai ya shashantar da maganar ya d’ago kanta yace “Shine harda kuka?”
Zuba mishi idanunta tayi tace “Bakasan matsayinka a wajena ba ko?, Ya Suhal ko kaina banaso kaman yanda nake son….”
Katseta yayi ta hanyar cewa “Shhhh, its okay, shikenan ki bar zubda hawayenki akaina kinji?”
Rungumeshi ta ‘kara yi kaman zata shige jikinshi tana sauke ajiyar zuciya, tunani sosai Suhal ya farayi “Ilham why me?, bakisan kallon ‘kanwa nake miki ba ko?, mesa zuciyarki zata wahalar dake haka?, ina tausayinki sosai don ban jin ko da d’igon soyayyarki a raina saidai i cant bear seeing u hurting, bazan iya ba, gashi Leena tazo tana neman shiga rayuwana ba tare da na sani ba, bazan ta’ba nuna bansonki ba Ilham don ABUN SIRRI NE acikin zuciyata”. Bayan ya gama sa’ke-sa’kenshi sai ya janyeta daga jikinshi cikin dabara, hannunta ya ri’ke yace “Cry no more okay?”
Jinjina kai tayi sannan ta sauko daga kan gadon ta mishi sai da safe gamida pecking nashi a kumatu. Har takai ‘kofa sai ta juyo ta kalleshi, murmushi yamata sai tasa kai ta fice daga d’akin.
Tana fitowa suka kusa cin karo da Fu’ad, wani kallon tuhuma yabita dashi don shi yanzu sam hankalinshi baya kwanciya yanda Ilham take shishshige ma Suhal duk da yasan Suhal will never hurt her. Sunkuyar da kanta tayi kaman mara gaskiya ta wuce ta gefenshi, shiga d’akin yayi don yi ma Suhal sai da safe. Nan ya tarar dashi a tsakiyan d’aki sai pacing to and fro yakeyi, gyaran murya da yayi ne ya fargar da Suhal akan Fu’ad ya shigo d’akin. Fu’ad ya ‘kare mishi kallo sannan yace “Dama nazo na maka saida safe ne”
Suhal ya d’an sosa ‘keya yace “Okay, Allah ya tashemu”
Jinjina kai Fu’ad yayi yabar d’akin batare da yace komai ba.
Daren nan Suhal bai samu ya runtsa ba, har hawaye sai da ya zubar don tausayin halin da ya tsinci kanshi aciki rana tsaka, soyayyar Leena yana azabtar dashi har yana ganin bazai iya jure rashinta akusa dashi ba, soyayyanta ya mishi mugun kamu da bai ta’ba zaton akwai irinshi ba duk da dai shi bai ta’ba soyayya ba. Ya mi’ke, ya zauna, ya kwanta, chan kuma sai ya sake mi’kewa har dai ya gaji ya yanke shawarar yin nafila don samun sau’kin abinda yakeji, alwala yaje ya d’auro ya dinga jerosu yanata kai ma Allah kukanshi, daf da asubah bacci ‘barawo ya saceshi.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Washegari kamar yanda Momy ta musu al’kawari kaisu su za’bi duk kalar motar da sukeso ta kuwa cika musu, motoci masu kyau suka za’ba;Leena wani chevrolet ta za’ba, Sofy ta za’bi wani Corolla, Rafee kuma Peaugeot ta d’auka. Kowanne daga cikin ukun bazai kasa million goma ba don sabbi gal a leather ne sannan su ke trending. Komawa gida kowaccensu da motarta ta koma, murnar da ke cikin zu’katansu baki bazai iya fad’a ba, agida suka rungume Momy suna ta zuba mata godiya suna shaida mata yanda suke bala’in sonta and they are lucky to have her, murmushi take ta zubawa tace musu “Ba ni kad’ai zakuyi ma godiya ba don ba da kud’ina kawai na siya ba”
Basuyi mamakin jin furucin nan daga bakinta ba don sun san tabbas kud’in daga wajen Daddy yafito, dama shi duk da bai zama dasu hannunshi bud’e yake;ma’ana yana tura musu kud’i ta hannun momy fiyeda misali. Rafee da Sofy suka wani gintse fuska alamun ko oho, ganin haka yasa Momy tace “Ni ku bar wani gintse min fuska, ku kirashi ku mishi godiya tunda da kud’inshi ne kuma ba yanda kuka iya, shine ubanku”
Leena murmushin ya’ke tayi tace “Okay Momy, saidai inaso nasan mesa daddy bai kula damu?, mesa bai damuwa da sanin ya muke?, ko hiran kirki fah momy baiyi damu, ni tsoronshi ma nakeji wallahi” tayi shiru, duk suka zuba mata ido suna jiran ta cigaba.
“Watarana wallahi I cant help but think, asking myself some stupid questions; ko dai daddy ba asalin ubanmu bane?, in ko asalin ubanmu ne toh tabbas bai ‘kaunarmu, ya….”
Da sauri Momy ta katseta “Kul!!, kar na sake jin wannan maganar daga bakinki, batun so kuma I can assure you babanku yana ‘kaunarku fiye da tunanin mai tunani don haka kibar ganin kaman baisonku ne, abinda yasa yake nisantarku kuma ku kanku kunsan he is a very busy man, duk wannan sungullan yanayi ne don ku, don ya tara muku dukiya da bazaku ta’ba neman abu ku rasa a duniyar nan ba, ku mishi uzuri” Momy ta fad’i hakan ne don batason yaran su tsani ubansu tunda bai basu duk wata kulawa da uba ke ba ma ‘ya’yanshi, shi a ganinshi kud’i, material things sune rayuwa, ya manta cewa kowanne mutum koman girmansa yana bu’katar UBA ko don neman shawara da sauransu, ba ranar da in sunyi waya bata mishi ‘korafi akan hakan amma dayake shi mutum ne mai bahagon tunani…har yau ya kasa fahimtar ta.
Hawaye Leena ta share tace “I’m sorry Momy amma don Allah ki fahimtar da Daddy munfi bu’katar fatherly love and care daga gareshi akan miliyoyin kud’in da yake turawa don mu, bawai nuna rashin godiya akan hidima da yakeyi damu bane, a’a, sai don kud’i baya ta’ba sayan farinciki, Momy akullum zuciya nah acikin ‘kunci yake na rashin daddy akusa damu, ko irin abu ya shigar min duhu tsoron tambayarshi nakeyi don tamkar wani stranger nake ganinshi” ta ‘karasa maganar muryarta yana rawa mai nuni da zuciyar tata a raunane yake.
Momy ta kalli Rafee da Sofy da tunda Leena tafara magana suka ja jiki suka zazzauna akan kujera ba tare da sunce komai ba. Kama hannun Leena Momy tayi tace “Kibar damuwa indai akan wannan ne, I’ve always been here for you ko ba haka ba?, ni mai baku shawara ne aduk lokacin da kuke da bu’katar hakan and whenever you need someone to talk to”
Leena tayi jim sannan ta shiga girgiza kai tace “Ke daban daddy daban Momy, each one of you yanada role da yafi iya playing, nasan kullum kina tare damu and banda bakin da zan nuna farinciki nah akan hakan” tayi shiru, sai kuma ta cigaba “We need a father, Momy ki taimakemu ki sa daddy ya zama uban da yake tarairayan mu, uban da zai yi mana holo idan munyi ba daidai ba, uban da zamu sha’ku dashi wanda bazamuji shakkarshi ba” da ‘kyar ta iya ‘karasar da maganar don yanda kuka ya taso mata. Sofy da Rafee ma saida suka zubda hawaye, Momy tayita basu baki tana encouraging nasu akan su dage da addu’a Allah ya karkato da hankalinshi zuwa gida, daganan tasa su kiranshi don su mishi godiya, as usual, daga ya amsa gaisuwar da lafiya saikuma da suka mishi godiya yace bakomai, batare da wani hira ba suka mishi sallama.
☆☆☆☆☆☆☆☆
3 days later
Suhal komai ya kunce mishi, ya zama kalar tausayi, duk surutun Suhal yanzu ya zama shiru-shiru. Yanason ko da kallonta ne yayi don ya fallasa mata sirrin zuciyarshi yakuma shaida mata tun ranar da suka had’u zuciyarshi ya kasa sukuni.
Around 4pm ya sha wanka cikin wani Blue shadda wanda aka mishi zubi na fitan hankali, ko mu MHS sai da muka ce “WOW” don iya had’uwa ya had’u, hularshi ya karya irin na samari masu ji da kansu, wankan turare yayi ma jikinshi don ya fesa kusan kala biyar, ‘kamshin suka had’u suka bada wani scent mai bala’in sanyi da dad’i, agogo ya d’auka ya d’aura a wrist nashi, ya ciro takalma “Bertozzi” ya sa, ‘kare ma kanshi kallo yayi a mirror yaga komai yayi sannan ya d’auki wayoyinshi da makullin motar ya kulle d’akin.
Har ya shiga motar ya tayar, juyawar da zaiyi sai yaga Ilham ta fito dagudu daga sashen su tana waving mishi hannu alamun ya tsaya. Saukar da glass d’in motar yayi lokacin da ta iso, ganin tanata ha’ki yasa shi cewa “Ya da uban gudu haka?”
Daidaita numfashinta tayi tace “Ya Suhal zan bika ne”
Girgiza kai yayi yace “No Ilham, meeting zanje ba wani waje ba, kinga ba yanda za ayi naje dake”
“Ba sai na zauna a motar ba?” Ta fad’a cikin marairaicewa
Tura hulanshi yayi zuwa gaban goshi yana sosa ‘keya yace “Please lil sis zakisa na makara, kingane ne ba?, wajen maza sunyi yawa ba yanda za ayi naje dake”(daman ance in namiji yana sosa ‘keya toh baida gaskiya ne, no be so??;))
Ilham ta zura mishi idonta, chan ko meh ta tuna sai tayi wani fari da ido tace “Ho!!, Ya Suhal does that mean kana sona?”
Cikin rashin fahimta yace “Bangane ba”
Du’kowa tayi daidai window d’in tace “Kana kishina, it means kana sona”
Zaro ido yayi yace “Wa ya gayamiki?”
Dariya tayi tace “Kai ka fad’a yanzu batare da ka sani ba, kace bazakaje dani ba don akwai maza sosai awajen”
Dafe kai yayi, ‘kasa-‘kasa yace “Oh my God”, shi ya rasa Ilham nan wace irin mutum ce mai negative tunani, shi yace akwai maza awajen so bazai tafi da ita ba don kar ta dage zataje ta kopsa mishi son ganin Leena da yakeyi, gashi bahagon tunaninta abinda ya bata daban, soyayya. Murmushi ya ‘kir’kiro yace “Hmmm, kina ‘bata min lokaci da surutunki nikuma na tsaya ina biye miki, na wuce”
Matsawa tayi daga kusa da motar tanata murmushi tana d’aga mishi hannu.
Eid mubarak to you all, Allah ya maimaita mana. Love❤
Haneefah.mywapblog.com
*REAL MHS*
Munay, Hanee and Stylish.
Skip to content
haneefahusman
SEPTEMBER 17, 2016
ABUN SIRRI NE 37-38
*ABUN SIRRI NE*
Na ‘yan uku
*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*
*NWA*
*37-38*
☆☆☆☆☆☆☆☆
A motar yana driving yana d’an tapping na steering wheel yana tunanin yanda zai tsara Leena, murmushi kawai yake sakewa kaman wanda aka mishi albishir da gidan aljannah. Minti goma yakaishi ‘kofar gidansu, parking yayi batare da ya kashe motar ba yana tunanin wa zai samu ya kira mishi Leena daga cikin gida, sai juye-juye yakeyi amma har yayi minti shabiyar bai ga alamun yaro ko d’aya ta wajen ba dayake anguwan shiru yake, kowa yana cikin makeken gidanshi. Da yaga ba sa’a sai kawai ya fito daga motar yanufi gate d’in su yafara knocking, chan sai maigadi ya le’ko yace “Wanene?”
Mi’ka mishi hannu Suhal yayi don suyi musabaha, cikin tsoro Tijjani ya bashi hannun suka gaisa sai yake tambayarsa “Y’alla’bai wajen waye kazo?”
Suhal yayi murmushi yace “Don Allah ko zakamin sallama da Leena?”
“Leena?, Leena?” Tijjani ya maimaita, chan dai yace “Malam da ma kar ka wahalar da kanka don ita wannan bata tsayawa da samari, ko na kirata ma ba zuwa zatayi ba”
Suhal ya jinjina kai, yana ‘kara girmama kamun kai irin nata yace “Amma dai da ka taimaka kaje kace don Allah tafito inason magana da ita”
Tijjani yayi jim sai yace “Toh amma dai ka gayamin sunanka don banaso nayi ‘kafa biyu”
Kai tsaye ya amsa mishi “Kace mata Suhal ne”
Kujera ya bama Suhal ya zauna sannan yanufi cikin gidan don kiran Leena. Tana kwance tana kallon MBC2 taji Tijjani yana kwad’a sallama, amsa mishi tayi absent-mindedly don movie da akeyi ya d’auke hankalinta. Bud’e ‘kofar parlourn yayi gamida rusunawa yace “Ana sallama dake awaje”
A d’an firgice ta mi’ke tana kallonshi, harara ta watsa mishi tace “Sau nawa zan gayama kar ka sake zuwa kirana cewa wani yana sallama dani?”
In-ina yasoma yace “Umm…eh…yi ha’kuri, wannan d’in ma don naga alamun mutunci a tattare dashi sannan yata had’ani da Allah saisa nazo na gayamiki”
Guntun tsaki taja tace “Mtchww, sai kaje kace mishi bana nan ai tunda kaud’inka yayi yawa”
Mi’kewa yayi ya nufi ‘kofa saikuma ya juyo yace “Aff!!, yace nace miki Suhal ne”
Shiru tayi tana tunanin ina tasan sunan don sosai sunan yamata sounding familiar, ta jima sannan ta tuno inda tasan sunan, nan take ta mi’ke tace ma Tijjani “Okay nasanshi, je kace ina zuwa”.
Daganan ta nufi d’akinsu don chanja kaya don riga da wando ne a jikinta, a gurguje tasa atamfa gamida yafa gyale sannan ta feshe jikinta da turaren “Victorious”. D’akin Momy tanufa ta gayamata Suhal yazo, Momy tace zata iya zuwa amma karta dad’e.
Tun da maigadi ya gayama Suhal ga Leena tana zuwa sai ya tsinci kanshi da fad’uwar gaba, rubbing na palms nashi ya hau yi daga baya kuma yafara jujjuya agogon dake wrist nashi. Sallamarta da yaji akanshi ne yasa shi saurin d’aga idonshi ya saukesu a kanshi, zama tayi ta gefenshi akan kujerar da Tijjani ya ajiye mata. Murmushi tamishi tace “Sannu da zuwa”
Zuciyarshi yasoma bugawa fat-fat kaman zai fito daga ‘kirjinshi, da ‘kyar ya iya furta “Yauwa, na sameki lafiya?, yagida?”, yama rasa me zaice mata don bai ta’ba soyayya ba kuma baisan ya akeyi ba.
Cikin sanyinta tace “Alhamdulillah, ina ‘kara mi’ka godiyata zuwa gareka bisa taimakona da kayi few days back”
Murmushi yayi yana kallonta yace “No ba komai”
Tana d’ago idonta yayi saurin kawar da dubanshi daga gareta kaman wani mai tsoro ko kuma ince cikeda jin kunyarta. Shiru sukayi na mintuna, Leena ta lura kaman akwai magana a bakinshi don sai ya bud’e baki zaiyi magana sai kuma ya had’iyeta, hakan yasa tace “Ko akwai abinda kakeson cewa ne?”
Diriricewa yayi, sam ya kasa furta komai, sai da ya dad’e sannan yace “Akwai kam, ko zaki ban number d’inki?, inaga ta waya zaifi”
Dariya ne ya kusan ‘kwace mata ganin gashi dai iya had’uwa ya had’u amma kaman tsoronta yakeji, darawa kad’an tayi tace “Meh zai hana?”
Wayarshi ya mi’ka mata tasa mishi number d’in, tana bashi ya mi’ke kaman wanda aka mintsila. Gyara hulanshi yafarayi yana cewa “Barina wuce, zan kiraki awaya”
Rakashi tayi har ya shiga motar sannan ta koma gida.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Abdulyassar zaune akan kujera Haj Hafsat kuma tana zaune a kujerar kusa dashi, hira sukeyi wanda yake nuni da irin sha’kuwar da ke tsakanin uwar da d’an nata. Jefi-jefi takan fakaici idon Abdulyassar ta d’auki wayarta tayi d’an danne-danne sai ta ajiyeshi, sam bai nuna mata ya lura da abinda takeyi ba amma chan ‘kasar zuciyarshi is full of curiousity don yanda Momy takeyi kaman tana ‘boye mishi wani abu. Yanaso yace mata ta ara mishi wayar tata amma yasan ko ya fad’a ba bayarwa zatayi ba don sun sha yin hakan, ko da wasa Momy bata gangancin ajiye wayarta ako ina, ko kitchen zataje da wayar take zuwa. Hamma yafara yi kaman yana jin yunwa, kallonshi Mummy tayi tace “Ya dai?”
Wani hamman ya sake sannan yace “Mummy I’m hungry”
Cikeda kulawa tace “Ga abinci a dinning ai, je kaci mana”
Girgiza kai yayi kaman ‘karamin yaro yace “Mummy ni miyar da kikayin ne sam bana sha’awar cinta, snacks nakeso”
“Haka zakata zama da yunwa kenan Abdul?, kaje ka saya tunda ba nisa sai kazo kaci”
Langa’bar da kai yayi yace “Allah ‘kiuya nakeji Mummy, ki taimaka kije ki siyomin kar yunwa ya illata ni”
Da saurinta ta tashi ta nufi d’aki don ba abinda tafi so a duniyar nan kaman d’an nata saisa bata iya jure ganinshi cikin wani hali. Bata jima ba tafito tana yafa gyale, cikin sauri ta suri key d’inta ta sallameshi akan zataje ta siyomishi, don saurin da takeyin ne yasata mantawa da