Showing 24001 words to 27000 words out of 37595 words

Chapter 9 - ABUN SIRRI NE Sirrin Rayuwa By MUNAYSHAT

11 Sep 2026

131

table gamida sakarwa junansu murmushi, hirarsu suka cigaba da yi.
Chan sai Sofy ta duba wayarta da ke cikin handbag nata, 2:55pm tagani, a rikice ta tashi ta fara gyara jikinta don dama ‘karya tayi ma Momy akan zataje gidan wata ‘kawarta, Momy kuma tamata kashedin kar ta yarda ta wuce la’asar gashi yanzu la’asar kam har ya doso. Kama hannunta Bash yayi yace “Babe, ina zakije kike gyara jiki haka?”
Ba cikin nutsuwarta ba tace “Bash I have to go, Momy zata min fad’a”
Wani makirin murmushi yayi da shi kad’ai yasan ma’anar shi sannan yace “Ki d’an tsaya kad’an mana”
Ta bud’e baki zatayi magana taji kanta yafara juyawa, batasan lokacin da ta fad’a jikinshi ba. Murmushi yayi cikeda jindad’i don ya lura maganin da yasa mata ne yafara aiki, shafa jikinta yasoma yi ahankali kaman tafiyar maciji yace “Hey, are you okay?”
Lumshe ido tayi don tuni tabar duniyar nan tamu, inaga ma har ta isa pluto, shafata da yakeyi ya ‘kara saurin aikin maganin a jikinta. Kasa magana tayi sai wani nishi takeyi kaman zata shid’e, aikam Bash yasamu abinda yakeso, hannun rigarta yafara sa’bulewa saikuma yayi saurin tashi don yatuna a club suke. Jan hannunta yayi ya d’auki handbag nata da ta yar, biyan kud’i yayi sannan ya ri’ke hannunta suka nufi hotel da ke manne da club d’in, neman yaga mishi riga tafara yi, dasauri ya biya kud’i a reception aka bashi key, cak ya d’agata, bai direta ko ina ba sai a cikin d’akin da ya kama musu.
Yana kwantar da ita yajuya don kulle ‘kofar d’akin amma Sofy ta cafko wuyarshi, idanunta jawur kaman garwashin wuta wanda Bash da kanshi sai da ya tsorata, da ‘kyar ya janye jikinshi yaje ya sama ‘kofar key. Juyowar da zaiyi yaga har Sofy ta cire rigar jikinta tana wani gantsarewa tana numfashi sama-sama, kayanshi ya cire sannan ya haura kan gadon, ai Sofy irin rikicewar da tayi har ya wuce tsammanin Bash.
Da zafi-zafi suka fara shafa junansu har suka tafi mai gaba d’ayan, ihu takeyi dayake its her first time amma da yake maganin yana aiki sai ma wani ‘kara haukace mishi takeyi. A ranar nan duk sun sha wahala musamman ma Bash don saida yayi nadamar drugging nata da yayi, sai kusan maghriba maganin ya saketa, duk yayi mata kacha-kacha ba ko kyaun gani, bedsheet fari da ke shimfid’e akan gadon ya koma ja kamar an yanka babban kaza an zuba jinin akan bedsheet d’in.
☆☆☆☆☆☆☆☆

*REAL MHS*
Munay, Hanee and Stylish.





Skip to content
haneefahusman
SEPTEMBER 28, 2016
ABUN SIRRI NE 51-55
​*ABUN SIRRI NE*
Na ‘yan uku
*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*
*NWA*
*51-55*
Haneefah.mywapblog.com
☆☆☆☆☆☆☆☆
Guntun tsaki Suhal yaja ganin Ilham ta tafi tana kuka, shi kad’ai yake magana “Kishi takeyi kenan ko meh?, lallai ashe nan gaba sai zuciyarta yakusa bugawa don bazan had’a son Leena da kowa ba”. Shareta yayi yafara danne-danne da wayarshi sai kuma wani zuciyar ta lurar dashi rashin dacewar hakan, mi’kewa yayi ya ja ‘kofarshi sai ya nufi sashen su Fu’ad(asalin sashen su Ilham) don yanada ya’kinin chan ta nufa.
Sallama yayi yaji shiru ba a amsa ba, haka yasa ya shiga kawai ya nufi d’akin Ilham da yaga ‘kofa a bud’e. Tsayawa yayi ganin Umma tasa Ilham agaba sai faman tambayarta takeyi, sallamar da yayi ne yasa duk suka kai dubansu wajen ‘kofar, ganin Suhal sai Ilham ta fad’a jikin Umma had’e da saka wani sabon kuka.

Cike da damuwa Umma ke tambayar Suhal “Ko kasan meh ya sameta?”
Girgiza kai yayi ya ‘karasa shigowa cikin d’akin sannan yace “Bansani ba Umma”
A sanyaye Umma tace “Bansan daga ina tafito ba, d’azun nan ina zaune a parlour kawai naga ta shigo a birkice ba ko sallama, da farko har zan tambayeta ya batayi sallama ba sai naga ta ruga da gudu tashiga d’aki tana kuka, da sauri na biyota nafara tambayarta meh yasata kuka amma kaga har yanzu ta’ki cemin ko uffan, ba abinda takeyi sai kuka”
Zama a bakin gadon yayi ya kalli Ilham sannan ya kalli Umma, murmushin ‘karfin hali yayi sannan yace “Umma d’an bamu minti goma, maybe in mu biyu zatamin magana”
Jinjina kai tayi ta janye Ilham daga jikinta sannan takoma parlour tazauna tanata faman tunani.
A d’akin kuwa Umma tana fita Ilham ta mi’ke zata bita, saurin shan gabanta Suhal yayi ya tare hanya sannan yace “Ina zaki?”
Kallonshi tayi ta watsar sannan tace “Ya Suhal ka matsamin a hanya kar kasa na gayama magana”
Baice komai ba ya tura ‘kofar d’akin ya rufe sannan yace “Ilham I’m sorry”
Ji tayi ya ma raina mata wayo, meh ya maida ita, toy ko meh?, ko kawai ya maidata abun debe mishi kewa whenever he is bored?, ji tayi gwanda kawai ta amayar mishi da maganganun da ke cikin zuciyarta, wata’kila taji sau’ki ko kad’an ne. Share hawayenta tayi tace “Ya Suhal meh ka maida ni?, wawiya?, wacce zaka juya yanda kaga dama?, wacce zaka azabtar don ka lura ina sonka fiye da kaina?, ya Suhal abinda kamin yau shi yafi cimin rai, muna zaune ka d’auki call na wata har kana wani lankwasa murya… agabana fah, sannan hakan bai isheka ba, tafiya d’aki ma kayi ka barni kaman wata trash, I cant take it anymore” ta ‘karasa maganar zuciyarta a raunane don muryarta har yana rawa kaman zata sake ‘barkewa da wani sabon kukan.
Kasa cemata komai yayi kawai ya jawota jikinshi ya rungume, nan ta shiga sau’kar da wani ajiyar zuciya. Suhal ya riga yagama gano lagonta, ko wani irin fushi ta d’auka dashi yana rungumeta had’e da lallashi sai taji ta yafe mishi, wani irin mahaukacin so take mishi da bata ta’ba tsammanin akwai wacce tayi ma saurayinta irinshi ba. Saida yaji bugun zuciyarta ya d’an dawo daidai sannan ya d’an janyeta daga jikinshi ya ri’ke hannunta yana kallon fuskarta, tausayi sosai ta bashi har yaji zai iya bata ko da rabin-rabin zuciyarshi ne don ya tsani yaga Ilham tana kuka.
Kanta a sunkuye tana hawaye d’ad’d’aya, d’ago kanta yayi ya ciro hanky daga aljihun shi ya fara goge mata hawayen, da ‘kyar dai hawayen ya tsaya don gogewan da yakeyi kaman ‘kara ma hawayen ‘karfin guiwan zuwa yakeyi.
Kissing na forehead nata yayi, a d’an rikice ta kalleshi da idanunta dake cike da mayen sonshi, coolest smile nashi ya sakar mata wanda ya ‘kara narkar mata da zuciya har tanaji ko mata goma ne zata iya zama dasu in har Suhal ya aureta, ita ya auretan shine babban burinta.
Murmushi ta sakar mishi itama, nan yace “Yanzu muje muyi ma Umma bayani ko?, kinga yanda hankalinta ya tashi sosai”
Bai jira cewarta ba ya bud’e ‘kofar, hannunshi ri’ke da nata suka fito parlour suka zazzauna. Umma mamaki ne sosai ya cikata don ko minti goma Suhal baiyi da shiga d’akin ba gashi har Ilham tabar kukan da takeyi.
“Ilham zo” Umma tace da ita
Sai sannan Suhal ya sake mata hannu, jikin Umma ta kwanta, Umma tace “Dama meh yasa kike kuka d’azun har ina tambayar baki gayamin ba?”
Kallon Suhal tayi taga ita yake kallo, sunne kai tayi tace “Umma komai ya warware, dama misunderstanding ne kawai muka samu”
“Ke da wa?” Umma ta kuma jefa mata wata tambayar
“Ya Suhal” ta fad’a tana nunashi da yatsa
Umma taso ta sake tambayarta sai kuma taga in tayi hakan tayi wauta, fasa tambayar tayi da niyyar samun Ummi, Abba da Baba su tattauna akan abinda take zargi akan Ilham da Suhal sannan su sa ido don kar abun yayi nisa.
Murmushi kawai Umma tayi tace “Ai shikenan tunda ni barè ne baza a iya gayamin sirrin ba”
Dariya Ilham tasa tace “Allah bakomai Umma”. Suhal kuwa murmushi kawai yayi, Umma ta girgiza kai ta bar su a parlourn.
Tana fita Ilham ta dawo kujerar da yake zaune ta dafa kafad’arshi tace a shagwa’bance “Ya Suhal ni fah nagaji da ‘boye-‘boyen da mukeyin nan”
Zaro ido yayi yace “Ilham hakan shine yafi for now, kibari sai nan gaba in yaso sai mu gayamusu”
Tura baki tayi tace “Ni fah Allah aure nakeso muyi dawuri, Ya Suhal inasonka fiye da komai nah, ina fatan Allah ya nuna min ranar aurenmu”
Mamaki kwance a fuskarshi ya gyara zama yana kallonta sosai, chan sai yayi murmushi yace “Meh kike sauri ne?, mene kikeso da bana baki?, yanda muke yanzun haka zai zama in munyi aure so banga meh amfanin damuwa ba”
Cikin rashin fahimta tace “Bangane after aure da yanzu rayuwa d’aya zamuyi ba”
Kama hannunta yayi yana murzawa yace “Ilham i dont want to hurt you saisa banson ayi auren yanzu”
“Kaman ya?” Ta tareshi da sauri
Daurewa yayi ya cire kunya yace “What I mean is bazaki iya d’aukar nauyina ba, bazan kuma iya yin komai dake ba don gaskiya sai kin ‘kara girma, gwanda kar ayi auren wannan nasan ko tunanin wani abu dake bazanyi ba, in anyi aure fah?, you know ba yanda za ayi ace na zuba miki ido nata kallonki alhalin lafiya na lau, Ilham ha’kuri zamuyi, banso na jimiki ciwo ko wani abu so please mubar maganar aure for the mean time”
Hawaye mai zafi ne ya gangaro daga idanunta zuwa kumatun ta, cikin kuka tace “Ya Suhal wallahi zan iya d’awainiya da kai da komai naka, Allah kuwa ni ba yarinya bace, akwai wasu da na girma amma ahaka suke zaman aure lafiya lau har ma su haihu, please ya Suhal ka yarda, ni zanje na samu su Baba na gayamusu in ma kunya kakeji”
“Toh fah, lallai Ilham tayi nisa” yace a cikin ranshi. Afili kuwa cewa yayi “Understand me, a ra’ayina banso na auri yarinya ‘karama, saisa nafiso in kin kai ko 23 haka sai mu fara batun aure, that time kin ‘kara zama cikakkiyar mace”
Hawaye ta dinga yi tana mishi magiya amma duk ya’ki, da ‘kyar yasamu ta amince akan zasubar soyayyar tasu as sirri.
Girki ta wuce kitchen ta d’aura shikuma ya koma d’akinshi ya d’an kwanta.
4:00pm
Daidai wannan lokacin Suhal yake faman d’aura agogo ba’ki mai wal’kiya a tsintsiyar hannunshi, sanye yake da black jean trouser sai t-shirt fari mai d’an blue ajiki, ‘kafarshi kuma bertozzi ne ba’ki, ya dai fito fes, daga nan ya feffesa turare har duk d’akin ya gauraye da ‘kamshin, gashinshi da yake kwance wanda yama askin “low cut” ya ‘kara tacewa ya shafa hair oil.
Key ya d’auka sannan ya d’auki wayarshi ya danna ma Leena kira. “Hello Dear” tace dashi
“Hey yanmata, yanzu nake barin gida, i hope dai kin shirya?”
Dariya tayi don ita lokacin ne ma take faman shiga wanka sannan tace “Ehh kai nake jira”
“Yauwa ko ke fa?, da baki shirya ba Allah fasa rakiyar zanyi don banson na shirya sannan na zauna zaman jira”
Murmushi tayi tace a zuciyarta “Ai kuwa kayi gamo da asalin mai african time anan baka sani ba”. Afili kuwa cewa tayi “In ka ison dai just flash me sai na fito”
“Toh sai na iso” yace da ita sannan suka yanke call d’in kusan lokaci d’aya.
☆☆☆☆☆☆☆☆
*REAL MHS*
Munay, Hanee and Stylish





Skip to content
haneefahusman
SEPTEMBER 30, 2016
ABUN SIRRI NE 56-60
​*ABUN SIRRI NE*
Na ‘yan uku
*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*
*NWA*
*56-60*
Haneefah.mywapblog.com

Stylishbichi.mywapblog.com

Munayshat.mywapblog.com

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Shafa sajen da ya kwanta luf-luf a fuskarshi yayi yana murmushi, ahaka har ya shige motarshi yaja yabar gidan.
4:12pm ya iso gidansu Leena, fitowa yayi ya gaisa da mai gadi as usual sannan ya danna mata kira amma har ya tsinke bata d’aga ba. Bayan kaman minti goma bata d’auka ba sai ya tura Tijjani akan ya duba mishi ita, Tijjani yadawo yace “Tana shiri ne, tana zuwa”
Ba ita ta fito ba sai quarter to five, Suhal yayi Allah wadai da soyayya yafi a ‘kirga, da ba don sonta da yakeyi ba…ba abinda zai sa shi zaman jiranta kusan rabin awa, ya tsani a mishi african time shiyasa shima he is always on time.
Daga nesa ya hangota tasa wani dubai gown sky blue mai ado, tayi kyau sosai, duk haushin da yaji sai ya nemeshi ya rasa. Tana isowa inda yake zaune ta sakar mishi murmushi tace “Tuba nake ranka ya dad’e, na ‘bata maka lokaci ko?”
A d’an rikice ya dubeta yace “Ba komai, muje ko?”
Waje suka nufa inda yayi parking na motarshi kamin gate nasu, a hanya suna hira sosai don yanzu Suhal yana ma ‘ko’karin hira da ita duk da still yana tsoron bayyana mata sonta yakeyi, bawai yana tunanin zata mishi ‘kusa bane, a’a, matsalar bai ma san yaya zai fara tunkarar ta da maganar soyayya ba.
Bank suka fara zuwa ta ciri kud’i daga ATM sannan suka nufi sahad stores. Sun kusa isa kenan Suhal ya kalleta ya kawar da kanshi, tun da yaganta yakeson ya yaba kwalliyarta amma ya kasa, kanshi akan titi da ‘kyar yayi gathering courage yace “You look amazing”
Kallonshi tayi disbelievingly, tama kasa yarda wai comment d’in daga bakin Suhal ya fito, murmushi tayi ganin yama ‘ki yarda su had’a ido don tun da yayi maganar bai sake cire idanunshi daga kan titi ba.
“Awwwn, Thank you, you look good too” tace dashi
“Dont flatter me” yace mata nervously
Dariya tayi tace “Im serious, ba wani batun flattering aciki, its the truth, you always look good”
Murmushi yayi ya dubeta amma sai ya kawar da kanshi da wuri ganin ta zuba mishi manyan idanunta masu birkita mishi lissafi, ajiyar zuciya ya sauke ahankali sannan yace “Ina godiya”
Daidai nan suka isa mall d’in, bud’e ‘kofofinsu sukayi suka nufi cikin mall d’in. Jerawa sukayi ta fara za’ban abubuwan da zata saya shima ya fara za’ba ma kanshi inda shi yamafi za’ban perfumes akan komai, Leena shopping sosai tayi, duk inda tayi Suhal yana tare da ita kaman wani bodyguard, ahaka har sukazo counter. Bayan anyi lissafin komai sai Leena ta fara ‘ko’karin bud’e bag nata don ciro kud’ad’en, da sauri Suhal ya mi’ka ATM card nashi yace su cire. By the time da ta gama lissafo kud’in tana mi’ka musu daidai lokacin matar ta mi’ko ma Suhal ATM card nashi tana cewa “Thank you for shopping with us sir”
Jinjina kai yayi ya kar’bi ATM d’in ya mayar aljihu sannan ya fara tattara ledojin kayakin da suka saya yana kai su motar. Har ya gama Leena tana tsaye ko motsi ta kasa kaman statue, ko kud’in haka ta ri’keshi a hannunta tana bin Suhal da ido. Dawowa mall d’in yayi ya hura mata iska a fuska, wani had’a fuska tayi tace “Suhal what’s this?”
“Babu, in akwai abinda kikeson ‘karawa ma ki ‘kara nayi settling sai mu tafi”
Mi’ka mishi kud’in tayi tace “No, bazan yarda da hakan ba, ni fa nace ka kawoni zan saya abubuwa, *with my money* ba wai nace ka biyamin ba, in da nasan haka ne da tun farko bance ka kawoni ba”
Marairacewa yayi yace “Im sorry Leena, bansan ranki zai ‘baci haka ba, don Allah karki maida hannun kyauta baya, please I beg you”
Karkad’a kud’in tayi tana kallonshi, zatayi magana kenan ya girgiza mata kai yace “In ba cewa zakiyi kinyi ha’kuri ba please dont say anything”
A sanyaye ta mayar da kud’in cikin bag nata, ita gani take laifinta ne, gashi tasa ya kashe wannan uban kud’in a banza, tunanin yanda zata iya repaying nashi kawai takeyi. Muryarshi ta tsinkayo “Kin gama?”
“Eh” ta amsa mishi blankly
“Ina zuwa” yace da ita sannan ya bata key na motar akan taje ta jirashi. Kar’ba tayi ta fita waje shikuma ya nufi wajen teddy bears da ya hango, tsayawa yayi yana duba wanda zai siya ma Ilham don yasan tana matu’kar son teddy.
Wani ‘kato wane mutum ya za’ba, da yaji kud’in sai da ya girgiza amma haka ya cire ya bayar. Awaje kuwa Leena tana fita bata shiga motar ba sai ta jingina da jikin boot tana jiranshi, sallama taji, d’agowa tayi gamida amsawa.
“Sannu ko, ko zan iya sanin sunanki?”
“Sunana?” Ta fad’a tana neman ‘karin bayani
“Eh, sunanki?” Ya bata amsa
“Leena” ta bashi amsa a ta’kaice
Murmushi yayi yace “I’m Salees, can I have your number?”
‘Kare mishi kallo tayi, fari ne, yanayin gemunshi irin quarter million d’in nan, yanada jiki saidai ba sosai ba, hancinshi yanada tsawo, baida tsayi sosai kuma baza asashi a layin guntaye ba. “Tohh fah, malam lafiya dai ko?”
“Lafiya lau, taimakamin da number d’in don Allah, ina d’an sauri ne saisa”
Kaman tace bazata bayar ba saidai kuma ganin kyakkyawa irinshi yazo yana neman numbarta ko ita mahaukaciya ce bazata ‘ki bayarwa ba, bashi number d’in ta fara shikuma yana dialing a wayarshi. Daidai ta kira number’n ‘karshe “2” Suhal ya iso wajen, godiya Salees yamata yajuya, saura kad’an suyi karo sai Salees yayi saurin dakatawa yace “Sorry, ban ganka bane”.
Bashi hanya Suhal yayi ya wuce bai ce uffan ba. Shiga motar yayi ya mi’ka mata hannu alamun ta bashi key, ba musu ta bashi, ta lura kaman ranshi a ‘bace yake. Zagayawa tayi ta shiga sannan tayi gyaran murya tace “Suhal are you okay?”
Guntun tsaki yaja yana jin zuciyarshi na wani irin tafarfasa saboda tsantsan kishi. “Karki damu” ya bata amsa
Jan bakinta tayi bata sake magana ba, sunyi nisa da tafiyar sai kawai taji ya taka birki kaman mahaukaci. Kallonshi tayi a razane tace “Suhal, meh ke damunka?”
Jajayen idanunshi ya zuba mata, dafe kanshi yayi don shi kad’ai yasan yanda zuciyar shi ke bugawa duk lokacin da ya tuna yaga Leena tana bama wani number’nta. Hucin da yakeyi yasa Leena bashiri ta kama hannunshi tace “Talk to me”
Cikin ‘bacin rai yace “Waye naga kuna tsaye d’azun sannan akan wani dalili kika bashi numberki?”
“Yace min sunanshi Salees….”
“Ba sunanshi na tambayeki ba, mesa kika bashi numberki nakeson ji” ya katseta da sauri
“Ya tambayeni ne nikuma naga bai kamata na wula’kanta shi ba tunda bansan da wani magana yazomin ba, na bashi saboda naga kaman ba mutumin banza bane”
Kallonta yayi yace “Ana gane mutum ta fuska ne?, mugu bai da kama Leena, mesa kika yarda dashi har kika bashi??!!”
Jin yanda yayi maganan cikin d’aga murya yasa bakinta yana rawa tace “Mugu bai da kama kace ko?, you are also a stranger to me Suhal, kana tsammanin in da nayi nazari da wannan kalmar ko sannu zanyi da kai ne balle mu tsaya mutunci?, kenan ma I’m the fool, ni wawiya ce da na yarda da kai, ni wawiya ce da har na kiraka kazo ka rakani ba tare da nasan daga ina ka fito ba, bansan da alheri ko sharri kake bina ba, haka kake nufi Suhal?” Ta ‘karasa maganar tana hawaye
Ganin hawaye yana zubowa daga idanun Leena yasa Suhal rikicewa sosai, ba abinda yake cemata sai “Thats not what I meant

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login