Showing 9001 words to 12000 words out of 37595 words

Chapter 4 - ABUN SIRRI NE Sirrin Rayuwa By MUNAYSHAT

11 Sep 2026

133

ta tafi da kayan akan in momy tafita zata mata waya ta kawo mata don yanzu in ta shiga da kaya ni’ki-ni’ki sai momy ta cikata da tambayoyi. Nazee da kanta taji mamaki har wani kishi-kishi tafara ji amma sai bata nunama Rafee ba, ta dai sa kayakin a motarta ta kama gabanta.
Wannan rana itace mafarin ‘kara kwa’bewan abubuwa. Sosai Rafee da Haj Hafsat suke fita yawonsu suje su aikata mad’igo ba tare da sanin momy ba.
Ku cigaba da ha’kuri, gobe ma zaku gani In Sha Allah, bama zama ne saisa muke muku bayan kwana uku-uku amma daga yau zaku dinga gani kullum da yardar Allah. We love you all

Haneefah.mywapblog.com
*REAL MHS*






Skip to content
haneefahusman
AUGUST 30, 2016
ABUN SIRRI NE 27-28
​*ABUN SIRRI NE*

Na ‘yan uku

*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*

*27-28*

☆☆☆☆☆☆☆☆

Abba da Baba sun had’u da Suhal da Fu’ad bayan an idar da sallar isha don haka tare suka tako daga masallacin zuwa gida don ba nisa tsakanin masallacin da gidan nasu. A side nasu Suhal yau za ayi dinner don haka Umma(maman fu’ad) taje taya ummi(maman suhal) girki, dama su haka tsarin gidan yake, yau ayi girki aci a side nasu Suhal gobe kuma ayi a side nasu Fu’ad sannan aci a wajen. Iyayen da samarin suna shiga suka samu sai sintirin jera kuloli da abubuwan bu’kata akan dinning ummi da umma ke yi, sannu suka musu sannan suka zazzauna akan kujerun dinning table d’in. Sai da suka gama komai sannan Ilham tafito daga d’akinta da ke side nasu Suhal(d’akuna biyu take dashi agidan, asalin nata a side na iyayenta da kuma na side nasu Suhal d’in), dinning table ta nufa taja kujera ta zauna tana hamma alamun ta kwaso yunwa.
Gaishe da iyayen tayi tana bubbud’e warmers na wajen, Fu’ad ya sake baki yana kallonta, da ‘kyar ya iya danne mamakin shi ya bud’e baki yace “Ilham, yanzu fisabilillahi abinda kikeyin nan abu mai kyau ne?, mesa kike haka?, rashin hankali ko kuma rashin sanin-ya-kamata?”
Ba tare da tabar bud’e bud’en ba tace “Meh nayi?”
Buge hannunta yayi ya kama ta ya zaunar akan kujera, tuni idanunta sun cicciko da ‘kwalla, iyayen kuma ba abinda sukace, sun dai zuba ma Fu’ad ido don jin laifin da yake i’krarin Ilham tayi. Cikin nutsuwa yasoma magana “Ba tun yau ba na lura, kullum umma da ummi ne ke yin duk girkin gidannan, bana ganin ko da shadow d’inki ne a hanyar kitchen, iyakaci abinda kika iya shine in an fito cin abinci zaki fito kina wani hamma kaman zaki had’iye mutane sannan ki hau bud’e-bud’e, wato kin iya ci amma baki iya dafawa ba ko?, baki sha’awar koyan girki?, ke fah macece ce lil sis, watarana aure zakiyi and ba namijin da zai iya jure zama da wacce bata iya abinci ba ko da kuwa yanasonta wane ranshi, ki gyara kinji?, daga yau ki dinga shiga kitchen kina ganin yanda sukeyi har nan gaba ma suhuta in kin iya”
Dukkansu jinjina kai sukayi alamun they are in support of abinda yace don kuwa abinda ya fad’a d’in gaskiya ne, Ilham tayi rau-rau da ido tana jiran taji iyayen sun kareta amma sai tajisu tsit kaman ma basu wajen. Hawaye ne ya zubo mata sharr, sharewa tayi sannan tace “Na fa iya girki ya Fu’ad, kabar cewa ban iya ba, yin ne kawai banaso”
“Kin iya girki?, meh da meh kika iya dafawa?” Fu’ad ya tambayeta
Tunani ta hau yi tana lissafi da yatsunta, chan tace “Na iya dafa indomie, na iya had’a quaker oats, na iya dafa su macaroni, spaghetti, frying na dankali da soya egg” tayi maganar tana washe ha’kora irin tayi abun kirkin nan.
Ran Fu’ad in yayi dubu toh ya ‘baci, in ba Ummi da ta d’aure mata gindi ba ya za ayi ace yarinya shekararta 18 iya abinda ta iya kenan, masifa ya hau yi kaman zai cinyeta “Ilham yanzu ko kunya bakiji ba kika lissafo min wad’annan shirmen wai ke kin iya girki?, a ganinki wannan ne girki?, an gayamiki kowa kamanki ne?, wad’annan tarkacen banza ne, wallahi gwanda ki nitsu kisan me kikeyi don wannan ba gata bane, ba namijin da zai aureki in har kika cigaba da tafiya ahaka”. Dinning area d’in tsit ba wanda yace ‘kala, tabbas maganar Fu’ad gaskiya ne, Fu’ad ya cigaba “Kinsan Allah, in nasake ganin ummi da umma suna girki bakya wajen wallahi…..”
Suhal ne ya katse shi ta hanyar d’aga mishi hannu don aganinshi bai kamata su taru su juya ma Ilham baya ba duk da gaskiya ake gayamata, murmushi kad’an yayi ya mi’ka ma Ilham hanky don ta goge hawayenta, ‘karfa tayi tana share hawaye kaman wacce aka mata shegen duka. Gyara zamanshi yayi sannan yace “Fu’ad, daga yau kar ka sake d’aga ma Ilham murya, in zaka mata magana kamata yayi ka kirata ku zauna ku tattauna ba ahaka ba, its embarrassing, in kai akayi maka haka zakaji dad’i?, oya apologise to her”
Umma(maman Fu’ad and Ilham) tace “Suhal kabar d’aure ma ‘karya gindi, bakasan kalan sangartan yarinyar nan bane, sam ba abinda ta iya, ban isa nayi magana ba nan ummi zata hau ni wai na cika takura ma yarinya, barshi ya ladabtar da ita ko zatayi saiti”
Fu’ad ya saki murmushi yana wani rubbing na palms nashi irin yaji dad’in nan. Ummi ta kama hannun Ilham tace cikin sigar lallashi “My dear yi shiru ki barsu, girki ne bazakiyi ba, wannan da kika iya ma ai wasu dewa basu iya ba, miji kuma kin samu kin gama, stop crying kinji?, haushi sukeji”
Suhal ya juya ya harari Fu’ad yace “Bazaka bata ha’kuri ba ko?”
Fu’ad ya wani d’aga kafad’a yace “Bazan bada ha’kurin ba, daga an gayamata gaskiya sai ta wani fara kuka kaman na duketa, ta had’iye zuciya ma in tanaso”
‘Kwafa Suhal yayi yace “Zamu had’u dakai” sannan ya hau lallashin lil sis nashi. Sam ta’ki shiru har sai da Abba(baban Fu’ad and Ilham) ya daka mata tsawa sannan ta nitsu tabar kukan. Serving na abincin ummi da umma sukayi ma kowa a plate, nan fah wajen yayi tsit sai ‘karan spoons da fork akeji. Acin abincin ma dafarko Ilham mi’kewa tayi zatabar wajen wai ita tayi fushi ta fasa ci, baba ne yayita bata baki har ta ha’kura ta dawo ta soma ci, abba da umma kuwa haushi ne ma ya cikasu da yanda sam iyayen Suhal basu ganin laifin Ilham ko da kuwa ta chanchanci a tsawatar mata.
Bayan dinner suka baje a parlour suna kallon 9pm news a NTA, Ilham kam daman d’akinta ta wuce don har yanzu fushi takeyi da iyayen nata(Abba da umma) da kuma yayanta Fu’ad. Chan sai Suhal yabita d’akin, kan gado ya sameta tayi ruf da ciki tana kuka, zama abakin gadon yayi sai yace “Lil sis bar kukan nan haka please, wipe ur tears ki tashi muyi magana”
Batayi gardama ba ta share hawayen had’e da dawowa bakin gadon ta zauna a gefenshi. Kama hannunta yayi sannan ya soma magana “Fushi kikeyi da su Umma?” Jinjina mishi kai tayi alamun eh, girgiza kai yayi yacigaba “Kibar fushi dasu, ba kyau fushi da iyaye”
D’ago jajayen idanunta tayi tace “Ai sun bar sona ne tunda har tsawa Abba ya min”
“Don sun miki fad’a ba wai sun bar sonki bane, in bakisani bama toh don suna sonki ne yasa sukayi hakan” Suhal ya fad’a cikin lallami, Ilham kuma ta wani tura baki kaman zata fashe. Ganin tayi shiru yasa Suhal cewa “And about girki, ya kamata ki koya, kinga in kinyi aure bazaku dinga samun problem da mijin ba, iya girki shine mace sannan the best way to a man’s heart is through his stomach, maza basu wasa da cikinsu, promise me daga gobe zaki dinga shiga kitchen kina koyan girki gun su ummi da umma”
Sai sannan ta d’an saki fuskarta tace “Ya Suhal kaima kanason matarka ta iya abinci?”
Ba tare da ya kawo komai a ranshi ba yace “Sosai ma lil sis, abinci, snacks, inaga ma before bikin zan sata a catering school ta ‘kara koyo wasu abubuwa”
Cikeda jindadi Ilham tace “Ya Suhal nice matarka ai ko?, saisa kakeso na koya girki”
Dum!! Yaji maganar ta daki zuciyarshi, wayancewa yayi, yayi kaman bai gane maganarta ba yace “Yanzu dai ba wannan ba, kinmin al’kawari zaki fara koya?”
Rungumeshi tayi tace “I promise Ya Suhal, i will do it for you, sannan kuma kacema Ya Fu’ad kar ya sakemin tsawa”
‘Ko’karin ‘ban’bareta daga jikinshi yayi yana cewa “Zan yi warning nashi karki damu, lil sis sakeni, kin girma kinyi nauyi, zakisa na kasa numfashi ai”
Sakeshi tayi tana dariya tace “Wani nauyi ne dani da in na rungumeka zaka kasa numfashi?, ko bakason matarka tayi jiki sosai ne?, in bakaso zan soma slimming” ta ‘karasa maganar pure-heartedly.
Girgiza kai kawai yayi yabar d’akin don yazama speechless, yanzu kam maganar Ilham yafara bashi tsoro da mamaki, akan wani dalili zata fara tsiro da sabbin abubuwa a tsakaninsu?, mesa zata dinga kiran kanta matarshi?, shi dai sha’kuwansu yana mata kallon ‘kanwa ne ba da wata manufa na daban ba, sannan aure fah, anya ma ilham tasan me take fad’a kuwa?, damuwan shi ma kar watarana ta kira kanta matanshi agaban iyayen nasu, ina!!, sam bazai iya auren Ilham ba, ba wai don batada kyau ko bata cika mace ba, Ilham ta wuce duk inda akeson kyakkyawar mace takai, bai mata kallon da ya wuce lil sis wacce ba aure tsakaninsu gashi kaman labari yanaso ya chanja.

Fans, ku cigaba da biyomu don jin ya wannan labarin zai kasance.

Haneefah.mywapblog.com
Munayshat.mywapblog.com
Munay, Hanee da Stylish

*REAL MHS*







Skip to content
haneefahusman
SEPTEMBER 4, 2016
ABUN SIRRI NE 29-30
​*ABUN SIRRI NE*

Na ‘yan uku

*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*

*29-30*

☆☆☆☆☆☆☆☆

Bayan sati d’aya

Rafee, Sofy da Nazee ne suna zaune a parlour suna kallon “The vow” a zee world, momy tafito daga d’akinta da shirin fita sai ‘kamshi takeyi. Kallonsu tayi sannan tace “Zan d’an fita anguwa, make sure kunyi girkin dare don zankai bayan Isha, Rafee da Sofy karku kuskura ku fita daga gidan nan, Leena dai banda damuwa da ita don batada rawar kai irin nakun nan, in kun fita ma nasa mai gadi ya gayamin, kunsan halina sarai”.
Sofy ta wani marairace fuska tace “Haba momy, wannan ai rashin yarda ne, kenan Leena ne kawai mai jin maganarki?”. Rafee ta ‘kara da “Bar momy fah Sofy, tana mana kallon marasa kunya bayan mun mafi Leena sanin-ya-kamata”.
Momy ta girgiza kai tace “Meh amfanin sanin-ya-kamata’n ku bayan baku amfani dashi?, Allah ya shirya”, ta maida kallonta wajen Leena tace “Auta kina bu’katan wani abu ne?”.
Leena tayi murmushi tace “Momy zan tura miki as text message, naga Sisters sai harara nah sukeyi”
Dariya momy tayi, ‘kasar zuciyanta cike da son yaran nata, ta d’auki key’n motarta sannan tace “Toh shikenan, ni na tafi”
Kusan atare sukace “Sai kin dawo”.
Tana tayar da motar ai kaman jira sukeyi har suna rige-rige wajen le’ka window da ke facing tsakar gidan, sai da suka tabbatar ta bar gidan sannan suka koma kan kujerun da suke zaune.
Rafee har jikinta yana rawa don dad’i, wayarta ta d’auka ta danna ma Nazee kira kaman yanda tayi al’kawari. Tana jin Nazee ta d’auka tafara magana “Nazee kizo min da kayaki nah yanzu, kiyi sauri, momy tafita”
Nazee ta amsa da “Okay, bani minti goma”
“Toh sai kin iso” shine abinda Rafee ta fad’a sai ta katse wayar zuciyarta wasai.
Sofy kuwa kiran Bash tayi akan yazo don kwana dewa momy ta kasa ta tsare ko bakin gate bata barinsu suje. Shima cikin jindad’i yace mata gashinan zuwa.
Kallon juna sukayi ita da Rafee sannan Sofy tace “Ya zamuyi da mai gadin nan ne?”
Rafee tana karkad’a ‘kafa tace “As usual, had’a kud’i zamuyi tunda shi mayen kud’i ne, mu bashi yabar su sushigo, kamin momy tadawo dai sun tafi”
Mi’kewa alokaci d’aya sukayi suka shige d’akinsu, jim kad’an suka fito da kud’i a hannunsu, basu tsaya ako ina ba sai a ‘kofar d’akin mai gadin gidansu. ‘Kwala mishi kira Rafee tayi “Tijjani!, Tijjani!”.
Da saurinshi ya amsa “Na’am hajiya” gamida fitowa yana ta rawar jiki.
Had’a ido sukayi sannan Rafee tayi nodding mata kai alamun tayi magana, Sofy ta le’ka bakin gate sannan tafara magana “Tijjani, alfarma muke nema a wajenka”, tana ‘karasa maganar ta karkad’a mishi sabbin 500 naira notes dake hannunta
Washe baki yayi yace “Toh toh, me za amuku?”
Rafee tayi wani murmushi tace “Dad’ina da kai akwai gane bayani, abunda mukeso da kai shine zamuyi ba’ki saidai bamuson ko da wasa Momy tasani”
Jim kad’an yayi yana nazari, chan sai yace “Amma dai hajiya bazasu dad’e ba ko?, don in tadawo ta gansu zan iya rasa aikina”
Caraf Sofy ta kar’be “Kai tsoronka yacika yawa don Allah, bazasu wuce bayan maghriba ba”
Jinjina kai yayi yace “Shikenan, meh zan samu?”
Kud’in suka mi’ka mishi, ‘kirgawa yayi yaga dubu biyar-biyar ne, yatashi da dubu goma kenan. Assuring nasu ya ‘karayi kan baza asamu matsala ba su kwantar da hankalinsu, cike da jindad’i suka nufi parlour kowaccensu da tunanin da takeyi.
A ‘bangaren Leena kuwa suna fita ta bisu da ido tanata sa’ka da warwara, wannan wani irin ‘kazamiyar rayuwa ne?, da taga hakan ba abinda zai haifar mata sai ba’kin ciki kawai ta mi’ke ta nufi kitchen don d’aura girkin da momy tace ayi don tasan yayyun nata bayi zasuyi ba.
15 mins later
Sofy ce tasha wanka cikin riga da wando ta hard’e akan kujera sai duba time takeyi a cikin wayarta. Horn da taji a gate ne yasata tashi dasauri ta nufi tsakar gida, mai gadi yana wangale gate motar Bash yashigo. Yana parking yafito daga motar ya nufota, itako dagudu ta ‘karasa wajenshi, wani wawan runguma sukayi ma junansu kaman zasu had’iye juna. Bayan sun d’an nitsu sai suka koma motar suka shiga gidan baya, wasu abubuwa ya fara mata wanda yasa tafita hayyacinta cikin lokaci ‘kan’kani dama kuma sunyi missing na junansu, ganin haka yasa muka tattara yanmatan ‘kafafunmu muka bar wajen.
Rafee tsaki take taja, sai faman kiran Nazee takeyi amma numbarta ya’ki shiga, tsaba ta tafi duniyar tunani har bata ji shigowar Nazee parlourn ba saida ta ta’bata, a firgice ta dubeta, wani ajiyan zuciya ta sauke gamida watsa mata harara. Cikin masifa tace “Nazee wani irin iskanci ne wannan?, tun yaushe kika cemin zakizo?, da kinsan ba a lokacin zaki taso ba da baki ce min nan da minti goma zakizo ba”
Zama a gefenta Nazee tayi tace “I’m sorry luv, hold-up ne ya tsaidani wallahi, kinsan bazan ta’ba ‘kin zuwa akan lokaci da gan-gan ba”
‘Kir’kiro murmushi Rafee tayi gamida mi’kewa tace “Shikenan yawuce, ina abubuwa nah?”
Nazee ta nufi ‘kofa tace “Muje, yana motar”.
Jido kayakin suka hau yi, sunyi ‘kafa uku-uku sannan suka samu suka ‘kare kaiwa. Jin ana shigo da abubuwa yasa Leena dake kitchen le’kowa parlour amma bataga komai ba sai muryar Rafee da takeji daga d’akinsu. Rage gas cooker d’in tayi tanufi d’akinsu don ganin ma idonta wainar da ake toyawa.
Har tasa hannu zata bud’e sai ta tsaya sakamakon taji Nazee na tambayar Rafee “Love, yanzu duk wannan kayan Hajiya ce ta baki?, tsaya ma tukunna, meh gaminki da ita?, mesa ta narkar da wannan uban dukiya a kanki?, meh dalili?”.
Rafee tace “Meh kike tsammani?”
Nazee tayi shiru sannan tace “There most be something, ba yanda za ayi haka kawai tayi wannan uban shopping nan a banza, ni gaskiya nafara zarginta ma”
Rafee tayi guntun tsaki tace “Ki bar zargin komai, Allah ne kawai yasa jininmu ya had’u, tana kyautata min ne bada wata manufa ba”
Nan ta murd’a hannun ‘kofar don ‘kara ma ‘kwanyanta haske akan abinda kunnenta suka jiyo mata, tana shiga tafara cin karo da tarkacen kayaki, baki bud’e ta ‘karasa shiga, tsayawa tayi tana bin kayakin da kallo, da ‘kyar ta iya cewa “Wai wai!!, ya Rafee irin wannan kayaki haka?”
Rafee sai lokacin tasan Leena ta shigo d’akin don ta bama ‘kofa baya tana jera kayakin acikin wardrobe, kallon uku saura kwata tamata sannan tace “Ehen, meh yasamu kayan?, meh gaminki dasu?”
In-ina Leena ta hau yi tace “Babu, naga sunyi kyau ne, waya miki wannan uban shopping haka?”
A fusace Rafee tace “Ubanki ne yayimin, ke naga kwanan nan kanki yana fizga ko?, in baki bar shiga sabgana ba sai na gyara miki zama”
Maganar yamata ciwo sosai amma saita danne tace “Allah yabaki ha’kuri, naga ke yayata ce, banga wani abu ba don naga kinsamu alheri har na tambaya waya miki”
Nazee taji haushin yanda Rafee tayima Leena, ita dai Allah ya d’ora mata son Leena kaman ‘kanwarta uwa d’aya uba d’aya, cikin nuna ‘bacin rai ta mi’ke tace “Rafee what is this?, why are you always rude to her?, itama fah ‘kanwarki ce kaman Sofy, u should treat her with love kaman yanda kikema Sofy, meh Leena tayi da har zagi zageta?, kuma ma wai akan wancan shegiyar tsohuwar, meh ma sunanta?, haj hafsat ne ko mene?, akanta kika zagi ubanki don bakida hankali”, taja wani dogon tsaki tana huci, sosai ranta ya ‘baci don ya had’u da kishin da takeji wata haj hafsat tana faman ‘kwace mata Rafee.
Das’karewa Rafee tayi ta kasa cewa komai, bata ta’ba ganin ran Nazee ya ‘baci irin haka ba, sai lokacin ta gane sam bata kyauta ma ‘yar innocent ‘kanwarta ba. Juyawa Nazee tayi da niyyar barin gidan, dasauri Rafee ta kamota tace “Yi ha’kuri, bansan me ya hau kaina ba”
Nazee ta maida kallonta wajen Leena da ke raku’be a jikin ‘kofa tana zubda hawaye, addu’a takeyi Allah yasa ba haj Hafsat ‘kawar momy ba ce, zuciyarta sai raya mata abubuwa da dama yakeyi.
Batayi aune ba taji Rafee ta kama hannunta ta fara cewa “Lil sis kiyi ha’kuri, bansan mesa namiki magana in a rude way ba”. Leena batace komai ba sai binta takeyi da ido wai yau itane Rafee take bama ha’kuri akan rude behaviours nata, bata ‘kara jin mamaki ba sai da Rafee ta d’auko wasu dogayen riguna guda uku tabata kyauta.
Godiya tamata sannan tace “Bari momy tadawo na nuna mata”
A firgice Rafee tace “No, no, wannan tsakanina dake ne, karki gayamata”
Dama Leena ta fad’i haka ne da nufin buga cikinta, jinjina kai tayi tace “Okay, bazan gayamata ba”. Tana kaiwa nan ta bud’e drawer d’inta ta ajiye gowns d’in aciki sannan ta koma kitchen don ‘karasar da girkinta da kuma yin shawara da zuciyarta.
Haneefah.mywapblog.com
*REAL MHS*




Skip to content
haneefahusman
SEPTEMBER 4, 2016
ABUN SIRRI NE 31-32
​*ABUN SIRRI NE*

Na ‘yan uku

*MUNAYSHAT*

*HANEEFAH USMAN*

*STYLISH BCH*

*31-32*

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Da fitan Leena daga d’akin Rafee ta rungumo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login