Showing 33001 words to 36000 words out of 37595 words
sara mishi wanda yana ganin kaman don rashin bacci ne ya jawo mishi, wankan shima yashiga yayi, wani plain long sleeve shirt yasa da wando, d’aukar wayarshi yayi yafara neman Leena yana fita zuwa parlour. Zama yayi, ya kirata bata d’auka ba sai a na ukun, shirun da yaji yasa yace “Hello, good morning”
Had’e fuska tayi kaman yana kallonta tace “Ka ri’ke good morning naka, I dont want it”
“Hey…Im sorry okay?, d’azun kin kirani ina bacci ne saisa”
“Ni ba ma wannan kawai ba, sabida meh kayi rejecting na call nawa jiya da dare?”
Kishi ne ya sake taso mishi sabo fil, iska ya furzar yace “Rai na ne ya ‘baci”
“Toh ni na ‘bata maka rai ne da zaka sauke zafin ranka akaina?”
“Akanki ne raina ya ‘baci Leena, that conference call”
“What about it?” Ta tambayeshi
“Wancan mutumin na mall chan ne ko?”
“Ehen…sai akayi yaya?” Ta tambayeshi a tsiwace
“Ni ba arguing nakeso muyi ba kingane?”
“Just go straight to the point, kanamin magana a murd’e”
Iska ya hura a bakinshi yana iyaka ‘ko’karinshi na ganin yayi keeping calm nashi sannan yace “Meh yakeso da ke?”
“Ba kaji komai ba?, ba na had’a call d’in ba?”
“Answer me Leena, banson masifa”
Murmushi tayi tace “Surutun shirme ya dinga yi, he’s so funny I tell you, wai fah aurena yakeso yazo ya nema”
“Leeeeena” ya kira sunanta yana jan sunan
“Na’am” ta amsa mishi
“Kinsan meh nakeso da ke?”
“Nop, what?”
“Gaskiya ni hankali nah bai kama guy nan ba, he talks alot, irin guys haka wallahi had’ari ne, and daga jin yanda yake magana in a flirty way mutum zai gane he’s used to talking to girls, ba ma magana kawai ba, ya saba neman mata, and I’m quite sure kanshi yana d’an banzan rawa, ya…..”
Katseshi tayi tace “Suhal ya zaka yi ma mutum mugun zato haka?”
“No Leena, understand what I’m trying to say, kingane ba?, just in ya sake kira karkiyi picking call d’in, he’s not a good match for you”
Shiru tayi tana tunani kala-kala, da ba don tasan Suhal as a friend ya d’auketa ba da sai tace yanasonta ne don wannan maganar da yayi kaman da kishi aciki. “Toh Suhal bazanyi aure bane?, kuma ma ni yanda guy d’in yake da surutu da wasa sai naji ya kwanta min arai” ta fad’i haka ne don tanason gaskata ma kanta zaton da takeyi
Murya asanyaye yace “Leena please don’t, karkice zaki aureshi, u barely know him, baki san mugu ne ko wani abu ba, I assure you wanda yafi dacewa da ke yana hanyar zuwa, just do as I say, block him”
Shiru bata amsa shi ba, lan’kwasa murya ya sake yace “Kinji?”
“Naji, zanyi tunani akai”
Wani murmushin jin dad’i ya sake sannan yace “Yauwa ko ke fah, so yakike?”
“Lafiya lau, ya weekend d’in?”
“Alhamdulillah, ban ma samu enough bacci ba wallahi”
Cikin tausayawa tace “Ayyah, kaje kayi breakfast sai ka kwanta kawai, zaka ji normal”
“Thank you my dear, will do just that, take care”
“Alright, bye”
Kusan lokaci d’aya suka katse call d’in kowannensu da tunani a ranshi. Kaman yanda tace haka yayi, cikin gida yashiga, a parlourn Ummi ya tarar da Ilham tana kallon wani movie, gaishe dashi tayi ya amsa mata cikin sakin fuska sannan ta kawo mishi abin karyawa, yana ci suna hira har ya gama ya sallameta akan bari yaje ya d’an kwanta.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Bayan kwana tara
Ayau Daddy zai dawo gida, tun asubah y’anmatan da Momy suka fara shirya abinci kala-kala don tarbanshi, Leena tanada lectures amma haka tayi cancelling don tanason taga daddy’nta, tana mai addu’a Allah yasa ya damu dasu kaman yanda kowanne uba yake damuwa da lamuran ‘ya’yanshi.
Misalin ‘karfe sha d’aya suka tarkata sai airport, ba tare da wani ‘bata lokaci ba aka gama mishi komai da komai dayake business class yashiga, inda ya hango suke tsaye ya nufa janye da wani d’an madaidaicin trolley ba’ki mai kyau, duk sunaso suje su rungumeshi kaman yanda sukaga sauran ‘yanmatan wajen ke yi ma iyayensu awajen amma shakka, tsoro da kuma rashin sabo dashi yasa suka daskare ba tare da motsi ba har ya iso wajensu.
Momy ne tayi saurin ‘karasawa murmushi shimfid’e a fuskarta ta rungumeshi tana mishi barka da dawowa, mai da dubanshi wajen yaran nashi yayi bayan Momy ta kar’bi trolley’n shi. Jiki na ‘bari, murya na rawa suka had’a baki suka d’an sunkuyar da kai sukace “Daddy sannu da dawowa”
Karo na farko da yaji rashin sakewarsu dashi ya ‘bata mishi rai, tun daman haka kullum suke tarbanshi, a d’ari-d’ari kaman sunga wani stranger, ranshi ya sosu sosai yanda ya lura duk ‘yanmatan wajen suna rungume iyayensu da suka dawo, murmushin dole ya ‘kir’kiro sannan ya isa gabansu, bud’e hannunshi yayi alamun suzo ya rungumesu. Kallon-kallo suka fara tsakanin su ukun, wani murmushi mai ciwo yayi sannan ya janyo su jikinshi ya d’an bubbuga bayansu yana cewa “Na sameku lafiya?”
Sun kasa yarda wai yau daddy ne harda rungumesu, bazasu iya tuna when last yamusu haka ba. “Lafiya lau” suka amsa mishi uncomfortably
“Alhamdulillah” yace sannan ya kalli Momy yace “Muje ko?, nagaji sosai wallahi”
Motar suka shiga, Momy ke driving daddy kuma a passenger seat, su uku kuma a baya. Zaman kurame sukayi har suka isa gida.
*REAL MHS*
Munay, Hanee and Stylish
[11/12, 9:07 PM] +234 812 202 4749: *ABUN SIRRI NE*
Na 'yan uku
*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*
*NWA*
*81-85*
Haneefahusman.wordpress.com
Stylishbch.wordpress.com
Munayshat.mywapblog.com
Masoya littafin nan bamusan da wani baki zamu baku ha'kuri bisa jinkirin typing da aka samu ba, please bear with us. Allah ya bar 'kauna, lots of love♡♡
☆☆☆☆☆☆☆☆
Daga Suhal har Ilham mi'kewa tsaye sukayi cikeda fargaba da kuma tsantsan mamakin jin wannan magana da suka fito daga bakin Ummi. Ilham ta taka dagudu ta isa wajen da Ummi take ta fad'a jikinta tana jijjigata tana girgiza kai tafara cewa "Noo Ummi, ya zakice aure ya haramta a tsakaninmu?, don meh kukeson haramta abinda Allah ya halarta?, saboda meh bakuson Ya Suhal ya aureni bayan duk munsan aure bai haramta a tsakaninmu ba tunda dai shi ba muharramina bane, why Ummi?, mesa kuka za'bi ku fad'a fushin ubangiji?"
Duk maganar da Ilham ke yi Ummi batace komai ba, parlourn yayi shiru sai sheshshekar kukan Umma, Ummi da Ilham ke tashi, mazan kuma duk idanunsu yayi jawur mai nuni da tsantsan tashin hankalin da suke ciki.
Bayan kaman minti biyar Baba yayi gyaran murya ya dubi Ilham sannan ya kira sunanta yace "Ilham" sannan ya kalli Suhal yace "Suhal"
A raunane ta d'ago tana kallonshi sannan ta amsa "Na'am"
Suhal samun kujera yayi ya zauna da 'kyar, yanaji kaman 'kafafun shi bazasu iya d'aukar shi ba, ahankali shima yace "Na'am"
"Inaso ku saurari abinda zan gayamuku ayau wanda duk duniyar nan ba wanda yasan da hakan sai mu hud'u(Abba, Umma, Ummi da shi Baba), tun da mukayi maganar kuwa muka binneta acikin zu'katanmu, muka bar ABUN SIRRI a cikin zu'katanmu, ko da wasa bamu ta'ba tunanin tonashi ba, ba don komai ba sai don ni halak malak na badake ma bappanki" ya fad'a yana nuni da Ilham sannan ya cigaba "Tun daga lokacin da aka haifi yayyunki Allah bai sake sa sunyi ciki ba har suka d'an yi wayo don time d'in Suhal yanada shekaru tara, Fu'ad kuma yanada bakwai, Allah cikin ikonsa ya sa suka d'auki ciki kusan lokaci d'aya, munyi farinciki sosai ganin zamu samu 'karuwar haihuwa acikin familynmu. Daf da zasu haihu sai Suhal da Fu'ad suka matsa mana akan zasuje gidan 'yan uwa achan bichi, mun so mu hanaso don bamuso iyayenku su haihu basanan amma da suka ishemu da rikici sai kawai mukasa aka kaisu chan don suyi kwana biyu akan kashedin ko washegari ne d'ayan su ta haihu toh za aje a d'aukosu.
Maimuna(Umma) ita tafara haihuwa amma sai 'yar batazo da rai ba, tayi kuka na fitan hankali don ta sa ranta sosai akan babyn, har wani zazza'bi tayi wanda hakan yasa bamu gayama kowa ga abinda ke faruwa ba har washegari inda Hasiya ta haife ki, wani abun mamaki kuwa tun da aka haifeki kina kama da Maimuna sosai. Maimuna tana d'ora idonta akanki sai ta tuno da nata babyn da batazo da rai ba, ta 'kara shiga 'kunci, ganin haka yasa Hasiya ta kirani tace min in zan yadda tanaso mu bada ke ma Murtala da Maimuna, halak malak, na yaba mata da wannan kaifin tunani nata don ko ni dafarko nayi tunanin hakan amma bansan ta yaya zan fara tunkararta da shi ba sabida tsawon shekarun da ta d'auka bata haihu ba.
Samun Murtala da Maimuna mukayi muka sanar dasu hukuncin da muka yanke, kukan farinciki Maimuna tayi sosai ta dinga mana godiya da sa albarka, ba mu bar asibitin ba sai da muka bari a tsakaninmu cewa ko dangi kar mu sanar musu cewa 'yar Maimuna ce ta rasu ma'ana mu ce musu 'yar Hasiya ce ta rasu sannan ko ku bazamu gayamuku ba sai dai in fad'an yazama dole. Da muka koma gida dangi suka fara zuwa barka har aka d'auko Fu'ad da Suhal da kullum suna cikin d'akin maijego suna jin dad'i sun samu 'kanwa, Hasiya kuwa sai dai azo ayimata jaje da ta'aziyar Allah yasa babyn mai ceto ne" Baba ya 'karasa maganar yana jin wani abu a zuciyarshi, kaman alokacin abun yafaru.
Tashi tsaye Ilham tayi tana share hawayenta tace "Ya za ayi ace muna uwa d'aya uba d'aya da Ya Suhal?, wallahi 'karya ne"
Suhal da tunda aka soma maganar yayi shiru sai lokacin ya d'ago jajayen idanunshi ya kalli Ilham sannan yace "Ilham wani irin maganar banza kikeyi haka?, abinda muka yi abaya cikin rashin sani mukayi, bai kamata muyi kunnen uwar shegu akan gaskiyar magana ba Ilham, gaskiya d'ayace"
Kan kujeran da yake zaune ta isa tazauna gamida dafa shi, kaman zautacciya tace "Ya Suhal do you believe them?, akan meh zaka yarda da maganar da ko a tatsuniya da 'kyar ake samun irinshi?, wannan 'kir'kirarren labari ne don kawai anaso a hanamu aure ya Suhal, don Allah kace musu baka yarda ba, su barmu muyi aure please...."
Wani irin tausayinta yaji ganin yanda ta fita hayyacinta, rungumeta da yayi ne ya bata damar yin kukan da ya ma'kale mata, bai hanata yi ba har ta gaji ita da kanta sannan ta rage sautin kukan. Wani irin kallo tayima Baba sannan tace "Aure dai sai munyi aure da ya Suhal, saidai in kasheni zakuyi" tashi yayi dasauri ya nufeta cikin 'bacin rai da niyyan dukanta, har rige-rige Abba da Ummi da Umma sukeyi wajen tareshi, masifa yashiga yi akan su bar shi ya koya mata hankali, batada hankali ne da zatace zata auri yayanta wanda suke uwa d'aya?. Umma da Ummi suka kamata suka shige da ita d'aki don lallashinta.
A parlour kuwa saida Baba ya gama bambamin bala'in shi sannan Suhal yace "Wallahi Baba an cucemu da ba a gayamana hakan tun farko ba sai yanzu da muka girma har nayima Ilham al'kawarin aurenta, soyayya fah mukayi da ita, soyayya ba tare da mun san ciki d'aya muke ba...."
Baba zaiyi magana amma Abba ya girgiza mishi kai don shi yafi Baba sanyin hali, Baba yanada zafi sosai don abu kad'an ke 'bata mishi rai. Tausasa murya Abba yayi yace "Mun san mun muku laifi Suhal, aganinmu hakan da zamuyi shi zai 'kara dauwamar mana son junanmu, munyi ba dai-dai ba da muka 'boye muku gaskiyar lamarin, sam bamuyi tunanin zaku fara soyayya bane da tun farko munyi ma tufkar hanci, duk wannan abun da ya faru sam bamuga laifinku ba sai ma mu da mukayi sanadi har kuka aikata haram(Suna soyayya bayan ciki d'aya suka fito)"
Idanun Suhal jawur yake kallon Abba, girgiza kai kawai yayi batare da ya 'kara cewa komai ba ya bar sashen, kanshi kaman zai rabe gida biyu tsaba yanda yake tunani da kuma tafarfasa.
Yana shiga d'aki ya jawo wayarshi ya danna kiran Fu'ad don shi kad'ai zai iya tayashi jimamin wannan batu, ringing na farko Fu'ad ya d'aga yana cewa "Bro yau antuna dani kenan"
Zama akan kujera Suhal yayi ya lumshe idanunshi gamida dafe kanshi, alokaci guda kuma ya furzar da wani iska mai zafi. Jin haka yasa Fu'ad yagane ba lafiya ba, daidaita nutsuwarshi yayi ya 'kara cewa "Meh ya sameka ne haka?, wani abu yafaru ne?, ko gida ne ba lafiya?"
Sai sannan ya bud'e idanunshi da suka 'kara rinewa sannan yace "Fu'ad, yau nan ba 'karamin tashin hankali nake ciki ba wallahi, can you imagine wai......" muryarshi ne ya sar'ke ya kasa 'karasa maganar don yanda maganar yake mishi d'aci.
Hankalin Fu'ad ya 'kara tashi, cikin in-ina yace "Meh....ya...fa...ru?"
Hawaye ne suka zubo daga idanun Suhal, bai damu da ya sharesu ba yace "Uwa d'aya uba d'aya nake da Ilham"
Fu'ad da ke kwance akan kujera bai san lokacin da ya mi'ke tsaye ba har yana neman fad'uwa tsaba yanda yaji maganar kaman saukar aradu a kunnenshi. "What are you trying to say Suhal?, lafiyanka 'kalau kuwa?, tukunna ma, waya gayama wannan maganar?"
Murmushin ya'ke yayi yace "Wallahi Im serious Fu'ad, yanzu su Abba suka fad'a mana a parlour"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Fu'ad ya shiga nanatawa yana ta zagaye tsakanin bedroom da parlour. Sai da ya d'an had'iye maganar sannan yace "No, it cant be, ya za ace Ilham Ummi ce ta haifeta bayan da girmanmu aka haifeta, karka manta fah ana haifanta mukaje asibitin, ya akayi hakan ya faru?"
"I still cant believe it Fu'ad, I just cant, bansan ya zanyi ba, ni kad'ai nasan how I'm feeling right now...."
"Calm down kamin explaining yanda abubuwa suka faru"
Shiru yayi na seconds sannan ya kwashe duk yanda sukayi a parlour ya gayama Fu'ad. Tashin hankali sosai Fu'ad ma yashiga har yanajin wani bell yana bugawa a 'kwa'kwalwarshi, buga kan yayi da tafin hannunshi sannan yace "You mean all this while 'boye mana sukayi?, mesa sukayi haka?, akan dalilinsu na banza har kuna soyayya ba tare da kunsan uwa d'aya kuke ba"
"Soyayya da 'kanwata uwa d'aya uba d'aya" shine sentence da ke ta yawo akan Suhal. "Abunda yafaru ya riga yafaru, we can't change that"
Cikin d'aga murya Fu'ad yace "Ilham!!, Ilham ne damuwa na Suhal, nasan wallahi maganar nan sai ya nemi tarwatsa mata rayuwa, irin son da take maka is extra-ordinary, ga....."
Katse shi Suhal yayi ta hanyar cewa "Look Fu'ad, Ilham will get over it eventually"
"Yaushe kayi developing wannan banzan I dont care attitude d'innan ne?, Ilham is our only sister, ONLY SISTER, in kai baka damu da ita ba ni ina jin ta har cikin raina as my baby sis...."
"I care about her Fu'ad, I really do saidai yanzu da abubuwa suka kwa'be dole naja jiki da ita for our sakes, both of us, in ina 'kara kulata baza ta iya yakice ni daga zuciyarta ba"
"Hmmm" Fu'ad yace sannan ya 'kara da "Suhal kenan, I know baka ta'ba sonta ba, baka ta'ba damuwa da ita ba so mu manta da maganar kawai"
Ajiyar zuciya Suhal ya sauke sannan yace "Ba zaka gane yanda nakeji bane, had it been yanzu hakan nan da kai yafaru wallahi im 100% sure reaction naka will be worse"
Guntun tsaki Fu'ad yaja yace "Kai dai share kawai, yanzu ya ake ciki?, how's she?"
"She will be okay, ta dai tafi tanata kuka wai ita bata yarda uwa d'aya muke ba, gani takeyi kaman su Abba sunason hanamu aure shine suka 'bullo tahaka"
"Zan kirata, will try to make her understand, ta cire sonka daga ranta don ba aure tsakaninku, kar ta kwasan ma kanta zunubi abanza"
Haka dai suka dad'e suna tattauna abinda iyayen suka bayyana musu ayau.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Few days later
"Rafee!, Rafee!!" Momy ce ke ta 'kwala ma Rafee kira, sai da ta kirata ya kusa baki hud'u sannan ta tsinkayo muryarta tana amsawa "Na'am"
"Zo mana, tun d'azun kinaji inata kiranki kinyi shiru"
"Ganinan zuwa" Rafee tace da ita sannan ta fito hannunta ri'ke da wayarta da gani chatting takeyi.
Zama tayi akusa da Momy tace "Momy akwai abinda zan miki ne?"
"Eh, je ki wajen Tijjani maigadi ki tambaya min shi ko an kawo min wani sa'ko"
Mi'kewa tayi tana cigaba da danne-dannenta har saura kad'an ta taka 'kafar Momy batare da ta sani ba.
Tsawa Momy ta daka mata "Lafiyanki Rafee?, meh kikeyi a wayar da ya d'auke miki hankali haka har kina nema ki karya min 'kafa?"
A rikice Rafee ta kawar da wayarta gefe tace "Im sorry Momy, bazan sake ba"
Harara Momy tamata sannan tace "Bani wayar"
"Momy?, ai nace bazan sake ba fah, kiyi ha'kuri" Rafee ta fad'a tana 'boye wayar a bayanta tana kuma ro'kon Allah ya rufa mata asiri don in Momy ta kar'bi wayar nan yanzu, kashinta ya bushe.
"Bani nace!!, in kin dawo kya kar'ba" Momy ta fad'a in a serious tone
Ba shiri Rafee ta mi'ka mata wayar ganin yanda Momy ta had'a rai. Juyawa Rafee tayi tafara tafiya amma tana waigowa tana duban Momy, itako ba abinda tamata sai hararar da ta galla mata a 'karshe, daga nan bata sake juyowa ba har ta fita daga parloun zuciyarta yana bugun goma-goma.
Seconds kad'an da barin Rafee cikin parlourn wayar yayi beeping sau biyar alokaci d'aya, bin wayar Momy tayi da kallo sai ta sharé, wasu messages d'in ne suka kuma shigowa kusan lokaci d'aya, tsaki Momy taja tace afili "Sai uban chatting kaman wacce tasamu aikin lada, ko wasu asararrun ne suketa mata messages haka oho?"
Cigaba da duba magazine da ke hannunta tayi amma duk 'karar da wayar yayi sai ta waiga ta dubeshi. Ana cikin haka ne wayar ya d'auki ruri, d'auka Momy tayi tana duba sunan, 'baro 'baro idanunta sukaci karo da "H babe", tunani tafara yi, itadai tasan Rafee ba kula samari takeyi ba, toh wayene wannan H babe d'in?, taso ta share don respecting privacy na Rafee amma part of her got curious, tanaso tasan wayene.
Wayar yana gama ringing ta shiga gallery, yana rufe da lock hakan yasa ta gwada typing "hbabe", cikin sa'a kuwa ya bud'u. Camera pictures da yake shi ke sama so shi tafara bud'ewa, hotunan Rafee ne dai gasunan birjik, wasu daga ita sai bra, wasu kuma ta d'aura towel soko-soko, wasu kuma ba kaya ma...ta dai kare 'kirjinta da tafin hannunta, hotunan dai gasunan dewa ba kyan gani.
A firgice Momy ta mi'ke sabida abinda ta gani mai matu'kar rikitarwa, wanda yayi mugun razana da firgitata, wanda yayi sanadin d'aukewar numfashinta na kusan da'ki'kai biyar, wani irin tashin hankali tashiga wanda bata ta'ba shiga irinshi ba tunda tazo duniya, ko amafarki bata ta'ba tsammanin zataga abu