Showing 36001 words to 37595 words out of 37595 words
mai muni makamancin haka ba. Hawaye ne ya fara ambaliya daga idanunta kaman an bud'e famfo, jikinta har 'kyarma yakeyi tsaba tashin hankali, wani irin kuka ne ya ku'buce mata mai cikeda 'bacin rai da takaici, kuka mai d'auke da ma'ana daban-daban.
Rafee daskarewa tayi a 'kofar falon don daman isowarta kenan taga Momy tashiga wannan halin, jikinta ya mugun yin sanyi don ta gama sada'karwa Momy taga abinda take 'boyemata tun watanni dewa abaya. Kaman ba jini a jikinta tafara 'karasowa cikin parlourn, kanta a sunkuye jiki yana rawa ta ajiye ma Momy leather bag da ta kar'bo mata daga wajen maigadi, murya yana rawa cikin rashin gaskiya tace "Mo...my...gashinan"
Ko kallon Rafee Momy ta kasa yi har tazo ta ra'be ta gefenta zata wuce, tsaida ita Momy tayi ta hanyar cewa "Ban gama dake ba, zo ki zauna!!"
Firgita sosai Rafee tayi, tunani kaloli kaloli sai zuwa mata 'kwanya sukeyi, ta kasa d'aga 'kafarta balle ma tajuyo ta kalli momy har saida Momy ta 'kara maganar cikin d'aga murya.
Tsugunnawa a 'kasa Rafee tayi don yau tasan nata ya 'kare, Momy ta rungumi hannayenta a 'kirjinta tanata safah da marwa a tsakiyar parlourn.
Cikin kakkausar murya Momy tafara magana "Rafee, meye gaminki da Hajiya Hafsat?"
B'ari jikinta yafara tana zuzzura idanu kaman 'barauniya, in-ina tafara "Umm...um...ba...."
"Dont you dare!!!, karki kuskura kimin 'karya, wallahi tallahi in kikayi 'karya sai na karyaki a gidannan!!"
"Kallon Momy tayi sannan ta sunkuyar da kanta dasauri, zufa tafara sharewa tace "Da...gas...k...."
Wani wawan mari da Momy ta kwasheta dashi ne yasa ta kasa 'karasar da maganar da ta fara, tuni bakin ya fashe yafara zubda jini, hawaye Rafee tafara tana yarfe hannu ta kasa 'kara magana.
Jefa mata wayar kan cinyarta Momy tayi tana cewa "Still kinaso kiyi denying ko yaya?!!!, zakice min baki san dasu bane ko sharri aka miki bayan acikin wayanki suke?"
Ko d'aga wayar Rafee bata iya yi ba, hawaye ne kawai take zubarwa akan carpet da ke shimfid'e a tsakiyar parlourn. Wani tsawa Momy ta kuma dakawa har saida duk gidan ya amsa wanda hakan yayi sanadiyyar fitowar Sofy, Leena da Daddy daga cikin d'akunansu.
Yanayin da suka riskesu aciki duk ya razana su, cikin sauri Daddy ya isa wajen Momy ya kama hannunta yana cewa "Rahma!!, lafiyarki?, meke faruwa haka?, meh ta miki?"
'Ko'karin fizge jikinta daga ri'kon da yamata tafara amma takasa, hakan yasa ta kuma fashewa da wani sabon kuka tana bugun 'kirjinshi tana nuna Rafee had'e da cewa "Ka tambayeta, ka tambayeta menene acikin wayarta?, ka tambayeta meke tsakaninta da Haj Hafsat"
*REAL MHS*
Munay, Hanee and Stylish
[11/12, 9:09 PM] +234 812 202 4749: *ABUN SIRRI NE*
Na 'yan uku
*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*
*NWA*
*86-90*
Haneefahusman.wordpress.com
☆☆☆☆☆☆☆☆
"Hajiya Hafsat?, wacece hajiya Hafsat kuma?" Daddy ya tambayi Momy cikeda son jin 'karin bayani don dai sun sa shi a duhu
"Wata k'awata ce" Momy ta fad'a still bata dawo hayyacinta gaba d'aya ba
"K'awarki?, meh kika gani da yasa kike tuhumar Rafee akanta?"
Sai sannan Momy ta fara dawowa taitayinta, kwapsawa tasan ta kwapsa don sam Daddy bai ma san da wata Hafsat ba. "Ba wai 'kawata har chan-chan bane sannan ni ban gama yarda da ita ba"
Jinjina kai daddy yayi yace "Bakisan halinta ba daman kuke 'kawance?, a ina ma kika santa in the first place?"
"A mall muka had'u har tace tana sona da 'kawance" Momy ta fad'a ba da son ranta ba
"Tanada wani halin Allah wadai ne?, and menene kika sani akanta?"
Runtse idanu Momy tayi tana kukan zuci, ita kad'ai tasan yanda takeji a zuciyarta; fargaban irin hukuncin da Daddy zai yanke mata in ta gayamishi asalin labarin 'kawancenta da Haj Hafsat da kuma tsoron Allaah da irin azaban da ya tanadar ma masu irin halin da ta tsinci kanta aciki, sanadiyyar haka kuwa gashi 'yarta ma ta lalace...a dalilinta. Wani irin haushin kanta tashiga ji sosai, da kaman zata kare kanta ta'ki gayamishi ala'karta da Hafsat saidai kuma taji gwanda kawai ayita ta 'kare, she can't live a lie anymore.
"Ya kikayi shiru?, ina jinki" maganar daddy ne ya katse mata tunaninta
Bud'e idanunta tayi hawaye suna 'kara zubowa tace "Tana harka da manyan mutane sannan tana lesbianism"
Salati ne yafara tashi a parlourn daga bakin Daddy, Sofy da kuma Leena da yake sunji abun wani bambara'kwai. Rafee kuwa kuka ta fashe dashi tayi rarrafe ta kama 'kafar Momy tace "Momy don girman Allah ki yafemin, bazan sake ba nayi al'kawari"
A razane duk suke kallon Rafee harda Momy, d'agota Momy tayi tana girgiza kai tace "Whattt???!!, na yafemiki Rafee?, meh hakan ke nufi?, kina harka da Haj Hafsat?, yaushe kika fad'a harkar nan Rafee?"
Jinjina kai Rafee tashiga yi tana cewa "I'm sorry Momy, wallahi itace ta jani, wallahi bani naje wajenta ba....."
Kuka sosai Leena ke yi, ta ma kasa yarda da abinda kunnuwanta suka jiyo mata "Lesbianism".
Jijjigata Momy tafara tana magana "Why Rafee?, meh kika rasa?, tun yaushe kika fara harka da ita?, me.....". Momy bata samu damar 'karasa maganarta ba Rafee ta fasa ihu sakamakon sau'kar wire a jikinta, Daddy ne ya ciro extension wire yana huci yana dukanta, kana ganin yanayinshi kasan zuciyarshi a cunkushe yake.
Ihu Rafee takeyi tsakaninta da Allah amma daddy sai cigaba da dukanta yakeyi kaman an aikoshi, gashi duk sun kasa kar'bota, ko tunkararshi ma sun kasa don tabbas duk wacce ta nufi wajen itama bulalar sai ya shafeta. Momy ba irin kuka da ro'kon da bata mishi ba amma bawan Allahn nan bai ma san tanayi ba, lura da tayi in fah bata dakatar dashi daga dukan da yakeyin nan ba tsaf Rafee zata iya mutuwa don har jini ya 'bata mata jiki sakamakon faffasa mata jiki da extension wire d'in yayi.
Shahada Momy tayi ta isa inda Rafee take ta 'kan'kameta suna kuka dukkansu biyu. Cikin masifa daddy yace "Rahma!!, ki sake yarinyar nan ki 'bacemin daga nan, ni zata zubarwa mutunci agari?, ni takeso a dinga yima kallon banza ace 'yata tana mad'igo?, ni takeson ta tozarta?, so take ace ban bata tarbiyyar da ya dace bane ko yaya?, ki saketa nace!, yau sai tayi nadamar shiga lesbianism"
Momy cikin 'karfin hali da tsananin 'bacin rai tace "Sai dai ka had'amu ka kashe don wallahi bazan bari ka kashemin 'yata ba, 'yar da kake i'kirarin ka bata tarbiyya mai kyau yaushe ma kakeda lokacinta?, yaushe ka zauna da ita for a month?, yaushe ka saba da ita har ka iya kwa'barta?, kama san WACECE ITA(book by Jaboncy) kuwa?, yarinyar nan laifin ta kaso arba'in take dashi kaikuma kaso sittin don kai ka nuna halin ko in kula akan abinda take ciki tun tasowarta, ba ma ita kad'ai ba, dukkansu uku baka damu dasu ba, Mustafa ayau zan gayamaka ka riga ka lalata familyn nan, ka ruguza shi, ka sa mun fad'a cikin wasu halaye wanda da ace kana tare damu hakan bazai faru ba. Ka had'a da ni ka duka don a sanadiyyar rashin kulawarka gareni nima na fara lesbianism...."
Tsananin firgita Daddy yayi har extension wire d'in ya su'buce daga hannunshi ya fad'i a 'kasa. Leena sulalewa 'kasa tayi ta dur'kusa a kan guiwowinta tana cewa "No momy, mesa zaki ma kanki sharrin nan sabida ki kare Rafee?, haba momy, in zaki kareta bai kamata ke ma ki d'aura ka kanki laifin da baki aikata ba"
Kallon Leena Momy tayi cikeda so da kuma tausayawa, hawayenta ta d'an share sannan tace "Ba sharri nayima kaina ba Leena, gaskiyar maganar kenan, nashiga lesbianism a dalilin babanku, nasan ni mai laifi ce ako ina amma shima yanada nashi kason don....."
Daddy da tunda Momy ta fara magana ya nemi kujera ya zauna don yanajin kanshi yana juyawa yayi saurin katseta cikin tsawa "Menene bana muku?, akwai abinda kuke bu'kata da ban baku ba?, meh kuka rasa a duniyar nan da sai lesbianism ne zai iya baku?, anya kuna tsoron Allah kuwa?, kuna tsoron had'uwa dashi da irin zunubin ku?"
Girgiza kai Momy tayi cikin takaici sannan tace "Maganar kenan kullum, kud'i...kud'i, kai a tunaninka kud'i ne komai?, ka fifita aikinka akan mu, familynka ne mu amma bakada lokacin mu"
D'aga mata hannu yayi yace cikin d'aga murya "Karki gayamin maganar banza!, don waye nake neman kud'in?!!, ba don ku bane?!!, duk abinda nake nema is for you"
Cikin d'aga murya Momy ma tace "Zan gayamaka Mustafa!, daman ance the truth is always bitter, your money is not enough!, kud'in banza kud'in wofi, ni banga amfanin kud'in ba wallahi sai ma takaici da 'kuncin da yasa kullum nake ciki, ba wai ina cewa na raina efforts naka na bamu a comfortable life bane...no, inaso na gayama ne kud'in bai da amfani tunda yayi mana katanga da kai, yayi mana katanga da farin cikinmu, in dai ni yanzu zan bama mace shawara akan za'ban mijin aure wallahi tallahi zance akam ta za'bi mai kud'i wanda baida lokacinta gwanda ta za'bi mai daidai rufin asiri don zai tarairayeta ya riritata, mai rufin asirin kullum zai dinga bata kulawa, zai san meh take ciki akowani rana, zai san meh take bu'kata, bazai ta'ba bari tashiga yanayin kad'aici ba sannan zaiyi iya bakin 'ko'karinshi ganin ya sauke duk ha'k'kokinta dake kanshi, masu kud'i kuwa akasarin su basuda lokacin familynsu, you dont have our time, you dont value us, sai ka share watanni baka waiwayemu ba, ina matarka amma sai muyi wata shida-bakwai bamu ga juna ba saidai muyi magana a waya, bazaka zo ba sai in kai da kanka kaji kana bu'katar zuwa, ka manta da ha'k'kina da yake kanka, nima fah inada bu'kata tunda dai ni ba dutse bace amma haka zaka manta ka ajiyeni agida kai kana chan uwa duniya. A dalilin rashinka kusa dani shaid'an da son zuciya suka rinjaye ni na fara rage ma kaina bu'katarka ta hanyar mad'igo "
*REAL MHS*
Munay, Hanee and Stylish