Showing 1 words to 3000 words out of 37595 words

Chapter 1 - ABUN SIRRI NE Sirrin Rayuwa By MUNAYSHAT

11 Sep 2026

139


ABUN SIRRI NE
*ABUN SIRRI NE*

COMING SOON!!!!!

Na ‘yan uku

MUNAYSHAT
HANEEFAH USMAN
STYLISH BCH

*MHS*

®NWA

☆☆☆☆☆☆☆☆
Parking tayi adaidai lokacin da wata motar ta paka a kusa da ita acikin farfajiyar wani matsakaicin gida mai kama da guest house, kusan atare suka fito daga motarsu. Kallo d’aya zaka musu ka gano irin manyan mata ‘yan bokon nan ne, murmushi suka sakar ma juna sannan suka nufi ‘kofar da zai sada su da asalin cikin gidan.

Ajiye handbags nasu sukayi gami da zama a kujera na zaman mutum biyu. Farar ce ta fara magana “Hajiya Rahma, yau dai nasha mamaki”

Haj. Rahma tace “Me ya baki mamaki har haka Haj. Hafsat?”

“Ya akayi yau muka iso lokaci daya bayan kusan kullum sai na jiraki kusan minti talatin kafin kizo?, ko yaran basunan ne?”, cewar Hajiya Hafsat

Dariya Haj. Rahma tayi sai tace “Wallahi yau wani dabara na tsiro, inaga kuma da hakan zan dinga fakewa daga yau tunda y’ay’an nawa basu ta’ba barina nasha iska”

Gyara zama Haj. Hafsat tayi tace “Haba tawan?, gayamin ya kikayi?”

“In gayamiki, ina gama shiri nah nafito parlour sai tambaya na sukayi wai ina zanje?, zama nayi akan kujera nace akwai wani organization da muke so mu fara ne don taimakawa marayu da marasa ‘karfi, duk suka jinjina kai cike da gamsuwa da kuma tausayawa sai Rafee tace “Allah sarki, in kun fara nima zan bada tawa gudunmawar, marayu abun a tausaya ma ne”. Nan fah Leena da ta fisu ustazanci ta dinga zuba maganganu irin dai na masu tsoron Allah, ni dai jinjina kai na dinga yi don ban so ta d’au lokaci tana jawo min ayoyi, daga ‘karshe ma sai cewa tayi zata bini, bakiga yanda na rikice ba amma cikin ikon Allah sai naci sa’a dabara ta fad’omin nace “Nan da wata biyu dai maybe mun gama komai, ki bari sai lokacin duk zamu dinga zuwa”

Haj. Hafsat tace “Wata sabuwa inji d’an chacha, toh yanzu ke in wata biyun sun cika ya zakiyi da ita in tace zata biki?”

Haj. Rahma tayi murmushi tace “Na samu abun fakewa in zamu had’u muyi soyayyar mu, kinga yanzu zasu bar damuna akan ina zanje don zasuyi tsammanin abubuwan bud’e ‘kungiyar ne yake sani rashin zama sosai ba wai yawo nah nake tafiya ba, in watannin da na gaya musu ya cika kuma abu mai sau’ki ne, zan dinga ce musu abubuwan ne sun kasa had’uwa, kinsan dai zasu yarda tunda 9ja muke inda abubuwa suke zama long procedures”

Dariya Haj. Hafsat tayi tace “K’awata kanki yana chaji, zamu sake kamin su gano ‘karya kika musu”

“Kamin su gano zamu ‘kir’kiro sabon plan, bazan ta’ba yarda su sa katanga tsakanin mu ba” inji Haj. Rahma

Kashe ido d’aya Haj. Hafsat tayi tana murmushi ta nufi wani d’an ‘kofa sai wani rangwad’a takeyi, mi’kewa Haj. Rahma tayi itama tabi bayanta suka kule a d’aki.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Haj. Rahma tana barin harabar gidanta Rafee da Sofy suka tafa sannan suka kwashe da dariya. Rafee tace “Sister mun iya saka matar nan acikin duhu fah wlh”

Sofy tace “K’warai kuwa, ita a tunaninta agida fah muke yini, batasan….”

“Tana sa ‘kafa ta fita mu ma muke tamu hanyar ba” Rafee ta ‘karasar

Wani dariya suka sake sawa sannan Sofy ta mi’ke tace “Barin tashi na shirya don Bash ya kusa isowa, har na ‘kosa na ganmu a wajen partyn”

Rafee ta d’auki wayarta tana dannawa tace “Nima yanzu zan mi’ke na shirya don Nazee zatazo ta d’auke ni muje wani waje”

Bayan dukkansu sun fita kaman ba musulmai ba cikin tsinannun kayaki ba ko d’ankwali balle gyale ne Leena ta zabga uban tagumi tana mai tausaya ma rayuwar yayyunta guda biyu, ita dai tafi ganin laifin Momy wato Haj. Rahma don a tunanin Leena da ace momy tana zama agida dasu, da Rafee da Sofy basu ‘bata tarbiyar su ba, amma ina!!, momy ba abinda tasa agaba sai yawo, bata ta’ba yini agida, yau tana meeting anan gobe ta tafi wani biki ko suna, haka dai rayuwar yake tafiya. Wani lokacin kuma Leena tafi ganin laifin mahaifinsu don da ace ya damu dasu da bazai ta’ba nisa dasu har tsawon watanni ba, daddy ba abinda ke gabanshi irin harkokin business nashi wanda ya fifita akan matarshi da ‘ya’yanshi yanmata guda uku, sam bai damu da sanin halin da suke ciki ba, momy haka zata wuni yawo shiko ko a jikinshi, in mutane sun mishi magana sai yace shi bai son takura ma familyn shi, hawaye ne ya sulalo daga idanunta, a fili tace “Ya Allah ka shiryar da yayyu na ka kuma karkato da hankalin daddy zuwa garemu, ya Allah ka nitsar da momy ta bar yawo ta dinga zama damu agida”.

☆☆☆☆☆☆☆☆

“Haba Fu’ad, abinda kakeyin nan aganinka ya kamata?, mesa abubuwan da bakayi a 9ja in mun zo nan kakeyi?, kana ganin don iyayenmu basu nan sabida haka basu san me kakeyi ba sai kayi abinda kaga dama?, wato kana tsoron yi agida Nigeria don bakason iyayenmu su sani amma baka tsoron azaban Allah?, kana tsammanin baya ganinka ne?, haba Fu’ad, kullum abu d’aya?, don Allah ka chanja hali ko kuma na kira gida na gaya musu”

Fu’ad ya kama ‘kafafun Suhal yace “Im sorry bro, bazan sake ba, na tuba, kar ka gayama Abba, kasan halinshi, zai iya hanani cigaba da karatuna, Ammi kuma kasan tanada ciwon zuciya, ka rufamin asiri, daga yau bazan sake ba”

Suhal ya girgiza kai yace “Allah yasa, kullum kana cewa zaka daina amma sai abinda yake ‘karuwa”.

Tohh fah jama’a, ku biyomu ‘yan uku MHS kuji yanda wannan labarin yake, muna fatan za ayi amfani da abinda zai koyar. Sai kun jimu ba da dad’ewa ba.

*MHS*






ABUN SIRRI NE 5-10
*ABUN SIRRI NE*

Na ‘yan uku

*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*

*(MHS)*

®NWA

*5-10*

☆☆☆☆☆☆☆☆
Leena ce cikin motar ta blue mai suna matrix, cikin natsuwa take tu’kin, gate d’in makarantar su (Northwest University, Kano) tadanna kan motar, kowa yaga tu’kin da takeyi sai ta burge shi, gaban department dinsu ta tsaya, jakarta tabud’e taciro ni’kaf d’inta ta d’aura a saman hijab d’inta sannan ta fito ta kulle motar.

Lecture room ta nufa cikin tafiyarta mai cike da nutsuwa, gab shigarta lecture room d’in wayarta tad’au ruri “Sis Rafee” tagani jikin screen d’in wayar, murmushi ne yasauka saman fuskarta, a fili tace “Oh my swt sis, me kuma yafaru?”, sannan tayi picking ta kai wayar kunnenta.

Daga d’ayan ‘bangaren ba ko sallama Rafee tace “Leena, mum tadawo ne?”

Leena cikin kulawa tace “Sister, wai tun jiya ina kika shiga ne?, lafiya ‘kalau kam ko?”

Tsaki Rafee taja, cikin masifa tace “Amsa zaki bani ko tambayata zaki tsaya yi?”

“Sorry sis, har na bar gida d’azun nan nazo school bata dawo ba, ban sani ba dai ko bayan fitana ta dawo”, ta ‘kara da cewa “Ina Nazee take?” Leena ta fad’a cikin sanyin jiki

“Bansani ba, ki kirata in kinaso”, Rafee tabata amsa cikin masifa sannan ta kashe wayar.

Leena ta ciro wayar daga kunnenta tana ‘ko’karin maida shi hand bag nata tana tunani “Oh ni Leena, ko yaushe yayyena zasu shiryu oho”, ‘dayan bangaren zuciyarta yabata amsa “Sai lokacin da mum da dad suka fara zaman gida”. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta shiga aji don duba hand-out nata kamin lecturer ya shigo.

☆☆☆☆☆☆☆☆
Hajiya Rahma ne ke d’aura d’ankwalin ta agaban dressing mirror dake guest house da suke zuwa da ‘kawayenta, tana gamawa ta d’auki jakarta ta rataya, daidai lokacin Hajiya Hafsat tafito daga toilet tana tsane jikinta da towel.

Haj. Hafsat ta kalleta sannan tace “Har kin shirya zaki wuce kenan”

“Gwanda na tafi yanzu don kinga asali ma ba da niyyan kwana nazo ba gashi har na kwana, nasan yaran nan zasuta tunani ko wani abu ne ya sameni ko kuma na bazama wani wajen, barin je na shirya ‘karyar dalilin kwanan da nayi” Haj. Rahma ta fad’a tana murmushi

Haj. Hafsat ta tako zuwa inda Haj. Rahma take tsaye sai tayi pecking nata gami da rad’a mata a kunne “Daren jiya yayi dad’i, sai mun sake had’uwa”

Haj. Rahma ta rungumeta tace “Kwana biyu nasan da ‘kyar na samu damar fitowa, koma yaya dai zamuyi waya”

Ahaka Haj. Hafsat ta rakata har ‘kofar parlour sannan suka d’aga ma junansu hannu alamar bye-bye.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Haj. Rahma tana danna kan motarta cikin gidan taga Sofy jingine ajikin motar sanye da riga da wando tana hira da Bash. Afusace tayi parking sannan ta nufosu. Sofy bata lura da ita ba saida ta iso daf dasu, Bash yana ganinta yace “Sannu da dawowa” gami da rusunawa kad’an. Ta amsa mishi ba yabo ba fallasa sannan ta watso ma Sofy wani uwar harara sai tayi ‘kwafa ta wuce cikin gida.

Jiki na ‘bari Sofy tace ma Bash “Barina je wajen mummy, naga like she is in a bad mood”

Matsowa kusa da ita yayi yana faman rungumeta amma sai tayi saurin ja da baya tana waigawa, a rikice tace “Not here, don Allah ka rufamin asiri, kai kanka kasan halin mummy kuma kasan ba son maganarka takeyi ba, yanzu in ta ganmu rungume da juna Allah ne kad’ai yasan masifar da zan sha, in banci sa’a ba ma har marina sai tayi, katafi, sai munyi waya”, tana kaiwa nan ta juya ta nufi parlour ba tare da ta sake waiwayan Bash ba.

Tana bud’e ‘kofa taga mummy sai kai komo takeyi a tsakar parlourn, da ganinta ansan tana cikin ‘bacin rai.

Cikin babban murya tafara magana “Sofy, mesa bakijin magana?, wato bazaki rabu da d’an iskan saurayin kin nan ba ko?, me kike samu a wajenshi da kika li’ke mishi haka?”

Sofy da ta gama tsurewa tace “Mummy ina sonshi, yace kuma zai aureni”

Wani ashar ta duruma sannan tace “Ni kike gayama wai sonshi kikeyi?, wallahi kinji na rantse miki, karki kuskura na ‘kara ganinshi a gidan nan, in ba haka ba zaki yaba ma aya za’kinta”

Sum-sum ta nufi d’akinsu tana mamakin hali irin na mummy, ita bata zama dasu, bata bincikar halin da suke ciki, batasan shige da ficensu ba, batasan me suka sa gaba a rayuwarsu ba, bata damu da sanin me suke shukawa a doron ‘kasa a bayan idonta ba, ba, ba, ba, ba, mara adadi don ita kullum yawonta take tafiya amma abun mamaki abun dariya wai in ta ‘kyalla ido taga sunyi abu guda d’aya mara kyau to fah ranar ta dinga bala’i kenan.

Tana zama akan gado taji knocking na ‘kofa. Mi’kewa tayi ta nufi parlourn, mummy ta tafi d’akinta, bud’e ‘kofar tayi, cikin mamaki tace “Rafee, jiya da dare muka yita trying numbarki ni da Leena amma ya’ki shiga don munaso mu rufe ‘kofa bamu san ko zaki dawo ko……”

Da sauri Rafee tasa hannu ta toshe bakin Sofy, murya ‘kasa-‘kasa tace “Ke yi shiru, naga motar mummy a garage, muje d’aki kar taji ba a gida na kwa…na….ba”. Da ‘kyar ta ‘karasar da sentence d’in sakamakon ganin mummy da tayi rungume da hannuwanta a ‘kirji, wani yawu mai d’aci ta had’iye sannan tayi ‘ko’karin fuskewa gamida cewa “Mummy ina kwana?”

Mummy tace “Wato don bananan shine kuke abinda kukaga dama ko?, don ubanki gidan ubanwa kika kwana da har bakiso naji?”

Cikin in-ina Rafee tace “Gi…dan…su Na…zee…na…kwa…na”

Batayi aune ba taji saukar mari akan fuskarta, cikin masifa mummy tace “Gidan ‘kawarki mara kunyar nan?, wanda batada tarbiyya, wacce bata san ta gaida ni a matsayin uwarki ba?”

Cikin sanyin murya tace “Im sorry mum, bazan sake ba”

Mum tayi tsaki ta nufi d’akinta tanata kumfar baki.

Rafee kuma d’akinsu ta nufa, nan ta samu Sofy ta ‘kurama ‘kofa ido, tana ganin Rafee tace “Sis, kiyi ha’kuri, wallahi yau nan ko ni sai da nasha masifa da bala’i daga shigowarta sanadiyar ta ganni tsaye da Bash, kinsan ta tsane shi”

Rafee tayi ya’ke tace “Ba komai, in tanaso tayita marina daga yau har gobe amma bazan fasa huld’a da Nazee ba”

Sofy tace “Ko ni nan bazan rabu da Bash ba, abinda zamuyi kawai shine mu chanja takun mu, mu toshe duk wata hanya da zai sa ta ganomu”

Rafee tayi murmushi tace “I have an idea”

Matsowa daidai kunnen Sofy tayi ta rad’a mata wani abu sannan suka tafa suna ‘kara tsara yanda takunsu zai kasance.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Bayan kwana biyu

“Fu’ad ka hanzarta mana, ka fa san jirginmu na 12:30 ne koh?, gashi yanxu har 11:35 amma ko wanka bakayi ba ka tsaya chatting, saisa yaushe ma zaka samu lokacin karatu?, mutum kullum waya na hannu yana danne danne”

Fu’ad ya kalli Suhal yace “Haba Suhal, wai mesa baka da hakuri ne?, shiri na sharp sharp ne kasani”

Tsaki Suhal yaja yana ‘kara duba agogon hannunshi yace “Daga yanzu dai na huta da ‘bacin ranka tunda ni na gama makaranta nah na huta, kai in kaga dama ka cigaba da shashancin da ka saba, its your future you’re ruining, not mine”

Fu’ad ya mi’ke tsaye ya nufi toilet yana sambatu “Ka cika takura da masifa wallahi, its my life, nasan me nakeyi tunda ni ba ‘karamin yaro bane”

Ko kallon inda yake Suhal baiyi ba ya sa’bi trolley d’in shi da niyyar jiran Fu’ad a motar sannan yace “Na baka 10 minutes, in baka fito ba sai mun had’u a gida don bazan zauna ina jiranka kasani missing na flight nah ba”.

Minti goma bai cika da Fu’ad ya fito shima ri’ke da trolley d’inshi. Ba wanda yace ma d’an uwanshi ‘kala har sukayi boarding.

Washegari jirginsu yayi landing a International airport dake Abuja. Wani ajiyar zuciya Suhal ya sauke sannan ya kalli Fu’ad yace “Alhamdulillah, daga yanzu na huta da rashin kunyar da kakeyi”

Murmushi Fu’ad yayi yace “Ai kam ni ne da hamdala don yanzu na huta da masifa da mitarka”

Suna d’an tsokanar junansu suka fito, bayan sunyi claiming luggages nasu sai suka nufi inda suka hango iyayen nasu tsaye bakinsu har kunne. Da gudu-gudu ko wannensu ya rungume iyayenshi suna masu matu’kar farin ciki.

Ku biyomu don yanzu ne labarin ya soma. Mu ‘yan uku muke cewa “We love you masoyan mu wherever you are, Allah yabar zumunci, Ameen”.

Haneefah.mywapblog.com
Stylishbichi.mywapblog.com
***MHS***






ABUN SIRRI NE 11-15
​​​*ABUN SIRRI NE*
Na ‘yan uku
*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*
*REAL MHS*
*11-15*
☆☆☆☆☆☆☆☆
Murnar wannan family aranar bazai misaltu ba, bayan sun d’an nitsa ne sai Suhal ya d’an fara dube-dube kaman yana neman wani abu, ganin haka yasa ummi tambayarshi, cike da kulawa tace “Son ya dai?, akwai abinda kake nema ne?”
Murmushi yayi ya shafi kanshi sai yace “Something is missing, banga lil sis ba, ina take?”
Abba ya bud’e baki zaiyi magana sai ummi tayi caraf tace “Tana gida, tana wani abu ne”
Jinjina kai Suhal yayi, daga nan basu tsaya ‘bata lokaci ba suka dunguma zuwa motoci biyu da sukazo dasu.
Gidan ‘katon gaske ne, tun daga garage Suhal da Fu’ad suka fara jin tashin kid’a kad’an-kad’an. Kallon junansu sukayi kowannensu bakinshi yana cike da tambayoyi. Suna dosan main house suka hango wasu bulbs masu wal’kiya an rubuta “WELCOME HOME SUHAL AND FU’AD”, cike da jin dadi Fu’ad ya kalli iyayen yace “Wow!!, ashe dai anyi missing namu tunda gashi har party an had’a mana”, duk suka sa dariya.
Wata matashiyar budurwa da bazata wuci 17-20 years ba ta rugo da gudu ta nufi wajensu. Suhal yana ganinta ya sake trolley d’inshi da yake ja, shima da gudu ya nufeta, rungume juna sukayi suna masu nuna tsantsar farin ciki, haka taje ta rungume Fu’ad ma wanda shima murmushin yakeyi.
Nan ne Suhal ya d’an harareta da wasa, kaman zaiyi kuka yace “Namanta ma ina fushi dake”
Zaro ido tayi ta dafe ‘kirji tace “Ni???, ya Suhal meh na maka?”
Jan kumatun ta yayi yace “Baki ji dad’in dawowar mu ba tunda ko airport bakije don tarbar mu ba”
Dariya tayi tace “Toh ai inada dalili”
Fu’ad yaja guntun tsaki yace “Dalilin me?, ke dai kice bakiso mu dawo ba don koma me kikeyi ai ya kamata ki ajiye shi tunda kinsan da dawowar mu”
Ta wani marairaice fuska tace “I’m sorry brothers” sai ta ruga ta shige ciki da gudu tana sharar hawaye.
Kasake suka bi bayanta da kallo, muryan Baba sukaji yace “Gashi kun sa daughter na kuka, maimakon ku tsaya kuji dalilinta amma sai kuka yanke mata hukunci”
Suhal yace “Meh dalilinta Baba?”
Baba yace “Mu ‘karasa ciki, duk zakuga komai”
Ba tare da musu ba suka cigaba da jan trolleys nasu har suka isa inda akayi decorations sosai in Blue and White, ga dogon table cike da kayan ciye-ciye kama daga snacks, drinks, cookies, cakes da dai sauransu.
Juyawa sukayi suna kallon iyayen nasu, Umma ta girgiza kai tace “Kun ga duk wad’annan abubuwan?, Ilham ce ta had’a muku musamman don tarbanku”
Daga Suhal har Fu’ad jikinsu yayi sanyi sosai. Bayan sun ajiye bags nasu a d’akunan su sai suka nufi d’akin lil sis d’in nasu, da sallama suka shiga, tana kwance akan gado tayi ruf da ciki tana kuka, amsa musu tayi ba tare da ta d’ago ta dubesu ba.
Suhal ya zauna ta damanta, Fu’ad kuma ta hagu, kallon juna sukayi sai Fu’ad ya mishi alama da ido akan ya fara magana.
Cikin lallashi Suhal yace “Lil sis, tashi don Allah muyi magana kinji?, kiyi ha’kuri ki bar kukan nan, we are sincerely sorry”
Batayi musu ba ta tashi zaune, nan suka sa ta a tsakiya. Fu’ad yayi magana, Suhal ma yayi har dai suka samu ta bud’e baki tace musu “Nafi kowa murna da d’okin ganinku amma da kukazo sai kuka nunamin wai sam banso ku dawo ba”
Suhal ya kama kunnenshi yace “Munyi laifi babba, bamu san kin tsaya shirya mana abubuwa bane”
Fu’ad ma ya ‘kara da “Ni har kunya ma naji wallahi, ki yafe ma brothers naki masu sonki”
Murmushi tayi sannan ta mi’ke daga zaunen da take, fad’awa jikinsu tayi ta rungumesu tace “I love you so much brothers, welcome home”
Ajiyar zuciya suka sauke kusan lokaci d’aya, dariya tasa sannan ta sakesu tace “Ya kukayi wani ajiyan zuciya sai kace kunyi gudu?”
Dariya dukkansu suka yi sannan Suhal yace “Mun ji tsoron fushin lil sis ne, mun tsamman bazaki yafe mana ba”, nan fah hira ya kaure tsakanin su ukun.
Chan sai Fu’ad yayi hamma yace “Lil sis, yunwa nakeji sosai”
Kama baki tayi tace “Sorry bro, na sha’afa ne, muje nayi serving naku”.
Jan hannunsu tayi suka nufi inda ta shirya musu abincin, basu kujera tayi sannan tace su jirata bari ta kira iyayen nasu.
A hanya ta gansu, nan suka iso wajen table d’in suka zazzauna. Sunci, sun sha sunata raha gwanin sha’awa, duk wanda ya gansu ko ma’kiyinsu ne sai yaji sun burgeshi don yanda suke masifar son junansu.

☆☆☆☆☆☆☆☆
Hajiya Hafsat ce ke ta knocking a ‘kofar parlourn gidan Haj Rahma, Leena ce tafito dagudu tana cewa “Wayene?”
Daga bakin ‘kofar Haj

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login