Showing 12001 words to 15000 words out of 37595 words

Chapter 5 - ABUN SIRRI NE Sirrin Rayuwa By MUNAYSHAT

11 Sep 2026

135

Nazee tana bata ha’kuri har dai ta ha’kura. Ba ita tabar gidan ba sai maghriba shima bawai don sun gaji da juna bane sai don gudun kar momy tadawo ta sameta.

Sofy da Bash kuwa holewa sukayi sosai har saura ‘kiris tabashi kanta, ko meh ta tuna kuma oho saita tureshi tana kakkare jikinta. A wahalce ya dubeta yace “Baby dont do this to me, aurenki fah zanyi, ki kwantar da hankalinki ki bari muji dad’in rayuwar mu kamin muyi aure”

Girgiza kai ta hau yi tana cewa “Im sorry Bash, bazan iya baka kaina ba duk da i love you more than my own self, lets just keep it this way, mu tsaya a romance da mukeyi, shi kad’ai ma ya ishi ya cire mana kwad’ayin juna whenever the need arises”

Jikin Bash rawa yafara yi don yasa rai sosai, jingina yayi da jikin window na motar yana maida numfashi sama-sama, ya d’au lokaci ahaka sannan yasamu ya saita kanshi, azuciyar shi ya raya ma kanshi dole ne ma yasan hanyar da zaibi har ya cimma burinshi akanta ko da kuwa ta ‘karfi ne. Da ha’kuri da banbaki ta samu ya sauko daga dokin fushin da ya hau, hirar su suka cigaba da yi wanda rabi hirar batsa ce. Bashi yabar gidan ba sai bayan Nazee ta tafi shima saida mai gadi yazo yace mishi “Yalla’bai kayi ha’kuri katafi kar hajiya tadawo na rasa aikina”.

Shigan Sofy gida tasamu Leena da Rafee suna hira kaman basu ba, ada kullum Rafee hantarar Leena takeyi amma abun mamaki yau gashi har dariya sukeyi suna labarai, shiga cikin d’aki tayi tashiga wanka sannan tasa wani short gown ta d’aura zani akai tayi sallar maghriba da Isha don lokacin Isha ma har ya shiga, da ta idar ne ta cire zanin ta ninke sannan tafito parlour suka sa abinci su ukun suna ci suna kallo.

Ahaka momy tazo ta samesu, mamaki taji sosai wai yau y’anmata ukun sunacin abinci a plate d’aya, rabon da taga hakan tun kamin su girma su mallaki hankalin kansu. Sannu da dawowa suka mata, amsa musu tayi gamida fad’awa kan kujera a gajiye, bayan tasha ruwa sai tace “Yanzu kam kun fara abun kirki, tun da nafita har nadawo Tijjani yacemin ko tsakar gida baku fita ba kuna cikin parlour”

Da yake dama ance “A criminal is always afraid” sai suka fara exchanging glances tsakaninsu wanda sam momy bata lura da hakan ba don a gajiye take. Leena ne tayi ‘karfin halin cewa “Momy ko akawo miki abinci ne?” don kawar da maganar.

Momy ta tashi da jakarta tace “Bari na watsa ruwa, zanzo naci”, bata jira cewarsu ba tayi shigewarta d’aki. Atunaninta yanzu yaran nata sun fara shiryuwa don yanda mai gadi ya dinga yabonsu, batasan sun manna mata hauka bane.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Suma bayan sati d’aya.

Yanzu Ilham ta dage da shiga kitchen don tun ranar da Suhal yace mata shi yanason matarshi ta iya girki bata sake missing na shiga kitchen ba, ba laifi ta fara picking na wasu girke-girke saidai har yanzu da sauranta kad’an.

Tsakaninta da Fu’ad kuwa tuni sun koma normal, haka iyayen nata ma taje ta basu ha’kuri sun kuma ji dad’in chanjawan halinta farat d’aya.

Tun daga nesa Suhal yake ‘kwala ma Fu’ad kira amma bai amsa ba, hakan yasa yanufi d’akin da saurinshi. Yana bud’ewa yaga Fu’ad du’kun’kune acikin bargo yana ri’ke da waya, lura da yayi sam Fu’ad bai san yashigo ba yasa yayi amfani da wannan dama don sanin meh ya d’auke hankalinshi har bai ji duk kiran da yake mishi ba.

Tsugunnuwa yayi ya bud’e blanket d’in a hankali ta baya, aikuwa idonshi suka sauka akan Blue Film da Fu’ad yake gani. Tsaba ya rikice har bai san lokacin da ya fizge wayar ya had’ata da bango ta tarwatse ba, a firgice Fu’ad ya mi’ke tsaya don ganin waya fasa mishi waya, zaro ido yayi ganin Suhal tsaye a gabanshi sai huci yakeyi.

Stammering yafara “Su…ha..l….yau…she….ka….shi…go?”

Suhal kama kanshi yayi yana tunanin yaushe Fu’ad ya fad’a wannan hali na kallon batsa baisani ba. Kallon Fu’ad yayi up and down sannan yace “Fu’ad, meh ya kaika fad’awa wannan hanyar?, are you out of your mind?, abinda kake ganin nan kai da kanka kasan haramun ne, mesa kake gani?, bakasan zunuban da kake kwasa ba ko?”.

Tsuru-tsuru Fu’ad yayi, gashi red-handed Suhal ya kamashi ba halin yin denying, ganin yayi shiru yasa Suhal magana cikin d’aga murya “Ba da kai nake magana bane?!!!!, answer me!!!”

Fu’ad ya bud’e baki zaiyi magana kenan sukaji Abba yana knocking na ‘kofar gamida cewa “Ya dai Suhal?”

Ido Fu’ad ya ‘kwalalo kaman zasu fad’o ‘kasa, takawa Suhal yayi ya tattara pieces na wayan ya mi’ka ma Fu’ad sannan ya bud’e ‘kofar. Abba yana shigowa yasake tambayar Suhal “Suhal meh ya faru naji muryanka har waje?, Fu’ad yayi wani abun ne?”

Tausayin Abba ne ya kama Suhal, yasan da ace zai gayama Abba abinda yakama Fu’ad yakeyi da matakin da zai d’auka Allah ne kad’ai yasani, mai da kallonshi wajen Fu’ad da ya zuba mishi pleading eyes yayi, harara ya watsa mishi sannan ya maida dubanshi wajen Abba, murmushi ya ‘kwa’kulo sai yace “Ba komai Abba”

Abba ya bishi da kallon karka maidani ‘karamin yaro mana, atake Suhal ya had’a ‘karya yace “Dama Ilham ne tacemin ya mareta bata mishi komai ba, nazo ina tambayar shi sai yamin shiru shine raina ya ‘baci, amma ba wani abu bane Abba”

Abba ya dai girgiza kai kawai ya sa kai yafice daga d’akin ba don ya yarda ba. Yana fita Fu’ad ya sauke wani wawan ajiyar zuciya don ya tsamman Suhal bazai rufa mishi asiri ba. Dur’kushewa yayi a kan gadonshi, Suhal kuwa waje ya nufa batare da ya sake waiwayan Fu’ad ba, har yakai ‘kofa yaji Fu’ad yana cewa “Wallahi sharrin shaid’an ne kuma bazan sake ba, don Allah ka rufamin asiri kar ka gayama iyayenmu, natuba”

“Ina tausaya ma rayuwarka in ka koma Turkey ba mai kwa’bar ka, gwanda tun wuri kayi ma kanka fad’a sannan ka ri’ke ro’konka, da naga dama da tuni na gayama Abba abinda ya faru, banyi don kai ba, don banason tayar mishi da hankali yasa na had’a ‘karya na gayamishi” duk maganan nan yayi sune batare da ya kalli Fu’ad ba, yana gamawa kuwa yabar wajen.

Fu’ad da kanshi yasan lallai yayi sa’an yaya yakuma shaida cewa ba ‘karamin so Suhal ke mishi ba tunda har ya iya ‘karya don kawai ya kare shi. Sim card nashi kawai yacire daga wayar sannan ya saka wayar a dustbin don in yace zai gyara ma kud’in da zai kashe ba kad’an bane, gwanda kawai ya siya wani tunda yanada kud’i a account nashi. Fita yayi ya d’auki motarshi yaje ya siya latest waya wanda ake yayi a lokacin.

Suhal ya fita harkar Fu’ad, sannu-sannu kawai yake had’asu wanda agidan sam ba wanda yagane. Har d’aki Fu’ad ya sameshi ya dinga bashi ha’kuri yana cewa yatuba, har kuka sai da yayi sannan Suhal yace mishi shikenan yawuce amma in ya sake kamashi da laifi irin haka ba abinda zai hanashi gayama iyayen nasu. Da wannan doka suka koma normal lives nasu kaman basu ba.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Tana cikin driving motarta ta tsaya, ba yanda batayi ba amma ya’ki tashi gashi wajen ba mutane, d’ai-d’aikun motoci ne suke wucewa jifa-jifa. Wayarta ta ciro don kiran mechanic shikuma wayarshi ya’ki tafiya, matsalar network. Ga uban rana da ake tafkawa, tun tana tare motoci har ta gaji don ba wanda ya tsaya, tana mamaki yanda na ‘kwarai sukayi kad’an a zamanin nan.

Ranar ya shiga jikinta sosai don takai kusan minti talatin a wajen, number momy da duk sisters nata kaman had’in baki suma sun’ki shiga. Ganin haka yasa ta kasa daurewa kawai sai ta fashe da kuka abun tausayi, chan taji ana mata horn amma bata d’ago ba don kukan da yaci ‘karfinta.

Mutumin yafito ya iso jikin motar inda ta kifa kanta tana kuka. Sallama yamata ta amsa batare da ta d’ago ta kalleshi ba, chan sai yace “Meh ya sameki kikazo tsakiyar hanya kika hau kan motar kina kuka?”

Sai sannan ta d’ago fuskarta, idanunta duk sun rine sun zama jawur, share hawayenta tafara yi tana cewa “Motar na ne ya ‘baci tun dazun, na kira mechanic da ‘yan gidanmu amma duk bai shiga, duk motar da na tsayar don in nemi taimako kuma ba wanda ya tsaya” tana ‘karasa maganar wani sabon kuka ya ‘kwace mata.

Tausayin ta yaji a lokaci d’aya kuma shagwa’barta ya burgeshi, cikin sigar lallashi yace “Yi ha’kuri ki sauko ki rufe motar in yaso sai na maidake gida, daganan sai ki kira mechanic d’in yazo ya d’auki motar don ni banda number mechanic nah”

Kallonshi tayi tana ‘ko’karin karantar shi, wani zuciyar yana ce mata ta bishi kawai don kaman ba mugu bane, wata zuciyar kuma yana ce mata MUGU BAI DA KAMA(Book by kausariyya). Daga ‘karshe dai kawai ta sada’kar akan zata bishi, sau’kowa tayi ta rufe motar kaman yanda yace mata sannan ya bud’e mata motarshi tashiga, da kwatance har ya kaita gidansu.

Godiya ta mishi, har ta bud’e motar sai yace “Sorry, ya sunan mai kukan?”

Kunya ne ya lullu’beta tunawar da tayi yanda ya ganta tana kuka shar’be-shar’be, sunkuyar da kai tayi tace “Sunana Yaleena amma ana kirana Leena”

Jinjina kai yayi yana mouthing na sunan, murmushi yayi yace “Nice and unique name, ni sunana Suhal”.

Tohh readers ku cigaba da biyomu

Haneefah.mywapblog.com
Munay, Hanee and Stylish

*REAL MHS*





Skip to content
haneefahusman
SEPTEMBER 8, 2016
ABUN SIRRI NE 33-34
​*ABUN SIRRI NE*
Na ‘yan uku

*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*

*33-34*

☆☆☆☆☆☆☆☆

“Thank you Suhal, Allah ya saka maka da alkhairi” Leena ta fad’a sannan ta fice daga motar. Wani gentle smile ya sakar mata, bai ce komai ba yaja motarshi, bin motar tayi da ido har saida ya ‘bace mata sannan ta sauke wani nannauyan ajiyar zuciya ta nufi cikin gida.
Tana shiga parlour taga Momy, Sofy da Rafee zaune suna hira, ganinsu yasa taji wasu zazzafan hawaye suka fara zubo mata. Duk sun rikice ganin yanayin da ta shigo cikin gidan, a kid’ime suka hau tambayarta me ya faru. Hawayen nata ta share gamida ‘karasawa ta zauna a kusa da Momy ta kwantar da kanta a jikinta sannan ta soma gayamusu irin wahalar da tasha har daga baya wani bawan Allah ya taimaka mata kuma shi ne ma ya kawota gida. Dariya sosai Sofy da Rafee suka farayi jin har kuka Leena tayi, Momy ma dai abun dariya ya bata amma ganin yanda Leena tayi rau-rau da ido kaman zatayi kuka yasa ta danne nata, hararar su Rafee tayi tana shafa bayan Leena alamun lallashi. Sai da tabar sheshshe’kar kukantan sannan Momy tace “Yi ha’kuri auta na, bari zan kira mechanic yazo ya kar’bi key d’in in yaso sai ki mishi kwatance yaje ya d’auka”
Jinjina kai Leena tayi, cike da shagwa’ba tace “Kinga sai dariya suke min ba?”
Momy tayi murmushi tace “Barsu suta yi tunda su dariyar mugunta suke ma auta nah, ki shirya gobe zamuje ki za’bi kowanne irin motar kikeso”
Wani ihun dad’i Leena tayi tana ‘kara ‘kan’kame uwar tasu. Su Rafee da Sofy kuwa kaman d’aukewan ruwa dariyar su ya tsaya, mamaki ne ya cikasu har basu san sanda suka wangale bakinsu ba. Sofy ne ma tayi ‘karfin halin cewa “Momy gaskiya baki mana adalci ba indai hakane, yaushe ne muka miki maganar munaso ki chanja mana motar amma kikace bakida kud’i?, yanzu kuma kwatsam sai kice zaki d’auki Leena ta zabi duk wanda takeso?, kuttt!!”
Rafee ta kar’be “Wallahi da sakel, bazamu yarda ba, wannan ai nuna bambanci ne, don Allah Momy karki mana haka”
Sofy tace “Kuma ma Momy last year fah kika saya mata wannan, nawa yanzu yakai shekaru uku, na Rafee kam yakai hud’u ma if i’m not mistaken”
Rafee ta wani marairaice tace “Please Momy….”
Duk protesting da sukeyin nan Momy batace dasu ‘kala ba sai murmushin da take binsu dashi, Leena kuwa gwalo take ta musu.
Da sukaga ba sarki sai Allah sai suka mi’ke suka nufi kujeran da Momy da Leena suke zaune gamida tsugunawa bisa guiwowinsu. Momy ta kallesu tace “Wayace kuzo kuyi kneeling?”
Leena ta gyara zamanta tace “Momy barsu, ha’kuri sukazo bayarwa”
Harara Sofy da Rafee suka watsa mata sannan suka maida dubansu wajen momy, kama kafafunta sukayi sai Rafee tace “Momy we are sorry, don Allah dont punish us this way, ki taimaka ki chanja mana motar muma”
Momy tayi jim sannan tace “Naji, naji, amma on one condition”
Bakunansu har kunne suka had’a baki sukace “Ko menene zamuyi momy”
Dariya tayi tace “Ku bata ha’kuri, in ta ha’kura fine, zan saya muku”
Sofy tace “Waye kenan?”
Momy ta nuna musu Leena tace “Leena mana, dariya kuka mata don motarta ya ‘baci, in ta ha’kura sai na saya muku”
Wani dakewa Leena tayi ta tsare ita adole tana jira abata ha’kuri, Rafee taja tsaki tace “Wannan ai zubda girma ne Momy, ‘kanwar mu ne fah ita”
Sofy tayi jim tana tunani, chan sai tace “Auta kiyi ha’kuri kinji?”
Cike da mamaki Rafee take kallon Sofy jin ta bada ha’kuri ba tare da gardama ba, zungurarta tayi tace “Ke fah wawiya ce, wannan jinjirar zaki bud’e baki kina bama ha’kuri?”
Leena tayi murmushi tace “Rise Sofy, kin samu kyautar motar”
Tsalle Sofy tayi tana rawa tasamu motar, tsugunnawa tayi daidai kunnen Rafee tace “Sis, ki rufa ma kanki asiri ki bata ko kuma kiyi bye-bye da chanja motar this year”
Momy kam me zatayi in ba dariya ba, kirar mechanic tayi yace gashinan zuwa. Rafee kuwa ta wani dake ita batason raini, chan sai ga mechanic kam ya iso, har ‘kasa ya dur’kusa ya gaida Momy, kwatance Leena ta mishi sannan ta bashi car key d’in. Har zai fita sai Momy tace “In ka gyara inaso kayi painting nashi don kyautar wa zanyi”
Mechanic ya amsa “Toh” sannan yasa kai ya bar parlourn.
Yana fita Leena ta saci kallon Rafee, tana dariya ‘kasa-‘kasa tace “Momy ina laifi abama Rafee tunda ita bazata samu sabo ba?”
Momy ta kwashe da dariya tace “Kin kawo shawara mai kyau auta, hakan za ayi, ita zan bama”
Rafee ta mi’ke tace “Whatt??!?, ni za abama kwancen motar?, wallahi bazai yuwu ba”
Momy ta gimtse fuska tayi ‘kwafa tace “Kina tsamman wasa nakeyi ko?, karki bama Leena ha’kuri, zakisha mamaki gobe”
Ganin kaman Momy dagaske takeyi yasa Rafee shafa ma kanta ruwa ta isa wajen Leena tana wani cin rai, dagewa tayi tace “Yi ha’kuri”
Leena ta juya kai kaman bata jita ba, hakan yasa Momy cewa “Open your mouth and speak in an audible tone ba ki tsaya kina wani cin magani ba”
Ba don taso ba ta bud’e baki ta ‘kara sautin magananta tace “Auta kiyi ha’kuri”
Murmushi sosai Leena ta sake, kallon Momy tayi tace “I forgive her momy”
D’aga mata kai momy tayi alamun “Noted”
Leena ta maida kallonta wajen Rafee da ke tsaye a gefenta tace “Go and sit down, kin ci sabuwar motar gal a leather”
Murmushi Rafee tayi takoma kujerar da take zaune. Hira suka hau yi sunata tsokanar junansu gwanin sha’awa, sai sautin dariyarsu ke tashi.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Suhal yana sauke Leena ya wuce Pharmacy da Abba da Baba suke gina mishi, duba cartons na drugs da akayi ordering yakeyi don kar a manta ba a siya wani ba amma sam ya kasa maida hankalinshi. Da yaga ba abinda zai iya tsinanawa sai kawai ya sallamesu yace bai jin dad’i zai dawo daga baya.
Yana driving sai tunanin Leena yakeyi, nutsuwar ta ya burgeshi, shagwa’barta, kukanta, idanunta sunfi komai d’imauta shi. Ahaka har ya isa gida, ya dad’e a garage sannan ya samu ya saita kanshi yafito yana Allah yasa kar ya had’u da kowa har ya isa d’akinshi don yasan duk wanda yaganshi zai gane akwai abinda ke damunshi. Cikin rashin sa’a yana wucewa zai shiga d’aki Ilham dake jiran dawowarshi taga giftawar shi, sam bai ma lura da ita ba don hankalinshi bai wajen, mi’kewa tayi ta kira sunanshi “Ya Suhal”
Wani takaici ne ya ziyarci zuciyarshi, ahalin yanzu ba abinda yake bu’kata kaman ya zauna shi kad’ai yana tunanin Leena. ‘Ko’karin mazgewa yayi had’e da juyowa yana kallonta, a gajiye yace “Lil sis, lafiya kam ko?”
Matsowa kusa dashi tayi tana karantar fuskar shi, lura da abinda take faman yi yasa shi saurin sunkuyar da kanshi, murmushi tayi tace “Tun dazun nake jiranka anan ai, ka dawo kuma bakama lura dani ba”
Kanshi a sunkuyen yace “Sorry, kaina ke ciwo saisa ban lura ba”
Cikeda kulawa ta kama hannunshi tana ‘ko’karin mi’kar da ‘kafanta don jin temperature na kanshi da yace yake ciwon, yaci sa’a kuwa kan nashi da d’an zafi kad’an, hakan yasa Ilham bata kawo komai a ranta ba. Jan hannunshi tayi tace “Muje ka kwanta sai in kawo ma magani kasha”
Murmushi ya ‘kir’kiro gami da bin ta, key ya bata ta bud’e d’akin nashi, zaunar dashi tayi akan kujera sannan ta juya da sauri tace tana zuwa.
Hulan da ke kanshi ya cire ya ajiye sannan ya cire rigan ya rage dagashi sai vest, fad’awa kan kujera yayi yana ajiyar zuciya. Bayan kaman minti biyu sai Ilham tadawo da magani da ruwa, bashi tayi, ba musu kuwa ya kar’ba ya sha don ya ma kasa gane kanshi, kanshi a ‘kulle yake, baya tunanin komai sai Leena.
Ilham ta zauna a ‘kasa tana wasa da hannunshi ba wanda ke magana a cikinsu, chan dai ya mi’ke ya kalli Ilham sai ta bashi tausayi, shafar fuskanta yayi yace “Lil sis barina shiga d’aki na kwanta, ina jin bacci”
Itama mi’kewan tayi tace “Toh muje in kayi baccin sai na tafi”
Da sauri yace “Kije kawai bakomai, in na tashi zan shigo cikin gidan” don so yake ya zauna shi kad’ai
Ba don taso ba ta fice daga parlour’n idanunta duk hawayen tausayinshi, atunaninta ko ciwon kai d’in ne yake damunshi sosai.

Haneefah.mywapblog.com
Munay, Hanee and Stylish

*REAL MHS*






Skip to content
haneefahusman
SEPTEMBER 12, 2016
ABUN SIRRI NE 35-36
​*ABUN SIRRI NE*
Na ‘yan uku
*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*

*35-36*

☆☆☆☆☆☆☆☆

Kwance yake yanata juyi akan gadonshi, sonta yayi mishi mugun kamu gashi bai ta’ba soyayya ba saisa yake ganin kaman soyayya wahala ne tsantsa, zuciyarshi da ‘kwa’kwalwarshi sun toshe, shi har abun ma tsoro yafara bashi, daga baya kuma yaja tsaki yace afili “Yarinyar da ban sani ba tana neman birkita min lissafi, I have to get her out of my mind don bana ra’ayin soyayya, ban shirya yin soyayya yanzu ba”. Da ‘kyar yasamu ya lallashi zuciyarshi har yayi bacci.
Kiran sallar maghriba ne ya tayar dashi daga baccin da yakeyi, da ‘kyar yasamu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login