Showing 21001 words to 24000 words out of 37595 words

Chapter 8 - ABUN SIRRI NE Sirrin Rayuwa By MUNAYSHAT

11 Sep 2026

130

idonta yarufe har batasan lokacin da ta mi’ke ta wanka mishi wani wawan mari ba, ji kake tassss!!!!!
A firgice ya d’ago kai yana kallonta don tun yana ‘karami ko da marin wasa ne Mummy bata ta’ba mishi ba amma sai gashi yau ta wankeshi da marin da yaji har kunnenshi saida ya amsa, cikin rawar murya mai d’auke da tsantsan mamaki yace “Mu….m….my……..”
☆☆☆☆☆☆☆☆
Tsugunnawa tayi ta ajiye tray d’in, batace dashi komai ba ta jawo plate da tazo dashi ta zuba mishi abinci sannan tasa mishi drink a cup, stool ta tura zuwa gabanshi ta d’aura plate da cup d’in akai. Komawa gefe tayi tace “Ya Suhal ga abinci kaci, karka kwana da yunwa”
Mi’kewa zaune yayi yace “Thank you lil sis”
Murmushi ta mishi sannan ta maida hankalinta zuwa kallon tv har ya gama cin abincin. Kwashe kwanukan ta fara yi tana maidasu kan tray d’in da tashigo dashi, mamaki ne ‘karara kwance akan fuskar Suhal ganin yanda Ilham yau tazama shiru haka bayan ba haka take ba. Saukowa yayi daga kan kujeran ya kama hannunta da take faman d’aukan tray, ahankali ta sauke idanunta akan hannunshi da ya d’aura akan nata sannan ta kalli fuskarshi.
Kallon cikin idonta ya shiga yi yana faman karantar halin da take ciki, har ta bud’e baki zatayi magana ko me ta tuna kuma oho sai ta girgiza kai tace “Ya Suhal sakeni barin tafi”
‘Kin sakin hannun yayi sai ma ya jawota jikinshi yace “Laifin meh nayi ake fushi dani?”
Cikeda masifa tace “I dont know!!, ka sakeni ya Suhal” sai kuma tasa kuka tana tutture shi tana naushin shi a ‘kirji, shiko sai ‘ko’karin kamata yakeyi har dai ta gaji ta bar tureshin ta fashe da wani sabon kuka.
Shafa kanta yafara yi yace “Lil sis bansan me na miki ba but I’m sorry”
Sai da tayi ya isheta sannan ya sassauta ri’kon da yamata, ahankali ta janye jikinta tana share hawaye, cikin sigar lallashi yace “Don girman Allah ki gayamin meh na miki”
Kallonshi tayi da rinannun idanunta tace “Ya Suhal bakamin komai ba, laifi na ne”
Cikin rashin fahimta yace “Laifinki kuma?”
Jinjina kai tayi tace “Yes, laifina ne da na koyi sonka tun ina ‘karama, laifina ne da na fara sonka tun bansan ma meh soyayya ba, its all my fault, kai ba sona kakeyi ba amma na nace da sonka, Ya Suhal don Allah mesa baka sona?, akwai abinda nakeyi mara kyau ne?, ka gayamin wallahi bazan sake yi ba na rantse ma, don Allah…” ta kai ‘karshen maganar tana kuka sosai.
Tausayinta ne ya mugun kamashi, cikeda damuwa yace “Ilham meh ya kawo wannan maganar kuma?, wayace miki bana sonki?”
Murmushin da yafi kuka ciwo tayi tace “I know, ko yau ma na ‘kara tabbatar ma kaina hakan, alokacin da kace min meeting zakaje baza kaje dani ba farinciki na shiga yi marar misaltuwa don a tunani na kana sona ne har kake kishin wasu su ganni, unfortunately ashe ba haka abun yake ba don da dare da ka dawo kace gidan abokinka kaje, ya Suhal at that moment my conscious whispered to me cewa ka je wajen wata ne bakaso nasani, Ya Suhal nasan bakasona kawai kanayi kaman kana sona ne don kar nashiga damuwa, hakan da kakeyin kuwa wallahi baka sani ba cutata kakeyi……” kuka sosai takeyi fiye da tsammani, kukan nadamar fad’awa son wanda bai sonta.
Suhal yama rasa ya zaiyi da ranshi don ganin yanda Ilham take kuka kuma shine sila, rungumeta gam-gam yayi ajikinshi yace “Ilham inasonki, kibar cewa bansonki sannan kibar ganin laifin zuciyarki”
Da sauri ta zame daga jikinshi tana dariya, hawaye suna kwararowa daga idanunta don jin Suhal ya furta yana sonta, kama hannunshi tayi tace “Kana sona ya Suhal?, dagaske?”
Suhal ji yayi kaman yasa hannu akai ya rafsa ihu, ba don yaso ba sai don fitar da Ilham daga halin da take ciki yace “Eh”
Share hawayenta tayi tace “Toh ya Suhal zaka aureni na haifa maka babies masu kama damu ko?, Allah ya Suhal zan maka duk abinda kakeso”
Maganar yajishi bambara’kwai, azuciyarshi yana Allah wadai da soyayya tunda gashi ya maida Ilham mara kunya ya makantar da ita tana ganin komai tayi daidai ne, shi kunya ma maganar ya bashi, daurewa yayi ya d’an kalleta yace “Aure Ilham?, kinsan me aure kuwa?”
Tura baki tayi tace “Wani irin tambaya ne wannan?, I’m 18 fah, nasani mana”
Kaman gunki ya tsaya yana kallonta yana tunanin yanda zai shawo kanta tabar maganar auren da take mishi, murmushi ya ‘kir’kiro yace “Aure ba yanzu ba kinji?, kibari sai kin ‘kara girma”
Kaman zatayi kuka tace “Sai na ‘kara girma?, yanzu ban girma bane toh?”
Gyara maganarshi yayi yace “Sorry I mean sai kinyi nisa a university, kinga yanzu kike neman admission, aure sai nan gaba kinji?”
Jim tayi tana tunani akan maganarshi sai tace “Eh kuma hakane fah, amma dai kace zaka aureni naji”
Ba tare da wani tunani ba yace “I promise you zan aureki”, saida ya ‘karasa maganar ya shiga salati a zuciyarshi, shi harga Allah bai san ya akayi bakinshi yafurta kalmar al’kawari ba. Innalillahi yashiga nanatawa tunawa da girman al’kawari da yayi.
Ilham tayi wani tsalle tana ihu, Suhal hankalinshi bai wajenta yana chan yana jajanta ma kanshi wannan furucin da yayi, pecking nashi tayi don bata lura da halin da yashiga ba, cikeda jindad’i tace “Toh Ya Suhal sai da safe, dream of me kaji?”
Bai ko iya amsa mata ba haka tafita tanata jindad’i Suhal ya mata al’kawarin zai aureta.
Tana barin d’akin bashiri Suhal ya mi’ke tsaye yana salati afili, shi kad’ai ya soma surutu “What was I thinking?, meh ya kaini?, al’kawari?, al’kawarin zan auri Ilham??, la ilaha illahi, meh ma yakai bakina furta wannan babban maganan?, Nooo ina!!, there must be a way, dole na nemi mafita, Leena ne kawai zan iya aura don ita nakeso sannan bana sha’awar auren mata biyu, toh ma idan na auri Ilham inyi meh da ita?, a matsayin ‘kanwa nake ganinta, kai ko gado bazan iya had’awa da ita ba balle wani abu yashiga tsakaninmu, ina!!”. A wannan daren dai ba abinda yake yawo a ‘kwanyar Suhal sai takaicin kanshi da yakeji.
Washegari duk wanda yaga Ilham sai yasan tana cikin wani irin farinciki. Tun daga ranar kuwa take ‘kara shishshige ma Suhal tana tarairayar shi, shi ko kawai biye mata yakeyi ba wai yana jinta a ranshi ba.
Bayan sati d’aya
Kullum sai Suhal yayi dialing na number Leena sai ya fasa kira, shahada yayi ya danna mata kira. D’auka tayi suka gaisa sannan yace mata Suhal ne.
Murmushi tayi tace “Suhal ya kwana biyu?”
“Lafiya lau, ya school?”
“Kalau wallahi”
“Okay dama nace bari mugaisa ne”
“Ayyah nagode, bye”
Yana cewa “Bye” ya katse wayar, kwanciya yayi danne da saitin ‘kirjinshi da yakeji kaman zai faso waje, chan kuma sai yafara jin haushin kanshi na yanda bai iya magana da Leena, magana yakeyi da zuciyarshi “Mesa nake kunyar gayamata ina sonta ne?, dole ne ma na nitsu na dinga dagewa ina kiranta muna hira kar wani yamin shigan sauri”.
Two weeks later
Zuwa yanzu Suhal ya rage tsoron Leena da yakeji don yakan kirata su sha hira kaman friends sabida yakasa gayamata sonta yakeyi, da yake Leena tanada son raha haka zata biye mishi suta hira suna dariya kaman daman chan sun saba, Suhal kuwa sai ‘kara nitso a cikin kogin sonta yakeyi wanda ita da alama bata ma san yanayi ba.
A ‘bangaren Ilham ita dai hankalinta kwance yake, gata da ya Suhal nata, haka zataje d’akinshi suyita hira, shi dai yi kawai yakeyi don bai son ya gayamata shi baya sonta ta fad’a ‘kunci, saidai fah saitace mishi “I love you” sau goma shi baice mata sau d’aya ba, hakan kuwa bai ta’ba damunta ba tunda yamata al’kawarin zai aureta ai shikenan.
Thursday 10:00pm
Fu’ad ne janye da trolley d’inshi ya iso tsakar gida inda iyayen dasu Suhal suke tsaye suna jiran fitowarshi. Motar biyu suka d’auka suka dunguma sai airport, achan iyayen suka ‘kara d’ora mishi wa’azi akan wanda sukata mishi agida.
Baba yace “Fu’ad yanzu kai kad’ai ne zaka koma chan inda ba wanda zai kwa’beka in kayi ba dai-dai ba, abinda nakeso dakai shine ka ri’ke mutuncin kanka ka kare kanka ka kuma ji tsoron Allah, in mu bamu ganinka toh shi yana ganinka, Allah ya bada sa’a”
Abba yayi murmushi yace “My son, nasan bakada matsala, ka cigaba da ri’ke addininka da kyau, Allah ya kare”
Umma da Ummi da suketa hawaye kaman yau ne zai soma tafiya yabarsu suma suka mishi Allah ya taimaka ya amsa jiki a sanyaye don wa’azin da Abba da Baba suka mishi ya matu’kar razana shi ya shiga jikinshi sosai.
Shan hannu sukayi da Suhal, Suhal yace cikin dauriya “Take care bro, all the best, Allah ya kaiku lafiya”
Fu’ad yayi mishi side hug yana murmushi, daganan ya rungume Ilham da ke ta shar’bar kuka, lallashinta yayi sannan sukayi sallama.
Iyayen basu bar airport d’in ba saida jirginsu Fu’ad ya tashi misalin 11:30pm. Sai muce Fu’ad a isa Turkey lafiya.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Toh anan zamu dakata yau amma you guys should ponder upon these questions:

-Shin mummy tana yarda da abinda Abdul yace akan tayi aure ko yaya?, in ta yarda ya zai kasance?, in bata yarda ba kuma ya?.

-Suhal yana cika ma Ilham al’kawarin aurenta da yayi ko kuma yana zama mai karya al’kawari?.

-Suhal yana iya furta ma Leena cewa yana sonta ko sai lokaci ya ‘kure mishi?.

-Momy, Rafee, Sofy, Leena da daddy kuma ya abun yake zama?.

Sannan a ‘karshe ya rayuwar Fu’ad yake kasancewa a Turkey?, yana shiryuwa ko kuwa rayuwarshi tana ‘kara zama abun “Allah sarki”?.
Muna jiran ra’ayinku ta blogs namu ko kuma ta WhatsApp. We love y’all.

Don samun wad’annan amsoshin ku cigaba da biyomu *MHS*, zamu fere muku biri har wutsiya In Sha Allaah.

*REAL MHS*



Munay, Hanee and Stylish






Skip to content
haneefahusman
SEPTEMBER 24, 2016
ABUN SIRRI NE 46-50
​*ABUN SIRRI NE*
Na ‘yan uku
*MUNAYSHAT*
*HANEEFAH USMAN*
*STYLISH BCH*
*NWA*

*46-50*
Ga masu so sai su duba: Haneefah.mywapblog.com
☆☆☆☆☆☆☆☆
Mummy cikin kakkausar murya tasoma magana “Abdul meh kake nufi?, aure?, baka yarda dani bane ko kuma meh kake zargi?” Sai kuma ta sassauta murya tacigaba “Aure Abdul?, kasan meh ya hanani aure tun bayan rabuwana da babanka?, toh yau zan gayama, na’ki aurene saboda banaso na rasa baka lokaci nah, na’ki nayi aurene don kar nayi yazamana mijina watarana ya bigeki ko wani abu don ni bazan d’auki a dukeka nayi shiru ba, na’ki aurene sabida kar naje da kai wani gida akiraka da sunan agola, sunan da bazan juri jin an kiraka dashi ba ko da wasa, Abdul na’ki aurene saboda kai, for your own happiness, nayi sacrificing jindad’i nah saboda na baka kulawa ta musamman nakuma baka dukkan lokaci nah, saboda wani dalili yanzu zaka tasomin da batun aure Abdul?, mesa?”
Hawaye ne ya zubo ma Abdulyassar a fuska, mi’kewa yayi dafe da ‘kuncinshi ya isa gabanta ya dur’kusa yace “Ki yafemin Mummy, ki gafarceni, nayi suggesting hakan ne don inaga shine zai ‘kara kare martabarki”
Kallonshi tayi tace “No Abdul, saboda ka girma ne kake gayamin magana, saboda yanzu kana ganin ka kai shekarun da zaka iya rayuwa batare dani ba, saboda….”
Mi’kewa yayi yasa hannunshi ya toshe bakinta yana girgiza mata kai “Mummy I’m sorry, don Allah kiyi shiru kibar wad’annan maganganun, in batun aure ne namiki al’kawari daga yau bazan sake d’agota ba”
Daga nan ya juya ya fice daga parlourn ba tare da ya sake waigowa ya kalleta ba duk da irin kiran sunanshi da takeyi akan ya tsaya. Yana fita ta tsugunna bisa guiwowinta tana kuka kaman meh, nadama ne ya dirar mata, sai sannan take jin haushin kanta akan meh ya kaita marin d’anta ‘kwara d’aya tal, wanda takeso fiye da kanta, tama kasa yarda wai yau itace ta d’aga hannunta ta saukar da yatsunta biyar a fuskar d’an nata wanda bashida laifin komai. Laifinshi d’aya ne da ya kawo mata maganar aure bayan ita hakan bai cikin tsarin rayuwarta kwata-kwata.
Abdul tun fitarshi daga sashenta misalin ‘karfe sha d’aya bai sake ko kallon wajen ba. Shiru-shiru har bayan la’asar bataji d’uriyar shi ba don ko abincin rana baifito yaci ba, a birkice ta nufi sashen nashi don ta tuna kashedin da dr yamata akan karta barshi cikin damuwa ko ya ‘kan’kantarsa. Kusan cin karo sukayi don alokacin Abdul yafito da niyyar zuwa wajen amininshi ko zai bashi shawara sabida kanshi ya kunce, bai iya tunanin komai gashi yana neman mafita cikin gaggawa.
Sunkuyar da kai ‘kasa yayi ya ra’ba ta gefenta yayi wucewarsa, baki bud’e ta bishi da ido don sam bai nuna ma ya lura akwai wata halitta awajen ba, “Allah sarki Abdul, marinka da nayi ba da sona nayi hakan ba” take rayawa acikin ranta.
Bata farga ba taji ya bud’e motarshi, gudu tasa takuwa isa lokacin har ya kunna motar yana faman rufe ‘kofa, kama ‘kofar motar tayi, d’agowa Abdul yayi ya kalleta ya sunkuyar da kai yace “Mummy fita zanyi, sakemin ‘kofar please”
Bata sake ‘kofar ba tace “Abdul ka fito inaso muyi magana”
Batare da ya kalleta ba ya fara tapping na steering wheel yace “In na dawo mayi, please mum i have to go”
Rau-rau tayi da ido kaman mai shirin kuka tace “Shikenan tunda yanzu ko maganata ka bar ji, kaje sai ka dawo” tana ‘karasa maganar ta sake murfin motar ta juya da zummar komawa gida amma sai tafara tafiya ahankali, atunaninta zai tsaidata amma sai taga sa’banin haka, har ta isa d’aki ta rufe yana nan yanda tabarshi, bai rufe ‘kofar ba sannan bai kashe motar ba.
Fad’awa kan kujera tayi tana hawaye, ita tsoronta ma kar Abdul yayi accident sabida ta hango ‘bacin rai shimfid’e akan fuskarshi. Chan kaman minti goma taji an ta’bata, a firgice ta bud’e baki har zatayi ihu sai taga Abdul tsaye a kanta.
Ajiyar zuciya ta sauke tace “Yaushe ka shigo?” Don ita harga Allah bataji ‘karar bud’e ‘kofa ba, ko don ta lula duniyar tunani ne oho.
Bai bata amsa ba sai ma tsugunawa da yayi akan carpet, kanshi a ‘kasa yace “Mummy kiyi ha’kuri, banson kina zubda hawaye saboda ni, bazan ta’ba yafema kaina ba”
Share hawayen fuskarta tahau yi sannan ta d’ago shi yadawo kan kujerar da take zaune, cikin muryar da yasha kuka tafara magana “Ka yafemin marinka da nayi, wallahi bansan lokacin da zuciya ya kwasheni nayi hakan ba, im so sorry my son” ta ‘karashe maganar tana share hawayen da ya zubo bisa fuskarshi
Kama hannun nata yayi ya ‘kir’kiro murmushi yace “Ba komai mummy, bansan maganar zai ‘bata miki rai bane da ban yishi ba”
Girgiza mishi kai tayi tace “I totally understand you, zanyi nazari akan maganarka”
Cike da mamaki yake kallonta, bakinshi har yana rawa yace “Mu…mmy da…gask…e kike??”
Nodding mishi kai tayi tana murmushi, dad’i ne ya ziyarci zuciyarshi wanda bazai iya misaltawa ba, da haka suka sasanta har ma yaci abinci, fitar da baiyi ba kenan don bashi yabar sashen ba sai da aka fara kiran sallar maghrib.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Three months later
Saturday morning, 9:30am
Ilham da Suhal ne zaune a tsakar gida sai hira sukeyi, suna cikin haka sai wayarshi da yake hannun Ilham alokacin tanata d’aukansu selfies ya shiga ruri, mi’ka hannu yayi da niyyar kar’ba amma sai Ilham ta mi’ke tana dariya, dariyarta ne ya tsaya cak sabida sunan da idonta yayi arba dashi ‘baro-‘baro akan screen na wayar “BAE”, wani kallo ta watsa ma Suhal da saida ya d’an ja baya. Hannu yasa ya kar’bi wayan daga hannunta don das’karewa ma tayi awajen kaman an dasata sai wasu hawaye da ke zuba daga idanunta, yana kai dubanshi kan screen na wayar yaga sunan.
Wani murmushi ya sakar yayi picking yana cewa “Hello, yanzu kuwa nake shirin kiranki” ya juya ya nufi d’akinshi don yama manta da Ilham a wajen.
A d’ayan ‘bangaren Leena tace “Kai dai kawai kanason kare kanka ne don tun safe baka kirani ba sai kaga na kiraka”
Murmushi yayi da saida Leena ta jiyo sautin shi yace “Allah kuwa kina raina, kawai ina d’an abu agida ne”
“Tohh shikenan, ya yau d’in?”
“Kalau fah, kin tashi lafiya?”
“Lafiya lau, umm dama zan tambayeka ne”
Daidai lokacin ya isa d’akinshi, kishingid’a yayi akan kujera sannan yace “Inajinki”
“Inaso ka rakani wani waje ne don Allah, wallahi ‘kiuyan driving nakeji”
Dariya yayi sannan yace “So…. ni nazama driver’nki right?”
Da sauri tace “A’a, ni na isa?”
Dariya sukasa dukkansu sannan yace “Kin isa mana har kin wuce ma”
“Thank you, yaushe zakazo d’in?”
“Ke zan tambaya ai your highness, just say the time nikuma zanyi iya ‘ko’karina na iso on time”
Dariya kad’an tayi tace “Kai kacika zolaya wallahi, around 4:30 haka if you are free”
“Free?, ai ko yau nan i’m the most busy man dole nayi squeezing time nazo”
D’an murmushi ta saki don har cikin ranta taji dad’i sannan tace “I’m honoured, sai anjuman kenan ba?”
Cikin sauri ya katseta da cewa “Ina ne zamuje d’in?”
Dariya ta kwashe dashi tace “Sayarda kai zanyi”
Shima dariyar yayi saiyace “No, gayamin kar nasa kayan da bai dace ba”
“Bank zamuje sannan zanje na siya wasu abubuwa a mall”
“Okay shikenan, bye”
“Bye, in zakabar gida sai ka kirani”
“Okay I will”
Da haka sukayi sallama kowannensu murmushi ne shimfid’e akan fuskarsa. Kukan da yaji da ‘karfi yasa shi kai dubanshi bakin ‘kofa, Ilham yagani, sai sannan yatuna da suna zaune ne Leena ta kirashi shikuma yamanta da akwai ma wata mai suna Ilham a duniyar nan.
Tashi yayi ya nufeta, saka hannu abakinta tayi tanata faman toshe bakinta don kukan da yake neman fin ‘karfinta, ganin ya nufota yasa ta ruga da gudu ta banko ‘kofar.

☆☆☆☆☆☆☆☆
Sofy kwance a jikin Bash a wani club nasu, wine kawai suketa d’irkawa cikinsu hankali kwance, hannu ya d’aga ma waiter da ke wajen akan ya ‘karo musu, cikin ‘kan’kanin lokaci ya kawo musu wani kwalba ya dire musu sannan ya ‘balle murfin yabar wajen. Sofy dai duniya ta mata dad’i, sai jijjiga kai takeyi kaman kad’angare, ahaka cikin sau’ki Bash ya faki idonta ya jefa wani tablet da ya ‘ballo daga wani sachet acikin aljihunshi, da sauri ya d’aga kwalbar wine d’in ya zuba acikin cup da tablet d’in yake. Ta’bata yayi tajuyo ya mi’ka mata cup d’in da tablet d’in yake ciki yace “Cheers”
Yamutse fuska tayi tace “No, I’m full, ya isheni, in nasha wani cup zan iya amai”
Ranshi ya ‘baci amma haka ya danne yace “Just one more, daga wannan shikenan”
Kar’ba tayi suka kara cups d’in sannan suka kafa kai suka shanye tas, kusan lokaci d’aya suka dire cups d’in akan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login