Showing 1 words to 3000 words out of 62823 words

Chapter 1 - UKUBAR KISHIYATA Sirrin Da Ya Rushe Aure by Ummee Yusuf

29 Jul 2026

26

๏ปฟCompiled By Umar Dalha Funtua.


Copied By Ummee Yusuf.






[3/24, 6:46 AM] Ummee Yusuf: ๐Ÿ™†โ€โ™€๐Ÿ™†โ€โ™€๐Ÿ™†โ€โ™€๐Ÿ™†โ€โ™€๐Ÿ™†โ€โ™€๐Ÿ™†โ€โ™€

*~UKUBAR KISHIYATA~*

๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ


( its all about love and betrayal)


Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)

๐Ÿ’ซ*~FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION~*๐Ÿ’ซ

*Gidan zaman lafiya, aminci hadin kai da yardar juna insha Allah๐Ÿค*

Assalamu alaikum masoyana,gani yauma nazo muku da wani sabon novel dina mai dauke da soyayya,yaudara da cin amana.da fatan zai ilimantar kuma ya nishadantar daku.sannan ina fatan zaku cigaba da biyayan novel har zuwa karshe sannan ina fatan zai samu k'arbuwa daga gare ku kaman yadda kuka k'arbi *~FARHAT~*.

*~ADDU'AR DA ZAKUYI A LOKACIN DA KUKA TASHI DAGA BARCI~*


ุงูŽู„ู’ุญูŽู…ู’ุฏู ู„ูู„ู‘ูŽู‡ู ุงู„ู‘ูŽุฐูŠ ุฃูŽุญู’ูŠูŽุงู†ูŽุง ุจูŽุนู’ุฏูŽ ู…ูŽุง ุฃูŽู…ูŽุงุชูŽู†ูŽุง ูˆูŽุฅูู„ูŽูŠู’ู‡ู ุงู„ู†ู‘ูุดููˆุฑู


*~Alhamdu lillaahil-lathee 'ahyaanaa ba'da maa 'amaatanaa wa'ilayhin-nushoor.~*

*~Praise is to Allah Who gives us life after He has caused us to die and to Him is the return~.*


*~Part one~*

Babban shopping mall ne mai girman gaske,wanda yake cike da kayan zamani kama ga kayan masarufi zuwa sutura,kayan kwalama da kayan tand'e-tand'e.

Duk wanda ka gani a wajan toh tabbas babban mai kud'ine ko kuma mai fad'a a ji a kasar ko kuma d'an siyasa dan haka kana zuwa bakin mall d'in sai ka saki baki wajan kallon masu zuwa shopping d'in, saboda ka zaci ko gasan nuna motoci ake ko gasan na sutura da k'walliya ake.

A'ameen da matarsa Latifa suna cikin masu shopping a wannan mall d'in,suna zagawa a hankali tare da zab'an abinda suke so fuskokinsu d'auke da murmushi kana ganinsu kasan hutu da naira sun gama ratsa jinkinsu.

Latifa sai jido kaya take hankali kwance Al'ameen na biye da ita, bayansu kuma ma'aikacin wajan ne yana tura d'an keken zuba kaya,duk abinda ta zab'a ta d'auka cikin keken take jefawa har suka gama sayayyan suka zo wajan da za'ayi musu bill.

Makud'an kud'in da zasu biya aka fad'a musu wanda ya ishi wani talakan yayi jari bayan na'uran ta gama lissafin kayan.ba tare da wani fargaba ko b'ata lokaci ba yaciro bounchs d'in 1k guda 2 ya ajiye suka fice zuwa parking lot abinsu ba tare da jiran canji ko kayan da suka saya ba.

Suna zuwa wajan motansu Al'ameen shiya bud'ewa Latifa gaban mota ta shiga ta zauna ya maida k'ofan ya rufe sannan shima ya zagaya driver seat ya bud'e ya shiga ya zauna,sai ga yaran mall d'in su 2 ko wanne da kaya niki-niki a hannu sun biyo su.boot Al'ameen ya bud'e musu suka zuba musu kayan suka rufe,sannan yaja motan suka fito a compound d'in mall din suka mik'e zuwa gidansu dake unguwar dosa.

Suna tafe suna hiransu cikin jin dad'i da annashuwa, suna wuce manyan gidaje masu k'yau har suka kawo bakin wani tangamemen gida mai kyau wanda duk layin ba gidan da ya kaishi k'yau da tsaruwa.

Tun kamin yayi horn mallam isa mai gadi ya bud'e musu k'aton gate d'in ya kutsa kai ciki.

Parking lot ya nufa wanda yake cike da cars birjik kala-kala kaman ta sayarwa,waje ya samu ya parker motan sannan suka fito zuwa cikin gida.

Masu aikin gidan sai tururuwan fitowa yi musu barka da zuwa suke,wasu kuma suna kwashe kayan da suka sayo na cikin boot suna shiga da shi cikin gida.

Cikin takun katsaita da da natsuwa suka shigo cikin waiting palour inda suka tarar da d'ika-d'ikan 'yan mata su 2 suna zaune suna charting a wayarsu.

D'agowa sukayi suna musu sannu da zuwa,kai tsaye Al'ameen ya wuce main palour,ita kuma Latifa ta nemi waje ta zauna cikinsu tana "wash Allah na gaji".

Har ya kai hanyar da zata sada shi da main palour ya tsaya ba tare da ya juyo ba yace" Latifa zo ki had'a min ruwan wanka" bai jira amsanta ba ya wuce ciki zuwa main palour wanda yafi wancan girma da tsaruwa komai na palourn maroon nd black ne hakan ya k'ara fito da k'yan palourn.

Hanyan part d'in shi yayi,yana taka stairs d'in a hankali har ya shigo palourn shi da yaji komai purple nd white ,an tsara shi sosai dan yafi main palourn kaya masu k'yau da tsada.

Bedroom ya wuce ya fara rage kayan jikinshi,hulan kanshi ya cire ya ajiye a kan side drower yayi dai-dai da shigowa Latifa,wuce shi tayi zuwa bathroom ta had'a mishi ruwan wankan.

Koda ta fito ta same shi ya gama cire kayan shi daga shi sai boxer da vest,tana murmushi tace "an gama ur Highness every thing is set"

Murmushi ya maida mata sannan ya wuce zuwa bathroom d'in.

Down stairs ta sauk'o har zuwa waiting palour,Fa'iza da shamsiya suna zaune suna chating kaman yanda ta barsu.zama tayi cikin su tace...
" ku dai kam ba kuda wani aiki sai ta latse-latsen waya,kuma me kuke jira tundazu a waiting palour?"

Fa'iza tace" uhum Aunty kenan chating fa muke kuma muna jiran wata friend d'in mu data ce zata zo".


"Hmmmm chatin ko,ba karatu ?yayi muku kyau".


Fa'iza tace"yauwa Aunty shekaran jiya dana je gida mama tace in fad'a miki tana buk'atan wasu kud'ad'e".

Harara Latifa ta balla mata sannan tace "shine sai yau kike fad'a min?"

"Wallahi Aunty mantawa nayi"tace tana maida hankalinta kan wayarta.

"Laifina mama zata gani taga kaman na share tane,haba aiko wannan jaraban charting d'in da kuka d'aura akan ku ba zai barku ku tuna da kanku ba bare wani abin".

Shamsiya tana jinsu bata ce komai ba.

Latifa mik'ewa tayi hanya part d'inta tana ta mita.

Wanka ta farayi sannan ta had'e cikin arnen less maroon d'inkin riga da skirt ya zauna das a jikinta.

Make up tayi mai rai da lafiya kaman mai zuwa gidan biki,perfumes masu d'an karan kamshi tayi amfani dasu wajan feshe jiki ta sannan ta tashi a gaban mirrow ta dawo kan gado ta zauna.

Hannu ta mik'a ta d'auko wayanta da ta ajiye akan pillow,no mamanta ta dannawa kira,yana fara ringing,sai da ya kusa katsewa sannan ta d'auka.

Sallama tayi ta amsa bayan sun gaisa Latifa tace" mama dan Allah kiyi hak'uri,wallahi ban samu sak'onki ba a wajan shamsiya sai yanzu take fad'a min kuma ashe tun wai shekaran jiya kika fad'a mata".


"Haba Latifa yarinya 'yar kwalisa tauraruwan 'yan mata ba sai kin bani hak'uri ba,nasan baki samu sak'ona ba akan lokaci saboda nasan ba kya wasa da al'amarina".mama tace a d'ayan b'angaren.

'Yar dariya tayi mai cike da jin dad'in irin yabo da kirarin da uwarta take mata tun kafin tayi aure,tace "toh mama gobe insha Allah Shamsiya ko Fa'za zata kawo miki saboda yanzu dare ya farayi".

Cikin farin ciki tace " yauwa Latifata godiya nake".

"Uhum mama ina baba?"Latifa ta tambaya.

Tabe baki Mama tayi kamin ta amsa " wannan solofiyon uban naku yana can me mataccen zuciya me ya iya banda zaman banza".

"Toh Mama sai da safen ko "?"Latifa ta katse Mama duk da tunda suka taso haka taga tsakanin Mama da Babansu amma sam baya mata dad'i.

" Toh Allah ya kaimu 'yar kwalisa".

Ajiye wayan tayi ta kwanta rigingine a hankali kan gadonta tana tariyo rayuwarta ta baya da yanda burinta ya cika na samun miji mai kud'i dan ta zama tauraruwa a cikin familynsu,nd ra'ayinsu da tsarinsu yazo d'aya dana uwarta nason kud'i.yanzu haka ita ta d'auki nauyin wasu daga cikin 'yan uwanta,shiyasa ta d'auko shamsiya da Fa'iza kannenta su samu karatu mai k'yau da inganci kuma suyi kasuwa.

Hope u will like it.
โœโœโœโœโœโœโœโœโœโœโœโœ
[3/24, 6:46 AM] Ummee Yusuf: . ๐Ÿ™†โ€โ™€๐Ÿ™†โ€โ™€๐Ÿ™†โ€โ™€๐Ÿ™†โ€โ™€๐Ÿ™†โ€โ™€๐Ÿ™†โ€โ™€

*~UKUBAR KISHIYATA~*

๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ


( its all about love and betrayal)


Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)

๐Ÿ’ซ *FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION*๐Ÿ’ซ


( *Gidan zaman lafiya hadin kai, aminci da yardar juna insha Allah*)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~Gaskiya naji dad'in yanda kuka nuna min kauna da goyon baya ta hanyan comments,ina yinku sosai sosai.dan haka nima zan cigaba da antayo muku ba kakkautawa~*

*~ADDU'AN DA MUTUM ZAIYI A LOKACIN DA ZAI SAKA KAYA~*


ุงู„ู’ุญูŽู…ู’ุฏู ู„ูู„ู‘ู‡ู ุงู„ู‘ูŽุฐููŠ ูƒูŽุณูŽุงู†ููŠ ู‡ูŽุฐูŽุง (ุงู„ุซู‘ูŽูˆู’ุจูŽ) ูˆูŽุฑูŽุฒูŽู‚ูŽู†ููŠู‡ู ู…ูู†ู’ ุบูŽู€ูŠู€ู’ุฑู ุญูŽูˆู’ู„ู ู…ูู†ู‘ููŠ ูˆูŽู„ูŽุง ู‚ูู€ูˆู‘ูŽุฉู

*~ALHAMDU LILLAHI LATHEE KASAANEE HAATHAA (ATHTHAWBA)Wa RAZAQQNEE MIN GYAYRI HAWLIM WA LAA QUWATIN~*

Praise is to Allah Who has clothed me with this (garment) and provided it for me, though I was powerless myself and incapable.


*~part two~*


Mallam Garba mai kayan miya da matarsa Hindatu cikakkun 'yan garin zaria ne.Allah ya albarkaci auransu da.'ya'ya 3 duka mata.

Latifa itace 'yata farko,akwai d'an tazara tsakaninta da mai bi mata wato shamaiya ta bata kusan shekaru 10.

Shekara d'aya da rabi kawai shamsiya ta bawa Fa'iza data kasance autarsu dan daga kanta haihuwar ta tsaya musu.

Mallam Garba irin mutanan ne da abin duniya bata dame su ba,hasilama shi ba mai magana bane.tsabanin matarshi Hindatu da takasance mayyar kud'i gata da zunzurutun kwad'ayi,baya ga haka masiffafiyace ta bugawa a jarida.

Dalilin haka ta raina mijinta take abinda taga dama,shi kuma ganin tafi karfinsa yafita harkanta tare da zuba mata na mujiya.

Halinta sak na son kud'i 'ya'yanta suka taso dashi more especially Latifa da tasu tazo d'aya da ita.

Duk abinda zasuyi indai zasu kawo mata kud'i toh fa batada matsala.dan haka Latifa tun tana s.s1 ta fara bin maza a lokacin ba ta fi 15years ba.

Maza ba irin wanda bata huld'a dasu amma babban saurayinta wanda suke son juna da gaske shine Salees.

A haka har ta kare secondry school,da cuku-cukun salees ya samo mata gurbin karatu a A.B.U zaria.

Da burin a ranta ta shiga sch d'in,babban burinta shine Allah ya had'a ta da saurayi d'an masu kud'i dan dama karatun bai dameta ba.

Ta shiga A.B.U da sa'a cox a lokacin an kawo musu sabbin malamai 'yan service.

Al'ameen mudassir yana d'aya daga cikinsu, ya kasance crsh d'in kowace yarinya mai ji da kamta a cikin sch d'in.shi yake d'aukansu languagelanguage.

Latifa tana d'aura ido akanshi taji duk duniya ba wanda take so bayan shi,bare ma da taji yanda ake zuzuta cewa mahaifin shi Alhaji Mudassir babban d'an kasuwa ne anan cikin gida da k'asashen waje.duk k'asashen da turai dana larabawa wa'yan da suka cigaba a duniya ,yana da companies da shares ba adadi akowane k'asa dan haka fad'an yawan kud'in shi dogon zance ne.

Duk haukan da 'yan matan keyi akansa ko kallo basu ishe shiba,saboda classy guyne shi


Alhaji mudassir inuwa haifaffen garin katsina state a batsari local govement.

Alhaji Mudassir ya gaji filaye da gonaki da sauran kadarori masu tarin yawa daga mahifinshi Alhaji Inuwa wanda ya rasu tun yana d'an shekara 17.

Bayan ya had'a degreensa na farko ya fara juya dukiyan shi,kuma cikin sa'a ya fara dan Allah ya sanyawa kasuwancin nashi albarka dan komai ya tab'a sai ya zama kud'i.

Auren zumunci akayi musu shida matar shi Halima wacce ta kasance 'yar baffan shi.bayan auren ne ya dawo kaduna da zama.

Allah ya albarkace su da yara 6 duka maza,Hafiz,Fawad,sudais,sa'ad,yusuf sai auta al'ameen.dukansu yayunsa 5 d'inan sunyi aure suna zaune suma nan cikin kadunan sai shi kad'ai ake sa ran ganin nashi in ya gama service d'inshi.

Alhaji mudassir ya d'aura 'ya'yan shi kan harkan kasuwancin sa,Sa'ad shine kad'ai yake son yin aiki.doctor ya karanta ,ganin yafi son aikin shi akan kasuwanci yasa Alhaji ya gina mishi asibiti anan cikin kaduna yake aikin shi.


Abinda Latifa ta lura dashi shine,Al'ameen yafi son mace mai kamun kai da shigan mutunci.saboda in yana musu lectures ta lura in akayi tambaya yafi daraja tambayan wacce ya ganta cikin shigan mutunci.

Nan itama Latifa ta dage da shigan mutunci musamman tasa akayi mata d'inkunan hijabai dogaye masu hannu har k'asa,duk dan ta ja hankalin shi,sannan duk wani hanyan da zai had'ata da al'ameen kuwa shi take bi.

Tayi sa'a dan sosai take burge shi wasa-wasa ta samu fada a wajan shi,har ya kai suna hira.kullum sai ta bi shi office ta fake da sunan karatu su sha hiransu.

Wani abinda ya d'aure mata kai game da al'ameen shine duk shak'uwar da sukayi bai tab'a furta mata kalman so ba,dan haka ta nemi shawaran k'awarta aina'u.


Labarin wani shahararren boka aina'u ta bata,dan haka ba b'ata lokaci suka isa gare shi dan neman taimako.

Cikin satin da ta fara amfani da k'walli da turare da boka ya bata Al'ammen ya furta mata kalaman so kuma yace da gaggawa yake son a d'aura musu aure.

Yanzu kullum shi yake kaita makaranta kuma ya dawo da ita gida da daddare kuma ya dawo suyi hira,takai ta kawo abincin dare ma agidansu yake ci wanda yasha surkullen boka.

Murna a wajan Hindatu da suke kira da mama ba magana ganin irin babban kamu da 'yarta tayi,saboda har sunyi hannun riga da talauci tun kamin ayi aure dan kullum Al'ameen yana cikin jik'asu da naira.

Wata 2kacal akasa na bikinsu murna wajan Latifa ba zai fad'u ba ganin burinta ya kusan cika.

Ana saura 1month bikinsu yace ta shirya ya kaita ta gaishe da mamyn shi da matan yayun shi.

Mamy kwata-kwata Latifa bata kwanta mata ba saboda kana ganinta zaka san idonta a bud'e yake.daurewa tayi ta.karb'eta hannu 2. ya zatayi tunda zabin d'an autan tane.

Brothers d'inshi ma basuyi farin ciki da zab'in shi ba sai dai ba wanda ya nuna mishi a fili tunda Mamy ma batayi magana ba.

Sa'ad shine kad'ai ya fad'a masa abinda sauran 'yan uwansu da mahaifiyarsu suka kasa fad'a mishi kuma a gaban Latifan ma ya fad'a saboda shi wani irin mutum ne mai wuyan sha'ani duk cikinsu ya fita daban,bai cika magana ba bare fara'a gashi da rashin shakka da tsoro in gasiyace ko ubanwa fad'awa yake.

Latifa hankalinta ya mugun tashi jin abinda Sa'ad d'in yace,taso yi masa rashin mutunci amma ganin yanayin shi kada'i yasa ta had'iye duk wani rashin mutuncinta.atake wani tsoronsa ya darsu a zuciyarta.

Ta d'an samu relief ganin Al'ameen bai kula da zancen d'an uwan nashi ba saima fushi da yayi suka bar gidan.

Ana saura 2weeks bikinsu yazo gidansu Latifa as usual suna hira yake ce mata baya son su sayi koda tsinke ne saboda ya gama tsara gidanshi ya zuba komai a ciki.

Cikin jin dad'i take kollon shi jin abinda yace tana yaba k'yau irn na Al'ameen gashi fari da dogon hanci sai dai bashi da manyan ido amma ya k'arawa fuskan shi k'yau gashi da pink lips,dogo ne shi mai faffad'an kirji.infact Al'ameen ya had'u over da ko wace mace zata so ta mallake shi.

Yayin da Latifa kuma ta kasance bat da wani k'yau saboda d'an hasken da take da shima na kanti ne,gata gajeruwa ga jiki.amma Al'ameen baya gani dan burin shi ya auri mace saliha dan samun zuri'a d'ayyiba kuma a ganin shi ya samu.


Kamin ya tafi 2millions ya damka mata wai na hidiman biki.

Kasa rutsawa sukayi ita da mama a wannan daren sai jujjuya kud'in suke cike da al'ajabi,ashe duk yanda suke jin labarin dukiyansu a gari ya wuce nan.

An daurauren su da Al'ameen an kashe kud'i anyi hidimomi da events na kece raini sai dai yawancin events d'in amaryace ta shirya su,wasu ango ya halarta wasu kuma bai je ba saboda shi baya son yawan hayaniya.

Danginta sai mamakin irin hidimomin suke saboda basu tab'a ganin biki makamancin sa ba,duk wanda yaga lefenta da kyar yake iya tashi wajan.ak'watuna set 2 aka had'a mata komai na ciki disiners ne masu tsada ga golds birjik kaman abin banza a ciki.

An gama hidiman biki lafiya ta tare a gidan mijinta wanda ya kasance kaman aljannan duniya dake unguwar dosa a cikin garin k.d

Babban burinsu ya cika ita da mahifiyarta na samun miji mai kud'i,tana abinda da taga dama da dukiyar mijinta ba mai taka mata biriki.

Matsala 1dake take fuskanta a gidan mijinta kuma yake gusar mata farin ciki a duk lokacin da ta tuna shine rashin haihuwa.

Shekararun su 7 da aure amma ko b'atan wata bata tab'a yi ba,gashi Al'ameen da hajiyarsa sun fara k'orafi akan rashin haihuwan nata.

Yasha ce su tafi asibiti ko kuma su fita outtside a duba lafiyarsu,amma sai tace mishi ai gaggawa aikin shid'an ne kuma komai na Allah yana da lokacinsa kila lokacin da Allah ya nufa su samu d'ane baiyi ba.nan zatayi ta kawo masa zancen Allah da annabi har sai taga ya hak'ura take k'yale shi.

Bakomai yasa take haka sai dankar asirinta ya tonu,sabida ita kanta bata sanadadin cikin da ta zubar ba,ko cikin saurayinta Salees sau hudu tana zubarwa banda sauran samarinta.ita kanta tasan zube-zuben cikin da tayi yayi muhimmiyar bada gudumuwa a wajan hanata samun ciki a gidan mijinta.


โœโœโœโœโœโœโœโœโœโœโœโœ
[3/24, 6:46 AM] Ummee Yusuf: . ๐Ÿ™†โ€โ™€๐Ÿ™†โ€โ™€๐Ÿ™†โ€โ™€๐Ÿ™†โ€โ™€๐Ÿ™†โ€โ™€๐Ÿ™†โ€โ™€

*~UKUBAR KISHIYATA~*

๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ


( its all about love and betrayal)


Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)

๐Ÿ’ซ*~FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION~*๐Ÿ’ซ

*Gidan zaman lafiya,aminci hadin kai da yardar juna insha Allah*๐Ÿค
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~ADDU'AR DA ZAKUYI A LOKACIN DA ZAKU SANYA SABBIN TUFAFI~*


ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู€ู…ู‘ูŽ ู„ูŽู€ูƒูŽ ุงู„ู’ุญูŽู€ู…ู’ู€ุฏู ุฃูŽู†ู’ู€ุชูŽ ูƒูŽุณูŽู€ูˆู’ุชูŽู†ููŠู‡ูุŒ ุฃูŽูŽุณู’ุฃูŽูŽู„ูู€ูƒูŽ ู…ูู†ู’ ุฎูŽู€ูŠู’ุฑูู‡ู ูˆูŽุฎูŽู€ูŠู’ุฑู ู…ูŽุง ุตูู†ูุนูŽ ู„ูŽู€ู‡ูุŒ ูˆูŽุฃูŽุนููˆุฐู ุจููƒูŽ ู…ูู†ู’ ุดูŽู€ุฑู‘ูู‡ู ูˆูŽุดูŽู€ุฑู‘ู ู…ูŽู€ุง ุตูู†ูุนูŽ ู„ูŽู€ู‡ู


*~Allaahumma lakal-hamdu 'Anta kasawtaneehi, 'as'aluka min khayrihi wa khayri maa suni'a lahu, wa 'a'oothu bika min sharrihi wa sharri ma suni'a lahu.~*


*~O Allah, praise is to You. You have clothed me. I ask You for its goodness and the goodness of what it has been made for, and I seek Your protection from the evil of it and the evil of what it has been made for.~*

*~part three~*


Ringin d'in da wayarta ya fara shi ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta lula.

Hannu tasa ta jawo wayan tana doka murmushi saboda ko bata kalli screen d'in wayan ba tasan mai kiranta domin ringing tone d'insa daban ne a wayarta.

Picking tayi tare da d'aura wayan a kunnenta tace " honey na ya akayine?"

" Sunan ya fita daga bakin ki coz u dont have d right to call me with dis name,yau kwana nawa ko tex d'inki ban gani ba bare call".taji ya amsa mata a d'an fusace.

Make murya tayi tace " oh! Salees darling am sorry ,wallahi zirga-zirgane suka min yawa".

" nasan ni kad'ai nake haukana tunda gashi kin kasa cika min alkawari da kika min".

Cikin tsigan lallashi tace " ina sane wallahi kayi hak'uri ka k'ara min kwana 2.in banyi maka ba wa zanyiwa honey?"


Ajiyan zuciya ya sauke irin na ya samu relief sannan yace " hmmm kin iya dad'in baki bayan kin san nayi missin d'inki sosai yauahe rabon da inji d'umin jikinki?"

Wani irin mik'a tayi akan gadon kana ta amsa da cewa " my Salees u knw i miss u 2,saboda kai na daban ne a rayuwata".

Cikin jin dad'i yace " toh ya anjima zamuyi video call ko zan d'an rage zafi?"

Tana murmushi tace " in dan wannane kasan baka da matsala all my time is urs.sai anjima".

Katse kiran tayi ba tare da ta jira amsan shi ba.

Tana shirin ajiye wayan kiran Al'ameen na shigowa,sai da ta d'an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login