Showing 3001 words to 6000 words out of 61932 words
Chapter 2 - DAN HAKIN DAKA RAINA Zuciyar Uwa BY UMMUH FATEEMAH
cewa tae da hapsatu maxa jeki aikenki karkuma inji bakinki kinjini ko toh Ummerh kar6a tae tawuce abunta ko kallonsu bataeba sunata habaecinsu Amman ko akanta dan ita dama bamaesan hayaniya bace arayuwarta
haka sukaeta duddube dubensu suna maganganu Amman ko cikanku Ummerh batace musuba har suka tattara suka tafi basu dade da tafiyaba hapsatu tadawo itada yara sundauko mata kaya akura guda uku makil suke
Shigatae tana sallama tacewa Ummerh gakayan nan munkawo shigo dasu xa'ai toh hapsatu kushigo dasu
Bawani daukar lokaci akaeba aka shigo da kayan suna tayata shiryasu saeda suka jerasu gaba daya sannan Ummerh tavasu dari bibbiyu kowa tace nagode sosae babu komae sukace kana suka futa
Yaukam sunsha aiki itada hapsatu dan saeda suka sassaka komae a muhallinsa sannan suka fara share share da wanke wanke bayan sun gama Ummerh tace maxa ki karasa kisiyo mana abunda xamuci da daddare dan dae baxan iya aikiba wlh dan nagaji
Toh Amman Ummerh kibari tunda lokaci bae wani kureba kawae saena daura tunda inna gama babu abunda xanyi sae wanka
Amman hapsatu kin gajifa dayawa Aa karki damu Ummerh xanyi Toh Allah yay mini albarka hapsatu
Amen Ummerh hakadae tagama aikin tadaura girkin sannan tae wanka tanata murna yau itama agado xata kwana kamar yadda mutane suke fada sun kwana agado kuma kayantama suna yar lokar da Ummerh tasiya mata lokar tata take ta kallo tana murna sosae abunta shiryawa tae cikin wata blue atamfa tasaka sabon hijabin da baffa yasiyamata futowa tae taga Ummerh tana vacci murmushi tae tace Allah sarki Ummerh kingaji sosae yau
Xama tae kusada ita saetaga kuma tafarka tace Ummerh abbana shiru shiru vaedawoba haryanxu
Aa yace inyaje kasuwa xae tsaya yashiga burni wajen su kakah hajja daganan kuma xae koma yaviyo motar kasuwa sae karfe 5:00 kuma kinga suke tashi
Toh Allah yakawosa lpy amen tana xaune aka kawo wuta tace Ummerh kinga sun kawo wuta dama munkae kayan kallonnan gyara ey wlh Kuwa Amman bari Alhaji yadawo sae gobe akira mae gyara yagyara
Sallamar da akece tasa hapsatu tashi dasauri Ummerh yunkurawa tae ahankali dan dakar take iya tashi saboda tagaji gashi kuma cikin nata yau yamata jingim sosae
Sannu da xuwa Alhaji kallonsu yake yana kuma karewa gidan kallo harda su aunty wutar nefa kuma aka saka musu toh wanan aikin rabi'atune ma yasani murmushi yay yajuya yadauko dayan buhun yashigo da sauran kayan sannan hapsatu ta tayasa kwaso su suka kawo tsakar gida
Sannu Alhaji yawwa ummerhn hapsatu yagidan yakuma kuke lpy alhmdllh wlh alhaji tavarma da dadduma hapsatu ta shinfida masa sannan ta ajiye masa ruwan alwala da ruwan sha abuncinsa yashiga daki yadauko masa tace sannu da xuwa abbah yawwa sannu hapsatu da kokari kallon gidan yake anutse sannan yacewa ummerh wannan kuma daga ina haka gyaran gidan nan
Hmmm alhaji kahuta mana saena fada maka hapsatu kawo masa cokali yaci abuncinsa
Murmushi yay bece mata komae ba dauko masa tae ya amsa ya ajiye saeda yay wanka yay sallah sannan yaci abuncin lokacin ma hapsatu tayi vacci ita Ummerh ce tabashi lavarin duk yadda akae sannan tace gobe inasan in tura hapsatu kasuwa tasissiyomin Yan kayayyakin daxan rinka siyarwa naso nasiyawa hapsatu keken dinki to abunne sae ahankali amman insha Allah indae nasamu yadda nakeso gakayan nan daxan siyar toko xan bayar asiyo mata acikin gari
Wasu kaya kenan wadan da xana siyarwa sbd kaga yanda rayuwa take yanxu sae addu'a tomexakina siyarwa Yan kayan miya busassu
Toh hakane kam Allah yasa mugana lpy amen dae
Haka sukaeta hirarsu daga karshe sukayi alwala sannan suka koma daki suka kwanata
Koda gari yawaye tum farar safiya abban hapsatu yagyara shagon waje anan yajera kayan siyarwarsa dama Ummerh tasa angyara masa har fenti anyi hapsatu ma da wuri ta tafi kasuwa dan Ummerh tace batasan tae dare
Wajen karfe biyu Ummerh tagama girkinta tagyara ko ina da ina tana xaune atsakar gida abbana hapsatu yashigo dauke da sallama abakinsa amsawa tae yace yawwa kisa hijav game gyaran TV dinnan yaxo xae duba
Toh tashi tae tasa hijava mae gyaran TV yashigo aka dauko masa TV yaduba yace kawae vurarda taene shiyasa yanxu xae tafi da ita aduba sosae sae'aturo adauka da yamman
Toh nawane Abba yace Aa karka damu vaxae ya garava ai dan dae gyaran TV baba xan gyara maka kawae dae aturo ko almajirine xan hadasa dawanda xae kawo toh shikenan ngd
Tafiya Abba yay yarakashi har kusa da adaedaeta sahunsa sannan yatafi
Dawowa yay yaxauna ashagonsa
Adai daitace ta tsaya hapsatu ce tafuto aka sassauke mata kayanta niki niki tavasa kudinsa sannan tashiga da wasu kayan abban tane yashigar mata da wasu kayan shima murmushi tae tace sannu abbah yawwa yar alvarka sannunki da kokari
Kallon Ummerh yay yace vari inje in kar6o TV nan dan naga kiransa yanxun Ummerh tace toh adawo lpy Alhaji Allah yakiyaye
Amen yace sannan yafuta dudduba kayan sukae suna hirarsu sunata dariya abunsu gwanin ban sha'awa hapsatu ce tace Ummerh mufara daurawa mana dan naga yanxuma karfe 1:00 tayi toh hapsatu amman dae kije kifarayin wanka maxa jeki dauki wancan ruwan cumin kiyi wanka
Toh Ummerh boket tadauka tajuye ruwan tasirka sannan tashiga daki danta cire kayanta
Karar motoci suka ji yana tashi akofar gidan hayaniya tayi yawa jisukae andaki......
[04/02, 7:56 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: 🍃✨🍃✨🍃✨
✨🍃DASHEN 🍃ALLAH🍃✨
WRITTER'S✍🏻 ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
🍃ALKALAMI ✍🏻YAFI TAKOBI🗡️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN🍃 DAKA RAENAH😏🤔✨
Page 9⃣&🔟
Jisukae An daki kofar gidan ana shewa karshen wata yaxo yau dan adaura hhhhh koda kika hanasa xuwa to kisani wakilansa sunxo andaura kuma sure yadauru
Itako Ummerh tunani tashiga dama yaune daurin amman meyasa Alhaji baegaya matava murmushi tae tace sannunku da xuwa maraba lale lale
Aiko aymana sannu kokar ayi saedae mun shigo daura kiris wata asirinta yatonu hhhhh hahayeeeeee Allah yakawomu yau dae karya ta kare tusa takurewa bodari wlh
Shiru Ummerh tae dan takasa gane inda kan xancensu yadosa va dan havaecin ma jitae basu iyaba komawa tae ta fara hada kayanta takoma dayar rumfar tacigaba da kullinta hapsatu wankanta tashiga koda tafuto shiryawa tae tafara taya Ummerh aikin har suka gama basu tanka musu ba dan Ummerh tace koda wasa kartace musu komae
Takaecine ya ishesu daya daga cikinsu tace wannan matar sae anyi da gaske fa akanta wlh kinga tamaedamu wasu yan iska tayi mana vanxa
Fauxiyace tace wlh kinsan babu abunda natsana irin ina magana amun vanxa abun nacimun rae wlh amman xamuyi maganin yan iska wlh
Ummerh tace waenikam kinci wani abuma kam?
Ey Ummerh naci abunci kafun nashiga wanka ok toh
Sallamar Alhaji mudance tasasu dago kae dakin Ummerh yashiga da TV hannunsa yace Ummerh hapsatu shigo kigani angyara wlh
Yunkurawa tae tashigataga angyara din stare suka shiga phalon itada hapsatu lokacin ma harya jonata hadawa yake yadauki remote din yadanna DADIN KOWA SABON SALO AKEYI A AREWA murmushi hapsatu takeyi sosae dan ganin yadda farin cikinsu yakeson dawowa
Haka sukaeta kallonsu ahankali kwance yan jerekam sakin baki sukae ganin suna gaeda Alhaji mudan Amman yay yakamar baesan da ruwan halittarsubama yashige daki yana kwala musu Kira
Lalle Balaraba saekin dage sosae dan wannan tarigada tashanyeshi
wlh kam wata ta amshe daga cikin su
Haka suka gama aikinsu suka tafi ko alamar xasu futo basu ganiba
Balaraba kam tacika tayi pamm
Nikam cewa nae dama ana xuwa jere da amaryah jama'a🤔🤔
Koda dare yay dakar Ummerh tasa abbah yaturamusu da Adaedaeta guda 5danshi cewayay ma sutaho da kafarsu kosunemi abun kawota
Haka aka kawo amarya lokacin ma Ummerh da hapsatu aphalo suke sun kulle ko ina sunrufe komae sun dawo phalon dan ananma suka saka katifa da net suna kallonsu
Abbah ne yashigo rike da leda guda biyu ahannunsa yakira daya daga cikin yaran Balaraba yace sukae mata yashiga phalon yaxauna plate din hannunsa ya ajiye guda biyu yaxubawa Ummerh nata kaxace da yohghout yaxubawa hapsatu ma yacewa hapsatu dauki naji kibawa Ummerh ki nata dauka tae tamika mata itama tadauki nata
Alhaji kam abun sakutar hakori yasa yana gogewa daga kishingide suna hirarsu atare sunaci har suka gama
Ummerh tace katashi katafi dakin amaryarkafa tana jiranka vanxa yay yacigaba da kallonsa Ummerh kam Takara maemaeta masa
Ina amaryar take vangantaba aikam suna cikin haka suka ji anbanko kofar da karfin tsiya mamakine yabayyaba akan fuskarsu gaba daya......
[04/02, 7:56 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: 🍃ALKALAMI ✍🏻YAFI TAKOBI🗡️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN🍃 DAKA RAENAH😏🤔✨
Page 1⃣1⃣&1⃣2⃣
Kallon kofar suke balarabace da fauxiyya da anas atsaye suna musu kallon tara saura kwata
Alhaji ne yatashi rae a6ace yahade fuska yace lpy menene haka vansan halin akuyoyi malama wuce daga nan
Aaaaaaaa🙄🙄🙄 vangane halin akuyoyi ba yaxa'ai ina amarya inaxaune gaho adaki kae kuma kana gurin wannan yar asarar mara tar......
Bae bari takarasa ba yadauketa da mari yace wlh kulll dinki ahirrrr dinki ina gaya miki daga rana mae kamar tayau karki kuskura ki kara mae maeta wannan tun yaushe natura fauxiyya takiraki kuxo in yi muku fada atare kuraba kwanan ku amman ko alamar futowa vakiyiba saeda nagaji dajira nakira anas yaxo yakar6i sakonki yakae miki wae menene ma tunanin ki xatonki kirinka juyani yadda kikeso kina ban doka da oder kamar yadda yan gidanku sukae suna wajen juya maxa a a a a sam baxae yuyuba ingaya miki dan haka hada kan "ya"yan ki maxa ku koma daki inba hakaba yanxunnan in baki red 🔴 card wlh
Balaraba kam tama rasa mexatace tarike kumatunta tasaki baki tana kallonsa dan mamaki ne dankare axuciyarta tanata tunanin yanxu haka xata cigaba da rayuwa acikin wannan gidan gaskiya dasake
Fauxiyya ce takama hannunta tace muje dan xuwa Lokacin Alhaji yarufe kofar yakoma cikin phalon Ummerh
Fauxiyya ce tace wae mamah bakiyi yadda boka nakan tsauni yace kiyi bane?
Nayi wlh fausuyya wlh duk yadda yafada haka nayi amman sam abun yaki cinsa wannan wane irin mijine haka?
Gobe da safe mukoma mamah toh shikenan Allah yakaemu goben da rae da lpy xanyi maganin su
Koda gari yawaye tun sassafe suka tafi gurin boka nakan tsauni anan sukae masa bayanin komae
Hhhhh hhhhh wlh wannan aikin yafi karfina dan kuwa wannan mutanen da kuke gani har dan da bata haefava anyi masa tsari fulanine wanda sukasan kan magunguna da tsari ko shima Baban ta abunda yasa akae nasara akansa sbd bayada tsari amman yana bawa "ya"yansa da kuma jikokinsa
Toh yanxu nakan tsauni yaya xanyi nikam wlh Alhaji sam bana gaban sa
Hhh toh yanxu dolene kibishi kiyi masa biyayyah sannan kuma kinuna masa kauna shida iyalinsa saekin shiga jikinsu sosae sannan saeki fara kokarin illatasu amman aikin akwae wahala indae akayi baeyiba toh xae dawo kanki ko kan "ya"yanki kinyarda
Aaaaaaa aaaaaaaa aaaaaaaa aaaaa nakan tsauni nayarda tokutashi kutafi maxa gurin suka rinka wucewa mugun doyine agurin kamar kayi amai ga wasu irin kwarangwal na mutane dana dabbobi agurin tsami doyi hamami duk yacika gurin amman sukam basaji haka suka dinga sakkowa daga tsaunikan suna futowa
Haka suka dawo gida da bakin ciki aransu sosae dan sun rasa ma yaya xasuyi tunda nakan tsauni yace vaxae iyaba to basusan yadda xasuyiba
Vadan Balaraba tasoba haka suka sakko suka fara xaman lpy dasu Ummerh tana kuma biyayyah ga Alhaji da Ummerh yadda yakamata dan kawae sucika burinsu
Akwana atashi babu wahala yau kam watan Balaraba 3 acikin gidan amman indae suka tambayi nakan dutse sae yace da saura
Da yamma suna xaune anata hira atsakar gida nefa aka kawo Ummerh tace alhmdllh ankawo wuta Allah yasa suvarta ta kwana tunda duk yau basu bamuba amen hapsatu da fauxiyya sukace
Kallo sukeyi daganan aka fara kiran magriba tashi sukae sukayi sallah sannan suka ci abunci har lokacin bacci yay suka kwanta
Koda gari yawaye yaune hapsatu suke gama exam dinsu ta karshe tun wuri tagama aikinta sannan tayi wanka tashirya makaranta ta tafi abunta itako Ummerh yau da ciwon mara ta tashi sosae takejin ciwon nadamunta daurewa kawae takeyi
Wajen karfe 5:00pm ummerh taji ciwo gaba yakeyi hapsatu tasa takira mata haviva likita
Basu dadeba suka shigo atare itako Balaraba tafahimta tun safe aikam da wuri tashirya itada fauxiyya suka tafi wajen nakan dutse dan yace inta tashi haehuwa suxo akwae maganin daxae basu wanda Ummerh xatae ta ciwo harta mutu toh daga nan xasu fara illatasu gaba daya dajinin haehuwar xasuyi amfani
Lokacin da haviva tashigo Ummerh ciwon yana damunta sosae tadubata taga ta kusa haehuwa tace Kiyi hkr Ummerh kin kusa haehuwa in sha Allah
Bayan sallar isha'i kukan jaririne yakarade gidan hapsatu wani farin cikine yakamata tanatajin dadi Ummerh ta ta haehu shiga tae dakin Balaraba danta gaya mata amman taga batanan futowa tae ta juye ruwan xafi a katon baho takae ban daki sannan ta ivi wani tasurka sannan tacewa likitar aunty garuwan xafin amsa tae tayiwa yaron wanka tashiryashi sannan tagyara dakin ta saka kayan dasuka 6ata arobar tace toh maxa kiwanke wannan kuma ki bunne ta tace toh
Ummerh kuma tafuto tashiga wanka tagyara jikinta sannan tasa kaya dakin yayi tsaf kamar ba'a ciki ta haehuba
Sallamar su Balaraba ce tasa hapsatu dagowa da murmushi afuskarta tace sannunku da xuwa amsawa sukae suna shigowa
Lokacin Hapsatu tana tsaka da yin...
Toh fah 'kara 'ka'ka 'ka'ka
Yaxata kaya
Transfer naera dari ko katin wya na MTN nadari duk wanda kae daya ne
TANAN
SADIYA ABDULLAHI UMAR
ACC- 0110015052
ECOBANK
KO KUMA KATIN MTN NA DARI TAWANNAN NUMBER 08032762588
Sainaji ku masoyana
[04/02, 7:56 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: 🍃✨🍃✨🍃✨
✨🍃DASHEN 🍃ALLAH🍃✨
WRITTER'S✍🏻 ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
🍃ALKALAMI ✍🏻YAFI TAKOBI🗡️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN🍃 DAKA RAENAH😏🤔✨
Page 1⃣3⃣&1⃣4⃣
Lokacin hapsatu tana tsaka dayin shanya dan tagama wankin gaba daya
Shiga Balaraba tae amman jikinta asake yake dan gava daya jitake kamar tayi hauka yau ranar datake ganin karshen Ummerh yaxo amman kuma ga'alama hakan vaxae yuyuba haka taeta yake amman vaekae xuciba
Bayan sallar isha'i abban hapsatu ne yashigo hannunsa dauke da ledoji sallamace dauke abakinsa
Akusan tare hapsatu da fauxiyya suka amsa masa suna kar6ar ledar dafadin sannu daxuwa Abba
Yawwa sannunku yagidan damae jegon
Suna lpy alhmdllh Abba hapsatu tafad'a shiga yay dakin da sallama suka amsa masa
Samun guri yay yaxauna Balaraba ce tashigo itama tana mae sannu da xuwa yayi dae dae da futowar Ummerh daga dakinta amsawa yay sannan balaraba ta mika masa yaron
Yana murmushi ya amshi yaron yana masa addu'oi sannan yay masa huduba da suna Abubakar
Ummerh ma murmushin take tana kallon su
Wajen karfe 10:00pm nadare balarabace taketa kae kawo adakinta tarasa mafita gashi dare yayi bare ta tafi gurin nakan tsauni gashi kuma sam batasan yadda xatae da maganin ba
Fauxiyyace ta tashi jin kae da kawon yayi yawa tace lpy Mamah naganki har yanxu bakiyi bacciba? 🤔🤔
Wlh fauxiyya vansan yadda xanyiba vansa maganin nan ba sannan kuma gashi narasa yadda xa'ai in koma gurin nakan tsauni
Mamah kawae mulalla6a mufita dan baxamu xaunaba wlh wannan mulkin mallakan ya isa haka sannan kuma kinga yanxu tahaefi namiji haka xamuyi taxama🙄🙄🙄🙄
Gaskiyar ki tashi mutafi haka suka lalla6a suka futa agidannan sukae cikin jeji gurin nakan tsauni dan yau so take saetaga bayan Ummerh
Sae Wajen 12:00pm sannan suka isa suka xayyane masa komae dayake faruwa
Hhhhhh tavvas gwara da kikaxo yanxu kidauki wannan kurciyar daranta kisata a turmi da wannan maganin ki kir6asu sannan kisoyasu kidiba kisaka mata itada mijinku da yarta a avunci suci inamae tavvatar miki indae sukaci wannan avuncin toh kin gama mallakarsu kenan sannan wannan kuma kidauka kihada da jinin vakar kaxa kibunne amakavarta toh yadda nacikin makavartar nan baxasu tashiba to haka itama in tafara ciwo saedae mutuwa kin gane gobe akeso kiyi wannan aikin ba'asan sanya acikinsa
Sannan aikinki vaxae kamava Sae nanda sati biyu
To nawane kudin aikin bana fada abani kawae😈😈😈
Dauko kuditae Wanda batasan adadin suba tabawa nakan tsauni sannan suka tashi suka futa
Vasuxo gida dawiriba dan haka suna xuwa vacci suka kwanta koda gari yawaye kam dukkan yadda nakan tsauni yasata tayi haka tayi babu ko kuskure
Takaewa Ummerh farfesun naman kaji Ummerh kuwa xuciya daya ta karba tana godiya koda dare yay naman sukaci itada hapsatu da Alhaji sunci sun koshi haka balaraba taeta aikinta cikin sirri dajin dadi sosae naganin tayi nasara
Akwan atashi vavu wahala agurin Allah yau yakama ranar suna yaro anrada masa suna Abubakar kamar yadda mahaefinsa yay masa huduba dashi
Ummerh kam tasha ado Sosae hapsatu ma haka sunyi shar dasu sallama akayi hapsatu ta amsa tana futa wani mutum tagani tace Ina kwana lpy qlu nan me gidan rabi'atu
Tace eh nan ne
Yawwa gawannan sakon kikae mata inji baffa shiyabani jiya akasuwa yace inkawo mata ayankawa yaro ranar suna
Xaro🙄🙄🙄🙄 👀👀👀👀ido hapsatu tae tace haydin boni ina xa'akae wadannan shanun sae kace yara goma ta haefa
Keee jeki kiramun ita maxa 😒😒
Haderae yayi babu alamar wasa
Toh vari inturoma ita shiga cikin gidan tae tana kwalawa Ummerh kira Ummerh... Ummerh... Ummerh kifuto Ana kiranki wanine yaxo yana waje
Ummerh ce ta futo daga daki tace lpyrk hapsatu kike wannan kiran haka
Hmmm 🤔 Ummerh kedae futo kawae kigani
Futowa Ummerh tae tabi bayan hapsatu suka je hargurin mutumun da sallama abakinta
Amsawa yay sannan yagaya mata sakon baffah yace ga sah da kuma shanuwa ayankawa dan da aka haefa
Toh ngd sosae Allah yasaka da alkaeri dubu 3taciro tabawa mutumin Amman sam yaki karba saema ledar daya mika mata yace ga nawa nima
Kallonsa Ummerh tae cikin mamaki tace aa wlh
Yace ni aminin baffane kuma yaronsa dama inata neman inda xan sakawa baffa da irin alkaeran dayakemun Amman bansamuba yau nasamu kuma yaxakicemun aa dan Allah ki amsa
Amsa Ummerh tae tana godeeyah sannan yajiya yatafi itama ta shiga cikin gida tana share kwallar data xubo mata
Saeda Alhaji yadawo sannan aka shigo da shanun aka dauresu acan bayan dakunan su
Alhaji yace baxa'a yanka suba avarwa yaro kayansa ayanka masa ragon daya siya da kuma wanda Ummerh ta bayar itama
Haka kuwa akayi Ummerh ansha suna anci ansha agurin sunan nan kowa yayi Kat Ummerh kam itada yaronta sunsha kayan varka da kudi sosae
Washe gari kuwa kuwa hapsatu da fauxiyya ne sukaeta suyan nama har kusan yamma sannan suka rarraba duk inda Ummerh tace
Haka akaeta xaman lpy kamar da gaske